Showing 66001 words to 69000 words out of 121625 words

Chapter 23 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

49

da Nafisan tayi wucewar ta ranta babu dadi, tafiya kawai take har tazo bus sto

p din ta wuce batareda ta shiga ba kawai ta miqe da nufin da fita a qafa ko zata samu sararin yin tunani dan inta je gidan ji takeyi komai yana suffocating dinta, tayi nisa da tafiyan ne wata babbar Jeep ta faka a gefenta se tayi saurin juyawa tana goge id

onta daya kawo hawaye, rolling glass din motar akayi Nafisa tadan leqo kanta tace "Na'ima shigo in rage miki hanya" sai Na'ima tadanyi murmushin dole tareda girgiza kai tace "A'a bakomai, ai na kusa isa titin ma" Nafisa tace "Ki shigo Dan Allah, meye haka

kuma kinata tafiya cikin ranannan" matsawa tayi jikin motan tareda bude front seat , sai Nafisa takai hannu tana kwashe su biscuits, iphad, laptop da sauran gadgets dinta dake kan seat din tana dan dariya tace "Sorry i made a mess" sai da ta wullasu duka b

ackseat sannan Na'iman ta shiga suka tafi, qin sauketa Nafisan tayi a main gate din tace ta fada mata unguwarsu takaita, bayan Na'ima ta fada mata sai ta dan ware Ido tace " Muna neighboring area daku ashe" Na'ima ta gyada kai kawai batace komai, har qofar

gida Nafisan takaita ta mata godiya sukayi sallama sannan Nafisa ta juya kan motanta ta fice daga layin...

Da safe taje gaisheda iyayen nata ta samu Bilal zaune kujera kanshi a sunkuye Alhaji na tsaye akanshi fuskanshi ta nuna alamun bacin rai ga Hajiy

a nan zaune dai itama fuskanta babu alamun raha, da farko kasa qarasawa tayi saboda yanda zuciyanta ta tsinke saida Alhajin ya mata iso cikin fara'a sannan, aikuwa tana gama gaishesu ta miqe ta fice daga falon cikin sauri ta koma dakinta, tananan zaune aka

banko kofar ta Bilal ya shigo, firgita tayi ganin ya kulle kofan ta nufi toilet da gudu yayi azaman fusgo gashinta dake daure cikin dankwali yayi baya da ita ta fada kan gado, kuka Na'ima ta fashe dashi ta matsa qarshen gadon tana kallonsa, cikin huci yac

e "Ki fadamin dalilin da yasa kika fadawa iyayena zaki aureni, am i your mate?" Tayi saurin girgiza kai cikin kuka tace "Wallahi ban fada ba Yaya" Mari yakai mata a fuska, ta dafe gurin tana dan qara, ya sake cewa "What's that your name ma?" tayi shiru kan

ta a qasa ya sake mata diri "Answer me" jikin ta har rawa yake tace "Na'ima" yace "Good, your doom has began Na'ima" da haka ya juya ya fice daga

dakin, kuka Na'ima ta fara har jikinta na jijjaga ta sulale anan kan gadon ta kwanta bata daina kukan ba, rana

r ko makaranta bata je ba haka ta wuni cikin hawaye, duk kuma Hajiya na lura da hakan amma tayi biris.....

Shirye shiryen Auren Na'ima da Bilal su Hajiya suka fara babu sanya, a lokacin da Alhaji Abdullahi ya kira ya sanar dasu kawu Ayuba murna sukayi n

ot minding ya Na'iman take, sudai kawai tunaninsu Na'ima zata auri dan Alhaji liqafa ta cigaba, zuwa wannan lokacin Na'ima har rama tayi dan makarantar ma ta daina gane komai yanzu saboda tsantsan damuwa data shiga ciki akan auren, tun daga lokacin da Bila

l din ya shigo mata daki kwanaki bata sake ganinsa ba, nan kuwa yayi magana da iyayensa akan zaije settling wasu sauran ayyukansa dake Lagos sai ya dawo kanon gaba daya, hakan be wani damu Hajiya ba sanin shirin da tayi masa akan hakan dan tasani Lagos ta

kusa fin qarfin dan nata kuma, fagen lefen dai toh sai dai ace Alhamdulillah amma dai kam Hajiya tayi son ranta da kudi, ta siyo abunda taga dama sanin masu kallon kayan ma mutanen qauye ne kuma sai akayi sa'a Hajiya babba tana Abuja gidan danta alokacin d

a za'ayi bikin ma..

Sai ana gobe daurin Auren sannan Alhaji ya tura motoci guda biyu zuwa Adamawa adebo 'yan uwan nasa da matansu suzo bikin, ranar da zasu zo Na'ima kasa zama guri daya tayi bini bini zata dauko tsintsiya kamar me sharan varenda ta zauna

nan bakin entrance din gidan ko zataji shigowansu, inta tuna zata ga Goggo da Anty Amarya sai taji damuwan nata na sauqa kadan, dan tayi making mind dinta sai ta fadawa Goggo batason auren nan da za'a mata, tasani in sauran kawunnan nata bazasu tsaya mata

ba to Goggo zata tsaya mata, gajiya tayi da jiran ta koma cikin gidan wanda babu kowa cikinsa banda tsirarun kawayen Hajiyan, babu wata alama da zata nuna wa mutum wai biki akeyi na dan gatan gidan...

Sai yamma suka iso duk a gajiye, Na'ima najin shigowan

mota ta fita da sauri harda dan gudunta, ganinsu tayi sun fito dukansu suna bin gidan da kallo, kawu Ayuba da Nasiru na fito da kayansu daga boot, saurin qarasawa tayi gurin Anty Amarya tanajin kuka na zuwa mata, rungumeta Anty Amaryan tayi tana murmushi,

Umma dake gefe baki washe tace "Oh ni Jummai, wai Na'ima ce ta koma haka" salame dake gyara goyon danta a baya tace "Toh umma ke bakiga gidan bane, ai Na'ima ta huta itadai" sake Anty Amaryan Na'ima tayi ta koma gurin umma Amma bata rungumota ba amma ta r

iqo hannunta tana murmushi, Hajiya ce ta fito cikin isa Umma tayi sauri karbe hannun ta daga gurin Na'ima ta nufeta tana tace "Hajiya sannu da fitowa" Hajiya tace "Yauwa sannunku da zuwa" sai ta kwala kira wa maigadi tace yazo su miqa kayan can BQ inda sha

fa take zama, sannu tayiwa su kawu Ayuban suka amsa cikin fara'a kamar ba ita tayiwa Ayuban rashin mutunci ba da dadewa, Na'ima sai rarraba Ido take tana jiran ko zata ga goggo acikinsu amma dai shiru sai tace da Anty Amarya "Ina Goggo fa, bakuzo da ita ba

ne?" Tsit gurin ya dauka kowa ya fara rarraba idanu, ita Hajiya sai lokacin ma ta tuna ashe zuwan Ayuba ya fada mata Goggon ta rasu da dadewa, ganin kowa yayi shiru yasa Na'iman kwantar da murya ta sake tambayan Antyn, sai Umma tayi saurin cewa "Tana gida

ai bata Jin dadin jikinta ne shiyasa ba'a zo da itan ba" sanyi jikin Na'iman yayi sosai a haka ta tayasu suka kai kayan can masauqinsu, da dare bayan sun gama dafa abinci da shafa ta tafi kai musu, tasamu duk sun kwamutsu nan falon suna hira, mazan kuma Al

haji yasa ankaisu nan wani gidansa dake cikin gari, Umma ce tace "Na'ima yaushe zamu shiga cikin gidan ne, duk mun matse anan din, gashi Hajiyan tace zatazo kuma shiru" batace komai ba ta ajiye musu

abincin nan tsakiyar falon, salame tace "Ni sai na lura m

a kamar ba mutane fa, sai kace ba biki za'ayi a gidan ba" Umma tace "Ko sai gobe zasuzo inaga, angon ne ma mukeson gani dan bamu taba ganinsa ba" nan kuma jikin Na'ima yayi sanyi, Anty Amarya ta fito daga bandaki ta zauna gefen Na'ima tace "Ya kamar ba'a m

iki gyara ba Na'ima, Hajiyan bata kaiki gurin gyaran jiki bane" nan ma batace komai ba dan tasan inta bude baki to kuka ne zezo shiyasa...

Zuwan da Hajiya batayi ba kenan gashi Na'ima nason jan salame suje dakinta amma tana tsoron Hajiya tayi mata fadan h

aka, sai tayi deciding ta kwanta nan tare dasu amma Umma tace gurin ya musu matsi ta tafi dakinta..

Washegari ranar daurin Auren Hajiya ta kirata da safe ta miqa mata wani lace tace in tayi wanka ta saka, haka ta karba tayi godiya ta fice, Ranan ba qarami

n dauriya Na'ima tayi ba gurin danne abun da takeji a zuciyarta, Lokacin da Anty Amarya ta fada mata an daura auren ji tayi iskan qirjinta ya mata kadan, kawai ta shige bandaki ta sulale jikin qofan tana kuka mara sauti, dasu kawu Ayuba da Alhajin suka kir

ata yi mata nasiha bata ma fahimtar su, dan abunda takeji ya wuce tunani, su Umma jummai dai anan Bq suka qare bikin dan Hajiya bata bar ko dayansu ya kwana cikin main building ba sai dai suje gaisheta sukoma, wannan abu ba qaramin daurewa Anty Amarya kai

yayi ba amma sanin tanayin magana mijinta ze ce ba haka ba yasa taja bakinta tayi shiru..dan komai na bikin bata ganin yana tafiya akan seti..

Na'ima na kuka kamar zata shiqe su Umma na bata hakuri aka sata a mota Sufi ya tuqasu aka kaita nan gidan da Alh

ajin ya siyawa Bilal din wanda babu wani nisan tashin hankali tsakaninsu....

KUNCIN ZUCI

📖📚



Bintu Musa







Chapter 29

Basu wani dade ba suka isa gidan Bilal din da ya kasance bawani babba can ba amma me kyau sannan stair building ne, har

dakin Na'ima dake sama suka kaita, ba laifi Alhaji yayi qoqari sosai gurin saka musu kaya masu tsadan gasken da ko 'yar cikinsa iyakaci, su Umma Jummai sai santin gidan suke bakin su yaqi rufuwa, itadai Na'ima na zaune kan gadon idonta yayi jaaa, sunanan z

aune Larai ta shigo dakin fuskan a dinke tace "Yauwa ga mota can za'a maida kowa gida" su salame suka bude baki cikin mamaki dan sun taho da niyyan kwana ne gidan, Umma zatayi magana anty Amarya tayi saurin miqewa tace "Ku taso mu tafi" fashewa da wani kuk

an Na'ima tayi sai Anty Amaryan ta riqota tana bata hakuri da kuma nasiha, itadai Na'ima duk nasihohin nan da ake mata bata gane komai dan har lokacin bata iya hasko wane irin zama zatayi a gidan bama balle taji aranta ga abunda ya dace tayi, Matar kawu Na

siru ma sai qananun magana take tana cewa "Toh angon da baya nan ne za'a bar yarinya ita kadai a babban gida haka" Larai tace "Ba matasalarku bace wannan, ango kam duk inda yake ai yau zezo tunda an kawo masa amaryarsa" Umma Jummai sai ido ba baki ganin Ha

jiya larai na magana jiki duk gwalagwalai, haka Larai ta tusa kowa na gidan a gaba suka fice Na'ima na kuka, bayan tafiyansu sai ta kalmashe kafafunta a qirjinta anan zaune kan gadon ta cigaba da kukan babu me lallashi...

Har dare yaja Na'ima nanan zaune

sai da taga kukan bazai kaita ko'ina ba sannan ta tashi fara cire kayan jikinta, kayanta ta gani plus na akwatin acikin wardrobe ta nemi dogon riga mara nauyi aciki ta saka sannan ta shiga bandaki tayo alwala, anan dakin ta sake neman sallaya tayi sallahn,

cikin sujud ta rinqa addu'an sauqi cikin lamuranta tana kuka, nan kan sallayan tayi bacci....Washegari tunda ta idar da sallah bata koma bacci sai ta sauqa falon qasa Jin kamar qarar gate, leqawa tayi taga ashe da megadi ma agidan, sai taji hankalinta ta

dan qara kwanciya jin ba ita kadai bace a gidan..har zuwa rana tana ta zuba Ido ko 'yan'uwan nata zasu dawo amma shiru, sai la'asar mota ta shigo gidan Na'ima tayi saurin leqawa taga Sufi ne ya fito daga motan ya qaraso yayi knocking, sai da ta koma ta sak

o hijab sannan ta bude masa suka gaisawa, zama yayi ta kawo masa ruwa sai ya miqo mata kwalin waya tareda kudi masu yawa yace "Gashi inji Alhaji, yace zai kiraki" godiya Na'ima tayi ta karbi wayan tanajin kamar ta tambayesa dalilin rashin zuwan su Umma, mi

qewa yayi ya mata sallama sai ta jefo masa tambayan ya amsa da "Ai sun koma Adamawa tun da safe" daskarewa tayi nan tsaye tanajin hawaye na zuwa mata, sallama sufin ya mata ya tafi, cikin sanyin jiki ta koma daki...

Ashe komawan su Umma washegari da sa

fe Hajiya ta kira motan da zai maidasu gida, aika shafa tayi akan ta fada musu su shirya da wuri drivers din na jiransu, da aka fada musu duk sunyi mamaki barin ma Anty Amarya da ranta yafi na kowa baci, cikin haushi suka fara hada kayan nasu sai ga su kaw

u Ayuba ma sunzo, da aka zo shiga motan ne Anty Amarya tace dashi "Yanzu Fisabilillah yarinyar nan ko sallama bamu je munyi da ita ba zamu koma, hakan ya dace kenan?" Ayuba yace "Toh daman sintiri zakuyi tayi ne gidan yarinya" Umma tace "Toh wai ina angon

ma ni Jummai" yace "Yana hanyarsa ta dawowa daga Lagos, ashe wani uzuri ne ya taso masa babba shiyasa be zo ba" itadai Anty Amarya kawai sauraronsa take amma komai na bikin nan ya sire mata arai kuma tausayin Na'ima take sosai ganin akwai abunda ke damun y

arinyar amma ta danne, saida suka shiga motan Hajiya ta fito ta miqawa Ayuba bunch din dubu ya karba baki har kunne yana godiya Anty Amarya na hararansa ganin shi ko ajikinsa wulaqancin da aka musu.....

Week Later...

Na'ima ita kadai take rayuwa ciki

n kadaicin a gidan kuma abu daya ne ke debe mata kewa shine Jin motsin megadin gidan, inta tashi da safe haka zatayi wanka ta shiga kitchen ta dafa abinci dayake akwai komai na amfani cikinsa, tayi sallah tayi bacci dan ko baqo batayi, dama tun ranar da Su

fi ya kawo mata waya bayan tafiyansa tayi waya da Alhajin suka gaisa ya tambayeta ko akwai abunda take buqata tace babu, hakuri ya bata akan Bilal din yana kan hanyar dawowa wanda ita Na'ima hakan fargaba yasaka mata da tashin hankali be sani ba, tun daga

wannan lokacin kuma bata sakeyin waya da Alhajin ba kasancewan ya fita qasar waje wani aikinsa shima, ranar da ta cika kwana goma sai ta shirya zata tafi makaranta abunta, bayan ta shirya cikin doguwar riganta da hijab tayi sallama da megadin gidan da ya k

asance bafulatani..

Batayi lattin zuwa ba dan tsirarakun mutane ta samu a ajin dayawa basu qaraso ba tukun ta samu waje ta zauna, can sai ga Nafisa ta shigo wadda ganin Na'iman yasata ware idanu ta nufeta, zama tayi nan kusa da ita kafin ma su gaisa tace

"Na'ima lafiyanki kuwa, meya faru bakya zuwa? gashi banida number'n ki balle in kiraki" sai Na'ima tayi murmushi tace

"Wani uzuri ne ya tasomin Nafisa" Nafisa bata ja tambayan ba ganin Na'ima bata sake da ita ba har sannan sai tayi shiru, ranan har yamma s

uka kai kafin su gama school activities din nasu, da Na'ima tayi wa Nafisan sallama sai ta nemi ta rage mata hanya, farko qi tayi sai da Nafisan ta nuna ranta ya baci sannan ta hau motan nata, sunyi nisa cikin tafiya Na'ima ta budi baki a hankali tace "Aur

e akaimin Nafisa" dan burki Nafisan ta taka kafin tace "What?..Aure kuma" Na'ima na kallonta ta gyada kai batace komai ba, ta sake cewa "Yaushe? within last week zuwa yanzu kenan?" Na'ima tace "Eh", da farko shiru Nafisan tayi sai ta dan yi murmushi tace "

Ayya Allah ya sanya alkhairy kice da amarya nake tare yau din" murmushin dole Na'ima tayi batace komai ba suka cigaba da tafiyan cikin shiru, sake kwantantawa Nafisan sabuwar unguwar su Na'iman tayi, bayan sun isa sai Nafisa ta kalleta tace "Na'ima, to tel

l you the truth gaskiya banji dadi ba, I understand that baki sanni sosai ba or you don't want to be friends with me, amma ace har kiyi aure bazaki fadamin ba in miki ko addua ma" sai jikin Na'ima yayi sanyi tace "Dan Allah kiyi hakuri auren ne yazo cikin

gaggawa shiyasa, na dade da daukanki matsayin kawata wallahi Nafisa, ga wayata ma ki sakamin number'n ki" karban wayan Nafisa tayi tace "Kuma dama tun can da goron sa ne akanki shiyasa akayi auren da wuri haka?" Na'ima ta danyi shiru sai tace "Cousin dina

ne" Nafisa ta gyada kai sai Na'ima ta sake cewa "Ki shigo mana ko ruwa kisha" sai Nafisa ta dan girgiza tace "A'a Amarya Nagode sai wani lokaci, may be ma Ango yananan ciki yana ta jiran dawowarki" ta qarasa maganan tana dan dariya, da farko dan stiff Na'i

ma tayi sai tayi murmushi ta mata sallama ta fice daga motan cikin sanyin jiki...

Kwance Bilal yake akan gado tareda stella dake kwance jikinsa, tunda Bilal ya dawo garin Lagos yake tunanin ta inda zai fadawa Stella maganar auren da akayi masa, gashi Al

haji ya bashi adadin wasu lokuta akan ya koma, shafa attachment din stella'n yafara yi a hankali yace "Baby i want us to talk" dago kai Stella tayi tana murmushi tace "What is it Baby?" Yana kallon idonta ya sake kwantar da murya yace "You know i love you

right?" Ta gyada kai tanajin wani dadi a zuciyarta, yace "No matter what.. you'll always be my woman, no one else" dan gyara kwanciya tayi takai hannu tana shafa fuskansa suna kallon kallo cikin ido, sai da ya sauqe numfashi yace "Iyaye na sunmin Aure Baby

" dan stiff tayi daga kwancen sai kuma ta fara kokarin miqewa daga jikinsa ya kamota ta yi saurin fincike hannun tace "Don't you dare touch me" miqewa sukayi dukansu suka tsaya nan tsakiyan dakin tace "Wallahi baka isa ba" ya girgiza kai kafin yayi magana

ta kai hannu tafara dukan qirjinsa tace "You've betrayed me Bilal, bamuyi haka dakai ba" ya rugume ta tareda cewa "Ke kadai nakeso Baby and you know that" hankali tashe Stella tace "You're not going anywhere Bilal" ta dago kai ta kallesa ta fara hawaye tac

e "In ka taba wata mace zan iya mutuwa" yayi saurin girgiza kai yace "What are you saying Baby? Me zanyi da yarinyar can da banason ganinta ko na minti daya" rungume ta yayi ya cigaba da fadin kalmomin lallashin da duk sukazo bakinsa, a wannan lokacin ji t

ake komai zata iya yi akan Bilal din kuma har iyayensa bazata bari ba....

A rikice Stella taje gidan qanwarta yammacin ranan bayan sun gaisa chiamaka ta fara tambayanta meya faru ganinta ba'a nutse ba, Stella tace "Shikenan Chi, they've won against me,

aure iyayen Bilal suka masa" chiamaka ta ware Ido tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login