Showing 117001 words to 120000 words out of 121625 words
dariya a gurin, Na'ima ta matsa kusa da Abu tace "Ka riqe tawan toh, daman ban cika driving sosai ba ai" sai Abu yayi dariya yana girgiza kai, Faruk yace "A'a Na'i
ma ki tuqa motan ki kinji, da haka zaki saba,ย I'll buy him the latest model shima" Mami na kallon Na'ima tana murmushi sosai, sai ta shafa kan Abu tace "Rabu da Nafisa Babana, kaji abunda Yayanku yace ma" aikuwa aranan Faruk yayi ordern motan Abu yace it'
s high time shima Abubakar din ya fara tuqa mota tunda ya shiga shekararsa ta sha takwas shima, da Abba ya dawo da dare yasha surutun akan motocin ranan, yana zaune sai murmushi yake yana sauraron kowanne daga cikin iyalin nasa, sai da suka gama zancen mot
an sannan yace da Na'ima "Daughter nayi waya da Adekunle yace you can go for an interview tomorrow" cikin ladabi ta amsa da "Toh Abba, nagode" sai yace da Nafisa "Kema nasa Yayanki ya yi magana da constructors na shagon naki, an samu location mai kyau, sai
kuje da qannenki ku gani" da fara'a Nafisa tace "Toh Abba in sha Allah" Faruk yace "Gobe ki sameni a part dina muyi maganan komai"..
Washegari da Na'ima ta shirya tafiyan sai su Mami da Nafisa suka ce taje da motan nata itama, haka ta fito cikin shirin
abaya, dan Na'ima na son Abayas sosai, da ta shiga motan sai ta tsaya tana kallon interior din, sai lokacin ta lura everything about the car scream luxury, no wonder Nafisa takeson motan ashe, wani kiran ta sake yiwa Ahmad dan sun gaisa da safe, bugu biyu
ya dauka lokacin yana office shima, sai tace "Thank you once again, i love everything about the car" daga dayan bangaren Ahmad ya kishingida jikin executive chair dinsa, anutse yace "Babe inata tunanin yanzu zata rinqa hanani daukoki" sai tayi murmushi tac
e "Kaga na hutar dakai ai" yace "Ki riqe hutun ki" dan dariya ta fara sai ya sake cewa "Da yaushe zaki koma gida?" Tace "Bansani ba, duk lokacin da suka sallameni"
sai ya kwantar da murya yace "Should i order food for us sai ki biyo ta office dina?"ย cikin
shagwaba tace "Uhm uhm" yace "Idanun ki kawai zan kalla i promise" sai tace "Okay ba idanuna kadai kake gani ba dama in muka hadu?" shiru Ahmad yayi har sai da ta dago wayan taga kiran is still going, ta sake cewa "Hello" ahankali yace "Your figure is so
mesmerizing Na'eemah" cike da kunya takai hannu idonta tana rufewa bata bar murmushi ba, cikin rada tace "Ahmad...what is this?" yana murmushi yace "I told you kina turning dina on baki yadda ba ko" bata ce komai ba sai ya sake mata rada "Watarana zan nuna
miki hakan kinji" ai da sauri ta kashe wayan tana dan dariya, tana mamakin halin Ahmad wanda in zata kwana dubu tana fadin haka gurin 'yan'uwansa bazasu taba yarda ba....
Visit ArewaPen..The Complete Book is also available there for FREE.
08134692758
Chat me up when you want a talk regarding the Book...
I repeat...Only regrading the Book please, don't call me for any other reason unless it's about my Books.
MURADIN ZUCI will be published within May or June in this 2026, in sha Allah..
Stay Tuned.
Love,
Bintu Musa
๐ค
๐
.
KUNCIN ZUCI
๐๐
Chapter 47
Har Na'ima ta bar gidan bata daina murmushin ba wanda hakan ne yasa bata ma lura da motan da ta bi bayanta ba, ahanya bini bini zatayi murmushi ta dan jijjaga kai in ta tuna abund
a Ahmad din ya fada mata, tasani wannan wani side dinsa ne da in ance ita kadai yake nunawa, zata yarda da hakan, but above all this, meyasa take qara sonsa despite duk abunda zai fada, meyasa irin maganganun nan da yake mata suke hautsina mata lissafi da
zuciyarta ne madadin ta kallesu a wata fuska daban, sai tayi murmushi tana dan jijjaga kai bata daina kallon titi ba, har ta isa babban bankin zuciyarta bata daina annushuwa ba, a can nesa da bankin tayi parking saboda bata da cikekken permit na shiga ciki
da motan nata, a lobby tayi tambaya aka kwatanta mata office din Mr Adekunle din ta wuce ta hau lift din da zai kaita floor dinda yake, isar ta nan ma ta samu ba ita kadai bane a line din and to her suprise sai ta samu wa'inda ke zaman jiran duk da suits
ajikinsu har matan, ai atake taji kalli jikinta amma ga mamakinta sai taji secretary din ta kirata, da taje sai ta tambayeta tace "Are you Na'ima Yusuf Dabo?" ta amsa da "Yes" sai secretary din ta miqe ta wuce babban office din Mr adekunle din, bata dade b
a ta fito tace Na'ima ta shiga, lallai qasar mu in kanada gata da wanda zai tsaya maka
an wuce gurin, dan Na'ima acikin mintunan da basufi talatin ba ta gama magana da adekunle, shima dan kar ace bata je bane if not straight zata samu aikinta daman, haka t
a fito ta wuce masu jiran shiga office din kiran Abba na shigowa wayanta, tambayanta yayi ya sukayi dashi Adekunle din saboda yanason ya kirashi, a hanyar ta na fita daga bankin ta masa bayanin komai sannan sukayi sallama, fitowanta daga gurin gaba daya ta
hango Bilal a jikin motanta a tsaye alamun yana jiranta, sai batayi mamaki ba tunda har a England ma sai da samota balle qasar nan, dakewa tayi ta qarasa gurinsa sai ya cire shades din idonsa yana kallon ta yace "Nice car Na'ima" batace komai ba ta zagaya
ta shiga driver's seat, kawai taga ya buge dayan side din ya shiga shima, ta juyo tanaย kallonsa tace "Ka fita" sai ya rinqa kallonta yace "Na'ima we need to talk" juya kanta tayi tace "Talk then" sai ya kwantar da murya yace "Mu samu wani gurin, I'm hung
ry" bata ce komai ba ta tada motan suka bar bakin bank din, har suka isa Bilal sai kallonta yake, he still can't believe wannan wai Na'iman daya taba rayuwa da ita a baya ce, idanun Na'ima na kallon titi har suka isa bakin wani open restaurants tayi parkin
g suka fito, kanta tsaye ta shige gurin yana biye da ita, sai da suka zauna a table waiter ta kawo abinci a Bilal din shi kadai dan Na'ima tace bazataci komai ba kuma har sannan taqi kallonsa, sai da yayi nisa da cin abincin ganin sunyi shiru ya ajiye spoo
n din yace "Na'ima ki dawo gidana, ki manta komai kamar yanda na manta ki dawo, na yafe miki abunda kikayi da Nasir sannan nima ki yafemin komai" Na'ima tayi wani murmushi me ciwo tana shafa tafin hannunta , sai ta dago kanta tana kallon idanun sa tace "Ba
n yafe maka ba, bazan taba yafe maka, bazan taba manta komai ba, duk abunda kayi min ban yafe ba Bilal" sai ta daga murya ta sake cewa "Ban yafe ba Bilal" kawai sai ga hawaye suna zubo mata, cikin bacin rai Bilal yace "You've hurt me too Na'ima, rashin ban
i kanki da kikayi kin dauka nima zan yafe ne, you're willing to give yourself to Nasir" sai ta dago idanunta da ke zubar hawayen tace "You know what? sai daga baya nayi tarin godiya ga ubangiji akan hakan, in sha Allah tun a duniya sai Allah ya sakamin aka
n duk cutarwan da kamin" rai a bace yace "Karki yafe din, f*ck you Na'ima, i said damn you, kuma kisani ko zaki mutu, duk inda zaki shiga sai kin koma gidana, ki gama maulan naki gurin wa'ennan pathetic people din, we are your blood Na'ima, nothing changes
that" ji tayi zuciyarta na zafi, sai ya sake cewa "Wait...kina tunanin akwai me auren ki after all you've done Na'ima" sai tayi murmushi me ciwo tace "Zanyi aure nan ba da jimawa ba Bilal, zan auri wanda nakeso, zan auri wanda yake mutuqar sona wanda yasa
n daraja da kimata, let's see in kanada halin hana hakan" aikuwa be san lokacin da ya tunkudar da plates din gaban sa ba, cikin huci yace "Damn you, I'll kill him, and I'll kill you Na'ima" sai mutanen gurin suka fara kallonsu, da gudu waiter tazo tana fad
in "Violence is not allowed here sir" Na'ima ta girgiza kai sanin Bilal bazai taba chanja wa ba, duk nutsuwar da zeyi ta bogi ce, sai ta miqe ta dauki jakanta ta barshi anan zaune yana kallonta, wani irin turirin kishinta ne yakejin ya taso masa a zuciya,
awannan lokacin ji yake zai iya kashe duk wanda yayi gigin auren Na'ima, yana nan zaune sai ya tashi kamar an mintsinesa yayi saurin bin bayanta....
Rai abace Na'ima ta isa gida, shigan ta compound din da motanta sai taga na Ahmad a fake nan cikin parki
ng lot din, da dan mamaki ta fito sai murmushi ya subuce mata tuna kashe wayan da tayi suna magana dazu, ahankali ta qarasa entrance din gidan tana gyara gyalenta, aikuwa sai ta samu Ahmad din tareda Mami har da Faruk a zaune suna hira, a sannu ta
qarasa f
alon Mami tace "Har kin dawo Habibti" ta amsa da "Eh" tareda zama anan falon tana gyara gyalenta ganin Ahmad din, duk yasa ta fara tsarguwa in his presence kuma, Faruk yace "Sun miki interview din?" tace "Eh Yaya, Abba yace zasuyi magana tukunna" sai ya gy
ada kai, Mami na murmushi tace "Masha Allah Habibiti" Ahmad dai yana ta danna wayarsa bai dago kai ba har sannan, cikin sanyin murya Na'ima tace masa "Ina wuni" ya dan dago yace "Lafiya, ya aikin?" Mami tace "Interview taje yau din tukunna" sai yace "Ma Sh
a Allah" Na'ima sai danne murmushi takeyi ganin yanayinsa, sai Mami tace da Na'iman "Mutanenki sun tafi dubo site din ko jiran Yayan nasu basuyi ba" Faruk yayi dariya yace "Nima sai na bata musu lokaci kafin naje ai" Mami na murmushi tace "Kayi hakuri" sai
ta sake kallon Na'ima tace "Ki debo abinci Habibti" tace "A'a Naqoshi" da haka Mami ta cigaba da magana da Faruk, Ahmad na saka baki jefi jefi, Na'ima dake zaune a falon ta rinqa kallon Tv tanajin kaifin idon Ahmad akanta bata juyo ba, wayanta dake jaka t
aji yayi qaran shigowan text amma bata kula ba, again ta sake jin wani ya sake shigowa sai tayi murmushi wanda se a dauka a tv taga abun dariya, Ahmad na shirin tura mata wani text din kira ya shigo wayansa sai ya miqe yana cewa "Mami bari na dau kira" tac
e "Toh son badamuwa" da haka ya fice daga falon, yana isa compound din gida ya daga tare da cewa "Talk Mazzy" daga dayan bangaren Mazzy yace "Man this job is huge, i should've said 20" sai Ahmad yace "That's not my answer, I've given you a week to finish e
verything" sai Mazzy yace "Boss, I'm trying everything i could, munyi binciken tun daga diddigi ne, six people fa" sai sannan yadan sauqo sanin Mazzy baya disappointing dinsa, gashi aikin mutum shida cikin sati yasan dole sai sun sha wahala, sai yace "Zan
qara maka kwana biyu, max shine uku" Mazzy da daman ya iya Hausa sai yace "Mun hada details na komai, one package is here with us, but i had a tip up yesterday, saying that...the other package is there in Abuja" confusedly Ahmad yace "What? here in Abuja?"
Mazzy yace "Yes, but i've sent my guys to wrapped it up, do you want it back here in Lagos or Abuja?" sai Ahmad yace "Bring the other one here, kasan inda zaka kai mun ai" Mazzy yace "All done Boss" da haka sukayi sallama sai Ahmad ya dago wayan yana kall
o ransa na baci, so yananan Abuja, jikinsa ya basa Bilal ne, hakan na nufin ya hadu da Na'ima kenan, lallai kuwa lokaci yayi da tsayar da rainin nan, dan hakan raini ne a gurinsa..Yananan tsaye ya danna kira a dayan wayansa da ya bari a falon da zai fito,
su Mami dake zaune a falon har sannan ta kalli wayan itada Faruk, sai tace "Habibti kaiwa Ahmad wayarsa a waje" asannu Na'ima ta miqe tareda daukan wayan ta nufi wajen, fitanta ta hango sa tsaye kamar me jiran fitowan nata, tana qarasowa gurinsa ta hau gya
ra gyalenta, Ahmad na kallonta ya danyi murmushi sai yace "Idanun ki nake kallo kadai fa" tace "Uhm Uhm, toh ka juya kanka" sai ya kauda kan yana dan dariya tareda cewa "Toh ki ban wayan" miqo masa tayi sai ya hada da hannunta wajen karba, dan jawotan da y
ayi sai ta taho gaba daya garesa har kanta na kusan bugewa da qirjinsa, sai ta ganta 'yar qarama a qasan sa ta kasa dago kanta sai Ahmad ya sunkuyo yana kallon ta nan ta damqe idanunta duka tana jin numfashinta na fita da sauri sauri, kallon lashes dinta y
a tsaya yi baya ko kifta ido, sai ya rinqa kallon features din fuskanta admiringly har sannan bata bude idon ba, Jin kamar numfashinsa na sauqa a fuskanta yasata kai hannu qirjinsa da nufin ta turasa baya, amma sai ta samu kanta da barin tafin hannun nata
akan qirjinsa dalilin jin bugun zuciyarsa da tayi a hannun nata sai ta bude idonta ya fada cikin nasa yana kallonta har sannan, saurin kauda kanta tayi jin idanunsa na mata kaifi dayawa tayi gyaran murya da dan qarfi, murmushi Ahmad yayi yace "Ki juyo in
kalli idon naki
ko in kalli inda bakyaso" da sauri ta juyo tace "Nidai ka rufe idonka please" dan dariya ya fara qasa qasa, sai ya duqa kamar ze mata rada kawai sukaji an banko qofar dake jikin gate din gidan, Bilal ya shigo cikin diri yace "Na'imaaaaa" da
sauri suka juya itada Ahmad suna kallonsa yana tahowa kamar wani mahaukaci, Ahmad na kallonsa kansa na ringing "So the package is right here in front of me" aikuwa da sauri Na'ima ta fincike hannunta daga na Ahmad din ta nufi Bilal, sai yabi bayanta da sa
uri shima, da sauri ta taho tana fadin "Bilal stop" sai yace "I'll kill him, so this is him" tana isowa gabansa ya hankadata da karfi kamar yanda ya saba sai tayi baya ta fada jikin Ahmad daya tarota da sauri ya miqar da ita, Ahmad beyi wata wata ya sauqew
a Bilal naushi a fuska, kafin ya farfado ya sake qara masa wani yana huci, nan ma yasa kafa ya debeshi sai ga Bilal a qasa shima tiim, Na'ima na kuka ta fara jan rigan Ahmad da ya duqa yana sauqewa Bilal duka ta ko ina kamar yasamu punching bag, Bilal na k
arban naushi yana fadin "I'll kill you, wallahi yau ko ni ko kai" Ahmad dake huci yace "Sai dai niiii" Na'ima na ihu ta sake Ahmad din ta nufi cikin gida da gudu tana fadin "Mamiiii, Mamiii" sai sannan maigadin ya dawo gidan shima da gudu ya nufi gurinsu g
anin Ahmad na dukan Bilal kamar ba mutum ba, da gudu su Mami suka fito da Faruk, Mami na fadin "Na shiga uku, Ahmad ka dagashi zaka kasheshi" Faruk dake jan Ahmad din baya yace "Ahmad meye haka wai" dakyar maigadi da Faruk din suka rabasu, Bilal na kwance
hanci sai jini da baki, da Ahmad ya miqe yana huci yace "Dan uw*rka a gabana zaka taba ta, waye baban ka ma dan bantan ub*nka" sai Bilal ya miqe dakyar Maigadin na riqesa yace "Ka shammace ni ne amma duk ranan da mukayi gamo na biyu sai na kasheka" Ahmad y
ayi murmushi Faruk na riqesa shima yace "Zaka maimaita maganan nan a gamuwata da kai next time, sai ka maimaita wallahi, yanzu ma ban barka ba" cikin tsawa Mami tace "Bilal Get out before i call the police" sai Bilal yayi kururuwa "Babu inda zanje kun riqe
min mata ta" Ahmad yace "Sai kayi claiming dinta yanzu ma in ka isa" kawai Bilal yayi murmushi yace "You're late... you're late motherfucker, kaganta nan" ya nuna Na'ima dake tsaye gefe tana kuka, yace "I've touched every core of her, you hear me?" "I've f
*cked every inches of her" Faruk ne ya dauke Bilal da mari wannan karon, cikin ihu Mami tace "Bilal ka fitaaaa" shi Ahmad ma daskarewa yayi yana kallon Bilal din, ji yayi komai na jikinsa ya daina aiki na wasu daqiqu, Faruk ya sake marin Bilal din tareda h
ankadasa baya yace "Durun uwarka, Durun Uwarka nace" Bilal na dariya yana kallon yanda jijiyoyin kan Ahmad suka tashi, ji yayi he has won this fight, yasani ya daki Ahmad din a zuciya ba kadan ba, maigadi na turasa waje yana tafiya da baya da baya ya sake
cewa "Tell him Na'ima, tell him how we do it every single night" Na'ima ta damqe idanunta tana kuka da qarfi, sai a sannan Ahmad ya zaburo kansa Mami ta riqe rigansa tana fadin "Don't let him get into your head, Ahmaaaad" da sauri Bilal ya juya ya fice dag
a gidan, aikuwa sai ga hawaye sun kawo idon Ahmad ya daga murya da qarfi yace "You'll scream my name while i slaughter you, I'll slaughter you like the pig you are" Faruk ya dafa bayan Ahmad kawai dan shima ya gagara magana, qoqarin tafiya Ahmad din ya far
a Mami tace "Kar kaje Ahmad, banason fadan nan" sai yace "Gida zan tafi Mami" Na'ima na kuka a gefensa yana jinta amma yanda zuciyarsa ke zafi sai ya kasa juyawa gurinta, Mami tace "Muje ciki Ahmad, you're not yourself, kar ka bisa kisa ya biyo baya" ahank
ali ya sake cewa "Mami i need to go" sai tace "Faruk ka tuqasa" sannan ta juya ta riqo Na'ima dake hawaye har zuwa sannan tarinqa shafa bayanta, har suka tada motan suka nufi gate Ahmad na jingine da kansa a kan