Showing 9001 words to 12000 words out of 121625 words

Chapter 4 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

15

fara'a yace "Anty nah oyoyo" tana murmushi ta shafa kansa tace "Kaima oyoyo" da haka suka zaunaa falon cikin w

alwala aka fara hiran yaushe gamo.

Mami ta fito daga kitchen dinda ke babban falon  hannunta riqe da food flask tayi gurin dinning area tana jerashi jikin sauran 'yan'uwansa akan table, sai ta juyo garesu tace "Abar surutun haka, kuzo kuci abinci tukunna"

sai suka miqe dukansu suka qarasa dining din, bayan sunyi settling Nafisa tace "Mami, Abba fa??" tace "Yana gurin aiki ai kinsani, bakuyi waya bane" Nafisa ta janyo coolern dataga favorite dish dinta ta fara zubawa a plate tace "Yacemin he'll be at home w

hen we arrive" sai Mami tace "Bai baro gurin aikin ba tukunna" ta juya tana maida hankalinta kan Na'ima data fara cin abincin da ta zuba, tace "Habibti ki dudduba coolers din ko akwai favorite dinki" Nafisa tace "Tuwon da ta zuba shine favorite dinta Mami"

Abubakar juya yana kallon Na'ima yace "tuwo kuma Anty" Na'ima ta gyada kai sannan tace "Ina yah faruk fa" Al'ameen yace "Wannan ya fice aiki tun safe ai" Mami ta qara da "Sai dare ma zai dawo halan, yace they have a lot of works" Na'ima ta gyada kai tacig

aba da cin abincinta.

Daren ranan bayan Abba yadawo yaci abinci ya huta suka je gaishesa cikin babban falonsa, bayan sun shiga da sallama Nafisa ta qarasa kusa dashi ta zauna tana fara'a tace "Abbaa" shima cikin fara'a ya amsa da "Yaran Abba, kun dawo l

afiya?" Na'ima ta qaraso zata zauna nan qasa yace "Tashi ki zauna a kujera daughter"  tana dan murmushi tace "Nan yayi" ya sake insisting ta tashi din sannan ta tashin ta zauna a wani kujera dan nesa dasu, Mami ce ta shigo falon hannunta riqe da tray na te

a flask da cups

akai Na'ima ta miqe ta karba ta qarasa  ta ajiye nan table din dake gaban Abban sannan ta koma ta zauna, sai Mamin ta wuce dakin Abban dake nan falon yin wani uzurin.

Gaishe da Abban sukayi ya amsa yana tambayansu karatun nasu

Nafisa na t

siyaya masa tea din a cup tace "Abba abokinka dinnan has been very helpful a lot, watanni biyu ma da suka wuce shi yakaimu London gidan anty Amnah" Mami ta fito daga dakin ta qaraso ta zauna nan gefensa itama, Abban yace "Haka yakamata ai, kuma yana bani r

eport ai yace kuna qoqarin karatun ba laifi" ya juya yana kallon Na'ima yace "Haka ko Na'ima"  ta amsa da "Eh Abba" Mami tace "Nafisa zaka tambaya dan Na'ima bani da haufin tana karatu" murmushi Na'ima tayi tace "Nafisa tana karatu fa sosai Mami" sai Nafis

an tayi saurin amsawa da "Sosai sosai ma" Atare Abba da Mami suka juya suna kallonta, sai Abba yayi murmushi yana kai cup din shayin bakinsa while Mami ta girgiza kai ita da Na'ima suka dan yi dariya sanin halinta.

Sunanan falon suna hira Al'ameen yashigo

falon da sallama yayi settling shima a kujera ya dan duqar da kanshi yace "Barka da dare Abba" sai Abba ya amsa then followed by Abubakar shima ya qaraso ya zauna kusada Al'ameen din shima ya gaishe da Abba.

Har kusan karfe tara suka kai suna hira, zuwa

sannan Na'ima ta sake anata hiran da ita jefi jefi take sa baki, Nafisa na bawa iyayen nasu labari game da rayuwarsu a England din Na'ima na tayata kadan kadan, by then sun sauqo qasa itada Nafisa da Abubakar kan babban carpet din dake shimfide a falon ha

nnunsu riqe da kofin shayin da Nafisa ta zuba musu daga cikin na Abban.

Faruk ne yayi sallama ya shigo cikin sanyi alamun gajiya a tattare dashi, yan'uwan na amsa masa tareda sannu, Nafisa ta ajiye tea din ta miqe tana riqo hannunsa yana fara'a yace "Yan

gatan Mami sun dawo kenan"  ya juya ya kalli Na'ima yace "Habibtin mami, kun iso lafiya" tana murmushi ta amsa da "Lafiya Yaya" suka gaisheshi gaba daya ya amsa tareda zama nan qasan carpet din shima yana me gaishe da iyayen nasa, suka amsa Mami na tambaya

nshi gajiyan aiki  Abba yace "Arinqa sararawa jiki da brain din dai babana" Faruk ya dan shafa kansa yace "Abba aikin ne these days suna buqatan lokaci sosai" sai Abba yace "Allah ya bada sa'a" ya amsa da Amin Mami ta tambayesa ko yaci abinci ya girgiza ka

i, nan falon Nafisa ta kawo masa abincin yanaci aka cigaba da hiran dashi cikin raha.  

Cikin walwala da fahimtar juna iyayen ke gudanar da hiran tsakaninsu da yaran nasu, wanda hakan yasa yaran suke bude cikinsu openly suna fadan abunda ke mind dinsu wa

jen iyayen, idan fannin gyara ne take iyayen suke gyara musu cikin lumana, idan kuma na raha ne suma ayi dariyan dasu.

And for that moment.

Na'ima knew..This is home.

These people right here.

Are like missing piece of her heart.

And she won't trade th

em for anything.

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa





Chapter 08

Washegari....

Na'ima ce zaune kan sallaya bayan ta idar da sallahn asuba hannunta riqe da qaramin carbi tana azkhar, bayan ta gama ta dauki Quran din gabanta ta miqe ta kaish

i ma'ajiyansa sannan ta nade sallayan, bata cire hijab dinta da ta dora kan dogon kayan baccin jikinta ba ta fice daga dakin ta shiga falon mami dake nan kusa da nata dakin, ta samu Mami zaune itama bisa sallaya tana azkhar

Mamin ta dago kai tace "Na'ima

kin tashi" cikin sanyi tace "Eh" ta qaraso ta zauna tace "Ina kwana Mami" Mami ta amsa da "Lafiya Habibti,.how was your night?" tace "Alhamdulillah" suna nan zaune Nafisa ta shigo itama sanye da hijab ta zauna kusa da Mami ta gaishe ta sannan ta juya suka

gaisa da Na'ima, Mami na kallon fuksan Nafisan tace "Baby, meya samu idonki haka?" dan wutan falon tar yake a kunne hakan yasa ta ga idon Nafisan wanda yadan kumbura, sai Nafisa tafara hamma tace "Bacci ne bai isheni ba Mami"  Mamin tace "Aikuwa kije kiyi

dan ga idonki nan ya nuna" da haka Nafisa ta miqe ta shige dakin Mamin, sanin Mami zata dade zaune nan bata tashi ba yasa Na'ima miqewa ta shige dakin itama, ta qarasa kan gadon Mami da Nafisa ke kai ta kwanta tana jawo bargon, sai Nafisa ta juyo tace "Kin

san Allah, har wani banging kaina yake" Na'ima ta dan kalleta tace "Sannu sis, halan bakiyi bacci da wuri ba jiya" ta amsa da "Fada mukayi da mutumin, in na tashi zakisha labari" sai Na'ima tace "Kuma dai, yi baccin to" ta gyada kai ta juya tana gyara kwan

ciyanta, da haka suka koma wani baccin.

Sai wajen qarfe takwas Na'ima ta tashi ta fita daga dakin tabar Nafisa dake bacci, sanin Mami na bangaren Abba yasa ta wuce nata dakin ta shiga wanka, bayan ta fito ta nutsu tayi shafe shafenta ta shirya ta sauqa ba

bban falon dake downstairs, hango faruk tayi zaune a dining yana breakfast shi kadai hannunsa riqe da waya yana dannawa, ta qarasa wajensa da murmushinta, ya dago kansa daga abunda yakeyi yace "Habibtin Mami harkin tashi" taja kujera daya ta zauna tace "Eh

Yah Faruk ba dai har fita zakayi ba" ya gyada kai "Yeah, I'm swamp up with work at office these days wlh" tace "Ayya, Allah ya bada sa'a" ya amsa da Amin sannan yace "Kun sake zuwa kallon wani match din keda Nafisan kuwa?" Kafin ta amsa taji Nafisan dake

bayansu tana tahowa tace "Me Nafisa tayi da sassafen nan Yah Faruk" ta qaraso taja kujera itama sai Faruk yace "Laifi kikayi babba" Na'ima na murmushi tace "He was asking ko mun sake zuwa kallon wani football match din" Nafisa ta kallesa tace "Can you beli

eve the tickets were sold out within 24 hours" yace "May be baki siya da wuri bane, first hours akafi samun tickets daman"  zatayi magana aka kirashi video call a WhatsApp dinsa, sai ya dan daga mata hannu yace let me take this, ya dauka yana kallon fuskan

wanda ke cikin wayan yace "Good morning Yaya" ta daya bangaren Ahmad ya amsa cikin deep voice dinsa "Morning Faruk, ya mutan gidan?" Faruk yace "Alhamdulillah" sai Ahmad yace "Good...I've send you some papers via email, I need your review on them" Faruk n

a kallonsa ya gyada kai, yace "Sure, ba matsala Yaya" sai Nafisa tazo bayan Faruk tasako kanta tace "Good morning Yaya" Ahmad ya amsa "Lafiya Nafisa, yaushe kika dawo?" tace "Jiya, yasu Mamma?" Na'ima dai na sauraronsu tana binsu da kallo, saita samu kanta

da sauraron na cikin wayan jin yanayin accent dinsa that was so thick and it sounds British but not that deep British.

Bayan sun gama gaisawa Ahmad ya maida hankalinsa kan Faruk yace "Please do take a good look on them I need your answers, karka dau lok

aci" Faruk yayi murmushi yace "in sha Allah Yaya, I'll drop by tomorrow to give you the feedback" Ahmad yace "See you then,thanks Man" da haka sukayi sallama Nafisa na kallon Faruk tace "Wai yadawo gari daman" Faruk yace "Ya rigaku dawowa ma" tace "Ya Adam

fa?" ya amsa da "Wannan yana gari da dadewa ma ai, what's with the questions?" tadan daga kafada tace "I just want to know ne" sai Na'ima ta miqe ta wuce kitchen tabarsu nan suna magana.

Shiganta kitchen tasamu lantana tana aikin hada breakfast dinsu ta

gaishe da Matar da kana ganinta kasan she's in her late 30's fuskanta cike da bille. Na'ima tace "Mama sannu da aiki, Ina kwana" Lantana ta amsa "Lafiya habibitin Mami, jiya kun dawo bananan ko" Na'ima tace "Eh mama, ya hakuri kuma Mami tace an muku rashi

" tace "wlh dai, can suleja naje, yar wata qanwata ce ta rasu, yarinya qarama da ita, jiya kwanana hudu acan" Na'ima tace "Allah sarki, Allah yasa mai ceto ce" tace "Amin Habibitin Mami, bakiga yarinyar ba kuwa fara sol kamar ke dinnan, abun dai abun tausa

yi" sai Na'ima tayi murmushi ta fara tayata aikin, suna aikin Lantana na bata labarai gameda rasuwan wanda itadai ba fahimtan wasu take ba, Nafisa ta shigo itama suka gaisa Lantana na fada mata uzurin rasuwan, bayan Nafisa ta gama nuna nata alhinin  tace "

Mama kince zaki soya mana gyada mai gishirin nan idan zamu dawo" ta qarasa maganan tana taya lantana bare maggin da zata saka a pepper soup dinda ke dahuwa akan gas cooker nan gabansu, lantana tace "aikuwa yau zan soya muku"

Nan suka kammala sauran aikin

tareda Lantana, Mami ta shigo kitchen din bayan sun gama tace "Sannu lantana, sannunku kuma" suka amsa.

Ta dauki breakfast dinsu ita da Abban ta tafi kaiwa can falonsa while su Nafisa suka kai nasu dinning Lantana na tayasu, basu jima da fara ci ba su Al

'ameen da Abubakar sukayi joining.

Bayan sun gama suka kai kayayyakin kitchen suka dauraye, don ladabtarwan Mami ne akan bakomai mai aiki zatayi musu ba, abubuwa da dama dakansu sukeyi a gidan, bayan sun gama Nafisa ta fice, sai Na'ima ta dauko plate ta

debi sauran cupcakes dinda Mami tayi musu jiyan ta wuce upstairs, dakin Nafisa ta shiga ta sameta gaban madubi zaune, sai ta tafi ta zauna kan gadon Nafisan dake gyare neatly ta ajiye snacks din hannun nata sannan tace "Oya..spill the beans, meya hadaki d

a Umar din jiya?" Nafisa ta miqe ta baro gaban madubin tadawo bakin gadon itama ta zauna tace "Sis I don't know what's wrong with Umar, bansani ba ko jealousy ne ko kuma insecurity ne yake damunsa, kai duka ma" Na'ima na kallonta tace "Amma ai so ne yasa h

akan sis" sai Nafisa tace "Ina sonsa ai nima but this is too much and i hate it with all my heart, sometimes I wonder why i stayed with him for this long and why i can't let go" Na'ima tace "I know that loop, kinsani...I know what it means to be trapped In

a loop going around without escape" sai Nafisan ta juyo tace "But...." sai kuma tayi shiru tana kallon Na'ima tarasa abunda zatace, ganin haka sai Na'ima tayi dan murmushi me ciwo tace "Shiyasa bazan taba judging dinki ba akan wannan conflict relationship

din da kuke having, the guy loves you and you do too, try and resolve things tunda kowa yasani ba iya rabuwa zakuyi ba" ta qarasa maganan tana murmushi. Nafisa ta dan harareta tareda daukan cake daya takai baki tace "Tabdi, rabuwa kai, jiya ma nace masa I

'm done yayi fushi kuma nakashe wayana" Na'ima ta jijjaga kai tana dan cin cake din itama tace "Nidai banason ku rabu, Ina laifin mai kishinka Nafisa?" sai Nafisa ta miqe ta koma gaban madubin tafara cleansing fuskan ta tace " I'm serious this time" Na'ima

ta jijjaga kai tana dan dariya kawai, ta

juya ta janyo laptop din Nafisa dake kan bedside drawer ta kunna zata fara kallo.

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa





Chapter 09

A Week Later...

Na'ima ce zaune cikin dakinta akan gado, hankalinta yana kan

abunda take typing cikin laptop dinta, yau satinsu daya da dawowa gida and a lot has happened, sunje shopping, Nafisa ta jasu outing cikin gari and all other fun things, jiya ma part dinsu Faruk dake gefen main building din gidan suka wuni suna game din Ps

wanda har da Al'ameen da Abubakar din sukayi.

Nafisa ce ta shigo dakin hannun ta riqe da leda ta miqa mata, karba Na'ima tayi tana duban cikin ledan taga sweets da chocolates masu yawa, Nafisa tace "karki fado sunana idan mami ta kamaki kinasha wlh" Na'i

ma tayi dariya sanin Mami ta hanasu yawan shan kayan zaqin, farkon dawowansu ta barsu suna sha amma ganin suna iya shanye chocolate kusan ashirin a zama daya tace bata so, kuma karsu sake siyo kayan zaqi masu yawa a gidan.

Nafisa na tsayen tace "Ki shirya

muje gurin fitting dinnan Meerah tana ta kirana a waya" sai Na'ima tayi mata questioning look tace "Fitting kuma Nafee?" ta amsa da "Eh na gown din da zamu saka wajen event din bikin Salma mana" Na'ima tace "Nifa bazanje event ba Nafisa" zama Nafisan tay

i kusa da ita tace "Meyasa? Mami ta hanaki ne?" ta jijjaga kai tace "A'a kawai bazanje bane" shiru Nafisa tayi batace komai ba har Na'ima ta maida hankalin ta kan laptop din dake kan cinyanta ta cigaba da typing, can Nafisan ta miqe ta fita sai Na'ima ta d

ago kai ta bita da kallo jikinta na sanyi.

Fitan Nafisa ta shiga falon Mami ta sameta nan zaune da Faruk suna magana, turaren wutane a gaban ta tana mixing dinsu cikin kwalba, Nafisa ta qarasa kan kujeran gefen Faruk ta zauna.

Hankalin Mami na kan abunda

take yin tace "Baby baku fara shirin fitan bane rana tana yi fa, kincemin zaku fita dazu" Faruk yace "Ina zasuje?" Nafisa tace "Dama fitting zamuje gurin Meerah na gown din event din bikin, Mami kinji wai Na'ima nacewan baza taje gurin dinnern ba" Mami ta

dago kanta tana kallonta sannan tace "Ai daman ban aika kayan events da ita ba" kafin Nafisa tayi magana Faruk ya katse ta da "Ai tafiki hankali datace bazataje ba" Nafisa tace "Haba Yah Faruk it's just an event fa" yace "Yes but Nafee kinsan kalan mijin

da Salma zata aura ai, you know who he is, yawanci guys masu ji da tashe acikin Abuja da wajenta zasu halarci event din, you can't be exposing Na'ima to that sort of places" Mami dai na sauraron fadan da Faruk yakewa Nafisan batace komai ba, sai Nafisa tac

e "but Yah Faruk i thought it's high time she starts living her life, doing the things she likes the way she wants to" Mami tace "Many things but not this nafisa, and you know things are not over yet" Nafisa na kallon Mami tayi shiru batace komai ba, sai M

ami ta cigaba "Quite sure zata je gidan bikin ta gaisa da wasu 'yan'uwan because it'll be rude of her not to, tunda komai dadewa zasu iya haduwa da ita a cikin gidan nan, but not going to parties...and that's final" cikin sanyin jiki Nafisa tace "Yes Mami"

sai ta miqe ta fice daga dakin suka bita da kallo.

Haka suka shirya akan Na'ima zata raka Nafisan gurin dinkin, ta saka black color Abaya da ta fito da haskenta da kyawunta while na Nafisan kuma maroon color, bayan sunyi sallama da Mami ta basu saqon t

oiletries da zasu biya super market su siya mata, suka fice daga gidan cikin motan Nafisan.

Bayan sun isa babban fashion store din wanda ya kasance gurin dinki, designing da kuma saida dinkakkun kaya sai suka tadda Meerahn tsaye a reception tana magana

da receptionist din nata, ganinsu Na'iman yasa ta tako garesu tana murmushi tace "Look who we have in town" ta qaraso tayi hugging din Nafisa suna fara'a sannan ta juya tayi hugging din Na'ima ta sake cewa "I've been waiting for you guys like for'everr" Na

'ima tayi murmushi dan tasan Meerah, ita tayi mata duk dinkunanta farkon zuwanta gidansu Nafisan, sai Nafisa tace "Sorry sis" Meerah na fara'a ta amsa da "Now you have to pay me double" sukayi dariya gaba daya, da haka ta jasu suka tafi fitting room din da

ya kasance a upstairs na building din, bayan tayi serving dinsu refreshments Na'ima na zaune kan resting sofa wasu staff mata guda biyu suka shigo tare da Meerah suka hau gwada Nafisa dake tsaye kan gajeran stool, sai Nafisa tace "Husna tazo kuwa?" Meerah

tace "Tazo almost a week now"

Bayan angama sukayi salla anan room din sannan suka wuce gurin aiken da mami ta musu, basu suka koma gida ba sai yamma.

Shigowarsu gidan bayan sunyi parking

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login