Showing 72001 words to 75000 words out of 121625 words

Chapter 25 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

33

nufi sama da sauri ransa a bace, tsugunnawa tayi ta fara kwashe kayan

idonta na cikowa da hawaye, saida ta gyara gurin sannan tafi dakinta, tana tsaye gaban mirror tana shafa rob a ciwon dake gefen idonta tajiyo fitar motansa, da sauri da shirya itama amma madadin ta tafi makaranta sai ta wuce gidansu aranta tana addu'an sam

un Alhaji....

Complete din Book dinnan yana kan Arewapen App for Free, Please like the story and follow my account...

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 31

Isarta gidan nasu bayan ta sallami mai mashin suka gaisa da megadi sannan

ta shiga cikin gidan tana gyara face mask din fuskanta, shiganta falon yayi daidai da fitowan Hajiya daga corridor'n kitchen hannunta riqe da tray alamun zata kai breakfast din Alhaji, tsugunnawa Na'ima tayi har qasa ta gaishe da Hajiyan ta amsa tana mata

wani kallo sai tace "Zauna anan bari inzo" gyada kai Na'ima tayi tareda amsawa da toh sannan ta zauna anan main falon Hajiya ta wuce sama, bata wani dade ba ta dawo, nan falon ta zauna tana kallon Na'iman tace "Ya da sassafe haka?" Na'ima ta danyi jim bata

ce komai ba kanta a qasa sai Hajiyan tace "Zama zamuyi tayi cikin shiru kenan" ta girgiza kai idonta na kawowan hawaye ta sauqe face mask din, kallonta Hajiya ta tsaya yi fuskan ta babu alamun wani emotion guda daya, cikin rawan murya Na'ima tace "Dukana y

ayi jiya Hajiya" kadan ya rage Hajiya batayi tsaki ba ta danne zuciyarta tace "Shine dan Miji ya dake ki sai ki taho gida da sassafen Allah ke mai iyaye kenan, kin fa san waye Bilal kuma kinsan muma a sannu muke bi dashi a gidan nan, in kikace

bazaki saka

hakuri cikin lamuranki ba to bazaki taba ganin daidai ba Na'ima, kowa da kika gani hakuri yake a gidan mijin nan, asannu ake bin miji sai kiga komai yawuce kamar ba ayi ba" Hawaye Na'ima ta rinqa yi tanajin zuciyarta na mata zafi, a hankali ta amsa da "Toh

Hajiya" miqewa Hajiyan tayi tace "Alhajin na bacci yanzu kije tukunna, dududu ma auren naku wata nawa ne ma har kin fara kawo qara Na'ima, hakane hakurin naki da muka sanki dashi kenan?" Na'ima ta girgiza kai bata daina hawaye ba, sai Hajiyan ta sake cewa

"Ki koma gida yanzu, in ya tashi zan san yanda zan masa maganan, kuma shima Bilal din zan ja kunnenshi" sai Na'ima ta gyada kai tareda miqewa itama tace "Zanje daukan kayana a daki" sai Hajiyan ta gyada kai tareda cewa "Toh, ki gaida gida, arinqa hakuri s

hine ribar zaman duniyan gaba daya" nan kuma Na'ima batace komai ba ta nufi dakinta da take zama a gidan a da Hajiyan na bin bayanta da wani kallo har sannan bata dai yi tsukan ba amma ita kwata kwata ma ji take ta tsani Na'iman, saboda ada tayi zaton aure

n zai zaunar da dan nata a garin sai kuma taga ba haka ba shikenan ta fara shiga dana sanin auren wanda har hakan kusan saka sabani yayi tsakaninta da Larai, ga abunda ta gano kwanaki a dakin Alhaji cikin takardun dukiyarsa...

Na'ima na shiga dakin ta f

ara kuka mara sauti ta zauna kan gado, tasani Alhajin na nan bai fita ba kuma taci alwashin sai ta hadu dashi yau dan babu wani abu da zata dauka a dakin kawai zaman jiran fitowan Alhajin zatayi, aikuwa bata wani dade ba taji alamun sauqowarsa yana waya ya

fita daga falon, cikin sauri ta fito daga dakin ta bishi, iddashi tayi a parking space yana waya har sannan bai gama ba sai ta tsaya tana jiran ya gama, bai dauki mintuna ba ya gama ya juyo yace "Ahh Na'ima yanzu kikazo ne, ya gidan naki" gaishesa tayi ya

amsa sannan ta ja face mask din fuskanta ciwukan fuskanta duk suka bayyana, kafin yayi magana sai ga Hajiya ta fito, juyawa Na'ima tayi ta kalleta sai da zuciyarta ta tsaya na wasu daqiqu ganin Bilal abayanta shima yana tahowa, hankali adan tashe Alhaji y

ace "Meya samu fuskarki haka Na'ima?" kasa magana tayi sai Hajiya tayi saurin cewa "Wai faduwa fa tayi a bandaki jiya shine tazo ta nuna mana" Alhaji ya sake kallon Na'ima yace "Subahanallah garin yaya haka ta faru?" sai Na'ima tayi qasa da kanta wasu hawa

yen na cikowa a idanunta, Alhaji ya juya ya kalli Bilal yace "Kana kula sosai Dan Allah son" sai ya sake kallon Na'iman yace "Sannu Na'ima Allah ya kare na gaba" Hajiya tace "Ita ce ai ya kamata tana kulan, banda rashin nutsuwa kawai sai ki fadi a bandaki

da girmanki" shidai Bilal sai kallon Na'ima yake yanajin ranshi na qunaa, Alhaji yace "Duk ba wannan ba yanzu dai son ka wuce da ita asibiti a wanke ciwon nan babu dadin gani" ciki ciki Bilal ya amsa da "Toh" sai ya kalli Na'ima yace "Ki samoni a mota" ya

qarasa magana tareda sallama a iyayen nasa, cikin tararradin Na'ima ta musu sallama Alhaji na sake mata sannu har da Hajiyan ma dan ganin idon Alhajin, sannan ta bi bayan Bilal din zuciyarta na bugawa, saida ta shiga motan ya tada suka fice daga gidan Alha

ji ya kalli Hajiya yace "Sai naga kamar batada lafiya ma, ko an samu qaruwa ne?" da sauri Hajiya ta kallesa sai tayi masking fuskan nata da murmushi tace "Ze yiwu, ai kasan yanzu wata kunya ta qaro, nikuma na fada mata ba sirikarta bace ni" Alhaji na murmu

shi yace "Allah yasa muji alheri" azuciyarta tace "Ba Amin ba" a bayyane tace "Amin" tana murmushi.....

A hanyarsu ta komawa Bilal baice da Na'iman qala ba kuma har sannan ji yake kamar ya shaqeta ko zai huta ma shikam, kiran wayansa akayi ya dauka tareda

sakawa a handsfree, Stella dake dayan bangaren tace "Baby har zanyi fushi bazaka kulani ba" yace "In kina biye Nasir zamu samu matsala

sosai kinsani" cikin shagwaba tace "Dagaske ne ya ganka da macen a club din fa, raina ne ya baci na koma Lagos" ya dan g

yada kafada yace "I'm not in the mood for this right now, I'll talk to you later" da haka ya kashe wayan be jira cewarta ba ya juya ya kalli Na'ima dake kallon window still be ce komai ba, gidan nasu ya nufa kamar yanda Na'iman tayi predicting, bayan yayi

parking suka fito sai taji kamar ta ruga da gudu ta fita daga gidan, bece komai ba ya nufi entrance din gidan ta bishi a baya cikin sanyin jiki, bayan sun shiga har ya fara takawa stairs sai ya juyo ya fara takowa gareta, da sauri ta juya zata gudu waje ya

funcikota ya hada kanta da hannun kujera, ihu tayi yana kallonta cikin bacin rai yace "Na'ima har kinyi gut din da zaki kai qarana gurin iyayena" tayi saurin girgiza kai hawaye na fitowa a idonta, ya sake cewa "Do you think ko matan duniyar nan zasu qare

I'll give a f*ck about you?" Nan ma ta girgiza kai bata bar hawayen ba, ganin kallon da yake mata yasa ta bude baki zata bashi hakuri ya dauketa da mari...ranan jikin Na'ima ya fada mata a hannun Bilal saboda duka ya mata sosai har se da ya gaji dan kansa

ya barta nan kwance gefen dining table jikinta babu qarfi, wucewa sama yayi yana cewa "It's you or me in this house Na'ima, get that in your dumb skull" sai sannan ta bude bakinta tafara kukan cikin sauti tana jin ta tsani komai a duniyar, a wannan lokacin

ji tayi tanason mutuwa dan ta huta da komai ma, tananan zaune ya fito ya sake wuceta ya fice daga gidan gaba daya, sai da taji kiran salla ta tashi tana jan jikinta ta wuce dakinta bata daina kukan ba wanda a sannan sautinsa baya fita ma... Dakyar ta wayi

gari washegarin ranar saboda komai nata jinsa take ba daidai ba, a hakan ta hada masa breakfast, data kawo masa nan inda yake zaune a falon yace "Fitan da kikeda freedom din yi ne yasa har kikeda tsaurin idon kai qarata gurin iyaye na, zanyi maganinki" ba

tace komai ta cigaba da zuba masa tea din tayi serving dinsa sannan ta miqe ta wuce sama cikin sanyin jiki yana kallonta, bata tashi yarda da maganansa ba sai da tazo fita zataje makaranta taga ya kulleta ta waje, dawowa tayi bakin window nan ma bataga ala

mun megadi ba, sai ta sulale nan gurin tafara wani kukan..

Fitan Bilal daga gidan ashe bayan ya kulleta sai ya sallami megadin yace zasuyi tafiya, daganan waya yayi da iyayen nasa akan maganar tafiyarsa da zeyi na company dinsu zuwa qasar china, har Alh

aji yace ya tafi da Na'ima amma tuna tana makaranta sai bai ja da maganar Bilal din da yace ai yayi magana da Na'iman akan zata rinqa binsa can lokaci zuwa lokaci ba, Hajiya dai daman tun dawowan Bilal din da ya fada musu batun tafiyan bata nuna tana so ba

har sannan, amma haka ta hakura sukayi sallama sanin dolenta zataje ganinsa bada jimawa ba..A ranan yayi sallama da iyayensa ya wuce Lagos da nufin ya dauki Stella su wuce china'n...

Wuni biyu Na'ima tayi cikin gidan tana jiran dawowarsa gashi maigadi da

ya tashi tafiya se ya kashe wutan gidan ta waje babu halin ta fita ta kunna, a rana ta ukune wayanta daya kusa mutuwa kiran Nafisa ya shigo wayan ta dauka da sauri idon ta na kawo hawaye, Nafisa dake dayan bangaren tace "Na'ima shiru kwana biyu ko a school

ban ganki ba, gani kofar gidanki kuma gate din a kulle" Na'ima batakai da magana ba wayan ya mutu ta nufi window da sauri, daga nan tsaye ta hango motan Nafisan sai ta juya cikin gudu ta sauka qasa ta dauko kwanon silver tadawo nan bakin windon tana bugaw

a da aqarfi ko Nafisan zata jiyo ta, bugawa take tana kiran sunan Nafisa sai gani tayi motan ya fara tafiya ze bar layin ta fashe da kuka me qarfi kanta na jikin windon...sai da Na'ima tayi sati cikin gidan bataga hanyar da zata fita ba, babu ranar da bata

kuka da roqon Allah ya

kawo mata dauki, a rana na takwas ne tana kwance nan falon tajiyo kamar qarar gate an bude, da sauri da nufi window sai ta ga megadin ne ya shigo, same abunda tayi na ranar da Nafisa tazo shi tayi yau ma, megadin ya taho building di

n da saurinsa tace "Ka budeni Dan Allah" nan ya ciro key ya bude ta tareda cewa "Hasbunallahu Hajiya kayi hakuri wallahi bansan kana nan ba, megidan cemin yayi kunyi tafiya inje gida, kaga dawowar nan danayi ma rashin abunda zanyi ne acan garin yasani na d

awo" Na'ima ta gyada kai tareda wucesa ta fita compound din ta tsaya dan gidan ma wani iri take jinsa, hakuri ya dinga bata har saida tace babu komai yaje abunsa sannan ya hakura, sai dare ta koma cikin gidan bayan ya kunna mata wutan gidan, da ta bude way

anta message har kusan guda sha biyar daga Nafisa, nan take ta kirata, tana dauka ta fara tambayan meya faru, sai Na'ima tasamu kanta da cewa tayi tafiya qauye ne, Nafisa tace "Tafiya kuma babu sallama, naje can gidan ku ranan basanan suma" Na'ima tace "Ki

yi hakuri dan Allah gobe zan shigo school muyi revision" da haka sukayi sallama..

Washegari da safe kuwa ta shirya ta tafi makaranta duk da batada abunda zatayi sai karatun saboda anyi placing time table dinsu, saida Sufi ya kirata dan sanar da ita ya t

ura mata kudin watan da ake bata sannan taji labarin tafiyan Bilal, shima a dalilin gaisheda Bilal din dayace tayi in sunyi waya, a wannan lokacin Na'ima ji tayi kamar an yaye mata damuwanta, babu abunda take fata irin yayi dogon zama acan kar ya dawo...

Haka Na'ima ta sake runguman rayuwa da karatun ta sosai, tun tana tararradin dawowan Bilal har ta sake ranta jin shiru bai dawo din ba, lokacin da suka fara exams da tayi waya da iyayen nata sai Alhaji yace ko zata koma can gida, ganin tana ta kame kame sa

i yace to tayi zamanta nan gidan mijin nata amma ta kula sosai..Sunyi exams dinsu sun gama lafiya a wannan hutun ne ta fara zuwa gidansu Nafisa, ranar da taje tun shiganta falon gidan tagane mutanen nan sun mata sani sosai a gurin Nafisa, Mami na falon Abb

a lokacin sai su Al'ameen tasamu a babban falon gidan suna PS, da gudu Nafisa ta sauko daga stairs ta rungumeta su Al'ameen na dariya wai finally aminiya tazo, Jan hannun Na'iman tayi ta kaita har falon Abba su gaisa, Na'ima na ganin Mami ta fara murmushi

zata zauna nan qasa sai gani tayi Mami ta miqe ta rungumota tace "Lale lale Na'ima munata jiran zuwanki shiru" Abba dake zaune yace "Yau zamu huta gurin Nafisa tunda Na'ima tazo" duk sai suka kama dariya harda su Al'ameen da Abu dasuka shigo suma, cikin ji

n kunya Na'ima ta gaishesu suka amsa cikin fara'a, nan falon suka zauna tun Na'ima najin nauyi har ta fara sakewa dan hira taga iyayen nayi da 'ya'yan nasu gashi an cika mata gabanta da kayan marmari, tashi Nafisa tayi ta riqo hannun Na'iman tace da iyayen

nata "Mami zamuje dakina" suka amsa da "Toh" Abu harda cewa zai bisu Nafisa ta hararesa while Na'ima na murmushi..wuni tayi a gidansu Nafisa cikin walwala ranan suna hira, da ta tashi tafiya ma Nafisan ce ta maidata gida tare da rakiyar Abu, sai da suka t

saya wani mall suka sayi kayan ciye ciye sannan suka kaita har gidanta ta musu sallama tanajin wani iri aranta...daga wannan ranar kuma wani zumunci ya sake dorewa tsakaninta da Nafisa da kuma 'yan'uwan ta...

Three years Later..

Na'ima tayi salloli t

ayi addu'o'i kuma Allah ya karbi addu'an ta ya zaunar da Bilal a qasar da yaje, while Hajiya tayi addu'o'i tayi kuka akan Bilal yadawo amma abun yaci tura, Alhaji yayi fadan, yayi fushin

amma Bilal bai waiwayo gida ba, a wannan shekarun abubuwa dayawa sun

faru, Na'ima taje Adamawa har sau uku kuma ko wanne da kayan tsarabarta lodi guda take zuwa amma ko "Ya hanya" babu wanda yake kira daga cikinsu yaji daga gareta inta dawo Kano, zuwanta da tayi na farko tasha kuka Jin labarin mutuwar Goggo, su Ayuba sunana

n a yanda Allah ya yisu, still those selfish and ingrates people da Na'ima ta sansu dai sudinne har wannan lokacin dan afili suke nuna son abun hannunta, a lokacin da taje din duk wani kudin cefane na gidan a gurin Na'ima ake karbansa, sai da ta koma ciyar

da gidan na wannan satin har kudin motan dawowa yaso gagararta..

Zuwa wannan lokacin abunda ke cin Hajiya akan Na'ima har ya fara bayyana, dan Na'ima tararradin zuwa gidan take saboda maganganun da Hajiya ke jefo mata na auren ta da Bilal ne silan qin

dawowarsa qasar ma, dan da babu auren at least ze waiwayo gida, da akwai ranar da Hajiyan tace "In dan Bilal ya dakeki ne kika kadamin shi toh gwara tun wuri kisan yanda zakiyi ki dawomin da dana, dan na lura ke ba damuwarki bane zama qaramar bazawara" wan

nan magana ta tsayawa Na'ima a rai sosai...

Zuwa wannan lokacin har dan qiba Na'ima tayi na kwanciyar hankalin da tasamu a gidanta, batada damuwa sai na makaranta, dan ko da wasa bata taba jin babu dadi na rashin dawowan Bilal ba, har mantawa take da au

ren ma wani lokaci, bata waya da Alhajin akai akai saboda shi nauyinta yakoma ji akan rashin dawowan Bilal din, zuwa sannan wani license me qarfi Na'ima ta samu na zuwa gidansu Nafisa freely abunta, ko Nafisan bata nan tana iya zuwa su taba hira da Mami da

sauran mutanen gidan amma bata samun Faruk saboda zaman Abuja yake yi, mostly sai weekend na biyu zuwa uku yake dawowa nan kano...makarantansu suke yi itada Nafisa hankali kwance inda a yanzu suna final dinsu ta fannin computer science dasuke karanta, duk

wanda yasan Na'ima shekaru uku zuwa hudu da suka wuce ya sake kallonta yanzu sai ya ga chanji sosai, da karfi da yaji Nafisa ta rabata da saka hijaban nan zula zula, sai dai bata cikason saka gyale ba sai ta dauko saka abaya sosai, kala kala Nafisa ke tus

ata su je siyowa, wannan yanayin na Na'iman ba qaramin baqin ciki yake sakawa Hajiya ba ganin hankalinta kwance bayan danta yanacan wata qasa dawowa ta gagara..

Ina Labarin Bilal?....wata sabuwar rayuwa ya bude a Shanghai dake cikin qasar China, gida comp

any din nasu suka bashi acan duk a tunaninsu Stella iyalinsa ce, dan rayuwansa yake da Stella tamkar matarsa, saida Hajiya ta kusayin dambe da Stella a wani zuwa da tayi ganinsa, da kuka tabar gidansa tana fadin "Yaje ta yafesa a Stella" wannan maganar ba

qaramin tsayawa Bilal arai tayi ba, tun daganan hankalinsa ya fara karkata kan komawa gida kuma, ta fannin aurensa da Na'ima kuma bawai mantawa yayi ba, asali ma rashin nemansa da tayi tsaya masa a zuciya hakan yayi dan yana yawan tunawa da ita, amma tauri

n kai irin nashi ya hanashi daga waya ya kirata, har zuwa sannan bazaice ga abunda yakeji akanta ba, iya saninshi Na'ima batakai matsayin aurensa ba, bata daga cikin kalan matan da yakeso, yana riqe da aurenta a wuyansa ne saboda bin umarnin iyayen sa..A l

okacin da ya tashi komawa gida sunyi rikici sosai da Stella har hakan yasa shi tafiya ba tareda yabi ta kanta ba, inda hankalin Stella ya tashi matuqa acewarta Bilal yafara juya mata baya, ba shiri itama ta koma Lagos....

A ranar da Bilal ya isa Kano gida

nsu ya fara zuwa, ga mamakinsa sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login