Showing 120001 words to 121625 words out of 121625 words

Chapter 41 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

16

seat yaqi kallon inda Na'ima take, Na'ima ka

llonsa tana kuka suka fice tanajin zuciyarta na breaking

into pieces... Da haka Mami ta jata suka shiga cikin gidan tana bata hakuri, har dakinta ta kaita suka zauna bakin gado, kuka sosai Na'ima takeyi tanajin zafi a nata zuciyar dan ji take kamar Bilal d

in yaci galaban rabata da Ahmad din, Mami ta rungumeta tana cewa "He'll pay for everything, shari'an da mukace zamuyi dasu din za'ayi" batace komai ba ta cigaba da kuka....Dakyar Mami ta samu tayi shiru, tana nan kwance a gadon taja mata blanket ta rage qa

rfin Ac din sannan ta fita, dago kai Na'ima tayi hawaye na kawowa idonta dan ba bacci tayi ba daman, har yamma tana dakin Mami na zuwa dubata akai akai, dasu Nafisa suka dawo tana jiyo hayaniyar su a falon amma ta kasa tashi bayan wasu lokuta Nafisa ta shi

go dakin tana fadin "Bobo bakida lafiya ne" taja bargon tana kallon Na'iman, aikuwa nan taji jikinta yayi zafi sai ta fita kiran Mami, kiran likita akayi da wannan yammacin yazo ya mata alluran zazzabin da ya rufeta gashi bini bini sai hawaye, da dare Nafi

sa na zaune gefenta bayan ta kawo mata abinci, Abu kuma yana zaune kan stool din mirror, sai Nafisan tace "Wai daga dawowan ki daga bankin ne zazzabin ya rufeki kenan" Na'ima ta gyada kai ahankali tace "Yayi sauqi ai na daina jin komai ma Nafee" kafin Nafi

san tayi magana Abba ya shigo dakin tareda Mami da Faruk, dan zuwa sannan Mami sun fada masa komai da ya farun, yayi ta fada akan meyasa basu kira polisawa ba anriqe masa yaron kafin yazo, sai Mami tace "Har da Ahmad din za'a kama kasani, which will link t

o su Baba su sani, and yarinyar nan har yau mun boye wa kowa wacece ita gudun maganganun cikin family", da wannan Abba ya fito ganin Na'iman a daki, yana tsaye a dakin Na'ima ta fara qoqarin sauqowa daga gadon yace "Yi zaman ki daughter, Allah ya baki lafi

ya" ta amsa da Amin kanta a qasa, da Abba ya gama mata sannu sai ya fita ya barsu Mami, ta qaraso gurin Na'iman tace "Daughter ya jikin" ta amsa "Na warke Mami" sai duk yan dakin sukayi murmushi, Mami ta shafa kanta tace "Haka akeso, Good night" Faruk dake

kallonta yace "Sannu Na'ima" sai tayi masa murmushin dole, da haka duk suka fice daga dakin aka barta da Nafisa dake gyara kwanciya a gadon dan anan zata kwana, cikin dare Na'ima ta farka ta jawo wayanta tana duba wa amma bataga miscalls din Ahmad ba kama

r yanda ya sabar mata, zuciyarta na nauyi ta danna kira a line dinsa sai taji baya tafi, the line is unavailable, hawaye taji ya kawo idonta kawai ta kwanta tareda jan blanket din har kanta....

Zuwa safiya Na'ima ta warware sai dai nauyin da takeji kawai

a zuciya, like every morning haka sukayi breakfast dinsu dan ranan kaman hadin baki duk an tashi tare a gidan, suna hira har aka gama breakfast din su Na'ima suka tattare gurin tsaf...Har la'asar su Na'ima na falon Mami, tana cikin hira da Nafee sai taga t

ana danna waya tare da dan ware ido, da sauri Nafisan ta dago kai tace "Bobo kinji wai Yaya Ahmad ya fadi da bike jiya?" sai da zuciyan Na'ima ya buga, ahankali tace "Wa ya fada miki?" Nafisa tace "Yanzu Husna ke fadamin, wai jiya Yaya Faruk ya maidashi gi

da hannunsa duk jini" jin haka yasa Na'ima taji nutsuwa sanin jini menene a hannunsa nasa ba faduwan bane, sai Nafisa tace "Bari muje dubasa Bobo" ahankali tace "Allah ya basa lafiya" da haka tayi shiru amma har zuciyanta itama tasan tanason ganinsa, zuci

yarta na mata wani nauyin da in ba ganinsa tayi ba tasan bazata daina ji hakan ba, Mami ce ta shigo falon sai Nafisa ta juya ta kalleta tace "Mami munason zuwa duba Yaya Ahmad wai jiya ya fadi da bike" dan stiff Mami tayi ta kalli Na'ima da kanta ke duqe,

sai tace "Ku dawo da wuri Baby, lantana batanan zakuyi girkin dare" cikin sanyi Na'ima tace "Zan zauna nayi Mami" sai tace "No Habibti kije ku dubosan" da haka ta nufi cikin dakinta yin uzurin da ta shigo yi, su Abu daman basa gidan ranan sun fice gari shi

da Al'ameen, da

motan Nafisa sukaje gidan, Nafisa nata yiwa Na'iman hira tana amsa mata akai akai dan tasan in tayi shiru yanzu zata shiga damuwa ta fara tambayanta, ita kuma ganin su Mami basu fada musu ba yasa tayi shiru itama, isarsu gidan suka fara zuw

a gaisheda Mamma sai suka samu tana aikin abinci a kitchen tareda Husna da Ummi last born din dakinsu Ahmad, a kitchen din suka fara gaisheta tace bakomai su zauna a falo tana zuwa, sai da ta fito suka gaisa kan Na'ima na duqe tayi shiru sai Nafisa tace "Y

a jikin Yaya" Mamma tace "Wannan har ya fita ma da safe, kaman dai ya dawo dazu yana side dinsa" Husna ta fito tana fadin "Muje ku rakani zan kai masa abinci" sai Nafisa ta fara miqewa Na'ima na zaune bata tashin ba, ganin hakan yasa Mamma tace "Daughter k

ije ku dubosan" Na'ima ta gyada kai sannan ta miqe ahankali suka fita, da suka fito compound din zasuje side dinsa Husna tace "Baba fa sai da ya hanasa fita yau wai ko akwai internal injuries tun da babu ciwon komai a jikinsa, amma inaga Baba yana fita Yay

a ya bisa a baya" Nafisa tace "Ai dai mayyar can bataji labari bako" Husna ta amsa da "Anty tasani ai to dole su salma zasu sani, amma kaman batazo ba, dan banganta acikin gida ba" Na'ima na jinsu batace komai ba har suka qarasa side din nasa suka shiga fa

lon tana baya, aikuwa shigansu suka ga Laila a agabansa tana zuba masa abincin da takawo ga Adam ma zaune a falon da wani friend dinsu daya shima, dan stiff sukayi dukansu a bakin qofan, Na'ima ta sauqar da kanta qasa tana dana sanin zuwan ma, Ahmad na dag

owan kai ita ya fara gani, sai ya kasa dauke idonsa akanta har suka shigo suka zauna, Husna ta ajiye masa abincin tana fadin "Yaya gashi Mamma tace kaci wannan saboda ta dafashi yanda kakeson" sai ya gyada kai ya sake juyawa yana kallon Na'ima dake kallon

gefe ma, zuciyarta quna taji nayi kamar wuta a lokacin, bayan sun gaisa da Adam sai ta dan kallesa idonta ya fada cikin nasa, atake ta sake dauke idonta, bai dena kallonta ba Laila ta zauna a gefensa tana fadin "Sannunku da zuwa Nafee" Nafisa na kallonta d

a mamakin yanda take musu abu kamar wasu baqi, sai bata kulata ba ta kalli Yayan nasu tace "Sannu Yaya, ina wuni" yace "Lafiya Nafisa" shiru tayi bata amsa ba ta juya gurin Na'ima tace "Muje sis" sai ta miqe Husna tace "Har zaku tafi kuma" Adam yace "Nafee

wannan gaisuwa taqu miqe ce" tana murmushi batace komai ba, miqewa Na'ima tayi itama, sai sannan ma ta tuna batace masa ya jikin ba amma haka tabi bayan Nafisa suka fice daga falon, ahanyarsu ta komawa sai Nafisa batace komai ba ganin sanyin da Na'iman ta

yi, da sukaje gidan sai suka samu Mami a falo tana zaune ita kadai tana waya, zama sukayi gurinta sai da ta gama tace "Har kun dubosan" Nafisa ta gyada kai kawai, sai Mami tace "Abbanku yadawo shima yana falonsa" sai Nafisa ta fara qoqarin miqewa tana cewa

"Jiyan ban masa maganan site din bama Mami" sai Mami ta amsa da "Yanzu dai kuyi abincin tukunna akwai anjima ai" Na'ima tace "Zanyi Mami, me za'a girka" ta amsa da "Ki duba dai, Abbanku na masa, naku kadai zaku girka" Na'ima ta gyada kai sannan tace da Na

fisan "Ki je gun Abban zanyi" sai Nafisa ta miqe tana fadin "Yauwa Anty Na'ima naa" suna murmushi itada Mami suka bita da kallo ta shige bangaren Abba, sai Mami ta kalleta tace "Are you okay Na'ima? ki fadamin meyake damunki kinji" hawaye taji yana zuwa id

onta sai ta danne tace "Babu komai Mami" sai Mami tace "Karki sa komai aranki kinji daughter, hakan bazai sake faruwa ba i assure you, jiyan ma Abbanku yasa a binciko masa shi duk inda yake" ta gyada kai ahankali sannan Mami tace "How's Ahmad?" cikin sanyi

tace "Yana lafiya" sai ta gyada kai tana kallon Na'iman, miqewa Na'iman tayi ta nufi kitchen zatayi abincin sai Mamin ta miqe itama ta nufi falon Abban, da tashiga kitchen din sai ta maida hankali tana ta aikin nata har ta gama bata daina jin zafin ganin

Laila gurin Ahmad ba, like how is she feeling this

way ne ma? Bilal da ya kasance mijinta abaya ma da ya kawo karuwarsa gidan bataji komai ba sai wannan da ba mijin ta ba, kuma wadda ta gansu taren ma 'yaruwarsa, sai ta jefar da soson da take wanke plate d

in hannunta ta daga kanta tana kallon sama da nufin ta hana hawayen idonta fitowa, ji tayi an bude kofan kitchen din amma bata juya ba, sai kuma tayi stiff jin turarensa, ai da sauri ta juya tana kallonsa yana tsaye jikin qofan bayan ya rufe shima yana kal

lonta cikin ido.....

Alhamdulillah nan na kawo qarshen Compressed Document din littafin KUNCIN ZUCI, Ban yarda wani ko wata su hadamin complete dinsa bada izini na ba.

Mazah Mazah ku garzaya Arewapen App domin karanta sauran shafukan littafin wanda

ya kasance FREE shima acan, karku manta da following Account dina tareda liking story din...

Love, Bintu Musa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login