Showing 57001 words to 60000 words out of 121625 words
kitchen din gudun ta kyare ta akan wani laifin da batasan sa ba, a tarun lokuta Na'ima ta kanji a ranta ko Hajiyar batason ganinta ne saboda indai tana waje sai Hajiyan ta tsiro da wani abun da zata k
yareta ko cikin magana ne, daukan ruwan tayi ta fita ta main entrance din falon, batakai da zagayawa baya ba maigadi ya bude kofa wata mota ta shigo gidan, tsayawa tayi tana kallon motan, cikin sauri driver ya fito bayan yayi parking ya bude bayan motan wa
ta babbar mace in her 70s ce ta fito riqe da sandarta na qarfe tana dan duqawa,
Na'ima na nan tsaye Matar ta fara takowa gurin entrance na gidan idonta be bar kan Na'iman ba, dan tsugunnawa tayi ta gaishe ta, ta amsa da "Lafiya 'yan mata" sannan ta shige c
ikin gidan, sai da Na'ima ta zagaya ta debo sabon ruwa sannan ta koma falon, nan ta samu Hajiya Babba hamkince kan kujera ga Hajiya nan zaune kan carpet suna gaisawa, cikin ladabi Hajiya ke gaisheta wanda Na'ima bata taba gani ba ko sanin akwai wanda Hajiy
a zata gani ta rusuna kamar haka ba, zata cigaba da goge gogen kenan Hajiya tayi mata tsawa "Bakiga munyi baquwa bane, fita da mopper'n nan" Hajiya babba tace "A'a barta mana tayi aikinta, ba mai aiki bace" Hajiya tace "A'a, baban Bilal ne ya dauko ta daga
Adamawa wai 'yar qaninsa ce" sai Hajiya babba ta juya tana bin Na'ima da tayi tsuru tsuru da kallo, sai tace "Toh sannu yarinya, jeki abunki" Alhaji ne ya sauqo shima ya qaraso falon cikin ladabi yafara gaishe da uwar goyon tasa, sum sum Na'ima ta bar fal
on bata sake komawa ba sai zuwa hantsi taji Hajiya ta kwalo mata kira daga can compound din gidan, da saurinta ta fita ta samu ashe Hajiya babban ce zata tafi su Alhajin sun rako ta, bayan Hajiya Babba tayi sallama da Hajiyan wadda ke ta murmushi kamar bak
inta ze yanke sai Abdullahi ya bude mata backseat ta shiga shima ya shiga gaban motan da nufin ze rakata, Na'ima na nan tsaye gefen Hajiya tana jiran sanin dalilin kiranta da Hajiyan tayi mata sai kuma ta ji shiru, dagowa tayi da nufin ta sake cewa "Gani H
ajiya" sai taga Hajiyan tabi bayan motarsu Hajiya Babba dake fita daga gidan da wani irin mugun kallo, bayan motar ta gama fita daga gidan Hajiya ta buga wani uban tsuka me karfi sannan ta juyo ta kalli Na'ima, shan jinin jikinta tayi da kallon da Hajiyan
ta bita dashi, sai kuma Hajiyan ta wulla mata ledan hannunta zuwa jikinta cikin bacin rai tace "Ki kai dustbin" sannan ta juya fuu ta koma cikin gidan tabar Na'ima nan tsaye riqe da ledan a jikinta, data je zubar da kayan ledan ne taga ashe fruits ne dasu
daddawa hajiyan ta kawo gidan, tana ta mamakin zubarwan da Hajiyan tace tayi amma haka dai tayi abunda aka satan sannan ta koma falon saman dan gama aikinta, bata kai ga qarasawa cikin falon ba taji Hajiya na waya cikin daga murya tana zubo duk zagin da y
azo bakinta, Jin takun mutum yasa Hajiyan juyowa kunnenta kare da wayan ta kalli Na'ima, sai tace "Ina zuwa Larai zan kiraki" sai tace da Na'iman "Meya kuma? Bakiga Ina waya bane?" Na'ima tace "Nazo wanke bandakin ne" Hajiya tayi tsuka tace "To ki je ba ya
nzu ba"...
Tafiyar Bilal qasar Luxembourg yin karatu be dawo Nigeria ba har se da Na'iman ta shiga ss1 a makaranta, zuwa sannan Na'ima har ta hakura da zuba ido akan ko Alhaji ze barta taje qauye, amma shiru gashi har zuwa wannan lokacin Allah be bata c
ourage dinda zata bude baki ta tambayesu iznin zuwa ba, suma duk 'yan uwan nata na qauyen aka rasa wanda yayi tunanin zuwa na musamman ya duba halin da takeci a rayuwa, abun dai kamar sun kyautar da ita ne babu me buqatar ta kuma wanda hakan ba qaramin zaf
i yake wa Na'ima a zuciya ba ganin qannen mahaifinta sun banzatar da rayuwarta cikin halin ko in kula...kafin zuwa wannan lokacin Hajiya da Alhajin sunje Luxembourg bila adadi dubo dan nasu amma be dawo ba, Na'ima ta kanyi mamakin sosai akan wannan qauna d
a suke masa, in the sense that komai na rayuwan gidan revolves around Bilal duk da baya nan, kullum sai Hajiya ta sata ta gyara masa dakinsa tayi mopping, hatta plates dake kitchen din gidan da cokula an ware na Bilal daban ko Hajiya bata amfani dasu..
Ga
nin gatan da Na'ima zatayiwa kanta shine karatun yasa ta maida hankalinta sosai akai, a inda akayi mata jumping din daga jss2 tayi jsce dinta ta wuce ss1, saboda girman da Na'iman tayi anan ma Sufi da aka
bashi ragamar kula da makarantar ta yayi magana da
Alhajin akan zuwa ss2 zata gwada rubuta waec da neco dinta plus jamb, Alhajin ya amince da hakan dan shima yanason Na'ima tayi karatun, kawai dai matsalar shine rashin maida hankalinsa sosai akan yarinyar da baya yi akai akai, duk wani ragamar rayuwan Na'i
man ya bada shine ga Hajiya wanda ita ma Hajiya se take riqon sakaina a marainiyar Allah'n...
A ranan da Bilal zai dawo har Alhajin ma be fita gurin aiki ba tare da hajiyan suka fita sufi ya kaisu airport dauko dan gudaliyan nasu, aka bar su Na'ima na k
acaniyar dafe dafen abinci daban daban, zuwa sannan Na'ima ta zama me aiki a gidan da qarfi da yaji dan ayyukanta a gidan sunfi na shafa yawa, samun sararinta shine in ta je makaranta, gashi islamiyan da aka saka shima sai Hajiya tana yawan hanata zuwa sab
oda sata aikin abincin dare da take yawan yi..
Isowar Bilal gidan suka fito daga motan bakin Hajiya kamar ya yage dan murna ta riqo hannun dan lelen nata, Bilal dake sanye cikin wata hoody riga ya saka duka hannayensa cikin aljihu sai wani shan qamshi yak
e, direct sama suka wuce suna magana da dan nasu dake amsa wa sama sama, Na'ima dake jera abincin nan kan dining table ta bisu da kallo, sai Bilal din duk ya canja mata a Ido, yazama wani cikakken saurayi dashi ga wasu Snickers da ya saka farare, kuma har
zuwa wannan lokacin chain dince sanye a wuyan sa... Sai da Hajiya ta tabbatar da ya sake wanka ya shirya cikin kayan da ta fito masa dashi sannan ta kamo kafadansa tana kallonsa tace "Babana kanacin abinci kuwa, duk ka rame" Bilal yace "Inaci mana, dole na
ai Hajiya" sai ta sake kafadansa ta kamo hannunsa tace "Muje gashican nasa ayi maka favorite dishes dinka" A falo suka tadda Alhaji ya kishingide akan kujera ya dago kai yana kallonsu, Bilal ya qarasa gurinsa zai zauna Alhaji yace "Muje kaci abinci tukunn
a son" dan bata fuska Bilal yayi ya kalli Hajiya dake tsaye yace "Hajiya kisa akawomin nan" tace "Toh babana" ta juya ta fita da dan saurinta fuskarta cike da fara'a, su Na'ima ta samu a kitchen din tana juye pepper chicken acikin wani flask, ta dago kanta
tana kallon Hajiyan data shigo, sa Na'iman tayi taje ta fara daukan wa'inda takai dinning table din ta miqa sama acan Bilal zeci abincin, Haka Na'ima ta debi kayan a tray babba ta nufi sama, tunda ta shiga falon Bilal yake kallonta har ta ajiye kayan ta j
uya zata sake zuwa dauko wasu yabi bayanta da kallo, azuwanta ta biyu ne suka hada ido ta dauke kai tana jera abincin anan gabansa, bayan ta ajiye flask na qarshe sai ta gaishesa cikin sanyinta, ya amsa da "Lafiya" bai kuma dena kallonta, miqewa tayi ta fi
ce ganin irin kallon da yake mata, dakinta ta koma tayi wanka bayan ta fito ta shafa Vaseline dinta ta nemi wani kayan cikin 'yan qalilan dinda hajiya ta qara mata, dan sai Hajiya taga kayan jikin Na'iman ya kode yana neman yagewa sannan take qara mata kal
a biyu zuwa uku kuma Alhaji yasha bada kudi a mata dinkin amma Na'ima ta rasa me yasa Hajiyan bata siya mata kayan...
Yammacin ranar ta je falon sama gurin hajiya tambayanta me za'a girka, tasamu tana zaune kujera daya da Bilal yana nuna mata wani abu a
waya tana kallo cikin murmushi, nan kan carpet Na'ima ta tsugunna tace "Hajiya me za'a dafa?" Hajiya ta kalli Bilal tace "Babana me zakaci?" sai yadan sauke numfashi yace "Komai ma is Okay" ta juya gun Na'ima tace "Kiyi wani abu light kawai" Na'ima ta miq
e Hajiyan ta sake cewa "Kije can dakin shafa ki kiramin ita" ta amsa da toh zata fita Bilal yace "Jeki kan gado na akwai laptop ki dauko" nan ma ta ce "Toh" taje ta dauko, miqa masa tayi sai yace "Ki riqe na baki" Hajiya ta wani hararesa tace "Ban gane ka
bata ba kuma, baka amfani dashi ne?" ya gyada kai, Hajiya ta sake cewa "Toh dan baka amfani dashi se kace zakayi kyauta dashi, ita me zatayi da laptop" Na'ima dai na nan tsaye tana addu'an Allah yasa Hajiyan ta yarda a bata, dan yawancin yan makarantar su
suna da laptop, Bilal yace "Com'on Hajiya, in inaso ai bazan bata ba" Hajiya tace "Toh sai ita kadai kagani da zaka yiwa kyautan, bani laptop dinnan Na'ima" Na'ima tayi saurin miqa mata, ta sake cewa "Yaushe tayi girman riqe laptop itadin, ni banason irin
haka" Bilal ya miqe zai fita tace "Ina kuma zakaje, fushi kayi?" bai kulata ba ya nufi hanyar fita daga falon sai ta wullawa Na'ima laptop din tace "Gashi ai na bata kuma" shidai bai kulata ba ya fice, ai da sauri Na'ima ta bi bayanshi gudun Hajiya ta kuma
kwace laptop din, A matattalan stairs din ta iddasa tace "Nagode Yaya" ya juyo yana kallonta yace "Kina aji nawa yanzu?" Tace "ss1" ya bita da kallo sannan yace "You've grown up Na'ima" sai tayi murmushi tazo zata wuce sa kawai ya kamo hannunta, saurin yi
n baya tayi ta janye hannun nata, sai yace "Kwaro nagani a hannun naki fa" tayi saurin dago hannun nata tana dubawa sai yayi murmushi yadan girgiza kai yace "Silly" sannan ya juya ya fice daga falon ya barta nan tsaye tana kallon bayansa, da murnanta ta ka
i laptop din daki tana murmushi, rabonta da tayi murna haka harta manta, dayake makarantar kudi Na'iman takeyi sai ya zamto ita kadai ce batada laptop din, kuma malamin computer dinsu yasha mata magana akan hakan, kawai batasan wa zata fadawa bane, dan tas
an ko giyar wake tasha bazata fara fadawa Alhaji a gaban Hajiya ba....
Bata sake haduwa da Bilal ba dan ya dawo da wani irin yawo na masifa, sai ya jera kwana biyar sai dare ya raba yake dawowa gida..
Ranan Na'ima na kitchen tana tace shayi da dare aka b
ude kitchen din Bilal ya shigo, kulle kofar yayi yana kallonta yace "Na'ima aiki kike" ta gyada kai tana dan gyara dankwalinta dan jikinta babu hijabi, sai ya qaraso nan inda take tsaye yace "Kwana biyu baki ganni ba bakya cigiyata ne" Na'ima duk ta taqura
da irin kallon da yake mata tace "A'a Yaya" sai yace "Nima zansha tea din kinji" ta gyada kai ta juya zata dauko cup yabi bayanta da kallo kamar idanusa zasu fado, bayan ta zuba shayin sai ta miqo masa, madadin ya karba sai ya hada da hannunta ya riqe, da
sauri Na'ima tayi nufin kwace hannun nata sai ya damqo dayan hannun nata shima yana kallon idonta, kiciniyar kwace wa ta fara tace "Yaya kabari" yayi qasa da murya yace "Babu abunda zan miki, kawai riqeki zanyi kinji" tayi saurin jijjaga kai tace "Banaso
Yaya" sai ya bata rai ya sake hannun nata tayi saurin yin baya ta fice daga kitchen din ta kofan baya jikinta na rawa, zagayawa Na'ima tayi ta shiga falon ta gaban compound din gidan, Hajiya ta gani nan gurin stairs tana sauqowa sai tayi stiff anan tsaye t
ana raba idanu, Hajiya tace "Ina shayin dana sa ki kawomin" Na'ima ta kasa cewa komai, Hajiya ta sake cewa "Daga ina kike daga wajen" jikin Na'ima na dan kyarma tace "Naje..uh..uh.." Bilal ne ya fito daga kitchen din fuskarsa a dinke, hannunsa riqe da cup
din tea yakai baki yana kurba anan tsaye yana kallon Na'iman, ganinsa yasa Hajiyan cewa "Babana yanzu fa nace ta zubo maka shayin ta kawo, ashe ka gaji da jira ka debo abunka" ya daga kafada baice komai ba, Hajiya ta kalli Na'ima dake nan tsaye tace "Wato
anfara zuwa gandun da zan saki aiki ki ajiye nawan kiyi wani abun gabanki ko" Na'ima tayi saurin jijjaga kai idonta na kawowan hawaye tace "A'a kiyi hakuri" Hajiya tayi tsuka ta juya ta nufi komawa saman ranta a bace, nan falon ta bar Na'ima tsaye ga Bilal
har sannan bai dena kurban shayinsa ba yana kallonta, sum sum ta juya ta nufi dakinta idonta na kawo hawaye ya bi bayanta da kallo.....
Da Na'ima tazo bacci sai taji ya gagara zuwa, kawai ta juya kanta ta kalli sama, qurawa pop'n dakin ido tayi hawaye ma
su zafi suna fita daga idonta, wata rayuwa take gudanarwa with no one to talk to, batada wanda zata ce yau ga abu na damunta bari tayi sharing dashi ko zataji sauqi sai ita kadanta babu wa ko qani, kuka ta farayi tana shessheka anan kan gadon maraicinta na
qara dawo mata sabo a zuciya....
Washe gari Saturday kusan 11 na safe tana share varenda na main entrance din gidan aka bude kofan dake jikin gate wasu 'yammata suka shigo su biyu, kai kana ganin irinsu kasan tarbiya bata biyo hanyarsu bama, dan miqewa
Na'ima tayi tana binsu da kallo ganin sunsha wasu irin matsattsun kaya, isowarsu gurinta daya na taunan chewing gum tace "Ke qanwar Bilal ce?" dayar tace "Baki ganta itama fara bane zaki tambayeta" wadda tayi tambayan da farko ta juya tasake bin Na'iman d
a kallo tace "Naga basa kama ne, anyway..Bilal yana cikin gidan" Na'ima da tunda suka fara magana take kallonsu sai sannan ta gyada kai alamun "Eh" kafin su kaiga shiga gidan Bilal ya fito dan tun shigowar su ya hangosu through window'n dakinsa sa dake sam
a, dan hararsu yayi yace "Kinsan nace karki biyoni gida ko" ta farkon nan dai datayi maganan ita ta sake cewa "Ai na fada maka sai na biyoka in baka turamin ba" ta qarasa magana tana hararansa bata daina taunan cingam din ba, wayansa dake hannunsa ya ciro
yayi mata transfer na kudade masu yawa taji alert anan take, cikin fara'a tace "Yanzu naji batu" ya bata fuska yace "Karki sake biyoni gida banason haka" dayar tace "Sai da na fada mata inka dawo hayyacinka zaka tura mata bataji ba" yace "I've warned you d
ai..now get out" ya qarasa maganar yana nuna musu gate, juyawa sukayi ta farkon tace "Sai mun hadu anjima" da haka suka fita Na'ima dai bata daina kallonsu ba tana nan tsaye, Bilal ya juya ya kalleta yace "Good morning pumpkin" sunkuyar da kanta tayi dan i
ta tsoro ma yake bata baisani ba, ze sake mata magana suka jiyo shafa na kiranta tana dosowa kofan, cikin gidan Bilal ya koma shafa ta gaishesa kansa a sama ya amsa tareda wuceta....
Sharan da Na'iman bata qarasa ba kenan haka ta tafi gurin shafa suna h
ira suna aiki, daren ranan tayi wanka ta fito jikinta daure da zani ta nufi wardrobe dinta zata nemi t-shirt dinda zata saka tareda zanin dan bacci, taji an bude qofan dakinta, bata dago ba sanin shafa ce me shigo mata daki daman, shiru bataji anyi magana
ba saita dago kanta, Ido hudu tayi da Bilal da yake bin dakinta da kallo, miqewa tayi da sauri ta qara damqe zaninta idanun ta awaje cikin firgici, cikin kwantar da murya yace "Heyyy...ba abunda zan miki kinji" ta girgiza kai tace "Yaya kayi hakuri" ya ma
tso yace "Haqurin me pumpkin?" tayi baya batace komai ba, ya sake matsowa a hankali "Dan kadan zan tabaki kinji" ta dago kanta tana kallonsa cikin firgici, ya sake cewa "Kinji Na'ima, i won't hurt you wallahi" gocewa tayi zata gudu yayi saurin kamota kamar
'yar tsana ya jefata nan kan gadon kawai ta fashe da kuka me qarfi still tana damqe zaninta, ganin ze hawo gadon yasa ta kwala ihu, beyi wata wata ba ya kai mata wani marin da saida Na'ima taga taurari na 'yan daqiqu, ya finciko ta cikin huci yace "Ni zak
iyiwa ihu" tana kuka ta jijjaga kai tace "Dan Allah kayi hakuri" sai kuma ya saketa yana kallonta, tsuka yayi ya juya cikin huci ya fice daga dakin ya barta nan zaune tana kuka hannunta damqe da zaninta har sannan...tashi tayi taje ta kulle qofan nata tana
kukan ta nemi riga ta saka duk a tsorace, a wannan daren shima tayi kuka sosai tana saqa da warwaran ya zatayi da wannan matsalan da ta fara fuskanta wajen dan lelen gidan...
Washegari da ta Kai breakfast nan falon saman Hajiya tace "Wuce ki kai wa Bil
al dakinsa yayi baqo" take duk jikinta yayi sanyi Hajiya ta bita da kallo ganin gefen fuskanta yayi jaaa amma batace komai ba, cikin sanyin jiki ta shiga dakin Bilal din ta samu yana zaune kan gado da abokinsa suna magana, qarasawa cikin dakin tayi kanta a
qasa jikinta na dan rawa, abokin nasa mai suna Nasir ya bita da kallo yace "Wannan fa, housegirl dinku ce?" Bilal ya dan girgiza kai idonsa na kan waya, sai Nasir ya sake cewa "Na dai san bakada qanne" nan ma Bilal bai amsa masa ba still, nan qasa carpet
Na'ima ta ajiye tray din abincin kanta a duqe cikin sanyin murya tace "A zuba ne Yaya?" dan qa'idar Bilal a gidan shine in an kai masa abinci