Showing 51001 words to 54000 words out of 121625 words
/>
Babu yanda Na'iman ta iya haka ta fara kula lawan ba'a son ranta ba, bin ta yake har gurin tuyan qosanta yana tsattsare maza masu kulata, har hakan yafara taba mata kasuwanta, Umma ce tayi magana da Ayuba akan yaja masa kunne tun ba'aje k
o Ina ba zai kashe musu kasuwa sannan yadaina zuwa, Amma kam duk dare lawan da guzurin ledarsa yake zuwa gurin Na'ima duk dan kawai yasamu kanta yanda yake so amma abu yaci tura, zaizo ya qaraci surutunsa amsarta sune "Uhm" ko "A'a", ranar da yazo yace mat
a zeyi tafiya zuwa Lagos Na'ima ji tayi kamar an yaye mata damuwanta bila
adadin, dan har ga Allah ta gaji da ganinsa bini bini koyaushe a qofar gidansu..
Watarana ta gamo sanarta da hantsi qannenta sun riqo mata murhu da robobinta suna tafiya, a hanya ta
gamu da qawarta wanda sukayi islamiya tare, a bakin sa'ade taji wai ashe tafiyan da lawan yayi zuwa Lagos din, zuwa yayi siyo kayan aurensu, dan sa'ade'n 'yar uwarsa ce, tabe baki Na'ima tayi tace "Allah ya taimaka" tayata riqe wasu kayan sa'ade tayi suka
tafi gidan tare suna hira jefi jefi, isarsu gidan suka samu wata mota dalleliya fake nan kofar gidan, tsayawa sukayi kallon motan dan ita dai Na'ima bata taba sanin kaf danginsu ma akwai me mota irin wannan ba.......
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 24
Qarasawa qofar gidan su Na'ima sukayi idonsu na kan motan, sa'ade na ware Ido tace "Wai, ke kinga wata mota, dama kunada 'yan'uwa masu kudi Na'ima?" shiru Na'ima tayi batace komai ba suna tafiyan, sai da suka zo daidai jikin motan su
kaga wani dan babba mutum daga daya barin motan yana zaro bendir din taliya, dagowa yayi suka gaishesa gaba dayansu, itadai Na'ima har sannan bata gane sa, shigan su dan lungun dazai sada mutum da cikin gidan sukaga wani babban mutum cikin manyan fararen k
aya hakimce nan kan babbar tabarma me dauke da darduma akai gabansa kuma ruwan pure water ne akan plate har da exotic, su kawu Ayuba da Nasiru zaune nan gefensa fuskansu cike da fara'a, dago kai kawu Abdullahi yayi ya kalli su Na'iman dake fama da kaya a h
annun duk sunyi wani kaca kaca dasu, Ayuba ya dago kai yana kallon Na'iman yace "Ai gatanan ma, me hasken cikin nasu itace yarinyar tashi Na'ima" sai kawu Abdullahi ya dan gyada kai yana kallon Na'ima yace "Allahu Akhbar, Allah ya jinqansa da rahama, zo Na
'ima".
Na'ima da ke masa kallon rashin sani ta fara takawa wajensu su sa'ade suka bita a baya, tsugunnawa nan tayi ta gaishesa ya amsa yana binta da kallo yace "Ya makaranta, kinayi kuwa" kawu Ayuba yayi saurin amshe zancen da cewa "Ta dan fara yi Yaya to
kasan yanayin rayuwa, ta abunda za'aci ake tukunna" Abdullahi yadan jijjaga kai yace "Yanzu bata makarantar kenan" Nasiru yace "Muna jira muga abunda hali zeyi tukunna, ko Allah ze kawo mijin auren ta kama dakinta" juyawa Abdullahi yayi ya sake kallon Na'
iman yace "Jeki ciki Na'ima" gaba daya suka miqe itada sa'ade har da sauran qannen nata suka shige ciki Abdullahin na bin bayansu da kallo, bayan shigarsu Abdullahi ya maida hankalinsa kan qannen nasa yace "Yarinya ba aure yakamata ayi mata yanzu ba, tayi
qanqanta ai" sai Ayuba ya marairaice murya "Toh Yaya daman ina ma mukaga kudin yi mata auren yanzu ma" Abdullahi ya sake gyada kai tareda cewa "Duk wannan ba matsala bane, ni in zaku amince zan tafi da yarinyar can gurina Kano ta zauna tareda iyali na, ku
bani riqonta sai in saka ta makarantan acan" daga Ayuba har Nasiru wangale baki sukayi da fara'a, sai Ayuba yace "Yaya ai kaima 'yar kace Na'ima kam, wallahi ba wani abu indai ta nine nabaka Na'ima halak malak" Nasiru yaqara da "Kaima kanada wannan ikon a
i Yaya, yarinyar ka ce, babu komai, godiya muke ma" Abdullahi ya gyada kai cikin
amincewa da zancen su yace "Nagode matuqa" ya saka hannu a aljihu ya ciro bendir din kudi sabbi na yan dubu dubu har guda biyar ya ajiye nan kan tabarman yace "Ga wannan kuma
ba yawa , yaranku kuma Dan Allah a daure asakasu ko a islamiya ne, yaro sai da ilimi a zamanin nan" jiki na kyarma Ayuba ya amsa da "Mungode mungode Yaya, Allah ya qara girma, in sha Allahu za'ayi yanda kace din" shima Nasiru sai godiya baki yaqi rufuwa, b
ayan Ayuba ya dauki kudin ya fara miqewa tareda cewa "Bari in shiga ciki sai a fara hada kayan yarinyar yanzu" da kamar Abdullahi ze ce wani abu kuma se ya basar tare da fadin "Toh shikenan babu damuwa"
Ayuba har yana tuntube da buta gurin shiga gidan, N
a'ima dake zaune kusa da umma suna qirga kudi a cikin wata roba ta dago kai tana kallonsa, Umma dai hankalinta na kan qirge ma bata dago ba, Ayuba ya kalli yaran tsakar gidan yace "Duk ku fice zamuyi magana" hanyar waje yaran sukayi cikin azama sa'ade na b
in bayansu, miqewa Na'ima tayi yace ta koma ta zauna ita sannan ya kalli Umma da ke qirga kudinta har sannan dan bataso tayi bata, yace "Jummai fara hada kayan yarinyar nan Yaya Abdullahi zai tafi da ita kano gurinsa" zubewa chanjin hannun Umman sukayi gab
a daya ta dago kanta a gigice tana kallonsa, ware Ido tayi tace "Iyee?" Ayuba yace "Tashi mana" miqewa tayi tace "Can gidan kudin zai tafi da Na'iman?" sai Ayuba ya gyada kai tareda cewa "Riqonta ya koma hannunsa kuma" Anty Amarya da fitowarta daga bandaki
kenan ta ajiye butan hannunta tana kallonsu, ita kanta Na'ima bata gane me kawun nata yake fada ba har yakai qarshen aya akan bayanin dayake wa su Umma na batun da Abdullahin yayi, Umma ta ware Ido tana washe baki tace "Ni fa daman yarinyar nan tun da nas
an da qashin arziqinta take yawo, Na'ima kin huta a rayuwa kekam, daga wannan abun arziqi sai wannan" Anty Amarya ta riqe haba tace "Malam Abu yayi kyau, amma kuma kayi ragon azanci da baka fada masa akwai goro akan yarinya ba" Umma ta bi ta da wani kallo
tace "Narantse da Allah Malam da kayi kuskuren bada Na'ima gurin Abida daman da kowanne abun arziqi haka zai wuce yarinyar nan a duniya, nidai Allah yaji ya gani inason Na'ima itama shaidace" Ayuba yace "Ku mata kullum matsalarku sabuwa take komawa, in anc
e ga gabas ku kullum yamma kuke kallo, ke yanzu Abida yau ko aure ne akan Na'ima Yaya yace zai tafi da ita bama tsinkashi ba sutafi?" Umma tace "Fada mata, wallahi fada mata Malam" Anty Amarya tace "Malam bafa cewa nayi kar a tafi da ita ba, nufi na da sai
ka fada masa alqawarin dake kan yarinya sai asan ta yanda za'a bullowa yaro in ya dawo" Ayuba yace "Ta inda aka hau tanan za'a sauqa" ya kalli Umma yasake cewa "Jummai hado kayanta" nan Umma ta tsallake kudin zata wuce daki sai kuma ta juyo tace "Toh Mala
m ai nima zan hada kayana sai in rakata ko, kaga gwara muga gurin da ta ke" Ayuba ya harareta yace "Aure ne abun da har sai an mata rakiya" tace "A'a malam, mutum yazo rana tsaka kawai sai ka dauki 'ya kabashi batareda ka taba zuwa inda yake ba kenan" yace
"Dan'uwan nawa na jini kike nufin da bare, wai meyasa kullum sai kin tada zaune tsaye ne Jummai" sai ta juya tana magana qasa qasa ta shige dakinsu Na'ima, sai kuma ta sake leqowa tace "Na'ima taso mu hada kayan" Na'ima dake zaune tun dazun suna magana ta
na binsu da kallo ta kasa magana, zuba kudin tayi cikin roban cinikin nasu sannan ta miqe tabi umma dakin cikin sanyin jiki, Anty Amarya ta kalli Malam tace "Malam kayi hakuri ni dai se na sake magana, ya fa kamata kaje ka sanar da goggo tukunna" Ayuba yac
e "In mun fita gaba daya zamuje can din" Anty Amarya ta rinqa kallonsa ta rasa ma me zata sake ce masa, tabbas tanason zuwan Na'iman Kano, Amma yanayin gaggawan lamarin ne bai mata ba kwata kwata, salame ce suka shigo gidan dasu Kamal Umma ta fito daga dak
in riqe da wata yagalgalalliyar Ghana must go din Na'ima a hannu tace "Salame.. 'yar'uwarki dai zata koma kano
gidan arziqi" Salame ta ware Ido tace "Ita kadai kuma Umma? nima ba'ace da ni ba?" Kamal ya kama dariya, Umma tace "A sannu zamuje mu ganta ai" A
yuba da ranshi ke baci akan sun ajiyesa nan tsaye ya karbi kayan ya nufi fita, juyawa Anty Amarya tayi ta shiga dakinta, Na'ima ta bita da kallo tanason bin ta cikin dakin amma ta rasa ya zatayi, itafa abun ji take kamar almara ace kwatsam zata koma kano d
a zama gidan mutumin da se yau ta taba ganinsa ma, hawaye ta fara sai Umma ta kalleta tace "Kiji ki da wani fi'ili, keda Allah ya aiko miki babban rabo a rayuwa shine zakiyi kuka" Na'ima ta jijjiga kai tace "Banason zuwa Umma" salame ta harareta tace "Kuka
n dadi ma kikeyi, ni adaukeni mana kigani in banyi murna ba" fitowa Anty Amarya tayi daga dakinta hannunta riqe da sabulu tazo ta kama Na'ima suka wuce bandaki da ita akan tayi wanka, Umma ta bita da kallo tana tabe baki, a gurin wanke kai ne Anty Amarya t
a rinqa nasiha a Na'iman tace "Kiyi hakuri kinji Na'ima" fashewa da kuka tayi tace "Wallahi bana son zuwa Anty" sai Anty ta kwantar da murya tace "Toh kinfison ki zauna kiyi ta tallan ne?" Na'ima ta jijjiga kai tace "Amma bansansu ba Anty" tace "Bakomai Na
'ima a sannu zaki sansu kinji, kiyi musu biyayya, in an saki aiki shima kiyi, kinga makarantar da kikeso din zasu sakaki in Allah ya yarda" Na'ima ta gyada kai bata bar hawaye ba, Anty Amarya dake kallonta ta share mata hawayen tareda karkade mata gashinta
daya zubo fuskarta aranta tana addu'an Allah ya bawa Na'ima gurin da zata nutsu tayi walwala a rayuwa itama kamar sauran yara....
Bayan Na'ima ta shirya tananan tsaye tsakar gida yaran gidan duk sun zagayeta, Umma ta dauko hijabi ta miqa mata ta saka sai
kuma ta kai hannu tafara gyara mata wuyan hijab din tana kallon ta tace "Inda rai wataran har saudiya se kinje kuma ki kaimu Na'ima, taurarinki masu haske ne" Anty Amarya ta jijjaga kai tana murmushi, shigowa Ayuba yayi hannunsa riqe da katon din taliya w
ani saurayi biye dashi da buhun shinkafa, nan ya jingina a qofar dakinsa ya juyo rai a dan bace yace "Kun ajiye babban mutum fa yana jira a waje, tafiya ce doguwa a gabansu " ahaka suka rako Na'ima har waje gurin motan, Abdullahi yace da driver su koma gid
an da suka fara zuwa which is gidan goggo kenan, Na'ima sai kuka, Abdullahi ya shafa kanta yana murmushi yace ta shiga bayan motan, haka ta shiga tana hawaye su Umma da Anty Amarya suna daga mata hannu, salame na gefe rai duk babu dadi tafiya babu ita, tar
e suka je gidan Goggon da su kawu Ayuba, a lokacin da su Nasirun suke mata bayani yanayinta ne ya fara canjawa sai kuma tayi saurin gyara fuskarta kasancewan Abdullahi na gurin shima, duk da ranta be so hakan ba dai sai ta nuna bakomai ai shima 'yarsa ce N
a'iman, dan tasan a yanda Ayuba suke rawan kafan a tafi da Na'ima ko bayan Abdullahi ya tafi sai sun bishi da yarinyar tunda yanada kudi, dan space din da Goggo zata kebe da Na'iman ma bata samu ba haka sukayi sallama, zuwa lokacin Na'ima ta hakura da kuka
n ma tana ganin ikon Allah kawai, dasuka fito Goggo ta shafa kanta tace "Allah ya yiwa rayuwarki albarka Na'ima" iya abunda bakinta ya iya cewa kenan...
Na'ima da kawu Abdullahi ne a bayan motan sai driver dake tuqi cikin gudu, dama Na'ima sarkin shiru
ce balle yanzu abun ya hade da baqunta, sai Ido..tun tana zuba Ido taga sun iso Kano har ta gaji tayi bacci, a Gombe sukayi sallan azahar driver ya siyo musu abinci, tanacin abincin kanta a qasa kawun yace "Ki sake kici abincin kinji daughter" ta gyada ka
i ta cigaba idonta dai still a qasa dan bata iya kallon kawun nata, da suka sake daukan hanya ne Abdullahi ya kalleta yace "Kin taba zuwa Kano?" Ta jijjaga kai tareda amsawa da "A'a" yayi murmushi yace "You'll love it there daughter" tsayawa kallonsa tayi
batasan kuma wane amsa zata bashi
ba, tuna batajin turanci yasashi sake cewa "Zakiji dadin zaman can, ai kinason makaranta ko" cikin sanyinta tace "Eh" ya shafa kanta yace "In Sha Allah zakiyi daughter" ....
Ranan sai dare suka isa Kano, Na'ima ta ware ma
nyan idanunta tana kallon komai, wata unguwa suka isa da kana ganinta kasan sai manyan mutane ne masu zaman cikinta, horn driver yayi maigadi ya bude musu suka shiga cikin babban compound din, idon Na'ima kamar ya fadi qasa dan kallo sai waige waige take t
ana bin parking space din da kallo.. Abdullahi ya zagayo ta inda take ya riqo hannunta suka wuce main entrance din gidan, shigan su falon nan ma Na'ima dai sai Ido, ita ba kallo ko karatun littafi take ba balle mind dinta ya kawo mata ire iren falo haka, b
asu kai ga qarasawa ciki ba Na'ima taga wata katuwar mata me qiba tana sauqowa daga stairs hannunta duk zobunan gwal tasha les, Abdullahi ya sake hannunta yace "Je ki gaida maman ki" kyam Na'ima ta tsaya anan falon tanajin duk wani kuzarin ta na tsiyayewa
ganin irin kallon da Matar ke mata.
Tun daga sama har qasa Hajiya Ladi ke kallon Na'iman har ta qaraso cikin falon, sannu da zuwa tayiwa mijin nata ya amsa sannan ya miqa mata babbar rigansa da ya riqe a hannu ta karba bata daina kallon Na'iman ba tace "W
annan fa? Baquwa mukayi ne" Abdullahi ya zauna kan kujera yana kallon Na'iman dake tsaye shima yace "Zauna Na'ima", nan kan carpet ta zauna kanta a qasa, yace "Yar marigayi Yusuf ce" Hajiya ta dan hade gira cikin son tuno waye haka, sai Abdullahi ya sake c
ewa "Yusuf dai qanina na Adamawa" tace "Ohh, Allah sarki, yarsa ce wannan din?" ya gyada kai bai ce komai ba, ta sake cewa "Ayya Allah ya jiqan rai" sai kuma ta nufi wani corridor dake nan falon wanda kitchen ne a gurin, shima miqewa ya sakeyi yace da Na'
iman "Bari tazo ta nuna miki inda zaki zauna, make yourself at home daughter" Na'ima ta gyada kai sanyin Ac na ratsa duk wata kafa na jikinta, wucewa yayi stairs ta bisa da kallo, sai yazamo daga ita sai Tv dake aiki a falon....can Hajiya ta fito daga kitc
hen d hannunta riqe da tray na abinci, zuwa tayi ta wuce Na'ima dake zaune nan falon ta haye sama bata ce mata komai ba, shiru shiru Na'ima na zaune sai ga wata babbar mata tashigo da alamun me aiki ce tace "Sannu yarinya, taso muje ga dakin da zaki zauna"
ta qarasa maganan tana nuna wani daki dake nan downstairs, wucewa tayi Na'ima ta bita a baya suka shiga dakin wanda akwai komai na amfani a cikinsa, matar me suna shafa tace "Ki shiga bandaki kiyi wanka bari na kawo miki abinci" ta juya ta fita ta bar Na'
ima nan tsaye tana tunanin kayan ta da bata ga an dauko mata ba, shiga bandakin tayi tana binsa da kallo tarasa ta Ina ma zata fara wankan, Allah ya taimaka sai ga shafan ta leqo tafara nuna mata itadai sai gyada kai kawai, bayan tayi wankan tadan taba abi
ncin da shafan ta kawo mata sai ta zauna nan qasa bata hau gadon ba tanajin wani iri aranta ganin wani babin rayuwa da ta shigo ciki wanda bata taba mafarki ba.......
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 25
Jingina Na'ima tayi da gadon stil
l bata daina tunanin yanda rayuwanta ta dauko canji ba, ta rufe idonta wasu hawaye suka zubo daga mata, kuka tafarayi nan zaune abincin na gabanta, sai da tayi me isanta sannan ta share fuskanta, tananan zaune aka bude kofar dakin nata shafa ta sake
shigow
a wannan karon hannunta riqe da Ghana must go din Na'ima, tace "Yar nan bazaki hau gadon bane, ga kayanki nan" Na'ima ta gyada kai tareda miqewa ta karbi kayan shafa na bin ta da kallo sannan ta bude mata wardrobe tace "Sa kayan naki anan" bayan Na'ima ta
ajiye gurin da shafan ta nuna mata sai ta sake komawa zata zauna a qasan shafa tayi saurin dauko blanket daga cikin wardrobe din ta ajiye nan gadon tana instructing dinta ta hau gadon, cikin sanyi Na'ima tace "Zan wanke hannu na" shafa ta gyada itadai bata
daina kallon yarinyar ba, ganin ta qarama ga kyau, ga kuma wani sanyin nutsuwa atattare da ita, bayan ta wanko hannun a toilet ta hau gadon shafa tayi mata saida safe sannan ta kashe wutan dakin tareda rufewa bayan ta fita..
Daren ranan dakyar Na'ima tay
i bacci, tana ta saqawa da warwara a zuciyarta, abu daya yake qara mata qarfin gwiwa akan zuwanta wannan gida, shine in ta tuna makarantar da kawun nata ya mata alqawarin yi....
Washegari bayan ta tashi tayi sallah batayi gigin fita daga dakinta ba, dan b
atasan me zata farayi bama a gidan, har gari ya gama wayewa kusan karfe takwas bata fito ba, sai da taji yunwa na neman nuqurqusar ta sannan ta bude qofan a hankali ta leqa babban falon, gidan shiru kamar Allah beyi halitta cikinsa ba, fitowa tayi ta tsaya
bakin kofan tana bin ko ina da kallo