Showing 105001 words to 108000 words out of 121625 words

Chapter 36 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

29

tace "Ke ya fara tambaya na da naje dazu Na'ima, and shi yace kar n

a fada miki amma tun kwanaki ya kulle Bilal a cell sai da zai tafin nan yasa aka sakeshi" kasa magana Na'ima tayi saboda mamaki, sai Nafisan ta shiga Instagram dinta ta kunnawa Na'iman voice note din da Bilal ya tura mata, sai da zuciyar Na'ima ya buga jin

Bilal na masifa yana ambato kashe Ahmad acikin maganansa, bata qarasa jin voice note din ba ta kalli Nafisa a dan rikice tace "Bilal ya masa wani abu ne da yake rashin lafiyan?" dariya ma Nafisa taso yi, aranta tana ayyana yanda hakan ma zaizo kan Na'ima

amma madadin ta amsa mata sai ta dan gyada kafada tace "A bakinsa zakiji wannan ba ni ba" da haka Nafisan ta miqe tashiga bandaki, shiru Na'ima tayi anan zaunen tana tunanin maganganun Bilal din zuciyarta na qara yin nauyi, cikin sanyin jiki ta miqe ta sak

a veil akan doguwar rigan jikinta na atamfa me dogon hannu, a jakan Nafisa ta dauki transport money tareda wayanta ta fice daga dakin, sauqinta bata samu Anty Amnah a falon ba sai twins da suke ta wasan ludo, ficewa tayi hankalinsu nakan wasan basu kulata

ba..A Uber taje gidan amma da ta isa sai ta tsaya a bakin gate din ta rasa me zatayi ma ganin bata san pin na gate din ba, kiran Nafisa tayi bayan ta dauka sai tace "Nafee bansan pin na gate din ba" kadan ya hana Nafee yin dariya sai ta danne ta fara fado

mata, da ta danna ta shiga sai ga ma'aikacin gidan ya fito daga backyard da saurinsa yace "Who are you?" tace "Tell him it's Na'ima" dan kallon attire dinta yayi sai aransa yayi tsammanin yar uwar ogan ce tunda bahaushe ne, sai yace "It's alright come in"

da haka ya bata hanya ta nufi entrance din gidan tana tafiya a hankali, tsayawa tayi bakin babban kofan falon bayan ta danna door bell, ana budewa idonta ya fada cikin na Ahmad, da dan mamakin ganinta ya fito daga falon yana murmushi, sai taji damuwan da t

azo dashi din yana sauqa a hankali ganin shi cikin kuzari, yana kallonta yace "Muje ciki Babe" da kamar zai kama hannun ta amma sanin da abokansa a falon yasashi beyi hakan ba, yana gaba suka shiga falon sai abokan nasa guda uku suka dago kai suna kallonsu

, Lamin dake cikinsu yana murmushi yace "Guys, our princess is here" sai sukayi murmushi gaba dayansu, Ahmad yace "Yau dai bazata kulaka ba" ai kuwa nan Na'ima tace "Ina wuni" sai biyun cikinsu suka fara dariya, Ahmad yana murmushi ya dafa goshinsa

alamun

Kash, sai ya juya yana kallonta bai daina murmushin ba, tsayawa tayi nan gefensa duk a taqure sai ya kalli abokanan nasa yace "Na'eemah meet my Gee's, Lamin kinsan shi, sai Mus'ab and Jason" tana kallonsu a kunyace tace "Ina wuni" suka amsa banda baturen d

a baya jin hausa, Mus'ab ne ya fara miqewa yana cewa "Muma lokacin tafiyar mu yayi daman" da haka suka miqe gaba daya Ahmad ya rakasu can wajen inda anan suka tsaya suna wani maganan kuma, zama Na'ima tayi a kujera tana jiransa sai ta hango Simba yana sauq

owa daga stairs, da saurinta ta nufeshi ta tsugunna a gabansa tana shafa gashinsa, Ahmad bai dade ba ya sake turo kofan falon ya shigo, ganinta tsugunna gaban muzurun yayi murmushi yace "Babe bakya tsoronsa?" ta dago kai tana murmushi tareda girgiza kai, k

itchen ya nufa bai dade ba ya fito hannunsa riqe da drink ya zuba mata a cup sannan ya taho gareta riqe dashi ahannu, miqewa tayi ta karba sai ya duqa ya daukin Simba yace "Kina sonsa har haka" tayi murmushi tace "Yana da kyau sosai, adopting kayi?" ya gir

giza kai yace "Stray cat ce ta haifa a forest din gefena dinnan na dauka" ta gyada kai suka nufi kujera, bayan ta zauna sai ya zauna agefenta ya bar gap a tsakaninsu, sai da ta aje cup din hannunta bayan ta kurba sannan tace "Ya jikin naka?" yana kallonta

yace "Me ya faru baki dauki wayana ba Babe" taqi kallon idonsa tace "Ban san inda na ajiye ta ba" sai yayi murmushi yace "Bari dai kiga zan fara kiran Anty ta rinqa hadani dake kawai" adan shagwabe tace "Uhm uhm nikam" sai ya rinqa kallonta, kauda kai tayi

tana murmushi, cikin sanyin murya tace "Ka daina min irin kallon nan" sai taga ya duqo kansa ahankali yace "Wane irin kallo nake miki?" nan Na'ima taji iskan falon ya fara mata kadan, she know it's risky zaman ta guri daya ita kadai da Ahmad amma batasan

me yazo kanta ba ma tazo din, Ahmad na kallon yanda take wuri wuri da ido yana murmushi, ji yake he can do alot to her at that moment amma sai yafara kokarin danne abunda yakeji din because ba irin wannan son yake mata ba, he purely wants her in a pious wa

y, dan gyaran murya Na'ima tayi tace "Nafisa ta fadamin ka kullesa" sanin me take nufi ya sashi gyara zama yace "I'm not even done with him, it's just a start" sai tace "I don't want you to get involved with him, he is so evil Ahmad" yana kallonta yace "He

is only evil akan mace, he's a fool Na'eemah, and i will give him what he deserves soon enough" cikin kwantar da murya tace "Komai ya wuce fa" sai ya kamo hannunta yana juyo da tafin yace "Abunda sukayi bazai taba wuce wa ba Na'eemah, look here" yana nuna

mata tafin hannun ya sake cewa "Wannan yayi kama da abun da zai wuce" ta girgiza kai cikin karyewan murya tace "Banaso ya cutar da kai" sai ya tallafo fuskanta yace "Sai dai kiji tausayinsa Na'ima, Billahi i'm going after him so hard that sai ya yi choosi

ng mutuwarsa" hawaye ne ya fara zuba a idonta tace "What if na yafe" sai ya kauda kai rai adan bace yace "Ni ban yafe ba" shiru sukayi babu wanda ya sake cewa komai acikinsu, ganin kamar ransa ya baci ya sa ta kwantar da murya tace "I'm sorry" sai ya juyo

yana kallonta yace "I hate him Na'eemah, i hate everything about him, inajin zafin saninsa da kikayi kafin ni, inajin zafin abunda ya miki a rayuwa" ahankali ta sake cewa "I'm sorry" sai kuma zuciyarsa ta karye ganin yanayinta, riqo hannunta yayi yace "It'

s alright Babe, ba laifin ki bane kinji" ta gyada kai sai ya kwanto da kanta a kafadansa bata daina hawayen ba, cikin lallami ya kwantar da murya yace "I Love You Na'eemah, Billahi ina sonki, inason in rayu dake" sai ya dago kanta tana kallonsa yakai hannu

ya share mata hawayen yace "Zan iya yin komai akan wanda ya tabaki" sai tayi murmushi hawayen bai daina zuba a idonta ba tace "Nima haka Ahmad, Nima haka" yana murmushi yace "Ranan da na ganki a karo na biyu a falon Mami, you know what i felt?" sai ta gir

giza kai tana kallonsa, yace

"Naji ajikina Allah ne ya sake bani wani daman a karo na biyu, shiyasa banyi wasa da ita ba Na'eemah" sai tayi murmushi tana duqar da kanta, ji take komai na duniyan na mata sanyi a rai, haka So din yake daman, haka akeji in an

a So, indai haka ne toh 'tanason Ahmad' kuma zata sake fada da babban murya tana sonsa, shiru sukayi kowannensu da abunda yake saqawa arai, Ahmad sai kallonta yake baya ko kifta ido, ganin taqi dago kan nata sai ya duqar da kanshi suka hada Ido, kawai ta f

ara dariya kadan kadan tana kare bakinta da hannu, bai bar kallonta ba shima yana murmushin yace "You're a Fulani right?" ta gyada kai ahankali tace "Duka fannin iyayena" sai yace "You're beautiful Na'eemah, idanunki sunada kyau sosai" ganin yana kallonta

dayawa yasata yin gyaran murya tace "I have to go, it's getting late" sai yace "So soon Babe" idon ta ne yakai kan abunda ke cikin laptop dinsa dake kan glass table sai tace "Wannan ma App dinka ne?" sai ya kalli laptop din yace "Yes, ina encrypting dinsa

ne, to tighten the security" ta dan duqo tana kallo tace "It looks unique, menene sunan" yace "Bizgo" gyada kai tayi tace "Sounds nice, what does it do?" sai ya dauko laptop din ya daura mata akan laps dinta yana nuna mata ciki, yana briefing nata yadda sa

les platform da freelancing features ke aiki acikin App din, sai da ya gama yace "Do you like it?" ta gyada kai tana murmushi tace "Ta yaya kake iya creating App irin haka?" sai yayi murmushi yace "App din ya miki kyau?" tace "Sosai fa" sai yace "Then, it'

s yours" ware ido tayi tace "What? A'a bazan karba ba" yace "Zan miki transfer din komai anjima, as a Data scientist nasan kinada developer account ba" Na'ima dake cikin mamaki har sannan ta kasa cewa komai, ganin haka sai ya kamo hannunta yace "It's your

graduation gift Babe" karbe hannunta tayi cikin sanyin jiki ta miqe dan tasan kome zatace bazai fasa bata din ba, ahankali tace "Zan tafi" sai ya miqe shima tareda daukan car key dinsa dake nan kan glass table din yace "Bari na kai ki" ta gyada kai kawai t

a nufi kofa yana tafe abayanta, ahanya ya tsaya a wani babban supermarket ya lodo mata kayan ciye ciye kamar bai san ciwon kudinsa ba, sai kallon kayan da suka cika back seat din take ta kasa magana, sai da yayi settling a driver's seat sannan ya bare wani

chocolate ya miqa mata yana cewa "Ci kiji, it's my favorite" sai da ya jira ta gutsura sannan ya karba daga hannun ta ya cigaba da ci tareda miqa mata wani sabo, sai taqi karba tace "Nidai kabani wanda nafara ci gaskiya" ya sake kaiwa baki yana danne dari

ya, ta shagwabe fuska tace "Kana cinyewa fa" sai da ya rage dan kadan sannan ya miqa mata, aikuwa ganin shi dan mitsitsi tace "Nafasa ci" dariyan da yake dannewa ce ta fito fili sai ta juya kai tana murmushi, dakyar ya lallabata ta karbi wani sabon chocola

te din sannan ya kunna motan suka tafi....

Daren ranan suna kwance Na'ima na game a iphad dinta taji qarar shigowan notification a wayanta, dago wayan tayi sai taga daga App store dinta ne, Ahmad ya mata transfer din komai related to App din nashi, da mam

aki ta rinqa duban App din, da tazo kan CPM na Ad's revenue saida takai hannu baki, bata gama shan mamaki ba sai da taga monthly income na App din, magana ake ta hundred of millions ne zasu rinqa shigo wa Na'ima duk wata, App din nada over four million use

rs and CPM din ta yana zuwa daga kasashen turawa ne wanda sune 80% users din, Na'ima batasan lokacin da takai duka a bayan Nafisa dake gefenta ba, agigice tace "Na shiga uku Nafisa ina zan kai kudin nan" da sauri Nafisa ta miqe tareda leqo kanta suna ganin

wayan tare, sai ta ware ido tace "Wooo, Na'ima what is this?" sai Na'ima ta kalleta tace "Nafisa bazan karba ba, maida masa ownership dinsa zanyi" Nafisa tace "Ya Ahmad ne ya baki?" ta gyada kai sai Nafisan ta sake cewa "Wallahi bazaki maida masa ba Na'im

a, Allah ne ya baki, and

you deserve more than this" cikin sanyin murya Na'ima tace "Toh muyi sharing, be a patner, kudin is too much for me Nafisa" ganin yanda Na'iman ta gigice yasa ta kamo kafadan ta tace "Rabon ki ne Na'ima, wannan shine son ai, yana s

onki ne shiyasa ya baki, ki karba ki gode Allah kinji" sai Na'ima tayi shiru ta sake juyawa tana kallon App din akan wayanta....Da Ahmad ya kirata da daren suna cikin magana tace "Me zance wa su Abba akan App din" cikin kwantar da murya yace "Zan fada musu

Babe, karki damu kinji" tayi shiru sai yace "Baki fadamin yanda kukayi da supervisor din ki ba" ahankali tace "Yace i'm good to go, Nagode sosai" yace "Ma Sha Allah, Allah yasa ku gama a sa'a" ta amsa da Amin....

Washegarin ranan su Mami suka diro qasar

itada dasu Abu, su Na'ima ne sukaje daukansu tareda da twins, da babban sign dinsu sukaje Airport din sukayi rubutu ajiki 'We Love You Mamii' Nafisa har da siyan balloon sukayi decorations a jikin, anan waiting area suka tsaya tareda da dagawa suna jiran f

itowansu, aikuwa suna fitowa suka hangosu, suna daga sign din Nafisa na cewa "Oyoyo..Mami, Oyoyo... Mami" juya kai Mami tayi tana dariya tace "Ji shiririta" Abu ya daga hannuwa ya taho yana cewa "We love you tooooo" da gudu Nafisa ta nufi Mami, Na'ima ta b

ita abaya riqe da twins, sai da ta kai kusa da Mamin kawai ta sake twins din ta nufeta da sauri itama, rungumesu duka Mami tayi tace "My babies" sai da ta cika su Al'ameen dake gefe yace "Ni komawa zanyi, har wani we love you Mami kadai ajikin sign din, to

mu din duwatsu ne?" sai Nafisa ta talli qeyarsa ya kai hannu gurin yana dariya, Abu ya matso kusada Na'iman yace "Anty this time zaku koma nikuma zan tafi, guess qasar da zan tafi karatun" kafin Na'ima ta amsa Mami tace "Muje sai mun huta tukunna ayi maga

nganun" sai Nafisa tace "Mami Ina Yaya Faruk fa" Na'ima ma sai kallon bayan su take tana duban inda zata ga bullowarsa...

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 44

Mami tace "Aikine yadan riqe Yayan naku, amma Abban ku zai taho gobe dag

a Toronto" sai Nafisa ta ciro wayanta daga jaka tace "Let me call him, ya mana alkawarin zuwa fa" Na'ima tace "Eh fa" Al'ameen ya kalli Mami yace "Mami nidai zan koma, ba ta mu suke ba" sai Na'ima tayi saurin qarasawa garesa tace "Haba dai, munyi murna sos

ai mana, kawo jakan naka in riqe maka" Mami tayi murmushi tana kallon Na'ima, aranta tanajin dadin ganin yanzu tafara zama lively ba kaman da ba, Al'ameen na murmushi yace "Wasa fa nakeyi Anty, ki bari zan riqe" da haka Mami ta riqo hannun su jafar tace su

tafi mota, har sannan Nafisa tanata trying line din Faruk baya tafiya, suna isa gurin motan Al'ameen yace "Ya Ahmad yana qasarnan ne, wannan kamar irin rides dinsa" Mami dake kallon motan tace "Nafisa motan waye wannan, ina naku?" Nafisa da ta zagaya daya

n side din motan tace "Na Yaya Ahmad ne Mami, tamu tana can Oxford" sai Mami ta gyada kai tace "Toh muje" sai ta juya gurin boys din tace "Al'ameen yi sauri ku saka kayannan da Allah, inason mu qarasa in huta, tsk zaman jirgi ko cin rai" su  Na'ima na dan

dariya suka shiga, sai da Al'ameen da Abu suka gama saka kayan a boot sannan suka shiga gaban motan suma, dan this time

Al'ameen ne ya karbi driving din,  suna kan hanyar tafiya Mami tace su kaita masauqi tukunna sai ta huta zasuje gidan Anty Amnahn, wani

babban Hotel suka kama dan Abba bashida gida a England sai Canada, har 'yan'uwansa su Baba da Daddy ma haka kasancewan familyn sun rayu a Canada sosai sai ya zamto kowannensu yanada gidan kansa acan, babban daki su Mami suka kama harda falo aciki amma su A

l'ameen sun kama nasu daban kusada na Mamin dan washegari zasu wuce Oxford kasancewan a kwana na biyun ne ceremony din, Mami ta sa sun taho da wurin ne dan taga kintsawan yaran nata tukunna, anan falon suka zauna dama tun shigowansu Nafisa tayi ordern abin

ci, madadin su ci a dining area dake falon sai suka zauna nan qasa kan babban carpet dukansu sunacin abincin, sai da suka gama suka tattare wajen , Nafisa na kurban Apple juice tace "Mami kun taho mana da gyadan da Lantana tace zata mana?" Al'ameen yace "H

ar nima tamin na tafiya" Nafisa ta hararesa tace "Ba dai acikin namu ka diba ba ko?" Abu yana dan dariya yace "Kema kinsan sai mun debi rabonm ai" ai nan suka hau musun da suka saba Mami na jinsu ko ta kulasu sai ta kalli Na'ima dake zaune gefenta dan twin

s sun samu su Al'ameen kuma, hannu ta kai taja dankwalin Na'iman tace "Habibiti ya baki gyara gashin naki ba, bakuje salon bane?" Na'ima tace "Dama mukace sai gobe zamuyi in munje Oxford" sai Mami ta gyada kai tace "Ga kayan naku da zaku saka din can a jak

a, in kun huta sai ku duba" Na'ima tace "Mungode Mami" murmushi Mami tayi sannan tace "Ya rayuwan makarantan, babu wani matsala dai ko?" ta amsa da "Babu komai Mami" sai Nafisa ta kalli Mami tace "Mami wai su Mamma zasuzo yau suma?" tace "In sha Allah, ca

n gidan Ahmad zasu sauqa tace min, zuwa anjima kuje ku gaisheta, saboda ku tazo itama"...

Kafin Mami suje gidan Anty Amnah sai ga ta bayan magrib ta faka motanta a bakin hotel din kuwa, da fara'anta suka yi hug da Mami da ta shigo falon, nan suka fara gai

suwan yaushe gamo, saida suka gama gaisuwan tace "Su Mamma ma sun iso munyi waya" Mami tace "Yanzu nagama waya da ita fa" sai Anty Amnah tace "In Allah ya kaimu goben zanje suma mu gaisa yanzu asibiti zan wuce" Nafisa tace "Anty ki bar twins su kwana anan

toh" tace "Gaku gasu ai ina zan kaisu" aikuwa jafar ya hau tsallen murna Na'ima na dariya, bayan tafiyanta sai Mami tace su shirya sai su kira su Al'ameen suje can gidan Ahmad din tare itama tanason tayi bacci tukunna, ahanya Nafisa tace su tsaya su sayi d

onuts da ice cream, aikuwa da ciye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login