Showing 78001 words to 81000 words out of 121625 words
gaba day
a, tananan kwance nurse din ta dawo tana mata sannu ta duba qarin ruwan da akayiwa Na'iman sannan ta taimaka mata ta miqe ta kaita bandaki, dakyar tayi alwalan bayan tayi sallah nurse din ta sake taimaka mata ta koma kan gadon, tananan kwance Bilal ya shig
o suka hada ido, juya kanta tayi other side of the room dan bata son ganinsa ma a wannan lokacin, qarasowa yayi bakin gadon yana kallonta yace "Ya jikin" kuka ta fara yi bata juyo ta kallesa ba, sai da ya gaji da tsayuwa ganin bazata juyo ba yasashi sake f
ita daga dakin, haka Na'ima ta wuni ita kadai a dakin sai Nurse dinnan ce ta taimaka mata da abinci da rana ganin babu wanda yazo duba yarinyar, sai dare Hajiya da Alhaji suka shigo dakin tareda Bilal, tsayawa a baya Bilal yayi while Alhaji ya riga Hajiya
qarasawa bakin gadon yace "Sannu Na'ima, yanzu yake fada mana abun da ya faru" Hajiya ta qaraso bakin gadon itama cikin nuna alhini tace "Sannu daughter, Allah ya kiyaye na gaba, dan Allah ki rinqa kula sosai Na'ima, taya zakiyi mopping baki nutsu kin goge
ruwan ba, yanzu badan Allah ya taqaita ba da sai dai wani labarin daban fa" Alhaji na kallon bandage din kafadan nata yace "Ta yaya kika yanke kuma" Hajiya ta saurin
cewa "Riqe take da plates din abincin lokacin da hakan ta faru ai" Alhaji ya sake cewa sa
nnu sannan ya zauna nan bakin gadon, abincin da Hajiyan ta shigo dashi ne ta zuba a plate ta miqawa Na'iman, sai sannan ta dago kanta idonta cike da hawaye ta karba ahankali tace "Nagode" bakin gadon Bilal yazo sai Alhaji yace dashi "Kayi magana da likitoc
in babu wani internal injuries dai ko" gyada kai yayi yace "Sun ce za'a cigaba da kula da ita tukunna incase of that" Hajiya ta zauna a kujera tace "Allah ya kare na gaba, ki rinqa kula du Allah Na'ima" itadai Na'ima kanta a duqe tana cakulan abincin dake
gabanta batace komai ba, ji take komai na duniyan ya fita kanta, sai da su Alhajin suka shafe awa guda a dakin kafin su mata sallama suna qara mata sannu, Hajiya harda fadin zata dawo da safe, Na'ima ta amsa suka fice tareda Bilal din, bai dade ba yadawo d
akin still taqi dago kanta ta kallesa, zama yayi bakin gadon yana kallonta yace "Sannu" bata dago ba har sannan idonta cike da hawaye, a nutse yace "Na'ima" sai a sannan ta dago kanta ta kalleshi hawayen na bin fuskanta cikin sanyin murya tace "Yaya dan Al
lah ka sauwake min" dan stiff yayi yana kallonta sai ta sake cewa "Ka sakeni dan girman Allah" miqewa yayi ransa a bace ya buga tsuka tareda juyawa ya fice daga dakin, kuka me sauti Na'ima ta fashe dashi ranta na quna...Dawowan da Bilal bai sakeyi asibitin
ba kenan dagashi har iyayen nasa, dan Alhaji da ya tambayi Hajiya ma cewa tayi an sallami Na'iman ai.
Ganin shiru babu ko abinci da zataci yasata Na'ima karban aron wayan nurse din ta kira wayan Nafisa, jin switch off yasata kiran sufi dan dukansu biyun
ta haddace numbernsu a kanta, bayan Sufi ya dauki wayan suka gaisa tafada masa tazo asibiti ne batada kudi kuma, nan take Sufi yace "Ayya sannu Na'ima, ki turo account number'n yanzu, ai bansani ba da nazo, dan yanzu ma haka ina zaria Alhaji ya turani wani
aiki, amma in sha Allah zanzo dubaki in na dawo" ta gyada kai tareda yi masa godiya sannan sukayi sallama yana qara mata sannu, through nurse din ya turo mata kudin, dayake ta hadu da mace ta gari sai taje ta ciro mata kudin harda siyo mata abunda take bu
qata, da wannan kudin Na'ima tayi settling bill na asibitin ranar da aka sallameta, likitan ya tambayeta ina mijin nata ya shige, dan ya kirashi baya dauka, rasa me zatace Na'ima tayi sai kawai tace yayi tafiya, nan likitan ya hau mita, nurse dinda ke gefe
nsa wadda take kula da Na'iman sai kallonta take fuskanta cike da tausayi, da ta tashi tafiya hakuri ta bawa nurse din me suna Amina akan zata dawo mata da kayanta dake jikinta tace bakomai, cikin sanyin jiki ta fito daga asibitin ta nemi abun hawa ya kait
a gida..
Isarta gidan bayan megadi ya bata makulli bata samu kowa cikin gidan ba, nan bakin stairs ta tsaya tanajin abunda ya farun na dawo mata sabo, kuka ta fara cikin sanyi jikin ta fara taka stairs din ta qarasa dakin nata, dauko akwatin ta tayi ta fa
ra hada kayanta bata daina kukan ba, sai da ta gama hada komai sannan ta shiga bandaki da nufin tayi wanka, dakyar tayi saboda gudun karta jiqa bandages din da suke bayanta da kafadan nata, har sannan goshinta da bandage din, shiryawa tayi cikin atamfa da
babban jalbab brown ta fara cicciban akwatin nata ta fice daga gidan bayan ta bawa megadi makulli, tashan da zata samu motan Adamawa ta nufa aikuwa bata dade ba motansu ya tashi, suna tafe tana addu'an Allah ya dafa mata yakawo mata qarshen wannan iftila'i
n na rayuwanta.....
Sai yamma liqis suka isa, ta tari mashin yakaita har qofar gidan kawunta Ayuba, tana shiga gidan su Umma dake abincin dare suka dago kai suna kallonta har Anty Amarya dake zaunen itama, Kamal yace "Hajiya Na'ima sauqan yaushe" Na'ima b
ata amsa ba ta tsugunna tana gaishe da matan kawun nata sunata bin fuskanta da kallo, miqewa Anty Amarya tayi ta qaraso
gurin Na'iman tace "Na'ima meya sameki haka" Umma tace "Ni sai naga kamar duk ta fita hayyacinta ma" Anty Amarya na kallon Na'iman tace
"Jeki daki ki huta tukunna" gyada kai tayi ta nufi dakin Anty Amarya suka bi bayanta da kallo..
Ranan Na'ima har shidewa take dan kuka gurin fadawa musu abunda Bilal din yake mata, ahakan tana kasa fadan wasu abubuwan ma, Umma dake tsaye bakin kofa ta riq
e baba tace "Wai dama dan giya ne yaron nasu daman, innalillahi wa'inna ilaihi rajiun dama karuwan har lasisi ne dasu haka a kanon" Anty Amarya da ke Jin ranta duk a bace tace "Kiyi hakuri Na'ima in Sha Allah komai yazo karshe bari kawun naki ya shigo" Na'
ima ta gyada kai bata bar kukan ba, sai dare Ayuba yadawo kasancewan yaje wani qauye nan kusa saro kayan miya, bayan ya gama cin abinci matan nasa suka sako masa magana, cewa yayi su kira masa Na'iman, da taje dakinsa har sauqe masa riganta kadan tayi dan
yaga kafadan nata, sannu ya rinqa mata yace taje zai kira Abdullahin yaji komai, aikuwa daren ranan sai ga kiran Hajiya a wayan Ayuba tace tana kan hanyan zuwa nan da kwana biyu dan maganar bata Alhaji bace ita tasan komai, zatazo suyi magana, cikin ladabi
Ayuba ya amsa da "Toh Allah ya kawoki Hajiya, dama ai kece uwa dole komai zai zamo da saninki" da haka sukayi sallama, cikin kwana biyun nan Anty Amarya tayi ta bawa Na'ima qarfin gwiwa sosai, da kanta take dafawa Na'ima abinci sannan ta tusata a gaba tac
i, Ranan da Hajiya ta iso gidan, nan tsakar gida Umma ta shimfida mata tabarma sai nan da nan take da ita kuttu kamar ya kashe Anty Amarya, fitowa Na'ima tayi ta gaisheta sai taqi amsawa ranta abace "Ni ban cancanci gaisuwa gurinki ba Na'ima karma ki gaish
eni, sai yanzu na tabbatar baki daukeni uwa ba" Anty Amarya ta tabe baki, Umma tayi saurin cewa "Haba dai Hajiya ai kaf duniya Na'ima batada uwar da ta wuce ki yanzu, riqon da kika mata ai ko yar cikin ki iya kaci" Hajiya ta tabe baki tace "Ita ai batasan
da hakan ba, shi dan yau dama kai dai kayi masa komai dan Allah kawai"...Kiran Ayuban Hajiyan tayi cikin sauri yadawo gidan, nan zaure aka shimfida musu tabarma Hajiya ta hau masa bayanin qanzon kurege, sai da ta shafe awa biyu tana magana Ayuba na fadin "
Hakane" "Hakane" "Ayi hakuri Hajiya" "Na'ima bata kyauta ba" maganganu iri iri dai marasa dadin ji..Da Ayuba ya tashi shiga gidan Hajiya bata bishi ba tananan zaune ya shige yabarta..
Cikin bacin rai yafara kwala kiran Na'ima, tayi saurin fitowa ya nuna t
a da yatsa yace "Fito ki tattara kayanki ki koma dakin mijinki, wato kina tsammanin zan goyi bayan rashin mutuncin da kike musu ne ko, Ashe ke nan har dambe kikayo da 'yar'uwar mijin naki sannan kika taho" Umma tace "Bangane ba Malam" ya kalli Umma cikin b
acin rai yace "Toh Na'ima dai 'yar uwar mijin nata ce taje gidan shine tsabar kishin bala'i sukayi dambe har abun yakoma kanta yarinyar ta ci galaba akanta ta turata ta fado daga benen" ya juya ya kalli Na'ima da ta shiga shock yace "Ke yanzu duk riqon ama
nan da mutanen nan suka miki sai kice bakyasan nasu Na'ima, maimakon ki riqe gidan mijinki sai ki tsiro da wani halin daban kenan, to wallahi ni Ayuba bazan lamunci rashin da'a ba, ki dauko akwatinki ga Hajiya can tana jiranki zaku koma tare" kuka Na'ima t
a fara, Anty Amarya na tafa hannu rai bace tace "Ke duniya..Allah ka rabamu da son zuciya" sai ta kalli Malam cikin Ido tace "Wallahi Malam kaga hakkin yarinyar nan, shi kadai sai ya hanaku kwanciyar kabari" atare Umma da Ayuba suka bude baki suna kallonta
, Umma tace "Abida lafiyanki, yarinya tayi ba daidai ba shikenan uban nata bazai ganar da ita ba" cikin bacin rai Ayuba yace "Abida ki tafi gidanku sai na nemeki, dan bazan zauna da matar da kemin fatan rashin gamawa da duniya qalau ba" Anty Amarya na kuka
tace "Wallahi Ayuba bakada zuciya me kyau, Allah wadai da halinka, mutanen da
basu dauke ka a bakin komai ba shine zaka bata lahirar ka dominsu, inace shekarun baya daka je sai daganan muka rinqa hada kudi muka tura maka sannan kasamu kudin motan dawowa m
a, sai yanzu dan ta zo ta baka wasu aninai da basu taka kara sun karya ba zaka maida marainiyar Allah'n nan gidan mashayin dan nasu, wallahi sai kayi bayani a gaban Allah" cikin bacin rai Ayuba yace "Ki fita ki barmin gida Abida, 'ya kuma tawa ce, abunda y
a dace inyi shi zan aiwatar akanta" tsugunnawa Na'ima tayi nan tsakar gidan tana kuka Umma tace "Sai hakuri Na'ima, kowama hakurin nan yakeyi, ke naki hakurin ma tare yake da kudi, Allah na tuba yau ko yanka namanki sukeyi ai kya zauna, wataran sai labari
duk ze wuce" Anty Amarya kasa magana tayi wa Umman saboda takaici ta shige dakinta...da kuka Na'ima ta sake dauko akwatinta Ayuba ya rakata har bakin motan da Hajiyan ke hakimce a baya, wani kudin ta sake cirowa ta miqawa Ayuban tace ya qara akan wanda ta
basa yayi cefane, godiya ya rinqa yi yana ba Hajiyan hakuri "Ku cigaba da hakuri Hajiya Allah ne kawai zai baku ladan hakan, yaron yau ne ka haifesa amma ba ka haifi halinsa ba" ...A hanyarsu ta komawan babu wanda yayi magana cikin ita da Hajiyan sai da su
kayi nisa Hajiyan ta fara zazzaga bala'i Na'ima ta kwantar da kanta a jikin window tana hawaye aranta tana ayyana "Yau ta sake fahimtan ko mutuwa tayi ba damuwan kowa bane a kaf danginta, Yayun ubanta sun nuna mata sunfi son duniya akanta, qanwar uwarta ba
ta sake waiwayanta a rayuwa ba, gidan mariqan ta kuma son zuciya da son dansu ya rufe musu ido, mijin nata ma kilaki ta fita a wajensa.....yau tagane in ta mutu ba faduwar kowa bane, yau tagane bayan Allah batada wanda zai tsaya mata a rayuwa kuma..
Masi
fa Hajiya ta rinqa yi driver na bata hakuri tana fadin "Ke yanzu kaf duniya ba gidan Bilal din bane gatanki da zaki sa kafa ki tafi qauyen naku, banda rashin godiyan Allah ma ace baki rasa ci ba, baki rasa sha ba, har makaranta gashinan kinayi amma sai ki
kasa hakurin zama da jinin mu Na'ima, dan cikin Alhajin kike gudu" ci kanki Na'ima batace ba tanata hawaye....
Sai dare suka isa Kano, har kofar gidan Bilal din suka ajiyeta Hajiya na sake cewa "In kin ga dama kiyi hakuri in kinga dama ki cigaba da tunzur
ashi yana miki illa" nan ma Na'ima batace komai ba taja akwatinta ta shige gidan, zuwa sannan ta daina kuka a abayyane sai na zuci kuma, ko abinci takasa dafawa taci haka ta kwanta nan kan gado batare da ta chanja kayan jikin ta ba..
Bata dade ba nan kwan
ce taji shigowan motan Bilal din, can taji an turo kofan dakinta bata juyo ba balle ta kallesa, still tayi shiru tana kwance ta yi pillow da hannunta tana kallon gini, qarasowa yayi gurin gadon yace "Kin dawo kenan" bata amsa ba ya sake cewa "You think you
can escape me Na'ima? you must be kidding yourself" miqewa zaune tayi sai sannan hawaye ya kawo idonta ta kallesa takasa magana ma, yana kallon cikin idonta yace "You're bound to me Na'ima, I've grown addicted to your presence, duk inda zakije sai kin da
wo gareni" ya juya ya fice daga dakin yabarta zaune tana swallowing maganar tasa, kamar an mintsineta tayi sauri miqewa tabi bayansa nan falon qasa ta sameshi a tsaye yana danna wayarsa ta tsaya bayansa tana kuka tace "Dan Allah ka sakeni" saurin juyowa ya
yi yana kallonta ta sake cewa "Ka rabu dani inje inyi rayuwata" ransa ne ya baci yace "Bar gabana ko in illataki" bata matsa ba ta hade hannayenta guri daya tana kuka tace "Idan ba tare aka halittomu ba dan girman iyayenka ka sake...." bata qarasa ba ya ka
i mata maruka a fuska, tananan tsaye taga yana qoqarin ciro belt dinsa, tsayawa tayi bata motsa ba ganin ya nufota da belt din zai daketa kawai ta rufe idanunta hawaye na zuba sanin dukan farkon ne wanda yafi zafi a ko yaushe.... Nan ne mafarin
abubuwa da
dama a cikin rayuwan Na'ima, a sannu ta fara shiga depression, mantuwa, da kuma firgita ita kadai, wani irin rama ce ta fara shiganta sanadin damuwan, zuwa makarantar nata ma yakoma sama sama, Nafisa tayi fadan har ta gaji ganin mutuwar tsaye Na'iman keyi,
ga final exams dinsu da ya tisosu gaba wanda Na'ima batasan ma me akeyi ba, zuwa sannan in Bilal yazo gareta ma bata yunkurin hanashi sanin bazai iya tabuka komai ba sai riqe kansa da kuma duka, har lokacin Bilal ya kasa aiwatar da komai akan Na'ima wanda
hakan ba qaramin kulle masa kai yake ba, baya tashi jin ciwon kai sai yaje gareta, gashi babu abunda yake so irin ya kusance ta amma abun ya gagara, kullum da haushinsa da kuma dukan da yake mata yake barin dakin nata, bayan ya fitan haka zata miqe tana h
awaye ta maida kayan ta jiki..
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 34
A wannan yanayin ne har lokacin Exams dinsu Na'ima yazo, da kyar Nafisa ta shawo kanta tafara yin karatun, sai ta bata shawaran ta daina yawan zaman gidan, zata rinqa
zuwa daukan ta suje makaranta karatu..
Nafisa tayi qoqari sosai wajen ganin Na'ima ta danyi karatu, har yawo tana dan fita da ita in sun fita daga school din dan Na'iman ta warware, kuma Alhamdulillah tasamu tayi exams din da dan nutsuwanta, zuwa sannan
Na'ima ta daina yawan fadawa Nafisa abunda Bilal din ke mata she just leave everything as it is sai addu'a..da taje can gidan gaishe dasu Alhaji bata ga alaman yasan taje Adamawa ba dan normal suka gaisa har yana tambayanta school da lafiyan gidan aurenta,
which means Hajiya ta boye masa abunda ya faru har sannan.
Ta wayi gari wani ranan Saturday Nafisa ta kirata akan bata da lafiya itama, bata iddasa yin wayar ba Bilal ya shigo dakin sai tayi saurin kashewa, yana tsaye yace "Da wa kike waya" cikin sanyi
n murya tace "Nafisa" zama yayi bakin gadon fuskansa a dinke yace "I don't like that girl, kar in sake jin kina waya da ita in ba haka ba ranki zai baci" dan juya kanta tayi gefe ta gyada kai sai ya kai hannu ya matse fuskan nata ya juyo da ita tana kallon
sa yace "Look at me when I'm talking to you Na'ima" sai tayi saurin gyada kai, kallonta ya tsaya yi da alamun bacin rai a fuskanshi sai tayi saurin bude baki tace "Toh, bazan sake ba kayi hakuri" sai sannan ya sake fukan nata bayan ya miqe sai ya dan duqo
yayi kissing kanta, rufe Ido Na'ima tayi har ya fita daga dakin tanajin qofofin tsanarsa na sake buduwa a cikin zuciyarta..Bata bar gidan ba saida ta ji fitan motansa sannan ta shirya cikin light brown abaya da side back dinta ta fice daga gidan, har qofar
gidansu Nafisan aka kaita, bayan ta gaisa da megadin ta shiga gidan kanta a qasa ta nufi entrance din gidan ko lura batayi da wanda ke can tsaye a parking space din gidan ba, barin danna wayar tashi Ahmad yayi, ya bita da kallo tana tafiya cikin sanyi har
ta shige cikin gidan, shiganta falon ta kusa cin karo da Faruk da yake shirin fita shima, sai yayi baya yace "Sannu Na'ima" itama baya tayi ta gaishesa ya amsa tareda cewa "Ya maigidan naki" ta amsa da "Lafiya" sannan ta bashi guri ya fice daga falon, Mam
i ta samu zaune a
falon tace "Oyoyo Na'ima, shiru kwana biyu bamu ganki ba" tana murmushi ta qarasa sai ga Nafisa ta sauqo daga sama tace "Bobo kinzo" Mami ta juya gurin Nafisan tace "Yauwa zo gashi yi sauri ki kai masa wannan, yana can parking space, kice
saqon Mammah ne" da saurin ta amshi ledan da Mamin ke miqa mata tace "Wai har