Showing 111001 words to 114000 words out of 121625 words
su Abu har da kai hannu baki yayi fito na murna, fuskan Na'ima cike da murmushi suka qarasa gaban shugabannin
makarantar, Bilal dake zau
ne cikin mutanen Hall din yayi ta kallon Na'iman har zuwa lokacin da sukayi bowing kansu kadan agaban professors din nasu, sai ya juya yana ganin yanda iyalin WADZANI suke ta tafin murna da farin ciki, ya sake juyawa ya kalli Na'ima data juyo kadan ta kall
i familyn nata tana murmushi me fadi sannan ta juya aka nuna musu hanyan da zasu fita, in akwai abunda yafi mutuwar jiki toh Bilal ya jita a wannan lokacin, this is not the Na'ima he knew before, wannan ba Na'iman da aka taba kawo ta gidansu daga qauye bac
e, wannan ba Na'iman da tayi rashin gata abaya bace, sake juyawa yayi yana kallon su Abu da suka nufi fita daga Hall din zasu bi bayan su Na'iman, sai ya tsinci kansa da dan duqar da kai ganin Ahmad ya dan juyo da kansa ta side dinda yake zaune.
Bai sake
ganin ikon Allah ba sai da ya fita haraban Hall din ganin yanda duk familyn suka zageya Na'iman da Nafisa kowa yanason yin hoto dasu, in Na'ima ta dauka da wannan sai wannan ya jawo hannunta adauka again, Hugs kuwa ta shashi ta ko ina, da tazo kan Faruk sa
i ya miqa mata hannu da nufin suyi handshake, dan kallon Ahmad tayi ganin yana tsaye a varenda din Hall din hannunsa cikin aljihu yana kallonsu ga Lamin da kuma Abba agefensa yana magana da wani babban mutum, sai ta juya ta miqa hannunta sukayi shake din y
ace "Congratulations sis, i pray this will be the beginning of your new beautiful chapter in life" hannunta na cikin nasa tana murmushi ta amsa da "Thank you yaya Faruk, thank you for everything" yana kallon idonta yace "You're welcome anytime Habibitin Ma
mi" sai ya juya yana kallon Ahmad yace "Kije kuyi hoto dasu Abba da Yaya mana" ta gyada kai sannan ta zare hannunta daga cikin nashi duk akan idon Bilal dake tsaye can nesa dasu, da taja Nafisa sukayi hoton dasu Abba din wanda itada Nafisan na tsakiya whil
e Abba da Ahmad na gefe, nan ma su Abu dasu Al'ameen suka shiga harda Faruk din sukayi nasu na maza, Nafisa na murmushi aka dauka musu tareda Lamin wanda har sannan kowa dauka yake kara ya musu a matsayinsa na abokin Ahmad yazo gurin taron, bayan an gama s
ai Ahmad yaqi barin gefen Na'ima yana tsaye sai yayi qasa da murya cikin rada yace "My beautiful Na'eemah" sai ta fara juyawa tana duban ko ana kallonsu amma sai taga anata hotuna ne hankali baya kansu, data juya ta sake hada ido dashi sai yayi murmushi ko
a jikinsa yace "In kama hannunki sai su san what is going on here?" ayanda tayi saurin barin gurinsa sai da abun ya basa dariya amma beyi ba, sai yayi murmushi yana bin bayanta da kallo, aikuwa juyawan da zeyi idonsa ya fada kan Bilal dake tsaye can nesa,
duk wani annuri bacewa yayi daga fuskan Ahmad ya gyara tsayuwa yana kallonsa.
Naima komawa tayi gurinsu Mami suka yi hoton tareda dasu Mamma da Anty Fatima, shima in group sukayi na iya matan, sai sannan Mami ta samu sararin Hugging yaran nata, bayan tay
i hugging Nafisa tazo kan Na'ima ta rungumota tana fadin "Ma Sha Allah Habibiti na, Allah ya qara kawo tarin nasarori cikin rayuwanki" sai sannan idon Na'ima ya fada cikin na Bilal dake kallonta shima cikin ido, bata dauke idonta ba ta rinqa kallonsa Mami
na shafa bayanta, sai da Anty Amnah taja hannun ta tana cewa "Daughter zo ku gaisa da sistern Abban twins" sannan ta dauke idonta suka tafi, sai shima Bilal din ya juya yana tafiya a sannu zai fita daga premises din yanajin jikinsa na sanyi, at that moment
..that moment da ya kalli mutanen dake zagaye da Na'ima ya gane wani abu da bai taba sani ba, He was never for once, 'Her Family'...talkless of a Brother to her. Ahmad dake tsaye a gefe har sannan hannuwansa cikin Aljihu yabi Bilal din da wani irin kallo s
annan ya juya ya kalli Na'ima dake gaisawa da qanwar Abban twins cikin fara'a, sai dariya take suna maganan, sai ya sake juyawa yana kallon Bilal har ya fice daga premises din...
Sai da aka gama duk hidiman sannan gabaki dayansu suka tafi gidansu Na'ima
n banda Lamin, dan Abba cewa yayi zai je ya ga inda yaran nasa sukayi rayuwa tukunna, Mamma da duk sun gaji aka tafi tare dasu can, cika falon sukayi matasan na zaune a dining area sukuma matan na zazzaune a falon, Abba ma na zaune bisa kujera twins suna j
ikinsa, saida duk akayi salla sannan aka bude kayan ciye ciyen da suka siyo kala kala ahanya, su Na'ima da Nafisa sannan Husna suka hau serving kowa a plates suna miqawa, hira sukeyi sosai afalon, da Na'ima sukaje serving din su Ahmad kanta a qasa take zub
a masa abincin, sai kallon hannunta da yasha henna yakeyi sai ya dago kai suka hada ido tayi saurin nufan su Abu tana taya Nafisa zuba musu mixed salad din, sai da suka gama sannan suka zauna nan gefen su Anty Amnah suka fara cin nasu, da aka gama suka tat
tare komai, sai mazan duk suka dawo cikin falon suka zauna sannan aka fara bawa su Na'ima da Nafisan gifts, Abba ne yafara musu albishir yace "Saura Umrah yaran Abba, that's my gift to you" idon Na'ima sai da ya kawo hawaye tana godiya Ahmad na ta kallonta
, Nafisa ma ta hau tafin mura zata koma wani umrahn, Mami tace "Nidai zuwana shine gift dinku" akayi dariya sai Mamma tace "A'a, yarana basu yarda da hakan ba" ta qarasa fadin hakan tana miqo musu babban box guda biyu mai dauke da dadduma, Qur'an da kuma t
asbaha acikin kowanne, kowa na falon sai da ya bada nasa kyauta, Faruk daman sabbin waya ya ba kowannensu, Al'ameen kuma Ps, Abu kuma sai ya nuna musu hoton Art frame dinda yayi musu installing a saman gadon su na can gida cikin dakin kowannensu, Husna ta
basu sarqan gold me dauke da harafin sunansu, Anty Amnah da Fatima ma da nasu wrapped gift din.
Saida kowa ya gama basu kyautan sai duk aka juya ana kallon Ahmad dake danna wayansa hankali kwance, Jin kamar falon yayi shiru yasashi dago kai yana ganin yan
da suke kallonsa, Anty Amnah ta daga masa gira daya alamun shi ake jira, sai ya kai hannu aljihun jamfan dake jikinsa ya ciro wasu papers guda biyu ya miqawa Nafisa yace "The car is yours, I'll shift it back home to you" wani tsalle Nafisa tayi tana murna,
Mami na murmushi tace "Ji shirme" Nafisa tace "Yaya nagode Allah ya baka abunda kakeso" ta qarasa maganan tana kallon Na'ima da ke wasa da bakin gyalenta, sai kuma duk aka sake zuba masa ido alamun ina na Na'ima, Faruk ma wannan karon shi ya daga masa gir
a daya, shi Ahmad abun nasu dariya ma yake bashi sai ya kalli Abba yadan sunkuyar da kai yace "Abba ina neman amincewan ka na barin Na'eemah tayi amfani da App dinda na bata, nayi mata transferring all ownership regarding my App Bizgo, sannan na baiwa Nafi
sa wani crypto App dina itama" dan stiff mutan falon sukayi, Mamma na mamakin dogon maganan dan nata, Al'ameen yace "Theee Bizgo?" Ahmad ya gyada kai sai Abba yace "Shi menene?" Mamma tace "Ahtoh duk yakai motan ne, adai bawa daughter babban abu itama" Abu
ne ya fara dariya sai Al'ameen ya dafashi suka rinqa dariyan tare Husna na tayasu da Anty fatima, Mami na murmushi tace "Wa'ennan, Allah ya shirya" Faruk ma yana danne dariya yace "Mamma App din babban ne sosai, sannan yasamu global ne kuma, ataqaice zai
iya bata 500 thousand US dollars duk wata" Mami ta kalli Ahmad din sai Mamma tayi murmushi tace "Ma Sha Allah, ka kyauta sosai, duk da haka muna maulan motan muma" sai Faruk yace "Zan siya mata ai Mamma" tace "Yauwa dai" Anty Amnah na kallon Ahmad tana ta
murmushi itada Anty fatima ganin har sannan bai kalli kowa a falon ba, Husna na murmushi ta zauna gefen Na'ima da har sannan kanta na qasa tanajin wani iri itama, Abba yace "Muna godiya son Allah ya biyaka" kan Ahmad na duqe yace "Nagode Abba" ahankali Na'
ima ta furta nata godiyan bata dago ba sai Nafisa ma tace "Mungode Yaya Allah ya biyaka" ta sake dago takardan motan nata ranta
tasss, dan ita bata App din take ba ma, saboda kaf cikin yaran falon babu wanda net worth dinsa baya bashi fin abunda Na'iman za
ta rinqa samu a watan, that's why babu wanda yayi mata qyashi cikinsu, sai suka cigaba da lamuransu kamar babu abunda ya faru, da su Mamma suka tashi tafiya sai Ahmad ya rigasu fita, Na'ima na zaune taga text dinsa sai ga kira ya biyo baya, miqewa tayi a s
annu ta nufi balcony kamar wadda zatayi waya sai ta leqa qasa ta hangosa jikin motansu kare da waya a kunne, tsayawa sukayi suna kallon juna babu wanda yayi magana a wayan Na'ima najin bugun zuciyarta na sauyawa har sannan batace komai ba tana kallonsa, ah
ankali yace "Sai a Nigeria zan sake ganinki Babe?" ta gyada kai tana sauqe kanta qasa sai ya sake cewa "Look at me Na'eemah" kasa dago kanta tayi, Jin yayi shiru sai ta dago din taga kallonta yakeyi yana murmushi, ahankali ya sake cewa "Gobe zan wuce Lagos
, nima na gama zamana a qasarnan" sai ta samu kanta da cewa "Yaushe zaka koma Abuja?" yace "Next week Babe, Next week kinji" ta gyada kai tana murmushi ahankali tace "I'll be waiting" yana murmushi ya cigaba da kallonta, sai da taga fitowan Faruk yana nufa
n Ahmad din tace "Allah ya kaiku lafiya" ya gyada kai tareda cewa "Amin, take care" da haka sukayi sallama ta koma cikin apartments din nasu....
A washegarin ranan su Na'iman suka kama hanyar barin Oxford bayan sun karbo certificate dinsu a inda ta samu d
istinction Nafisa kuma ta samu second class upper amma, Abba yayi farin ciki sosai ya rinqa shafa kansu yana cewa "I'm proud of you my kids", wani farin ciki Na'ima ta rinqa ji ganin murnan iyayen nasu, tana ganin soyayyarta a idanunsu, a zuciyarta tana fa
din "What more could she wished for after this?"....
Ranan da suka dawo Nigeria daman ko gyara kayansu basuyi ba su ka rinqa bacci a dakin Nafisa dan a dakin Na'ima suka loda kayan nasu, da safe basu tashi ba sai guaren 9 sannan suka fito yin breakfast, s
uka samu Mami na zaune da Faruk suna cin abincin, ganinsu yasa Mami cewa "Kun tashi" Nafisa ta gyada kai tana hamma tareda jan kujera ta zauna, da Na'ima ta zauna sai Mami ta zuba abinci a plate ta miqa mata sannan ta zubawa Nafisa itama, suna ci Faruk yac
e "Yara welcome to labour market" Nafisa ta ajiye cup din tea dake hannunta tace "Sai nayi shekara ina hutu tukunna" Mami na murmushi tace "Ji lalaci" sai Faruk ya kalli Na'ima yace "Na'ima kefa" cikin sanyinta tace "Duk abunda Allah yayi" Mami tace "In sh
a Allah ko wanne aiki kikeso, matuqar bai sabawa addini ba zakiyi Habibiti" Na'ima tayi murmushi sai Nafisa tace "I thought we were a team Na'ima, i rest...you rest" dariya su Mami suka fara Faruk yace "Sannu mamanta" sai Na'ima tace "A'a zan huta din nima
Yaya" ware ido yayi ganin zasu hade masa kai sai Mami tace "Kwaji dashi dai, bari sai kun dawo daga Umrah muji me Abbanku zaice akan batun aikin" Na'ima na murmushi tace "Toh Mami" su Lamin ne suka shigo falon, Mami tace "Wai dama baku tashi ba kuma" dan
tun asuba ta gaisa dasu, amsa mata sukayi tareda zama, Na'ima ta miqe tayi serving dinsu abincin sannan aka cigaba da hiran dasu....
Zaune Ahmad yake cikin wani tsadadden Bar dake cikin garin Lagos, ya kishingida jikin leather seat din tareda crossing l
egs dinsa yana kurban champagne cikin glass cup din hannunsa, ta gefensa wani inyamuri ne shima adan jingine da kujeran wanda duk jikinsa yasha tattoo da chain a wuya yana zuqan taba, Bar din babban ne wanda kana gani kasan ba wajen zuwan yaro bane sai wan
da yakai, magana Ahmad din keyi sama sama da inyamurin me suna Don Mazzy, wata mace ta zo cikin yari yarin kaya ta zauna a gefen Mazzy din wanda ko kallon inda take Ahmad beyi ba yana danna wayarsa da hannu daya, sai da ya gama typing message din da yake y
iwa Na'iman sannan
ya ajiye wayan ya kai hannu gurin qaramar brief case dinsa dake gefensa ya ciro wani folder ya jefa akan glass table din da ke gabansu, yana kallon Mazzy yace "I need every details on them, Everything..." Mazzy yakai hannu yana ciro hotu
nan da suke cikin foldern sannan ya zubasu akan table din, Hotuna ne kusan guda shida, tun daga kan Bilal har iyayensa da Nasir sannan na Stella, Mazzy na kallon hotunan yace "My, My, what do we have here?" sai ya dago kai yana kallon Ahmad din yace "Boss,
you know it's gonna cost you big, right?" Ahmad yace "Name your price" sai Mazzy yace "10 M, scratch that..15" sai Ahmad ya gyada kafada yace "Done...I'll make it 30 if you conduct everything in a week and deliver it to me with a package" sanin me package
din yake nufi yasa Mazzy yin dariya yace "Ahmad you're a Bad guy" sai Ahmad yakai hannu yana zaro hoton Bilal sannan na Nasir ya turasu gaban Mazzy yace "I want them in wrapped package" Mazzy yace "Let me handle them for you nah, let me end them in one go
" sai Ahmad ya girgiza kai yayi sipping champagne din sannan yace "No Man, i want them to taste something different" ya qarasa maganan yana kallon Adam dake nesa dasu yana buga snooker da wani friend dinsu bahaushe..Bayan sun fito daga Bar din zasu koma gi
da sai Adam yace "What's with you and Mazzy again?" Ahmad bai kulasa ba ya nufi wajen baqar jeep dinsa dake fake a gaban gurin, bin bayansa Adam din yayi ya sake cewa "Ahmad" sai sannan ya juyo ya kallesa, sai Adam din yace "Banaso kasani, the last time da
na ganka tare dashi, you almost killed Saddam after that" anutse Ahmad yace "Kana ganin ina shiga gonar mutum in bai shiga tawa ba?" da zafi zafi Adam yace "Abunda ya faru tsakaninka da Saddam yawuce abadan sannan ka rama Ahmad" rai abace shima Ahmad yace
"Yeah.. that's the problem with me Adam, i don't tend to forget things easily, kuma Billahi..ko waye ya shiga gonata sai na masa iyaka" shiru Adam yayi yana kallonsa da mamaki sai yace "Who is it this time?" Ahmad bai amsa ba ya bude motansa ya shiga tare
da tayarwa ya figeta yabar Adam din nan tsaye shima ransa na baci, a sannu ya nufi tasa motan yana tuna incident din da ya farun tsakanin Ahmad da wani competitor dinsa da ya masa wani tuggun da ya taba Ahmad din sosai....
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu M
usa
✍
️
Chapter 46
A week Later..
Na'ima ce kwance a gado bayan tayi sallahn asuba da azhkar dinta ta qudun dune cikin blanket kamar wata Baby, waya ce a kare kunnenta tana magana da Ahmad, shiru tayi tana sauraron abunda yake fada, sai tayi
murmushi batace komai ba, daga bangaren Ahmad dake kwance shima a nashi gadon ya sake kwantar da murya yace "Babe answer me" sai ta sake yin murmushin tace "Nidai uhm uhm" sai yace "So kike na bar komai na dawo ayau ko?" Na'ima tadan ware ido sai tayi dan
dariya tace "Ai kace zaka dawo satin nan" sai yace "Kinason in dawo?" tayi qasa da murya tace "Uhm" sai yayi murmushin da har tana jiyosa, shiru sukayi Na'ima na kallon pop na dakin,
wani irin abu takeji yana mata yawo a zuciya a duk lokacin da take waya
da Ahmad, ahankali taji yace "I dreamed a life with you Na'eemah, A life where you and me will build everything together, only you by my side Na'eemah...Side by side" ji tayi hawaye na kawowa idonta, tayi shiru tana tuna yanda rayuwanta ya zamo bari biyu,
ta inda past dinta Namiji ya nuna mata tsana mai qarfi sannan present dinta kuma wani Nimijin yake nuna mata qauna mai tsayawa a zuciya, Namijin da keda burin yin rayuwarsa tareda ita, Jin Ahmad din yayi shiru ya sata cewa "Nima inason yin rayuwa dakai" sa
i yace "And we'll have our kids Na'eemah, beautiful ones like you" murmushi tayi me sauti sai ya qara cewa "Duka mata nakeso kuma masu irin gashin ki" tadan ware ido cikin kunya tace "Son kai ne hakan fa" yace "Na yarda i'm selfish akanki, i want you all t
o myself Babe" tana murmushi tace "What about Simba?" sai yace "Kinason in kawo miki shi bayan aurenmu?" ta gyada kai tace "Uhm" sai Ahmad ya gyara kwanciyarsa yace "Then angama Babe"...Hira sukayi me sanyaya musu zuciya a wannan asuban, hiran da shiru yaf
i yawa acikinta, amma jin shirun suke shima wani muradi na daban wanda basa gajiya da yinsa, shiru kan zama boring while on call amma ba'a gurinsu ba, in the sense that jinsa suke kaman wani maganar zucin me zaman kansa... Na'ima ce ta fara masa sallama da
lilin zata je su gaisa da Mami dan tasan tana falonta, da haka sukayi sallama ta nufi dakin Mami sai ta samu Nafisa acan tareda Mamin suna gaisawa, zama tayi anan qasan carpet din itama