Showing 69001 words to 72000 words out of 121625 words
"Ta nan suka bullo kuma, lallai da mu suke zancen" Stella tace "I can't let Bilal touch her, zan iya mutuwa Chi"
tace "Meyasa zaki tada hankalinki akan wannan, kema fa kinsan abunda baze yiwu bane" dan
jijjaga kai Stella tayi tace "Sai kin ga yarinyar zaki shaida hakan Chi, i can't compete with her, duk da inada tabbacin Bilal ba sonta yake ba in fact nasani yama tsaneta sosai, amma kinsan in akwai abu daya da bariki ya koya mana shine rashin yadda full
y da namiji, wallahi bai isa yazauna da wata mace ba, wahalar da nayi akansa bazata fadi a banza ba" ...Stella bata bar gidan qanwar ta taba sai da suka gama qulle qullen yanda zasu bullowa lamarin kuma duk ba ta hanya me kyau ba...
Two months Later..
Zuwa wannan lokacin Na'ima har ta saba da rayuwan kadaici cikin gidan aurenta, sabo ne sosai ya shiga tsakaninta da Nafisa zuwa sannan, yawonsu a makaranta tare, cin abincin su tare karatunsu tare, kuma har zuwa wannan lokacin Na'ima bata samu courage di
n bayyana damuwanta ga Nafisan ba, ranar da Nafisa ta fara zuwa gidanta wuni sukayi suna hira, sukayi girki sukaci anan kitchen din ma suna raha kamar ba Na'iman da take fargaban zamanta gidan ba, tana iya qoqarinta na zuwa gaishe dasu Hajiya in anyi kwana
ki amma har zuwa lokacin basa wani dogon magana ita da Hajiya, Alhaji ne dai gamuwanta dashi baifi sau biyu ba saboda baya zaman gida sosai gashi bayan auren nasu yayi wata doguwar tafiya zuwa china wanda har sai da Hajiya ma ta bisa, a wannan haduwar nata
dashi ya bata hakurin rashin zuwan Bilal, har ya nemi tabbatar da karyar da Bilal din ya masa akan suna waya da Na'iman har ya so ta bishi can Lagos din to sai tace A'a, shi Alhaji Jin wai Na'ima tace A'a din se ya dauka akan makarantar ta ne tace haka di
n shiyasa bai ja maganar ba, amma a zahirin gaskiya ma Bilal be san Na'ima na zuwa wata makaranta ba ma, Na'ima ta amsawa Alhajin da cewa "Eh hakane" saboda batasan me zatace ba toh, dan har ranta batason dawowan Bilal Kano saboda tasan ba alkhairy ne zai
hadata dashi ba...
Ranar wata asabar Nafisa tayi alkwarin zuwa gidan Na'iman akan zasuyi karatun exams dinsu dake gabatowa, zuwa 11 na safe sai gatanan da motarta, Na'ima na bude mata qofa suka fara fara'a, Nafisa ta dago ledan hannunta dake dauke da snac
ks da sweets tace "Da guzuri na nazo, Mami bata bari insha zaqi a gida" Na'ima tayi murmushi tace "Tanada gaskiya ai, kuma bakya ciwon ciki?" Nafisa ta zuba kayan nan kan kujeran falon ta zauna itama sannan tace "Tab babu abunda yakemin, a boye nake sha in
na seta lokacin da bata kusa ai" sai Na'ima ta danyi dariya tace "Laa to sai na fallasaki" Nafisa tace "Aikuwa Mami na tambayanki sosai, yaushe zakije? kinsan na nuna mata hoton ki, da zan taho dinnan ma har Abu saida yace in gaishe da ke" Na'ima na fara'
a tace "Ina amsawa, in sha Allah zan je Nafisa" da haka suka hau hira a anan zaune falon basuyi karatun ba, sunayi sunashan chocolates din Nafisa na bata labarai suna dariya, sai da Na'ima taga lokaci na neman qurewa ta tafi kitchen dafa musu abinci, nan k
itchen din Nafisa ta biyota tafara tayata suna hira, bayan sun gama Nafisa tajiyo wayanta na ringing acan falo ta fice daukowa, zuba abincin Na'ima tayi a plates guda biyu zata kai musu falon, shiganta Falon ta ganshi tsaye ga Nafisa nan zaune waya kare ku
nnenta tana binsa da kallo tareda wacce ke bayansa, wani irin bugawa zuciyan Na'ima tayi saida plates din suka fadi daga hannunta, da sauri Nafisa ta nufi gurinta ta tsugunna zata dauke plate din tace "Lafiyanki Na'ima" idon Na'ima na kan Bilal dake kallon
ta kamar yaga mutuwar sa, qarasawa kan kujera Stella tayi ta zube alamun ta gaji tana bin Na'iman da kallo, Bilal na kallon
Na'iman ya nuna Nafisa yace "Who is this?" Kasa magana tayi jikinta na rawa Nafisan na kallonta, sai Bilal ya sake mata wani tsawan
yace "I'm talking Na'ima" murya ta na rawa tayi saurin cewa "Kawata ce Yaya" yace "Me tazo yimin a gida?" Miqewa tsaye Nafisa tayi hannunta riqe da plates din ta dan ware ido cikin mamaki sai Na'ima ta girgiza kai tace "Kayi hakuri" kallon Nafisa yayi yac
e "Get Out" sai ta tsaya kallonsa cikin ido amma data juya ta kalli Na'ima taga tayi tsuru tsuru da ita sai batace komai ba ta ajiye plates din nan qasa kusada inda abincin ya zube sannan ta nufi kujera ta dauki jakanta tana bin Stella da wani irin kallo,
cikin sanyin jiki Nafisa ta fita daga falon Na'ima na nan tsaye ta kasa bin bayanta...
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 30
Sai da Nafisa ta fita suka jiyo tashin motanta sannan Stella ta kalli Bilal tace "Baby i need water" yace "Okay" s
ai ya sake kallon Na'ima yace "Get her water and clear this mess now, you stupid" ya qarasa maganan tareda nuna mata abincin dake zube nan qasan, gyada kai Na'ima tayi sannan juya ta koma kitchen din, sai sannan Bilal ya zauna nan kan kujeran kusada Stella
yace "Sorry Baby, me kikeson ci?" tadan kwanto jikinsa tareda kashe murya tace "Something light" Na'ima ce ta fito daga kitchen din hannunta riqe da bottle water da drinks dan dama Sufi ke siyo mata duk wani kayan buqatu na gidan tareda umarnin Alhaji, qa
rasowa tayi ta ajiye musu nan kan glass table din idonta a qasa bata kallesu ba, cikin isa Bilal yace "Cook something light now" ta amsa da "Toh" still idonta na qasa, Stella na kwance jikin Bilal din sai kallonta take tana qarajin wani abu ya tsaya mata a
zuciya ganin irin kyan Na'ima'n me fusgan hankali, saida Na'ima ta zuba musu juice din a kofi sannan ta juya ta koma kitchen din tana dan gyara wuyan riganta saboda taquran datayi under their Eyes, bayan ta gama kwashe abincin qasan tana aiki a kitchen di
n tana jiyo dariyan su, da ta gama ma nan dining area ta ajiye bata kallesu ba tazo ta wucesu zata tafi dakinta, Stella har da janyo fuskan Bilal zuwa gareta tana kissing, itadai Na'ima kanta na qasa ta wucesu..Fitowan da bata sakeyi downstairs ba kenan, b
ayan tayi sallahn ta ko wanka ma bata samu yi ba ta hau gado ta zauna, Jiyo muryansu tayi sun hawo saman sai taji an bude dakin da ke facing din nata, dan bariki sai Stella taqi rufe qofan, haka Na'ima ta fara jiyo badalarsu Stella har da ihun ta, cikin sa
uri ta nufi drawer na mirro'nta ta dauko auduga tasaka a kunne sannan ta qudun dune da bargo nan kan gado tana addu'an Allah yasa kar suyi dogon zama a garin su koma inda suka fito....
Dakyar Na'ima tayi bacci saboda yanda takejin zuciyarta a wannan daren
, wayewar washegari shima kasa fita tayi, tana nan zaune aka fara buga mata qofa da karfi tayi sauran tashi ta bude, Ido hudu tayi da Bilal yana kallonta yace "Do i have to say it before you make breakfast?" Tayi saurin girgiza kai tace "Yanzu zanyi Yaya,
Ina kwana" bai amsata ba ya juya tareda banko kofar a fuskanta tana nan tsaye, sake budewa tayi ta fito tareda wuce kofar dakin nasu dake kulle ta sauqa qasa zuwa kitchen din, cikin sauri ta kammala musu breakfast din tana cikin jerawa a dining Stella ta s
auqo sanye cikin t-shirt din Bilal din da bum short, fara bude flask din tayi ta bi chips da fried egg din da wani kallo sai ta yamutse
fuska tace "Where is the tea?" Na'ima tace "Yana kitchen tukunna" sai ta juya zuciyarta na quna ta shige kitchen din, sa
ida ta zubawa Stella tea tananan zaune hakimce a dining chair, takai baki ta kurba sai tayi saurin burtsoshi daga bakinta wanda hakan yayi daidai da sauqowan Bilal, yayi saurin qarasowa yace "What happened Baby?" Stella na kyabe fuska tace "Baby what kind
of tea is this, jiya ma haka naji gishiri cikin abincin nan" karban shayin yayi ya kurba sai ya jefawa Na'ima cup din tayi baya duk da haka saida shayin ya zuba jikinta tajiyo zafinsa har cikin jikinta, bata farfado daga wannan ba taji Bilal ya sauqe mata
wani mari mai dauke ji a kunne, dafe fuskanta Na'ima tayi ta sake yin baya idonta na kawo ruwa, jikinsa har wani tsuma yake tsabar masifa yace "Dan ub*nki kashemu zakiyi, bakiji yayi daci bane" batayi magana ba kanta a qasa sai ya kai mata wani dukan a fus
kan yana cewa "Sai na rinqa repeating magana sannan zaki amsamin kenan" kuka me sauti Na'ima tafara yi tana bashi hakuri, Stella ta dauko chip daya takai baki tana kallonsu with amusement batayi magana ba, Na'ima na kuka ta koma kitchen ta dora musu wani s
hayin, da ta gama nan ta sake kawo musu suna zaune a dining din ta zuba musu sannan ta koma sama cikin sauri, kuka ta fashe dashi bayan ta shiga dakin tana tsaye, saita juya ta kalli mirror nan taga gefen fuskanta yayi ja ga lebenta na dan fitar da jini, t
ana hawaye ta dauko tissue tafara gogewa bata daina kallon kanta a madubin ba, gashi tanada lecture zuwa 11 batasan ta yanda zata fara fita daga gidan ba, dan tsoron tambayansa take kuma...
Allah ne ya taimaketa ta Jiyo muryansu a parking space can kuma
taji tashin motan nasu megadi ya bude musu gate suka fice, da saurinta ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya sai ta hau neman face mask cikin kayanta tayi sa'a kuwa tasamu..
Bayan ta rufe gidan sai ta rasa yanda zatayi da key din kawai ta baiwa megadi
tayi saurin tafiya bakin hanya dan neman abun hawa, isarta makarantar ta samu class mates din nasu suna fitowa daga hall din da za'ayi combined lecture din da nufin an samu change of venue, hango Nafisa tayi sai taga tayi saurin qarasowa wajenta tace "Na'i
ma lafiya kikayi latti, it's unlike you" ta amsa cikin sanyin murya da "Ban lura da lokacin bane" sai Nafisa ta gyada kai still tana kallonta ganinta yau kuma sanye da face mask, fara tafiya sukayi sai da sukayi nisa duk anyi gaba an barsu sai Na'ima ta ka
lli Nafisan cikin kwantar da murya tace "Nafisa Dan Allah kiyi hakuri da abunda ya faru jiya" da farko Nafisa batace komai ba sai kuma ta jefa mata tambaya tace "Wacece wadda yazo tare da ita jiyan?" juya kai Na'ima tayi idonta na kawo hawaye tace "Bansan
ta ba nima" cikin dan mamaki Nafisa ta kamo hannunta, qarqashin wata bishiya ta jasu suka tsaya sannan tace "Na'ima you can tell me everything, inaji ajikina akwai abunda yake damunki bazaki fada ba" kuka Na'ima tafara mara sauti sai kawai Nafisan ta dan r
ungumota tafara buga bayanta itama idonta taji yafara kawo hawayen, sai da Na'ima tayi kukan sosai sannan suka zauna kan wani rest bench a gurin Nafisa tace "Na'ima me yake faruwa dake Dan Allah?" tana kallon gefe tace "He's assaulting me Nafisa" tsabar ma
maki har bude baki Nafisan tayi sai Na'ima takai hannu tacire face mask dinta, cikin tashin hankali Nafisa ta kai hannu tana taba fuskan tace "He did this to you?" Na'ima ta gyada kai batace komai ba still idonta na hawaye, Nafisa tace "Wane irin dabba ne
wannan da zai kai hannu jikin mace, kuma kin fada a gidanku?" sai Na'ima ta girgiza kai, Nafisa ta sake cewa "Baki fadawa maman ki ko babanki ba? Na'ima what is wrong with you, ace mijinki ya duke ki kuma sai kiyi shiru" tsayawa
kallon Nafisan tayi cikin s
anyin murya tace "Iyayena sun dade da mutuwa Nafisa, a gidansu mijin nawa na tashi" zuwa lokacin kan Nafisa ya kulle kuma sai ta damqo hannun Na'iman tana squeezing tace "Tell me everything please" nan Na'ima ta sauqe idonta qasa tiryan tiryan tafara bawa
Nafisa labarin ta tun tana qauye har kawo yanzu da take zama gidan Bilal, hawaye Nafisa ta rinqa yi tana sharewa bata daina kallon Na'iman cike da tausayi ba, tace "You have to tell his father, this can't continue Na'ima, kuma kinayin addu'a sosai?" sai Na
'ima tayi shiru batace komai ba, Nafisa ta sake cewa "Kina tashi cikin dare ki kai kukanki gurin Allah Na'ima?" Tunani Na'ima tafara dan gaskiya ta fannin addini tanada rauni kasancewar both gidajen da ta taso duk ciki babu wanda aka bada himma ta fannin k
aratun addininta, sai ta girgiza kai Nafisa na kallonta tace "Kina sake sosai Na'ima, Bilal yana alaqa da irin wadda nagani jiya kuma ace bakya yawan addua?" cikin sanyi Na'ima tace "Ai bansan addu'o'in da ya kamata inyi ba" nan Nafisa ta fara karanto mata
ganin bata ganewa sai ta dauko takarda daga jaka tafara rubuta mata su, shawarwari sosai Nafisa ta hau bata suna nan zaune, lecture dinda basuyi ba ranan kenan, da Nafisa ta tashi maidata gida nan ma tayi ta encouraging dinta akan ta samu Alhaji da magana
n, itadai Na'ima sai gyada kai babu magana a haka har suka isa, tayi sa'a basu dawo ba kuwa nan ta hau dafa musu abinci cikin sauri, basu dawo gidan ba sai tsakar dare, Na'ima na kishingide kan sallaya tajiyo buruntun su, washegari ma sai da ta jira fitan
su sannan ta fice school din, a bakin class ta hango Nafisa na tsaye tana jiranta bata shiga ba, tana murmushi ta iddata sai Nafisan tace "Thank God, nazata wani abun ne ya faru" murmushi me fadi Na'ima tayi sai tace "Shine kikaqi shiga class kuma" bata am
sa ba mata ba sai tace "Bazai barmu mu shiga ba yanzu, ya kusa gamawa", jansu tayi gurin cin abinci tayi musu order sunanan zaune, bayan sunci Na'ima tayi insisting biya sai Nafisa ta hanata tareda saurin miqa card nata, sai da suka tashi komawa gida Na'im
a tasan Nafisan bata zo da motanta ba, tace su jira Yayan ta da zai zo daukanta sai suka samu guri qarqashin wani bishiya suka tsaya, basu wani dade ba wata Wagon Jeep ta faka a gabansu nan inda suke tsaye akayi rolling glass din gefen me zaman banza wani
kyakkyawan yaron da bazai wuce shekara 13 ba ya leqo kansa yana dariya, Nafisa ta hararesa tace "Wallahi fitowa zakayi ma, dan ajiyata ce a gaban motan nan" wanda ke driving din yayi dariya yace "Hala kwai kikayi a wajen" ta bata fuska tace "Yah faruk meya
sa zakazo dashi Fisabilillah" bude motan yayi sannan ya fito be zagayo ba ya tsaya yana kallon Na'ima dake dan kauda kai dan ta cire face mask din a sannan, Nafisa tace "Yaya meet my friend Na'ima" da sauri Abu ya fito daga gaban motan yana murmushi yace "
Itace Anty Na'iman dama, ina wuni" murmushi Na'ima tayi ta amsa sannan ta kalli Faruk tareda gaishesa, ya amsa bai bar kallonta ba, Abu na murmushi ya danyi qasa da murya yace da Nafisa "She's beautiful" a bayyane Nafisa tace "Kai dalla tanada Aure" sai sa
nnan Faruk yayi saurin kauda idonsa yace dasu "Ku shiga muje mana"... Har gida suka kai Na'ima dazata fita tayi musu godiya Abu yace "Yaushe zakizo gidanmu Anty?" tana murmushi tace "Zanzo wani sati in sha Allah" da haka sukayi sallama Nafisa tace "I'll ca
ll you" shidai Faruk bai sake cewa komai ba idonsa na kan wayarsa yana pressing...
Karfe dayan dare na ranan tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallah taji shiru har Lokacin Bilal basu dawo ba gashi ta bar qofan falon nasu a bude, tsoro ne taji ya
dan fara shiganta sai ta miqe ta fice daga dakin taje ta kulle kofan sannan ta koma daki, bata fi 30 minutes da fara bacci ba taji an fara buga kofan falon da qarfin bala'i, ta miqe da sauri har
jikinta na rawa ta isa falon ta tsaya, kasa budewa tayi dan b
ugun ya mata karfi sosai, Jin muryan Bilal tayi da qarfi yace "Open this damn door Na'ima" sai tayi saurin qarasawa jikin kofan, bata qarasa bude kofan ba ya banko ta tareda hankata tayi baya ta fadi da karfi, fuskan nan tasa tayi jajir sai warin taba da a
lcohol yake, miqewa Na'ima ta farayi ganin yanayinsa aikuwa beyi wata wata ba ya qaraso ya kwasheta da kafa, tiim ta fadi qasa tareda yin qara, yana huci yace "Ko a gidan ubana da kika zauna kin taba ganin sun kullemin kofa?" Ta girgiza kai tana kuka dakya
r kafin ta sake wani magana ya sake kai mata wani harin da qafa, dukanta ya hau yi iya kafinsa yana cewa "Who are you, da zaki kullemin kofa" tana kuka ta cigaba da jijjaga kanta, sai da ya gaji dan kansa sannan ya sake mata wani tsawan "Answer me" tana da
ga kwancen kan tiles tana kuka tace "Kayi hakuri" ya buga tsuka me karfi ya tsallaketa ya wuce sama, kifa fuskanta tayi kan tiles din tana kuka mara sauti tareda dafa cikinta, saida takai almost 1 hour a wajen sannan ta miqe dakyar ta gyara gashinta daya s
auko fuskanta, dafe da cikinta ta nufi saman zuwa dakin ta tana hawaye, baccin da batayi ba kenan har asuba idonta biyu, data hada breakfast ma shi kadai ta samu zaune kan dining chair din, tayi serving dinsa hannunta nadan rawa shikuwa gogan idonsa na kan
wayarsa, tsuka ya buga me karfi tareda Kai hannu ya tunkude plates din suka kife nan qasa, da sauri Na'ima ta masa gefe tana damqe idanunta dan ta dauka duka ze kai mata ma sai taga ya