Showing 27001 words to 30000 words out of 121625 words

Chapter 10 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

51

kitchen din sai gata tadawo da waya a hannunta tayi dialing line din Ahmad t

absaka a handsfree..daga wayan yayi tacan bangaren tareda sallama, Nafisa tace "Yaya nafito banganka ba nace ko wucewa kayi babu sallama" cikin nutsuwa yace "Eh Nafisa, sorry something came up ne" sai tace "Bakomai Yaya mungode Allah ya saka da alkhairy, s

ai munzo din muma" Yace "Okay ba damuwa" tareda kashe wayan.

Nafisa ta kalli Na'ima tana nazarinta batace komai ba, cikin sanyin murya Na'ima tace "Shine kika ce in fito kuma na fiton ke kika shige daki Nafisa" sai Nafee ta danyi dariya tana kai chips bak

inta tace "Abu fa naje nema a dakin kuma bansamu ba" jijjiga kai kawai Na'ima tayi ta juya ta fice da kitchen din Nafisa na bin bayanta da kallo, murmushi tayi sai kuma ta juya ta kalli kofin shayin data samu a gaba Na'iman alokacin shigowanta...

Bayan

Na'ima ta koma daki tayi changing into qananan kaya mara nauyi, fitowa tayi ta hau share gidan Nafisa ma ta fito suka hau tsaftace gidan tare suna hira, sai da suka ga ko Ina yayi tsaf yana kyalli sannan suka tafi yin wanka kuma, Bayan Na'ima tayi wanka ta

saka wani kayan ta dauki kayan Nafisa dake dakinta ta fita kai mata.

Yammacin ranan suna zaune anan falo itada Nafisa, cheese ball ne a hannunta tanaci amma absent-mindedly, ta qurawa carpet ido bama ta jin gulman da Nafisa dake gefenta take mata akan la

muransu na IG, tunani Na'ima ta fada sosai .... Tayi abu kuma ya dameta, duk wani iri takeji wunin ranar akan maganganun da ta fadawa Ahmad.

Wani fannin na zuciyar na encouraging dinta akan abunda tayi yayi daidai amma wani fannin kuma akasin hakan takeji

, bini bini zata dago hannun nata ta kalli tabon, Amma inta tuna cewa dalilin namiji wannan tabon ya zanu a tafin hannunta sai taji cewa gwara da ta kyari Ahmad din, ta dade da yiwa kanta alqawarin itada maza kuma haikata haikata sai kallo daga nesa, shiya

sa har yau duk mazan da suke binta anan Oxford bata taba sauraran ko daya ba kuma bata jin zata sauraran, Amma meye Ahmad yake yiwa zuciyarta aduk lokacin da suka hadu ne? Ta sake tambayan kanta a karo na ba adadi kuma babu amsa..

Jin shirun nata yayi yaw

a yasa Nafisa dago kai ta kalleta tace "Na'amaa" juyowa tayi adan birkice tadan ware ido tace "Uhh" sai Nafisa tace "Tun dazu inata miki magana, me yake damunki ne" ta girgiza kai tace "Babu komai fa" Nafisa ta sake cewa "Gashinan kinata tunani tun dazu, m

e ya faru dazu tsakaninki da Yaya Ahmad?" Na'ima tace "Ni babu komai" nazarinta Nafisan ta tsaya yi sai kuma ta juyo gaba daya tana facing dinta tana murmushi tace "Akwai abunda ya hadaku ne da muka koma gida sis...Ina jin kamshin wani abu a tsakaninku" sa

i Na'ima ta cusa cheese ball din hannunta a bakin Nafisan tana dan dariya tace "Wai kamshi..mezanyi dake ne Nafee? Yaushe ma na hadu dashi" Ta qarasa tana jijjaga kai, Nafisa ta fara tauna cheese din tana dariya itama tace "In tayi tsami zanji ne, da bakin

ki za kimin bayani yarinya" Na'ima ta girgiza kai tana murmushi sai ga kiran Mami yashigo wayanta....

Washegari ya kasance Monday akwai zuwa school amma Na'ima bata tashi ba sai wajen qarfe 10 kasancewar batada lecture ranan kawai submitting wani essay

dinta zata je yi, brush tayi harda wanka kafin ta fita zuwa kitchen dan tayi breakfast, Nafisa ta samu a kitchen din ta dafa musu noodles tana zaune jikin kitchen island din suna video call da Faruk, leqawa Na'ima tayi tana murmushi tace "Yaya Ina kwana" F

aruk yana murmushin shima yace "Habibtin Mami na kiraki ashe kina bacci" ta gyada kai cikin sanyin muryarta tace "Yau baka fita aiki ba ne Yaya" yana kallonta yace "Eh banje ba....a train kuka dawo ne jiyan? naji muryanki wani iri kamar sanyi ya kamaki" ka

fin ta amsa Nafisa tace "Yaya Ahmad ne fa ya kawo mu" Faruk yadanyi stiff sai kuma yace "Ma Sha Allah, cemasa kukayi yazo ya kaiku kenan?" cikin sanyin murya Na'ima tace "Nafisa ce ta fada masa Yaya" Faruk yadan kalli Nafisa data dan harari Na'iman, yana d

an hade giran sa yace "Ce miki akayi baida aikin yi ne" Nafisa tace "Nifa shi ya tambayeni yaushe zamu koma, kuma laifi ne dan ya kawomun Yaya" sai Faruk ya dan sake fuskansa yace "Yayi kyau hakan, ya taimakeku ma" da haka suka gama wayan, bayan sunyi brea

kfast din suka fice zuwa school din.

sai da suka biya park dinda suka bada ajiyan motan su lokacin da zasu koma gida, suka dauko ta sannan suka wuce makaranta..

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 17

Hankali suka maida sosai akan karatunsu

, basa wani samun lokacin kansu kuma yawanci a gida suke yin researches din nasu kasancewar sunzo wannan gandun, gidan Anty Amnah ma saida sukayi wata guda tukunna suka je shima waya ta kira ta rinqa mita sannan suka je, zuwa yanzu Na'ima ta dan cire tunan

in Ahmad daga ranta ganin babu inda tunanin zai kaita, tana jin time to time yana gaisawa da Nafisa tun tana expecting zai tambayi ya take har ta hakura ganin yayi keeping boundaries dinsan yasa itama ta dan ajiye batunsa a gefe dan harga Allah batason abu

nda zuciyanta keji a duk lokacin da idanunta sukayi tozali dashi, Nafisa ma bata sake zancen suje gidansa ba wanda daman Na'ima batada niyan zuwa koda Nafisa ta nemi hakan.

Watarana suna zaune a falo da daddare Na'ima na typing abu cikin laptop dinta, N

afisa dake kwance gefenta tace "Kin fara dissertation din ki kuwa?" sai Na'ima ta bar abunda takeyi ta juyo tace "Kin tuna course mate dita dinnan wanda nace miki sunanta Zara?" Nafisa ta gyada kai tace "Yar Lebanon dinnan, Na'ima ta cigaba "Ita..jiya ta t

ambayeni ko zan amince mu hada study group da ita akan dissertation din" sai Nafisa tace "Dama bakida writing buddy kedin?" Na'ima ta gyada kai tace "I thought zan iya ne, kuma naga yamin wahala sosai yanzu" Nafisa tadan jijjaga kai tace "Kinada matsala Na

'ima, ai dole sai kin samu group mates daman a irin situation haka, yanzu me kika cewa zaran" Na'ima ta amsa da "Na amince ai tun jiyan tace zamu rinqa ware lokacin shiga school din" sai Nafisa tace "Hakan yafi ai, namu fa study group din munkai takwas" Na

'ima ta juya ta cigaba da typing tace "Naku da maza ai naganku ranan" dariya Nafisa tayi tace "Ke kuma sune abun gudunki, sis many men don't bite" Na'ima batace komai ba ta cigaba da aikin gabanta..

Ranan wata talata bayan sun gama baccinsu da hidimomin

su Nafisa ta jasu suka tafi shopping abubuwansu da sukayi qasa, sai da sukayi sallahn la'asar sannan suka shirya suka tafi, kaya suka siyo dayawa na abinci dana qananun buqatunsu, bayan sun gama jera kayayyakin a kitchen suka fito Na'ima ta zauna nan kan k

ujera a falon ta fara ware kayan toiletries din nasu da na skin cares din, Nafisa ma ta zauna ta ciro wayanta tafara dannawa, shiganta cikin IG taga saqo a DM dinta dauke da sunan da ko cikin magagin bacci zata gane waye, dan gyara zama tayi daga zaunen ta

dan dago ta kalli Na'ima da hankalinta ke kan duba kayayyakin gabanta bata dago ba, miqewa Nafisa tayi asannu ta shige dakinta ta rufo qofan sannan ta sake kallon message din me dauke da rubutu kamar haka.

Bilal Dabo: Saqo na ke son ki isar wa kawarki,

tunda alamu sun nuna batasan ma'anan space dinda na bata ba and she's taking it too far, Tell her "it is not Over until i said so" ta dawo da kafarta , karta bari inzo daukanta dan lamarin bazai mana dadi ba, AUREn mu kuma na maidashi....

Saboda wasu d

alilai ne kawai yasa nafisa bata maida masa da amsan zagi ba, dan ko jahili yasan auren da ya mutu kusan wata goma baya, bazai maidu ba sama taka, sanin cewa ko weed dince ta motsa masa yasa Nafisa qin maida masa martani, atake kuma taji duk wani

kuzari n

a jikinta ya bace, bata san ma me zata fara tunani ba, a wannan lokacin kuma babu abunda take tunani irin kwanciyar hankalina Na'ima, she can't know about this and there's no way she's telling Mami saboda tsaf zata iya aiko Faruk yayi wasu cike cike a scho

ol ya koma mata da Na'ima saboda nutsuwan Na'ima yafi komai a wajenta, ji tayi jikinta yayi sanyi sai tafara safa da marwa a dakin abubuwa dayawa suna dawo mata, in ta tuna ranar da Na'ima tazo gurinta da dare zuciyanta qara karyewa yake, ji tayi hawaye na

kawowa idonta takai hannu tana sharewa.

Tana nan tsaye a dakin ta kasa zama Naima ta shigo hannunta riqe da laundry basket zata debi kayan Nafisan dazata wanke mata, juyowa Nafisa tayi suka hada ido a take taji zuciyanta ya kuma karye wa, ta daure tace

"Har kin gama ware kayan" Na'ima dake dan lura da yanayinta ta jijjaga kai tace "Eh ga naki ma" gyada kai Nafisa tayi ta juya a sanyaye ta zauna bakin gado tana dan kallon Na'iman, wuceta Na'ima tayi ta qarasa gurin madubi ta debo wasu mayuka daga cikin ba

sket din tafara jerawa sannan ta wuce toilet takai sauran, dawowa tayi gaban wardrobe din Nafisan ta bude zata debi kaya ta ajiye basket din a qasa ta fara duba kayan, sai kuma ta juyo a nutse tace da Nafisan "Akwai wasu kaya dana ware anan Ina kika kaisu

kuma"

Nafisa tace "Kamar yana qasa ai" duqawa tayi ta fara bincikawa nan qasan tana mita "Haba Nafee nafa waresu ne zan wanke kika hadesu guri daya da masu kyau" qunquni takeyi Nafisa na kallonta tana dan murmushi mai ciwo, aranta tana ayyana how kind and

innocent Na'ima is, Allah kuma ya jarabceta da wasu irin mutane zagaye da ita sukayi amfani da shirunta da kuma haqurinta wajen cutar da ita.

Inaaa...ai bazata taba bari Bilal ya samu haduwa da Na'ima a qasar nan ba, dan guntun nutsuwan da suka samu Na'i

ma tadawo cikinsa duk zai wargaza komai, ya kuma hanata karatunta da yazama saura kadan ta gama,

Miqewa Na'ima tayi bayan ta gama zuba kayan a basket ta kalli Nafisa, sai ta samu kanta da tsayawa tana nazarinta tace "Nafee meya faru ne?" Saurin jijjaga ka

i Nafisa tayi tace "Babu komai, me kika gani?" sai Na'ima ta matso kusada ita ta ajiye basket din ta zauna tace "Naganki kinyi sanyi

ne all of a sudden, Dan Allah me ya sameki?" dariyan qarfin hali Nafisan tayi tace "Gani uwar surutu kullum, kawai kaina ke

ciwo" Na'ima tace "Ayya sannu" sai ta dauki basket din ta fice daga dakin Nafisa na kallonta, tashi tayi ta rufe kofan sannan ta qara daukan wayan tafara dialing numbern Anty Amnahn..

Bayan ta dauka suka gaisa Nafisa ta fara mata bayanin saqon da tagani

a wayanta, dayake Anty Amnah tasan almost everything gameda Na'iman yasa ta fahimta, itama tace kada Nafisan ta kira Mamin dan sai hankalinta yafi na Na'ima tashi in ta sani.

Na'ima ce ta dawo dakin dauke da maganin ciwon kai da ruwa ta balla ta miqawa

Nafisan, karba tayi amma bata sha ba sai tace "Sis tunda bama shiga school din yanzu, why not mu koma gidan Anty Amnah toh" dan hararanta Na'ima tayi tace "Keda kike mitan gajiyan zuwa shine kuma all of a sudden zakice muje" Nafisa tace "Ji nake kaman bani

da lafiya ne sis, kafin yayi nisa gwara muje ta dubani" sai Na'ima ta dan bata fuska tace "To ki bari mana kigani, may be ma stress din fitan nan da mukayi ne" ganin kamar ba yarda zatayi ba yasa Nafisan gyada kai tace "Toh shikenan" ta juya ta kwanta Na'i

ma ta miqe ta dauki qaramin blanket din gadon ta lullaba mata tace "Sannu" sannan ta fice daga dakin.

Ranan anan dakin kusada Nafisan ita Na'iman ta kwana, Nafee sai tunanin uzurin da zata bullo dashi take, wanda zai sa Na'ima ta yarda su koma gidan Anty

Amnah in yaso sai su rinqa zuwa school din daga can din jefi jefi tunda ba wani activities suke gudanar wa a school din ba yanzu.

Washegari ma Nafisa qin fita tayi suyi breakfast sai Na'iman ce ta biyota dashi nan dakin tana mata sannu, kadan Nafisa taci

abincin tayi wani laushin qarya duk acikin batada lafiyan, ita kuwa baiwar Allah Na'ima sai hankalinta yafara tashi kuma tace "Sis ko zamu je asibiti to" Nafisa tadan koma ta kwanta tace "A'a kam, ai nadan fara jin dama dama" shiru Na'ima tayi batace komai

ba....

Yammacin ranan Na'ima na zaune anan falon aka danna musu door bell, dan tsayawa tayi da duba wani takarda dake hannunta tana son qara tabbatar da kofan su ne ake dannawan kuwa, qara ringing din akayi kafin ta miqe sai ga Nafisa ta fito daga dakint

a cikin sauri ta nufi qofan kamar zata fadi, bin ta da kallon Na'ima tayi tana dan mamakin firgicin nata itama ta miqe, ganin Nafisan tayi nan bakin kofan bata bude ba tana leqa peephole din jikin kofan, sai tace "Nafisa waye ne?" Juyowa Nafisa tayi kamar

mara gaskiya tace "Order nayi mana na pizza sai na zata mai delivery dinne ya qaraso" Na'ima na kallonta ta gyada kai tace "Toh bude mana muga waye" budewa Nafisan tayi su kaga ashe Lauren ce , hugging din juna sukayi itada Nafisa cikin fara'a suka wuce ci

ki Na'ima tabi bayansu, zama tayi nan gurinsu a falo bayan sun kawo mata abun sha..

Nan Lauren tafara zuba musu surutu, itadai Nafisa tanason ta zage suyi hiran dayake kawar surutun ta ce amma babu hali saboda tayi qaryan rashin lafiya, ga Na'ima kuma zau

ne gurinsu itama, sai kawai ta rinqa amsawa sama sama har se da Lauren din ta tambayeta ko lafiyan ta, Na'ima ce ta amsa da "She's sick"...

Sai dare lauren ta tafi, bayan tafiyanta Nafisa ta koma daki ta kwanta, abinci Na'ima ta dafa musu bayan ta gama

ta debi na Nafisan ta bita dakinta dashi, duqe ta sameta ajikin gado, dasauri ta ajiye abincin ta qarasa gurinta ta dagota tana tambayanta "Meya faru" Nafisa ta amsa da "Amai nayi sis", sannu ta fara mata sai ta dagata ta zaunar da ita akan gadon cikin dam

uwa tace "Sis bari in fara hada mana kayan mu mukoma gurin

Anty Amnah din gobe, this is getting worse, sannu" gyada kai Nafisa tayi tanajin dadi aranta, dama abunda takeso kenan.

Kayan Nafisan tafara hadawa cikin babban akwati sannan ta wuce dakinta dan h

ada nata kayan itama, bayan ta gama tace da Nafisa "Yanzu yaya zamuyi sis, ko bus zamu hau, dan kinga ni hannu na bai fada sosai ba a driving din, kuma kema babu lafiya" tace "Nakira Yaya Ahmad yanzu yace yana gari, zaizo ya kaimu goben" sai Na'ima tadan

bata rai tace "Ba ga bus ko train ba Nafisa" Nafisa tace "Sis gwara dai shidin yakaimu" shiru Na'ima tayi tana jin wani iri, tarasa ma ita fushi zuciyanta keyi dashi ko kuma son ganinsa takeyi oho..... dan har yanzu bata manta da maganganun da ta kyaba mas

a ba ranan, ta kuma quduri niyyan zata bashi hakuri akan hakan.

Ranan ma sake kwana Na'ima tayi a dakin Nafisan washegari bayan sunyi sallah da sassafen ta fara tattare gidan, kayan abincin da suka siyo jiyan ta ware wanda tasan zasu baci ta maidasu led

a zasu tafi dasu can gidan Anty Amnahn, bayan ta gama tayi wanka ta gyara gashinta into dough ta shirya cikin wani sky blue din abaya tayi rolling gyalen, lip balm ta shafa har da mascara sai kuma ta tsaya kallon kanta a madubin, aranta tana dariyan meyasa

take saka effort gurin kwalliya kuma, tananan tsaye ta jiyo door bell dinsu yayi qara...

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 18

Goge lip balm din Na'ima tayi tana kallon kanta a madubin, sai ta koma gurin wardrobe dinta ta cire kayan jikin

tan sannan ta nemo dogon jalbab maroon ta saka, dan zama tayi bakin gado bata fita daga dakin ba ta jiyo fitan Nafisa zata bude kofan.

Saida taji shigowan Ahmad sun gaisa da Nafisan ya tambayeta ya jikin sannan ta bude kofan ta fito a nutse, bata kallesa

ba tace "Ina kwana" taji ya amsa ya kuma cewa "Hope kun shirya" Nafisa tace "Eh yaya bari mu dauko kayan", bin bayan Nafisan itama Na'ima tayi suka fara dauko na Nafisan tace "Ki bari sis in fitar, jikin ki babu karfi" ta qarasa ta dauko akwatin suka fice,

ahaka suka fitar da kayan Ahmad na tayasu, sai kallon Na'ima yake zuciyarsa na muradin su hada ido ganin taqi kallonsa kwata kwata..

Fitansu waje Nafisa ta ware ido ta tana kallon motan da yazo da ita wata sport wrangler jeep baqa, wuce su Ahmad din tayi

ta qarasa gaban motan tace "Yaya this car is fire" dan murmushi Ahmad din yayi suka qarasa gurin motan shida Na'ima da itama sai kallon motan take, yace da Nafisa "Bakida lafiya da kinyi driving dinmu ai" juyowa Nafisa tayi ta kalli Na'ima da suka hada id

o tace "Hakane Yaya, amma naji sauqi sosai ai yau din" ta qarasa maganan tana yin mita aranta tayi qarya kuma abun ya dameta yanzu ga ci ga rashi, zagayawa bayan motan Ahmad yayi ya fara saka musu kayan nasu yana cewa "Sai kinji sauqi sosai tukunna" sai Na

fisa ta dan turo baki ta bude back seat zata shiga Na'ima tayi saurin riqe hannunta tayi qan qan da murya tace "Nafee ki shiga gaban mana" Nafisa na danne dariyanta tace "Zan kwanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login