Showing 21001 words to 24000 words out of 121625 words
su Na'ima ya qare suka fara shirye shiryen komawa makaranta, duk wani abu da zasu buqata 'yan qananu qananu na amfanin yau da kullum Mami ta hada musu, bawani shopping sukayi ba don acan din babu abunda suka rasa.
Dawowar da Na'ima taji b
ataso sai akasin hakan ya faru, batayi tsammanin zuwanta gidan zai saka mata nutsuwa mai tarin yawa ba wanda har zataji batason komawa England ba, sai dai tasani komawanta school din yazama dole shiyasa ta ke ture iren iren tunanin nan daga ranta.
Zaune
suke a main falon gidan da yamma, Na'ima dake sanye cikin boubou mara nauyi tana zaune qasa a gefen Mami nan kan carpet tana tayata ware
wasu kaya a leda da Mamin ta aiki driver ya siyo safiyar ranan, sai Mami ta ciro wani expensive air freshener ta miqaw
a Na'ima tace "Habibti sa muku wannan cikin kayanku zai muku amfani" karba Na'ima tayi tace "Toh" ta ajiyeshi gefenta a kan carpet, Nafisa ta dan dago daga kwancen da take akan kujera tace "Mami duk munadasu fa" sai Mami ta kalleta tace "Wai da nace ku qar
a akan nakun" Nafisa ta qarasa miqewa zaune tace "Mami kayan zasu mana yawa fa" Mami ta juya gun Na'ima tace "Habibti barshi toh" Na'ima tace "A'a Mami munaso, mungode" Mami tace "To ke kadai zaki rinqa amfani dashi kar naji kin bata, tunda ita ba'a mata g
waninta" sai Nafisa ta fara dariya tace "Kiyi hakuri Mami" tace "Ke kika sani, yauwa nasa Lantana ta siyo muku kuka da busasshen kubewa sannan ta hado da daddawa mai dadi dan nacan basa sarrafashi me kyau" bude baki Nafisa tayi saura kadan Na'ima ta kwashe
da dariya sai ta dan kauda kanta tana murmushi, Nafisa tace "Mami daddawa fa..wallahi warinsa duk cikin jirgin nan sai kowa yaji" Mami tadan tsaya kallon Nafisan, dan turo baki Nafisa tayi alamun shagwaba ta koma ta kwanta akan kujeran tana gyara skin fac
e mask din da ta saka, Mami ta juya ta kalli Na'ima tace "Bakwa yin tuwo ne Na'ima?" sai Na'ima tayi saurin jijjaga kai alaman A'a, tayi murmushi tana dan kallon gefen Nafisan tace "Munayi Mami"
Faruk ne ya shigo cikin qananun kaya bai dade da dawowa dag
a gurin aiki ba, ya zauna nan falon shima, bayan sun gaisa Nafisa tace "Yaya kaji wai daddawa Mami zata bamu mu sa cikin kaya mutafi dashi" Faruk ya danyi dariya yace "Daddawa kuma?" Na'ima tayi murmushi, sai Mami tace "Ni tambayata anan shine, basa dafa t
uwo ne ko me?" Faruk yace "Mami inkinga fridge din yaran nan da naje last time, inaga sai kin kai hannu a kowaccensu, fast food kawai suke dirkawa cikinsu" Mami ta dan bude baki sai ta juya ta kalli Na'ima tace "Harda ke Habibti? naga kuma tuwon yana cikin
favorite dishes dinki" Na'ima tayi saurin gyada kanta tace "Allah Mami muna dafawa time to time, amma miyan ganye" sai Mami ta kada kai tace "Ya muku kyau, nasan kuma Baby ce shugaba, da Abban ku ya siya muku mota kurinqa uzurirrika da ita bakwa zuwa shop
ping na kayan abincin ne ko me?" Nafisa tace "Wallahi muna zuwa shopping din Mami" Mami ta harareta tace "Na kayan kwalliya da fata ba, my friend shut up, kin wani maka leda a fuska" Faruk dake zaune ya kada kai shima yana murmushi sai Nafisa takai hannu t
ana gyara facial mask din nata tana dan dariya itama, Mami ta sake kallon Na'ima tace "Na'ima ku rinka yin abinci me kyau kunaci banason zama da yunwa, ko baby bataje siyo kayan ba ke kirinqa zuwa kina siyowa inyaso in kin dafa ma karki bata" Nafisa tayi d
ariya tace "Na'ima sarkin karatun kike bawa saqon nan Mami" Mami tace "Nidai na fada muku, meye kuma na rayuwa da fast food da lafiyanku da komai ku ba kutare ba, banason haka kuna jina ?" suka amsa da "Toh" sai Mami tace da Faruk "Kuma fa tsaf nake hadawa
Al'ameen daddawan in qulle masa ya tafi da ita Toronto baya wani zancen wari" Faruk yace "Al'ameen kikace Mami ba mai bakin rezan nan ba" Nafisa da Na'ima suka kama dariya...
Ana gobe zasu tafi Na'ima na tsaye gaban madubi a dakin Nafisan tana tattare
mata mayukan da zata koma dasu, wasu oil ta dauka ta juya gurin Nafisa dake zaune kan gado hannunta da waya, tace "Zaki koma da wannan?" Nafisa ta dago kai ta kalle ta tace "A'a inada irin wannan acan" sai ta maida kanta kan wayan ta cigaba da dannawa.
De
ban wasu mayukan Na'ima tayi a hannunta ta nufi gurin akwatin Nafisan da take mata arranging kayan aciki tace "Har zamu koma baki hadu da Umar ba Nafee, meya faru ne?" Nafisa ta ajiye wayan hannunta tana kallon Na'iman tace "We broke up since" Na'ima na ar
ranging kayan cikin akwati
ta dago kai ta kalleta tace "You're taking a break dai, ba dai break up ba" Nafisa ta gyada kafada tace "Dagaske I'm done with that guy kuma, i need my sanity, it's high time infara prioritizing peace of mind dina nima" Na'ima da
i sai kallonta take sanin it's a big decision for her, aranta tana ayyano yanda Nafisan keda kyau, gata, kudi amma sai Allah bai sa mata sa'a akan soyayya ba, namijin da bai kai ba yake juya zuciyar kawartata son ransa.. Miqewa tayi ta zauna kusada Nafisan
cikin kwantar da murya tace "But are you okay with this decision?" Nafisa ta gyada kai tace "Tunda mukayi fadan nan nayi blocking dinsa, he makes no efforts akan gyara relationship din, zanyi ta bata lokaci na ne akan someone that will not make effort to
have me neh Naima?" sai Na'ima tadan riqe hannunta tace "It's okay...Ina bayan duk abunda kikeso ko kikayi deciding..in Umar ba alkhairy bane a cikin rayuwanki a sannu Allah zai kawo wanda yafishi, the one that will make the most effort to love you earnest
ly" Nafisa tayi murmushi tana riqe da hannun Na'iman tace "Thank you sis, you know I'm grateful to have you in my life right?" Na'ima tayi murmushi tace "Me too Nafee" sai ta miqe ta kama kunkumi tafara bin dakin da kallo tace "Saura me kuma zan hada miki,
banason sai mun koma ki fara mitan bakiga wasu abubuwanki ba" Nafisa tayi 'yar dariya ta koma ta kwanta tace "Toh mummy Na'ima,nkin sakamin inner wears din" Na'ima ta gyada kai ta sake komawa bakin madubi tana duban ko akwai abunda zata qara dauka...
W
ashegari ya kasance flight din sha dayan safe garesu, dawuri suka tashi kasancewan Na'ima anan dakin Nafisan ta kwana yasa bayan sun idarda sallah suka wuce dakin Mami tare.
Zaune suka sameta kan sallaya dan yawanci in Abba yatafi masallaci ita dakinta ta
ke dawowa tayi nata sallan..bayan sun gaisa Mami tace "Kun gama shirya kayan naku dai ko, dan banason mantuwa" Na'ima tace "Eh Mami in sha Allah" nan suka zauna tare da Mamin sukayi azhkar dinsu da karatun qur'ani, Mami na musu nasiha akan makarantan daza
su koma.....Karfe goma saura suka shiga falon Abba, sun sameshi zaune kan kujera hannunsa riqe da cup din tea yana hira ya samarin gidan, Na'ima ce ta fara zama a qasa nan kan carpet sannan Nafisa ta bi bayanta suka gaishe da Abban, yana murmushi ya amsa g
aisuwan sannan yace "Yaran Abba kun shirya ko" suka amsa a sanyaye, Abba ya sake cewa "Toh, Allah ya kaiku lafiya, Allah ya bada sa'an karatu" suka amsa da Amin, Abba ya cigaba.."Banason wasa, ku maida hankali akan ibadunku da karatu, I'm very proud of how
hard kuke maida hankali ga karatun amma ku qara himma, sannan a batun ibada kuma nasan indai akan tarbiyan da muka baku ne banida haufi akan kuna maida hankali, Amma tunda ba'a gabanmu kuke ba inason kuji tsoron Allah ku maida hankali akan sallolinku, All
ah ya muku albarka.. we'll surely missed you" kasa amsawa Nafisa tayi ta miqe ta qarasa gurin Abban tafara kuka tana riqe hannunsa, ajiye tea cup din yayi ya bude mata hannunsa ta fada jikinsa tana kuka, yana dan bubbuga bayanta yace "Saura kadan ai daught
er, besides zamuzo celebrating gamawanku ai" , idon Na'ima itama ya kawo hawaye tananan zaunen, Mami dake zaune kan kujera a gefe ta bude nata hannun tace "Zo Habibti" tashi Na'ima tayi ta qarasa gurin Mamin itama ta shige jikinta tana hawaye, barin jikin
Abba Nafisa tayi ta koma jikin Mami itama tana sake wani kukan, Al'ameen da Abubakar suka koma gurin Mamin suka tsaya jikinsu duk yayi sanyi, Faruk yace "Kukan nan ya isa ku tashi mutafi kafin lokaci ya qure" suka dago daga jikin Mamin tana goge musu haway
en tace "Saura kadan fa yarana, ku maida hankali kunji,
sannan ko menene yafaru ku kiramu, it's just a call away" suka amsa da "Toh Mami".
Haka su Na'ima sukayi sallama da iyayen nasu cikin sanyin jiki, Faruk ya tisa qeyarsu mota, maigadin gidan ne ya q
araso ya taya su Al'ameen saka kayansu a booth, tare suka tafi dasu Abubakar airport din suka bar Mamin da Abba nan tsaye bakin entrance din gidan suna daga musu hannu cikin sanyin jiki.
Zaune suke a waiting lounge na Airport din suna jiran lokacin tash
in jirginsu yayi, Nafisa tace "Abu please siyo mana abun tabawa, banason zaman shiru" miqewa Abubakar yayi ta sake cewa "Iced coffee please" ya tambayeta flavor din da takeso ta fada masa sai ya juya gurin Na'ima itama ta fada masa kalan wanda takeso, miqe
wa Al'ameen yayi suka tafi siyowa tare.
Sunanan zaune Na'ima ta hango shigowar su Ahmad gurin shida Adam kafadarsa rataye da jaka while Adam jaye da qaramin akwati, sai Laila dake biye dasu itama, kauda kai Na'ima tayi daga kallonsu,
Faruk ne ya fara
miqewa ya isa wajensun yana miqa musu hannu sukayi musabaha sannan su Na'iman suka miqe suma, Nafisa tace "Ita kuma wannan me kama da mayun ko meye na biyosu airport oho" Na'ima na jinta bata ce komai ba suka qarasa wajen da su Ahmad din suke tsaye, gaishe
su sukayi Ahmad ya amsa yana kallon Na'ima wadda itama yau tayi nata jarumtar ta kallesa, amma baifi na few seconds ba ta dauke idonta jin yanayinta na canjawa sai ta juya tana kallon Laila dake kallonta itama, samun kanta tayi da qin saka mata gaisuwa ta
kuma dauke kai... Adam yace "Yan makaranta, za'a koma kenan" Nafisa tace "Wallahi kuwa Yaya, kuma London din zaku je ne?" Adam ya nuna Ahmad daya maida hankalinsa kan waya yace "Ga mai tafiyan nan ai" Nafisa ta kalli Ahmad tace "Ashe flight dinmu daya Yaya
" sai Ahmad ya dago kansa daga danna wayan, cikin nutsuwa yace "It seems so..kuma flight din 11 dinne?" Nafisa ta gyada kai tace "Eh" sannan ta juya ta na kallon Laila, in a mocking way tace "Hajiya Laila..kema London din kika nufa ne?" A daqile Laila tace
"A'a" tana dan qara matsawa kusa da Ahmad, Na'ima na kallonsu... kallonta Ahmad yayi suka hada ido sai taga yadan matsa daga kusa da Laila still bai daina kallon idanunta ba, Na'ima ta kauda kanta jin zuciyarta namata wani iri sai ta koma kallon mutanen d
ake zirga zirga acikin Airport din.
Su Abubakar ne suka qaraso wajen hannunsu riqe da iced coffee din, Adam yace "Wannan kuma fa, nasu waye?" kafin Nafisa ta karba sai Laila ta rigata miqa hannu ta karbi duka cups biyun dake hannun Abubakar tace "Abunda
naketa craving this days..thanks" Nafisa ta dan harari Lailan sannan ta karbi na hannun Al'ameen, Abubakar ne yace "Anty Laila ki riqe nawan amma vanilla flavor din na Anty Na'ima ne" Laila tace "Oh sorry" tareda miqawa Na'iman, sai Na'ima ta miqa hannu a
mma kafin ta karba Laila ta sake mata shi a jikin ta, nan iced coffee din ya kware gaba daya a jikin brown abayan Na'ima, baya tayi da sauri tace "Bismillah" ta riqe daidai gurin da ya zuban gashi har gyalenta ya taba, Faruk ya taka zai je gurinta sai gani
n Ahmad yayi ya rigashi isa, kowa daskarewa yayi nan tsaye, Ahmad ya kamo dan bakin gyalen nata daidai inda shima ya tabun, cikin kwantar da murya yace "Are you Okay?" gyada kai kawai Na'ima tayi, sai Ahmad ya juyo ransa adan bace yace da Laila "Are you bl
ind?" Laila ta wani juya kai tace "To ai bansani ba" Nafisa ta harareta sannan ta isa
gurin Na'iman ta ciro hanky daga jakanta dake sakale a kafadanta ta fara goge mata jikin rigan..Sai sannan su Abubakar suka nufi gurin Na'ima suna mata sannu, Faruk dai n
a tsaye shida Adam.
Adam sai kallon abokin nasa yake da dan mamaki, Nafisa na goge wa Na'iman jiki tace "Muje restroom a dan wanke" ta kalli Ahmad tace "Yaya bari muje restroom kawai" Gyada kai Ahmad yayi ya sake bakin gyalen Na'ima suka wuce, Laila kaman
ta fashe haka taji a wannan moment din, bata taba zaton Ahmad din zai nufi gurin Na'ima ba, atake abubuwa dayawa suka darsu mata acikin rai.....
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 15
Tsaye suke a restroom din gaban sink me madubi, Nafisa
ta kunna famfo ta tara hanky din sannan ta cigaba da goge jikin rigan Na'ima, itadai Na'ima ta riqe rigan tana kallon yanda Nafisan ke goge mata, ranta in yayi dubu to ya baci a wannan lokacin, dan itadai tasan miqa hannun da tayi beci ace hannunta ne bey
i reaching to Laila ba har coffee din ya kware mata a jiki, tarasa me ta tsarewa yarinyar da ta fara sakota a gaba haka, tana cikin wannan tunanin taji Nafisa tayi tsuka me karfi tace "Narasa ta ina Laila ke tunani wani lokaci, ita duk wani abu da zatayi c
ikin rashin da'a yinsa take kamar ba mace ba, dan ko kaffara bazan yi ba da gangan ta juye miki a jiki, kuma wallahi kinji nayi rantsuwa..bashi taci"
Na'ima tadanyi murmushi da iyakacin sa leban ta tace "Ki barta Nafisa, yaushe ma zata sake ganina?" sai N
afisa ta dago ta kalli Na'iman tace "Ai batada hankali ne shiyasa zan koya mata" Na'ima ta girgiza kai tace "A'a wallahi ki barta Nafisa" Ahaka suka gama goge gurin da coffee din ya taba suka fito tare daga restroom din.
Komawansu gurin 'yan'uwan nasu bas
u samu Laila ba a wajen sai mazan dake tsaye still, dan barinsu Na'ima wajen takaici ya ishi Laila anan tsaye ta musu sallama inda ba wanda ya kulata cikin su sai Adam da Al'ameen, haka ta juya cikin qunan rai ta bar gurin ta koma gida..
Isowarsu Na'ima g
urin Faruk ya dan matso garesu yace da ita "Are you sure you're okay Na'ima?" tayi murmushi ta gyada kanta tace "Ya gogu ai Yaya" Faruk yace "But you're drenched ai, ko zaki koma a chanja kayan" Na'ima ta sake girgiza kai tace "A'a babu komai zai bushe a
hankali" Ahmad dai dan kallonsu yake baice komai ba, Adam yace "Sorry Na'ima" ta gyada kai tana murmushi tace "Laa bakomai dai Yaya"... iced coffee din da kowa bai sha ba kenan aka barshi anan waiting area kan kujera.
Sunanan tsaye bada jimawa ba akayi ca
lling jirginsu, sallama suka farayi da juna, Nafisa tayi hugging siblings din nata da daddaya, Na'ima na tsaye tana kallonsu jikinta duk a sanyaye, kasa daurewa Abubakar yayi sai da ya matso gurinta yayi mata hug din, yace "Anty na..we will miss you" tadan
shafa bayansa tana dan dariyan qarfin hali ta kasa magana.
Ahaka sukayi sallama Ahmad yayi gaba su Na'ima na biye dashi a baya janye da boxes dinsu, shigarsu cikin jirgin suka ga shi yayi hanyan kofan da zai sada mutum da first class, qarasawa seat dinsu
suka yi dake business class..bayan sun ajiye kayan nasu a sama Na'ima ta zauna a seat din jikin window ta fara maqala seatbelt dinta..
Basuyi nisa da tashi ba wata waitress tazo seat dinsu ta tsaya ta kalli Na'ima tace "Are you Na'ima?" dan gyada kai Na'
ima tayi tana yiwa
waitress din kallon tambaya while Nafisa ta amsa da "Yes..she is" sai ta miqo wa Na'ima jacket din hannunta wanda qamshinsa duk saida ya cika musu hanci, tace "Here...someome from other side of the plane send me to give you this" kallon
waitress din Na'ima ta tsaya yi bata karbi jacket din ba, sanin Ahmad ne ya aiko wa Na'iman jacket din jikinsa ganin jikinta a dan jiqe earlier yasa Nafisa karban jacket din daga hannun waitress din, tayi murmushi tace "Thank you Miss" murmushi waitress di
n tayi ta juya tabar gurin su, Na'ima ta juya kanta tana kallon window batace komai, kawai ji tayi Nafisa na lulluba mata jacket din a jikinta sai tayi saurin juyawa tana kallon Nafisan dake murmushi kamar bakin ta ze yanke, hannunta tasa tafara ture jacke
t din daga jikinta itama tace "Ni nace miki inaso ne, ke ki lullaba ajikin naki mana" dan dariya Nafisa tayi tace "To ai bani na jiqe ba Baby Na'ima" sai Na'ima ta harareta tace "Wace babyn?" Nafisa ta dan daga gira tace "Ke mana... gashinan saboda riganki
ya jiqe ana lallabaki harda jacket" kawai Na'ima ta tsaya kallonta takasa magana ma, dariya Nafisa tayi itama tana kallon nata tace "Kinga wani instinct dana gani gurin yaya Ahmad yau, girl you have alot to gist me and i mean everything" sai Na'ima ta sak
e juya kanta tace "Kin shiga uku da wannan mind din naki Nafisa, ni babu komai tsakaninmu" Nafisa ta cigaba da lullaba mata jacket din tace "Naji..yanzu dai let's get you warm baby" Na'ima ta sake buge hannunta tana dan murmushi tace "Zan miki ba dadi Nafi
sa"
Nafisa na dariya ta sake cewa "Baby"
Haka ta hakura Nafisa ta lulluba mata jacket din