Showing 87001 words to 90000 words out of 121625 words
din cikin bacin rai yace "Da Nasir na kamat
a fa a dakinta" cikin masifa Hajiya tace "Wannan dan iskan abokin naka ko ni in da hali bazai haikemin bane, toh wallahi tun wuri ka maida matar ka shine rufin asirinka, babu me iya zama dakai sai itan, kai kasan kokarin da nakeyi akan tsakaninta da Alhaji
kuwa? an fada maka da lafiya qalau ne Alhaji zai zuba ido kana mistreating din ta ne, kana tsammanin nida kai din zai bar mu ne?" qoqarin miqewa Bilal ya fara yana cewa "Gaskiya bazan maida ita ba, i don't even want to see her now" sai ya nufi upstairs za
ije dakinsa, da sauri Hajiya ta bi bayansa, anan falon saman ta kamo hannunsa tace "Toh kar ka sake ka fadawa mahaifinka ka saki yarinyar nan in ya dawo daga
tafiyar nan" gyada kafada yayi ya shige dakinsa, a daren Hajiya ta tambayi Bilal address din asibi
tin, da taje bata samu Na'ima ba sai ta wuce gidan Bilal din nan ma megadi ya fada mata babu kowa gidan, bata yarda ba saida ta shiga cikin gidan ta duba, da ta koma gida sai tayi deciding zuwa washegari zata kira Ayuba taji ko Na'iman na can, aikuwa washe
garin da sassafe ta kirasa amma sai bata tambayesa Na'ima ba tana jiran taji ko zai mata maganan, sai taji har tambayan ta lafiyan Na'iman yake, nan hankalinta ya fara tashi kuma, Bilal kuwa the following day ya hada ya nasa ya nasa ya tafi Lagos ko sallam
a beyi da uwar tashi ba...Hajiya na cikin tararradin lamarin Alhaji yadawo gari, bata fada masa a ranan ba sai washegari da safe suna breakfast, farko cewa yayi "Whattt? Bangane ta gudu ba?" Hajiya na hawayen makirci tace "Kamata yayi da qato a daki, kuma
da ta tashi guduwan bata nufi Adamawa ba, sai Allah kadai yasan inda taje" cikin tashin hankali yace "Da namiji kuma, anya kinsan me kike fada kuwa Ladi" kuka ta fara tace "Zan mata sharri ne Alhaji, Na'iman nan dai nima 'yata ce, riban me zanci in nayi ka
rya akanta, halin dan yau kawai ta nuna mana, shiyasa bahaushe yace in kaga mutum a rana kawai ka barshi, dame muka ragi Na'ima fisabilillah" sanyi jikin Alhaji yayi yace "Toh yanzun da ta tafin, sakinta Bilal din yayi" ta girgiza kai tace "Shima nemanta y
ayi ya rasa" yace "Shine baki kirani kin fadamin ba Ladi, wai meyasa a yawancin lokuta kikeson aiwatar da abu gashin kanki ne, Bilal din ya bada cigiyanta ne yanzu?" Tace "Toh ta Ina zamu fara cigiyanta ita ba qaraman yarinya ba, badai duniya bace, taje ta
isheta riga da wando, munanan zata dawo ta samomu" ..Kiran Bilal din Alhaji yayi yace duk inda yake ya dawo yanason ganinsa, daga Toh dinda ya amsa kuma sai kashe waya, iyayen sukayi ta kiransa basa samunsa har suka haqura suka zubawa sarautan Allah Ido..
da aka kwana biyu sai Hajiya tace yakamata ya kira Ayuba ya fada masa dan sunada hakkin sanin abunda Na'ima tayin, magana dai da taje kunnen Ayuba sai da ya tsinewa Na'ima ranan Alhajin na bashi hakuri, sai magana taje cikin gidansa, sannan gidan Nasiru da
iyalinsa, kai har yan uwan nesa sun ji labarin Na'ima ta shiga duniya bayan duk Alkhairyn da su Alhajin suka mata, babban abun ma shine mijinta ya kamata da abokinsa a daki daya, duk yanda Alhaji yaso Bilal din ya dawo qi yayi dan daga baya ma ji sukayi y
a koma China...
Rayuwan Na'ima gidansu Nafisa har sannan dai gatanan ne, yau tayi walwala kadan, gobe ta wuni cikin kunci tana kuka, lokacin da Abba ya kirata ta masa bayanin abubuwan da suka faru kasawa tayi saboda kuka, hakan ya famo mata abubuwa da d
ama a zuciyarta, sai cikin hira da lallami Mami ke sanin abubuwan da suka farun a sannu, Ahalin gidan suna iya kokarinsu na ganin sun kyautata mata, har rige rigen kyautata matan suke, kowa nason ganin ya saka murmushi a fuskanta amma abu ya ci tura, dakya
r Na'ima ta fara fita falon gidan ana hira da ita, gashi nan dai ta warke sosai amma wannan kuncin har sannan yana tare a zuciyarta, Mami da Nafisa duk sun shiga damuwan ganinta hakan, ganin haka Abba yayi shawara da Mamin batun kaisu makaranta itada Nafis
an ko karatu zai debe mata damuwan, dan sosai Na'ima tayi sanyi kamar ba ita ba, watarana haka zata rinqa kuka cikin dare ita kadai tanajin zuciyarta babu dadi, gashi dai bata dana sanin tahowan da tayi amma har sannan zuciyarta ta kasa samun nutsuwa...da
Abban ya kirasu ya fada musu zai nema musu gurbin karatu a oxford, Na'ima taji dadi na cewa zata bar qasar, and she can't wait for a fresh start in England....Faruk da Nafisa ne suka je Kano karbo results din nasu ita da Nafisan, daman tun kafin su tafi Ab
ban yayi waya sai basu sha wahala ba.....
Sai da Bilal yayi 8 months a China kafin ya dawo gida, wanda sai da Alhajin da Hajiya sukaje, dawowan ma a firgice yayi ta dalilin wani bala'i da ya fada masa, aka wayi gari an sace Stella a qasar kuma duk wani
zargin batan nata is pointing directly at him, sai da aninan Alhaji suka kai qasa sosai kafin ayi belin Bilal, wanda dawowarsa qasar ne ya fara neman Na'ima ido rufe, kuma sai a sannan yace da Hajiya zai maida auren nasu, murmushi kawai tayi a lokacin tace
"Kayi latti Bilal, ai danace ka maida ta tun farko din ka dauka ban san me nakeyi bane? ni banason ta dawo ma, Yanda ta dau lokaci har haka ma ka hakura da itan kawai, dan zuwa yanzu bariki ta zauna mata sosai" be ce komai ba Hajiyan ta cigaba "Dan ni ban
san ya zanyi ba in yarinyar nan ta dawo yau, na dawo daga rakiyarka Bilal, gwara ma ka fada masa nima baka fadamin batun sakin ba duk ranar da Na'iman ta waiwayi gida, dan ko jahili yasan babu aure a tsakanin ka da Na'ima yanzu"....
Bilal bai hakura ba y
a cigaba da neman duk wata hanya da zai same ta, har Abujan yaje bayan ya samo address din gidansu Nafisa amma baiga alamun Na'ima na rayuwa a gidan su ba, sai after a month ya samo link na cewan Nafisa na tare da Na'iman suna karatu a Oxford amma kuma ya
rasa in da zai samu direct contact din Na'iman, sai ya fara bibiyan Nafisa sosai, handles dinta na social media kowanne bi yake yana neman ta inda zai ga ko da wani qaramin clue da zeyi Linking dinsa to Na'ima..A ranan da ya tabbatar da inda suke zama a Lo
ndon ne ya turawa Nafisa message through Instagram dinta, ranan kuma be kwana a Nigeria ba yayi booking din jirgi sai london, he spend weeks going to their apartment before that fortunate Day da Na'iman tazo diban kayansu....
Toh Jama'a....Menene manufa
r dawowan Bilal cikin rayuwan Na'ima?
Shin Bilal yana da tabbacin Na'ima zata dawo garesa da duka this time around?
Shin me Ahmad zeyi bayan yaji abubuwan da suka faru a rayuwan sanyin idaniyan tasa?
Wane mataki ze kai na ganin ya kawar da duk wani qa
lubalen da zeyi masa katanga da Na'ima?
Shin kuna ganin wani gumurzun ne zai faru da Na'ima tsakaninta da Laila kaman yanda ta sha fama da Stella?
Menene manufar Faruk akan Na'ima?
Ku biyo ni Bintu Musa, zan warware muku komai a sannu..
Karku ma
nta nace "A Love that stood a chance amidst chaos ko" Toh yanzu soyayya da ruguntsumin zasu soma....
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 37
Back to main story....
A wannan lokacin Na'ima kasa daukan wayan hannunta tayi, ta rinqa kal
lon duka maza biyun da ke da alaqa da ita, dukansu tsaye anan street din, gani tayi Ahmad ya sauqar da wayan daga kunne yana kallon screen din dalilin bata dauki kiran ba sai ya maida wayan cikin aljihunsa ya fara takawa alamun zai taho cikin building din
nasu sai tayi saurin kiransa ya sake ciro wayan ya daga, cikin kwantar da murya yace "Babe i'm outside" kintsa muryan ta tayi tace "Yanzu zan sauqo, kayan nake hadawa" sai yace "Bari nazo in tayaki dauka" Na'ima tayi saurin girgiza kai tareda cewa "No no n
o..ai ba yawa ma, ganinan zuwa" Ahmad yace "Okay", sai lokacin Bilal ya samu abun hawa, tana gani ya shiga suka tafi, cikin sauri ta juya ta nufi dakin Nafisa dan nata mirro yayi kaca kaca a tsakar dakin, jawo jaka tayi kawai ta rinqa tula kaya aciki batar
eda sanin ma wanne take diba ba, tana hawaye ta qarasa gaban madubin dakin ta kalli fuskanta, gefen lips dinta ne yadan fashe sai can saman goshinta da ya dan tashi sanadin bugata da kujeran da Bilal din yayi, dago hannunta tayi tana kallon yanda glass din
ya yanke ta, sai ta fashe da kuka tana kallon kanta a madubin, share hawayen ta tayi da bayan hannu afili tace "You won't see fall Bilal...You will never see me fall" ta qarasa maganan tana fashewa da wani sabon kukan, sai tayi saurin shiga bandaki ta wan
ko hannun nata da ya dan baci da jini tareda wanko har fuskanta ta gyara gashinta, face mask ta nema bayan ta fito, anan falon ta dauki veil dinta da ke yashe a qasa sannan ta fice riqe da jakan a hannunta, kanta a kasa ta fito wajen, Ahmad dake tsaye jiki
n mota har sannan yayi saurin qarasowa gurinta tareda karban jakan yana kallonta yace "Kin dade Babe, meya faru?" kanta a qasa tace "Kayan na rasa" sai ya tsaya kallonta ganin tana ta sunkuyar da kai, ganin yana kallonta yasa ta fara nufan motan ya biyota
ya bude mata front seat din, a back seat ya saka jakan sannan ya shigo bai daina kallonta ba, ahankali yace "What happen Na'eemah?" juyowa tayi ta kallesa sai tayi murmushi tacikin face mask din tace "Babu komai, kaine kemin ciwo na dan buge a daki ne dazu
" da sauri yace "Subhan Allah, sannu Babe" ta gyada kai kawai tajuya tana kallon window, a hanyarsu ta tafiyan bini bini Ahmad zai juya ya kalleta har sannan kanta yana jingine jikin window din and she was trying so hard not to tear up a gabansa, sai da su
ka koma school din Ahmad ya kira Nafisan a waya ta fada musu tanacan wani underground parking lot, takai ajiyan motan nasu saboda zasu koma acikin na Ahmad din, lokacin da ya faka a gurin da suke hango Nafisan na tahowa sai ya kalli Na'iman, cikin kwantar
da murya yace "Babe are you sure you're Okay?" dan yanayin nata yasa jikin sa ya bashi she's not alright, kallonsa tayi sai ta kasa jure irin kallon da yake matan tayi saurin sauqe idonta tace "I'm fine" sai ya duqo kansa ze sake magana Nafisa ta iso, dan
gyara zama yayi ya juya yana kallon street, shiga backseat Nafisa tayi tareda sallama sannan ta gaishe da Ahmad, a nutse yace "Lafiya Nafisa, ya school?" ta amsa da "Alhamdulillah" sannan ta kalli Na'ima tace "Sorry Bobo I've missed your call dazu, ina gur
in supervisor na lokacin" dago kanta Na'iman tayi wanda hakan sai da yasa zuciyar Nafisa bugawa ganinta da face mask, a iya saninta da Na'iman tasan bata saka face mask sai in tana son rufe ciwo a fuskanta, dan tsayawa kallon kallo sukayi sai Na'ima tayi s
aurin kauda kanta ta koma kallon window gudun kar tayi kuka, sai sannan Ahmad ya tada motan suka dau hanyan barin Oxford, shiru motan yayi babu me cewa qala acikinsu kowa da abunda yake saqawa a zuciya, basu tsaya da tafiyan ba sai da suka isa Beaconsfield
town dake kan hanyarsu na tafiyan, nan wani filling station Ahmad ya tsaya zai qara mai a motan yace "I'm coming please" Na'ima ta
gyada kai, yana fita Nafisa ta sako kanta gaban motan tace "Na'ima ina kikaje?" sai tace "Not now Nafisa" ta juya kanta, san
yi jikin Nafisan yayi ta koma ta zauna....Lokacin da Ahmad yayi parking a kofar gidan Anty Amnah da dan sauri Na'ima ta yi masa sallama ta fita ya bita da kallo yana dan jin wani iri, sai Nafisan ta masa sallama itama, kafin ta fita ya miqo mata ledan maga
nin da ya siyawa Na'iman na ciwon kai, bayan sun shiga gidan sai ya kasa tafiya ya fito shima ya rufa musu baya...
Shigan su Na'iman falo suka ga Laila zaune da Anty Amnahn suna hira, ita Na'ima har ta manta ma Lailan tazo garin, Anty Amnah tace "Kun dawo
" suka qarasa Nafisa nacewa "Eh Anty", Laila da bata kulasu ba sai kallon Na'iman take gashi har sannan bata cire face mask din ba, basu zauna ba Nafisa tasake cewa "Anty bari mu watso ruwa mu dawo, duk mun gaji wallahi" Anty Amnah ta amsa da "Toh, in kun
huta ga abinci can a kitchen" kafin su amsa Ahmad ya shigo sai Laila ta miqe tana masa murmushi, Nafisa ta amsa da toh tareda dan riqo hannun Na'iman suka shige dakin nasu, saida Nafisa ta rufe kofan dakin da key sannan ta juyo tana kallon Na'iman dake zau
ne bakin gado tace "Ina kikaje Na'ima?" sai lokacin Na'ima ta cire face mask din nata tafara hawaye tace "Meyasa zaki boyemin Bilal yazo London Nafisa?" cikin shock Nafisa ta ware ido tace "innalillahi... did that idiot hit again?" Na'ima bata amsa tambaya
n ba ta sake cewa "You should've told me Nafisa" dan stiff Nafisa tayi sai ta zauna gefen Na'iman tace "I'm doing this for you Na'ima, billah na boye miki ne for your sanity, i don't want you to get worried" hawayen Na'ima ta cigaba dayi tace "He beat me N
afisa, wai saina bishi" Nafisa ta riqo hannunta tanajin zuciyar ta babu dadi sannan tace "Babu inda zaki bisa wallahi, shi din banza" sai ta dago wayanta tareda cewa "I'm calling Mami now" da sauri Na'ima tace "Karki kirata please" tace "We have to tell th
em Na'ima, har Yaya Ahmad ma" girgiza kai Na'ima tayi cikin sauri tace "Dan Allah karki fada masa komai Nafisa, na shiga uku" kawai ta fashe da kuka, sanyi jikin Nafisa yayi sai ta rungumota tace "it's Okay, it's Okay, i won't tell him har saikin amince" t
a dago Na'ima tana kallonta tace "Amma ki fadamin dalilin da bakya so ya sani" Na'ima na share hawaye tace "I just...I just" ganin haka yasa Nafisan cewa "Don't tell me kina tsoron yasan kin taba aure Na'ima" ta girgiza kai ahankali tace "A'a" sai Nafisa t
ace "Then what?" shiru Na'ima tayi at first sai can tace "Nasir...i don't even know how he'll take that Nafisa, I'm not ready" tsayawa kallonta kawai Nafisa tayi takasa cewa komai, can ta sauqe numfashi tace "Do you really think Ahmad zai gujeki akan haka
Na'ima? what are you even thinking? Do you see the way he look at you everytime? That guy loose his guard anytime he's in front of you Na'ima, wanda cikin mu kaf danginsa babu wanda ya taba ganin wannan side din nashi sai ke, why are you even thinking of h
iding such thing from him?" Na'ima ta kasa magana ma at that time, sai Nafisan ta cigaba "I know you like him too Na'ima but stop holding yourself back akan pig dincan, sannan kisani...this time around Bilal has found a match beyond him, kiyi addu'a kar Ah
mad ya kashe shi in yaji abunda yayi wallahi" shiru Na'ima tayi har sannan batace komai, sai Nafisa ta tashi ta fita, study room din Anty Amnah ta nufa ta wuce Ahmad dake sallah a falon, Anty Amnah da Laila suna kitchen, dauko maganin shafawa tayi ta koma
daki, nan kan gadon ta zauna taja veil din Na'iman data rufa goshinta sannan ta fara shafa mata, rufe Ido Na'ima tayi tanajin komai na dawo mata sabo, dukan da Bilal din ya mata a baya ta fara tunawa har sannan bata bar hawaye ba, Nafisa na kallonta cikin
karyewan zuciya tace "Ki fadamin me ya miki Dan Allah" cikin rawan murya ta fara fada mata abunda tayiwa Bilal din, har ta gama
magana Nafisa na kallonta cikin mamaki, sai tace "Abunda nakeson kiyi tun shekarun baya ne Allah ya baki ikon yi yau" ta kamo ka
fadan Na'iman tace "And you did the right thing Bobo, I'm so proud of whom you're becoming"...Bayan sunyi sallah sai Na'iman ta kwanta nan kan gadon tace ba yanzu zata fita ba kanta yana ciwo, da haka Nafisa ta fita falon tasamu su Ahmad din a dining area
Laila na serving dinsa, dan bin bayan Nafisan yayi da kallo amma baiga Na'ima ba, Anty Amnah tace "Ina Na'iman fah" tace "Ta dan kwanta kanta na ciwo" Jan kujera tayi tana kallon Laila dake serving Ahmad din cikin yanga, dan kadan ya ci abincin sannan yash
a ruwa yanajin zuciyar babu dadi ya miqe, Laila tace "Haba Yaya, bakaci sosai ba fa" bai ce komai ba Anty Amnah tace "Na fada miki cin abincinsa ba sosai bane ai kika dafa dayawa" Nafisa dai sai kallon Lailan take ganin ta wani shagwabe fuska, aranta tana
fadin "iska na wahalar da me kayan kara"...Na'ima bata fito taci abincin ba har dare, dan nan dakin Anty Amnah ta shigo tareda twins suka kawo mata abincin jin shiru bata fito ba, bayan ta mata sannu ta gyara mata blanket din sannan ta kama hannunsu suka f
ice, har lokacin Na'ima ba baccin tayi ba kawai ji take komai baya mata dadi, tana kallon kiran Ahmad na shigowa wayanta amma bata dauka ba, har Nafisa tayi bacci a gefenta idonta biyu, ganin hakan yasa ta tashi tayo alwala, sai bayan ta idar da