Showing 36001 words to 39000 words out of 121625 words

Chapter 13 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

38

Nafisa ai" tuna Nafisan nason ire

iren abubuwan nan din yasa Na'ima bata sake protesting ba tace

"Tace in siyo mata dunut" yace "Okay" gurin part na snacks suka je nan ma ya dibo masu yawa dayake acikin package suke, bayan yayi inserting card nashi anan counter aka cire kudin sai cashier'n

ta hada kayan ya karba, miqa hannu Na'ima tayi zata tayasa riqewa ya kada kansa alamun ta bari but sai da ta karbi wani ledan suka fice..

A komawa gidan ma shiru sukayi sai Ahmad dinne yace "Kina yin WhatsApp?" Ta girgiza kai tace "A'a" kallonta yayi sai

kuma ahankali yace "Then how am i supposed to see your face anytime" ta juya kanta tace "Nidai banayi" murmushi yayi bai sake cewa komai ba har suka isa, tana shirin bude kofan motan ya tsayar da ita ta dalilin dan riqe bakin gyalenta da yayi, ta juyo ta

kallesa batace komai ba, sai kallonta yake wanda hakan yasa ta sauqe idanunta, yayi qasa da murya yace "I'd love to wake up everday seeing those Eyes Babe" rufe idonta tayi tafara murmushi muryansa na kashe mata duk wani kuzari na jikinta, iskan cikin mota

n ne taji yafara mata kadan ta sake juyawa zata bude kofan yace "Yaushe zaku sake fita karatun" shiru tayi kamar baza ta amsa ba, ahankali kuma tace "Sai jibi Saturday" ya gyada kansa yana sakin bakin gyalen nata suka fice daga motan tare, sai da ta jira s

hi nan tsaye ya debo kayan daga booth sannan ta qaraso garesa zata karba yace "Barshi, muje ciki" ta dan ware ido tace "Shiga zakayi" yana kallonta ya amsa da "Eh, ko da wani abun?" sai ta dan turo baki tace "In suka ganmu tare fa" murmushi yayi yace "Toh

ki fara shiga sai anjima can in biyo bayanki" ta gyada kai sannan ta nufi gidan yana kallonta fuskansa dauke da murmushi ya dan jijjaga kai, tana bude kofan ta shiga kenan mutanen falon suka dago kai duka suna kallonta, Anty Amnah, Abban twins, Nafisa da k

uma twins din, tsayawa Na'ima tayi itama tana kallonsu ganin irin kallon da suke mata, lura tayi ba itan suke kallon ba bayanta suke kallon sai itama ta juya, ganin Ahmad tayi a bayan nata ta dan ware ido, shima yana dan murmushi ya wuce ta ya shiga falon

hannunsa riqe da kayan, miqewa Nafisa tayi ta karbi kayan tana masa sannu da zuwa, Anty Amnah tace "Son sannu da zuwa" samun guri yayi gefen Abban twins ya zauna, sai a sannan Na'ima ta fara takawa a hankali cikin falon ta nemi waje ta zauna tana kallonsa

yana gaisawa da Uncle, Anty Amnah tace "Na'ima kin dawo" ta gyada kai tareda cewa "Eh Anty" ta sake tambayanta ya karatun ta amsa da Alhamdulillah, gaishe da Abban twins tayi ya amsa shima, sai ta dan juya tana kallon Nafisa dake mata wani irin kallo tana

qunshe baki kamar me tare dariya, dauke kai Na'ima tayi tana shafa kan jafar daya zo kusada ita, Anty Amnah ta sake cewa "Son kai ka kawota kenan" yace "Eh Anty" Anty Amnah tace "Ma Sha Allah" Na'ima sai jira take taji yace haduwa yayi da ita sannan ya kaw

ota gidan amma sai taga shi ko a jikinsa ma yana barewa jabeer ledan biscuit, miqewa tayi tace "Anty zanje ciki" sai Anty Amnah ta gyada kai tace "Okay, amma inkin gama ki fito kici abinci fa" ta amsa sannan ta wuce dakinsu tabar Ahmad nan yana hira da Unc

le Yasir..

Sai da tayi wanka ta fito daure da towel ta zauna kan stool nan gaban mirror zata shafa mai Nafisa ta shigo dakin hannun riqe da dunut tana ci, Na'ima ta wani daure fuska ita a dole kar Nafisan ta kawo mata wargi, dariya Nafisa ta fara ta qar

asa wajenta tana cewa "Inaaa..ai ko aman wuta idonki yakeyi Na'ima sai nayi magana" Na'ima batasan lokacin da tafara dan dariyan ba itama ta jawo cream dinta tafara shafawa, tsayawa nan gefenta Nafisa tayi tadan jingina da mirro'n tace "Iyee Na'ima, Au Ant

y Na'ima zance dan na fara shinshinowa kinbzama Anty na ma" Na'ima ta dan jijjaga kai tace "Kici kanki Nafisa"  Nafisa bata dena dariyan ba tace "Naji..yanzu dai fadamin a Ina kuka hadu harda siyayyarsa haka, chaiii

Na'ima" sai Na'ima tace "Toh dena dariya

n tukunna sai in fada miki", gyada kai Nafisa tayi takai dunut baki ta gutsira bata daina kallonta ba fuskanta da murmushi, Na'ima tace "A Cafe din da muka je karatun na hadu dashi, shikenan?" Nafisa ta gyada kai tace "Sai me kuma?" Na'ima tace "Kamar me?

ni babu komai kuma"  tace "A sannu zaki fadamin komai ma, sun tafi yin sallah shida Uncle yanzu" itadai Na'ima bata sake cewa komai ba ta cigaba da shafa manta, can kuma Nafisa tace "Oh Yaya Ahmad, kuma nikam tayaya kuke maganganun soyayyan ne ma" Na'ima t

a dago ta kalleta sannan tace "Ce miki akayi maganganun soyayya yakeyi?" sai Nafisa ta dan daga hannu tace "A'a mu yayanmu ba daga nan ba wallahi, yana da himma a lamuransa" Na'ima ta dan ware Ido tana dan dariya tace "Tanan kika bullo kuma Nafisa" tace "A

'a ai ni bani nan bani can ne, dangin miji ce nima kuma dangin mata" miqewa Na'ima tayi ta nufi wardrobe zata saka kaya tana dan kada kai tace "Kin fi qarfina kuma". Haka Nafisa tayi ta janta da surutu tana amsawa har ta gama saka kayan suka fita cin abinc

in tare, basu samu Ahmad a falon ba ashe daga fitansu sallan bai dawo ba kuma ya wuce gidansa.....

Daren ranan Na'ima na zaune kan gado tayi shirin bacci hannunta riqe da wayanta ta maida hankali tana dannawa, Nafisa ce ta shigo dakin tace "Bakiyi bacci

ba" Na'ima ta gyada kai batace komai ba, nan kan gadon itama Nafisan ta zauna ta jawo laptop dinta zata bude, can dai Na'ima ta dan gyara zama tace "Nafisa kiga...uh..uh..idan na bude WhatsApp da number'n da nake amfani anan qasar, in na koma gida sai nay

i changing number ko?" Nafisa tace "Bangane ba, WhatsApp zaki bude kaddai" Na'ima ta dan gyada kai tana kallonta, ai da sauri Nafisa ta ajiye laptop din tace "Na'ima yau din..Bobo kece kuwa?" sai Na'ima tayi murmushi tana dan basarwa alamun kunya, Nafisa t

a sake cewa "Kin gaji da Zoom app din ne"  tace "A'a, nidai ki bani amsa ta mana" karban wayan Nafisa tayi tace "Ai kawo ma in bude miki" tana danna wayan kuma tana dariya tace "Na'ima you're full of surprises these days" itadai batace komai ba tananan zau

ne sai murmushi takeyi...

Washegari Friday Nafisa nada uzuri a school tun da sassafen ta tafi school din tabar Na'ima nan dakin tana baccin ta, jiyan saida tayi bacci Ahmad ya kirata ta dauka muryanta cike da bacci, shima jin hakan yasashi cewa tayi bac

cinta sai da safe zai kirata.

Bata tashi ba sai kusan goma na safe, sanin masu gidan sun fice yasa ta fito jikinta sanye da pajamas ta nufi kitchen neman abunda zataci, sai tasamu Anty Amnah ta ajiye mata nata breakfast din bisa dining table, zama tayi za

ta fara cin abincin sai kuma wayarta tafado mata a rai ta sake tashi ta koma dakin ta dauko, aikuwa miscalls dinsa tagani guda biyu duk a lokaci ma banbanta, sai da ta zauna gaban abincin sannan tabi bayan kiran, Ahmad yana office a wannan lokacin kiran ya

shigo wayansa ya juya yana kallon wayan, saida ya jira kiran ya katse sannan ya bi bayan atake, shiru sukayi a farko kowa da wayan a kunne sai Ahmad yace "Babe yanzu kika tashi ne?" Na'ima ta gyada kai tace "I'm sorry ka kira Ina bacci" yace "Bakomai nayi

tunanin hakan" gaishesa tayi ya amsa suka sakeyin shiru, can yace "Do you have Zoom app?, I want to see you" shiru Na'ima tayi at first sai kuma a hankali tace "Na bude wancan din" Ahmad yace "WhatsApp din?" Ta amsa da "Eh" yace "Okay let me call you" sai

tayi saurin kallon kayan jikinta tace "No,I'm in my..." Sai taji ta kasa fada masa kayan bacci ne a jikinta , ji tayi yace "Irin wa'inda na ganki dasu a gidan Mami?" cikin jin kunya tayi shiru batace komai ba tana murmushi,

ya sake cewa "Babe kinyi kyau r

anan, dakyar na dauke idanuna" murmushi me sauti tayi shima daga can bangaren murmushin yake, sai ya kuma cewa "Yanzu dai iya fuskanki kawai zan gani, I promise" tace "Uhm uhm" yace "Nayi alqawari fa" ta sake cewa "Ni dai A'a" haka Ahmad yayita lallabinta

akan fuskanta kawai yakeson gani Na'ima taqi, ganin bazata yarda ba yasa shi hakura ya sake tambayanta gobe Saturday din zata fitan tace "Eh" yace "Ko nazo na kaiki" ai da sauri tace "Nidai wallahi a'a, ai ban manta abunda kayimin jiya ba" sai ya dan fara

dariya, ta sake cewa "You broke our plan" yace "Babe I'm sorry, shikenan bazanzo ba toh"...haka suka dau lokaci suna hira wanda ta fannin Ahmad barin aikin nashi yayi duk ya lalace a jikin wayan, hira sukeyi jefi jefi cike da annushuwa wanda hakan ke sake

sarqe zuciyoyinsu guri daya...sai Na'ima ce ta fara masa sallama tace zataci abinci sannan Ahmad ya kashe wayan ya koma kan aikinsa...

Da Nafisa tadawo da yamma ne take fada wa Na'iman boat race din da za'ayi between Oxford university da Cambridge, Anty A

mnah da fitowanta daga kitchen kenan tace "Au wai har gobe ne sport din?" Nafisa tace "Eh Anty, ban iya riding bane ai shiyasa babu ni, amma ni da Lauren muna cikin cheering squad" Na'ima tadan ware ido tana dariya tace "Sannu Nafisa" sai Nafisan ta kallet

a tace "Da ban karbo matching wears din dake bama ki gode Allah" Na'ima tace "Bama zanje ba" Anty Amnah tace "Gaskiyarki daughter yayi hayaniya gurin, akwai jama'a" Nafisa tayi dariya tace "It'll be so much fun kuwa,bAllah kizo muje Na'ima" ta kalli Anty t

ace "Anty ki fada mata ta shirya muje" ganin Anty Amnah ta dan jijjaga kai alamun tabar maganan yasa Nafisa gane me take nufi sai tayi shiru kuma, dan ita harta dan manta dalilin zuwansu nan gidan Anty Amnahn ma in the first place...

Ranan Saturday din

da safe Zarah ta kira Na'iman a waya akan su hadu at same Cafe din ranan can, bayan Na'ima ta gama shiryawa cikin farin blouse din riga mai dogon hannun wanda qarshen hannun da roba, tahada da brown jeans ba matsattse can ba, rigan a bude take sosai ta sau

ka har gwiwanta ta yafa brown veil, saida ta gama shirin tace da Nafisa dake nan kwance "Sis ba yanzu bane game din naku" Nafisa ta qara Jan blanket tace "Sai dan anjima tukunna" ta qarasa maganan tana sake lulluba blanket din har kanta..fita Na'ima tayi b

ata ga su Anty Amnah a falon gidan ba kasancewan Saturday sunacan ana bacci sai ta ciro wayanta tafara kiranta, tananan tsaye Anty Amnahn ta fito daga side dinsu jikinta sanye da kayan bacci tace "Har kin shirya daughter" Na'ima ta gyada kai sai Anty Amnah

ta sake cewa "Bakiyi breakfast ba kuma ai" tace "Zanyi acan Cafe din Anty" Anty Amnah ta gyada kai tareda cewa "Toh, ki kula sosai fa Na'ima" tace "Toh" sai kuma ta tsaya bata tafin ba kanta adan duqe tarasa ta Ina zata fara maganan datake son yiwa Anty'n

, ganin hakan yasa Anty Amnah'n ta sauqar da murya tace "Daughter menene? feel free with me kinji" sai Na'ima ta dago kanta ahankali tace "Dama rancan da Yaya ya kawonin a Cafe din muka hadu Anty" murmushi aynty Amnah tayi tace "Ya fada mana bayan tashin k

u daga gurin, kuma ma ai shi Yayanku ne Na'ima, what's there dan ya kawoki gida?, I know who is Ahmad" sai Na'ima ta gyada kai sannan suka yi sallama ta fice Anty Amnah na bin bayanta da kallo still bata daina murmushin ba...

Nan Cafe din Na'ima tayi mu

su ordering sandwiches da tea itada Zarahn, sai da suka gama ci sannan suka fara research din nasu, yau ma dogon discussion sukayi sosai, sun dauki lokaci me tsaho suna abu daya sannan kiran Ahmad ya shigo wayan Na'ima dake nan kan table, dauka tayi suka

g

aisa daga can bangaren a nutse yace "Nazo at the wrong time ko?" sai Na'ima ta daga kanta tafara bin Cafe din da kallo tana nazarin mutanen cikinsa, kusada entrance ta ganshi tsaye waya kare a kunnensa yana kallonta, hannunsa daya cikin aljihu, murmushi ta

masa wayan yana kare a kunnenta, cikin sanyin murya tace "Sorry.. dan qaramin few minutes Dan Allah" ya dan yi murmushi tareda gyada kai sannan ya nemi table ya zauna yana kiran waiter..

Magana ta cigaba dayi ita da Zarahn jefi jefi tana kai idonta gur

in da yake zaune yana kallonta, aduk sanda suka hada ido zata dauke kai ta cigaba da magananta da zarah, sai taji duk ta taqura kuma under his eyes, kawai tace da Zarahn su bari sai wani lokaci yanzu Yayanta yazo daukanta.

Zara tace "Where is he?" Kallo

n gurinsa Na'ima ta sakeyi sai zarahn tabi gurin da kallo itama, ganin Ahmad yasa cikin fara'a ta daga hannunta alamun gaisuwa, sai ya taso ya qaraso gurin nasu ya zauna anan gefen Na'ima, qara gaisawa yayi da Zarahn kafin tafara tattare kayanta zata miqe.

...

Bayan tafiyan Zarahn ya juya yana kallon Na'ima yace "Ya research din?" tace "Alhamdulillah" ya sake yin qasa da murya yace "Kinyi kyau Babe" ta dan yi murmushi sai kuma yau din ta amsa da "Kai ma kayi kyau" dan bin jikinsa da kallo yayi yana dan murm

ushi yace "Really?" ta gyada kai tana kallonsa still da murmushi a fuskanta, yace "Thank you dear" sai ya sake cewa "Akan me kuke yin research din, Na'ima ta juyo masa da fuskan laptop din ta fara masa bayani a nutse tanayi tana dan nuna masa lines din da

yatsanta, gyada kai yakeyi akai akai alamun fahimta yana dan mamakin iliminta, sai kuma idonsa yakai kan tabon hannunta ya rinqa kallon baya ko kifta ido, ganin kamar hankalinsa ya tafi wani gurin ne yasa Na'ima dan kallonsa sai taga hannunta yake kallo, s

aurin boye hannun tayi ajikin riganta, sai Ahmad yadan matso ahankali yace "Babe please ki fadamin tabon menene wannan a hannunki" ta sauqe idonta qasa tace "Dagaske da wuqa naji ciwon" sai yace "A garin yaya kika yanke sosai hakan?" sai ta rasa me zatace,

shidai sai kallonta yake yana jiran amsanta, tace "Da ina yanka..uh..lokacin ina yankan dankali ne" sai taji shiru be ce komai ba tadan dago idonta taga kallonta yake alamun maganan bata shigeshi ba, sai kuma ya sauqe numfashi yace "Allah ya kare na gaba"

tace "Amin".

Ce mata yayi ta tashi su tafi akwai gurinda zai kaita ta tambayesa ina ne, yace "itt's a surprise" tace "Nidai ka fadamin Dan Allah" yace "Akwai boat race na 'yan school naku da za'a yi yau" Na'ima tace "Nafisa tace zataje" yana kallonta ya

sake cewa "Bakya son zuwa?" sai Na'ima taji tanason zuwan tare dashi, jijjaga kai tayi tace "A'a inaso" sai ya fara tattare mata kayanta yana sawa a jaka suka miqe, sai da ya biya kudin abunda taci itada Zarahn wanda Na'ima tana ta magiyan ya bari yace A'a

, sannan suka fice daga Cafe din..

Isarsu London bridge din suka samu acike da mutane ta ko Ina, ahaka ya kamo hannunta suka kutsa cikin mutanen har suka kai gaba inda suke kallon komai a gabansu, Na'ima tsayawa tayi tana kallon racers din da duk suke cik

in nasu boat din suna jiran abasu dama sufara, Ahmad ya sunkuyo yace mata "A bayan wane team kike?" Tadan kallesa tace "Na makarantar mu mana, kaifa?" Ahmad yadan daga kafada yace "Ya na iya, ina bayan na makarantar naku nima" ta danyi dariya tace "da Camb

ridge ka zaba?" yana murmushi yace "Kedai ina bayan nakun kawai" ta cigaba da dariyan tadan jijjaga ta maida hankalinta gurin tseren..

Wasa yayi dadi saiga Na'ima har da ita acikin masu ihun son team dinsu suci, Ahmad sai kallonta yake yana dariya ganin t

a dage itama tana daga hannu tareda cewa "Go,go,go" wayarsa ya ciro yafara daukanta hoto batasani ba, ana cikin haka ta hango Nafisa da team dinsu daga dayan bangaren bridge din sai yekuwa suke, dukansu sanye suke cikin blue din polo shirt da facing cap, t

urawan duk suna sake cikin gajerun wanduna baqaqe while Nafisa ta saka dogo ita..Na'ima tadan tabo Ahmad tana dariya tace "Yaya ga can Nafisa" kallon gurin yayi yana dan girgiza kai ganin su Nafisan sun dage da ihu harda waqa yace "Hajiya Nafisa"..

Maka

rantar su Na'ima ne suka lashe kofin wasan, dazasu bar gurin bakinta yaqi rufuwa dan murna sai hiran take wa Ahmad shidai yanata binta da kallo ganin fara'anta abun sha'awa, tana yi masa kyau matuqa in tana dariya...

Basu hadu da Nafisa ba dan tabi 'yan q

ungiyarsu sun tafi, Ahmad dinne ya maida Na'ima gida ranan, da suka isa ta rikice masa akan ala dole bazai shiga gidan ba, yana dan dariya kuma yana kallonta kamar yau ya fara ganinta, ta wani bata fuska bata sake cewa komai, ganin haka yasa Ahmad din yana

murmushi yace "Okay, Okay, bazan shigan ba, are you happy now?" ta gyada kai ta juya ta bude motan sannan ta fita yana kallonta har sannan bai daina murmushi ba, hakanan ya hakura yaja motansa yatafi tananan tsaye, ta dan bi bayan motan da kallo sannan ta

juya ta shige gidan.....

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 21

Zaune suke a falon suna hira banda Laila da ta wani bata fuska tana jin ranta duk a dagule, wayanta ne riqe a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login