Showing 81001 words to 84000 words out of 121625 words

Chapter 28 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

46

ya tafi?" Mami tace "Yi sauri da Allah kar ya tafin" cikin sauri ta bar falon tana cewa "Ina zuwa Na'ima" gyada kai Na'ima tayi ta zauna a kujera, dan kallonta Mami ta tsayayi b

ayan sun gaisa sai tace "Na'ima me yake damunki kika rame haka?" tayi murmushi tace "Babu komai Mami" sai Mamin tace "Ko exams din da kukayi ne, kinacin abinci dai ko" nan ma ta gyada kai bata bar murmushin ba, basu dade nan zaune ba Nafisan ta dawo, bayan

sun dan taba hira tareda Mami sai suka tafi dakin Nafisan dake upstairs, sai da suka shiga Na'ima tace "Kika ce bakida lafiya kuma sai na ganki garau" dan dariya Nafisa tayi tace "So nake kizo muyi hira karki zauna shiru" murmushi kawai Na'ima tayi suka z

auna nan kan gadon Nafisa takawo mata abubuwan ciye ciye.. sai yamma ta koma gida dan tasan Bilal ba wunin gida yake ba, sai da ta dafa masa abinci ta ajiye anan dining area sannan ta tafi dakinta, a wannan daren sai Bilal yace takai masa tea dakinsa, nan

kan gadonsa ya ritsata duk a tsammaninsa ko dakinta ne yake sashi ciwon kan, amma duk fitinarsa abu yaci tura, miqewa yayi tsaye yana shafa fuskarsa bai bar kai komon da ya keyi a dakin ba cikin tsawa yace "Damn you Na'ima" baiwar Allah tana kwance akan ga

don duk ta galabaita gashinta yayi daddaya akan pillow tana hawaye, fusgota yayi yace "Are you even a woman?" sai ta rufe idonta tana jiran ya mareta amma beyi hakan ba, tsayawa kallonta yayi sai ya hankadata ta fada gadon cikin bacin rai yace "Dauki kayan

ki ki fitamin daga daki, you witch" cikin sanyin jiki ta tsince kayanta da yayi daddaya dasu anan tsakar dakin ta fice da bedsheet a lullube jikinta, bin bayanta yayi da kallo zuciyarsa na qunaa...

Washegari kulleta yayi a gidan, hakan kuma bai tada mata

hankali ba ta cigaba activities dinta a gidan, ashe dai tafiya Bilal yayi dan sai da Na'ima tayi sati biyu cikin gidannan bai dawo ba, da ya dawo ma bai kulata ba, haka ya rinqa kulleta a gidan kullum in zai fita, ranar da Nafisa tazo gidan sai Na'ima ta l

eqo ta window takira sunanta Nafisa tadan hade gira alamun confusion tace "ki budemin mana" hawaye Na'ima taji yazo idonta tace "ya kulleni Nafisa" ran Nafisa inyayi dubu ya baci ranar, sai ranar Na'ima ta fada mata kulletan da yayi shekarun baya, zama Naf

isa tayi anan varenda'n taqi tafiya, sai da Na'ima tayita roqonta sannan ta tafi...Dare sai ga Bilal din ya dawo a bugensa abun mamaki sai bai kulata ba har sannan, washegari tayi masa breakfast tana serving dinsa yana nan zaune a dining chair din yana sip

ping tea kawai aka fara banging kofa da karfi, da sauri Na'ima ta ajiye serving spoon din hannunta ta nufi kofan ta bude Bilal na kallonta..Nafisa ce ta shigo ranta a bace ta dan ture Na'iman sannan ta qarasa cikin falon tana kallon Bilal fuskarta bayyane

da bacin rai, Na'ima tayi saurin kamo hannunta tace "Nafee muje sama" sai ta fincike hannunta ta qarasa gurin Bilal dake sipping tea yana kallonta har sannan , cikin daga murya tace "Anya kai musulmi ne Bilal, bayan dukan har kulle ta kakeyi kamar akuyar k

a, wai kai wane irin dabba ne nikam" ajiye cup din yayi yana kallonta with shock, ganin haka Na'ima tayi sauri shiga gaban Nafisa tace "Nafisa ki tafi dan Allah" sai Bilal yace "No barta ta gama then I'll show her waye dabban nida ita" cikin hargagi Nafisa

tace "Wooohh..Lallai Bilal da kasan ba kowacce mace ake tabawa akwana lafiya ba" miqewa yayi, ganin haka cikin sauri Na'ima ta tunkuda ta zuwa kofan fita tace "Get out Nafisa" ran Nafisa a bace tace "Ki barshi ya tabani yagani in beyi kwanan cell ba

walla

hi ban cika yar Wadzani baaa" tsayawa kallon Nafisan yayi, ta cigaba da magana rai a bace "Wawa mai gwada qarfinshi akan mace, kai har wani jan wuya ka dauki kanka" Na'ima tayi mata tsawa "Enough Nafisa, ki fita daga gidan nan, meye hakan kikeyi?" Nafisa n

a kallonta tace "Na'ima ni zaki kora daga gidan ki akan Bilal?" ranta a bace ta amsa da "Ki tafi banaso" hawaye Nafisa ta fara sai ta juya ta fice daga gidan..juyawa tayi zata qarasa gurin Bilal kawai ya dauki mug din tea ya wurgo mata ya bugeta a kafada t

ayi saurin kai hannu gurin, rai a bace yace "So you're going around telling people I'm a monster" kuka ta fara tana girgiza kai, yace "Zan nuna miki ni monster'n ne Na'ima" ya qarasa maganan tareda nufota...

Sai da tayi sati tana kiran Nafisa wayan baya

tafiya duk hankalin ta ya tashi da hakan gashi violence din Bilal na kullum daban, abun sai ya hadewa Na'ima har ya zamto bata cin abinci akai akai, tana cikin wannan halin ne wani taro ya tashi a school din nasu na wa'inda suka gama, burin Na'ima a wanna

n lokacin ta gamu da Nafisan su shirya dan ita kanta tasan bata kyauta ba, all that Nafisa did was out of love, tasani ranta ne ya baci har tayi abunda tayi, da suka hadu a wajen taron ne Na'ima tayi saurin nufan ta sai Nafisan ta dauke kai ta kai waya kun

ne, sanyi jikin Na'ima yayi sai ta nemi guri ta zauna tana kallonta jefi jefi, sai da aka tashi tayi sauri zuwa gurinta tareda riqo hannunta, rai a dan bace Nafisan tace "Ni ki sakeni, na rantse ko kasheki mahaukacin nan zeyi bazan sake cewa qala ba" Na'im

a tace "Dan Allah kiyi hakuri wallahi nayi hakan ne dan ki tafi saboda nasan zai iya dukanki Nafisa" dan dariya Nafisa tayi tace "Bilal fa sai ranan na gane da hankalinsa, ba kowa yake duka ba wato, kinsan Allah bazai iya duka na ba, duk dama jikina rawa y

a fara daga baya amma shima na hango shakku a idonsa" Na'ima tace "Nidai kiyi hakuri" sai tace "Kiyi hakuri kema, nasan ban kyauta ba amma wallahi raina ne ya baci dan ko Mami batasan na fita ba" dan murmushi Na'ima tayi, Nafisa ta cigaba "Kiyi hakuri Dan

Allah, dan nasan ya dakeki bayan tafiya ta" shiru Na'ima tayi sai hakan ya tabbatar wa Nafisa hasashen ta, tace "Allah ya kawo miki sauqi cikin lamuranki Na'ima, Allah zai kawo qarshen Bilal a sannu, watarana komai zai wuce" sai Na'ima taji zuciyarta ta ka

rye dan ita dai kullum tunaninta shine yaushe ne lokacin wucewan komai din zai zo, dan ta gaji....

Ba'a rufa kwana biyu da haka ba Stella ta dawo gidan, ranan da ta iso Na'ima kadai ta samu a gidan, sai da Na'ima ta tsorata da ganin kallon da take mata da

n kusan bangajeta tayi a bakin kofar ta shiga ciki, ganin haka yasa Na'iman tabarta anan falon tayi saurin komawa dakinta ta saka key...sai bayan Isha Bilal ya dawo gidan a sannan stellan tana kwance a dakinsa, direct dakin Naima ya wuce sai yaji a kulle,

ransa a bace yace "Uban meyasa zaki rufemin kofa" cikin sauri ta bude kofan yace "I need tea" ta amsa da Toh, da haka ya wuce nashi dakin Na'ima ta sauka zuwa kitchen din, bata dade da shiga ba ta jiyo ihun Stella daga dakinsa alamun duka Bilal din ke mata

, dan fitowa tayi falon sai taji kamar ta fita compound saboda dan tsorata da tayi, tananan tsaye Stella ta sauqo falon, saurin matsawa gurin dining area Na'iman tayi sai taga ta nufi kitchen ta fito hannunta riqe da wuqa ta nufe ta gadan gadan, da qarfi S

tellan ta nemi caka mata wuqan sai tayi qara ta riqo bakin wuqan da bare hands dinta, tura wuqan Stella tayi da dukan karfinta tana harin cikin Na'iman tace "Yau sai nayi ajalinki, wallahi sai na kasheki" duk yanda wuqan yake tsaga hannun Na'iman bata sake

shi ba, Kiran Bilal ta rinqa yi da qarfi, aikuwa ya fito da saurinsa beyi wata wata ba ya saka kafa ya

kwashe stellan anan falon, ji kake tim ta buga kanta da tiles, da gudu Na'ima ta nufi kitchen ta kulle kofa hannunta na zuban jini ba qaqqautawa, dankwa

linta ta ciro a gigice ta kulle hannunta nata, daga nan tsaye cikin kitchen ta rinqa jiyo bala'in Stella tana qundumo duk zagin dayazo bakinta, da mamaki Na'ima ta Jiyo Bilal na fadin "Baby tayaya zan bari ki kasheta, I'm sorry na dakeki cikin fushi ne but

I'm sorry" Stella na kuka tace "Wallahi sai ka rabu da yarinyar nan Bilal ko duk muyi mutuwan kasko" Na'ima na hawaye tajiyo Bilal yace "Ni banaso ki rinqa tada hankalinki akan yarinyar can, she's nothing to me, now let go to my room mugama maganan acan"

Stella tace "Ni bazan zauna a gidan nan yarinyar nan tana nan ba" yace "It's alright muje duk inda kikeso to" da haka suka fice daga gidan Bilal bai bi takan Na'ima ba, bayan taji fitan motan nasu tayi sauri fitowa tana kuka ta nufi dakinta da gudu, hankal

i a tashe ta dauko wayanta ta kira Nafisa, tana dauka tace "Dan Allah kizo yanzu, zan mutu wallahi jinina zai qare Nafisa, ta yanka ni" ta dayan bangaren Nafisa ta miqe daga cin abincin da sukeyi itada Mami da Al'ameen sai duk suka tsaya kallonta, tace "In

a zuwa yanzu" da haka ta fara kokarin barin gurin Mami tace "Baby meya faru?" cikin tashin hankali tace "Na'ima ce Mami, cewa tayi inje yanzu" da confusion Mami tace "Me ya faru?" da gudu Nafisa ta nufi upstairs Al'ameen dake gurin ya bi bayanta tareda Mam

in, da mayafin ta a hannu ta fito da gudu Mami ta riqeta tace "Ke ki nutsu ki fadamin me ya faru da Na'iman" tace "Nima yanzu zanje in gani" fita sukayi compound din tare Al'ameen ya karbi car key din hannun Nafisan ya shiga driver's seat, sai da suka tada

motan Mami ta leqo kanta tace "Ki kirani in wani abun ya faru Nafisa, zan kira ma"....

Kuka sosai Na'ima takeyi har lokacin tananan zaune aqasa cikin dakin nata duk ta hada zufa, zuwa sannan dankwalin duk ya jiqe shima da jini, a haka ta Jiyo horn kama

r tsayuwan motansu Nafisan, dakyar ta qarasa falo aikuwa aka turo kofan da sauri su Nafisan suka shigo, da gudunsu suka riqota Na'ima na kuka tace "Kasheni zatayi wallahi, Nafisa kukaini asibiti" da gudu Nafisan na kuka ta nufi dakin Na'iman dan dauko mata

dankwali, dan gashinta ya ware gaba daya a firgice take, cikin tashin hankali Al'ameen yayi sake kamota yace "Innalillahi, muje mota Anty" yana riqe da ita suka tafi motan Nafisa ta biyo bayansu, nearby asibiti suka nufa da ita basu sha wahala ba aka karb

i Na'ima suka wuce dakin dinki da ita, bayan angama har allura likitan ya mata, Al'ameen ne ya fita siyo magungunan da likitan ya rubuta, da likitan ya gama sai yayi ta mata fadan ta rinqa kula dan ce mishi sukayi langa langa ne ya yanke ta, bayan sun koma

gidan, Nafisa tace da Al'ameen ya zauna nan falon zatakai Na'iman daki, gyada kai yayi tareda miqa musu ledan maganin yace "Allah ya qara sauqi Anty, Allah ya kiyaye na gaba" Na'ima ta gyada kai tareda da masa godiya suka wuce dakinta, sai da Nafisa ta kw

antar da ita a gadon ta tsaya tana kallonta tace "Na'ima Ina addu'an Allah ya baki qwarin gwiwan barin wannan trapped rayuwan" shiru Na'ima tayi sai Nafisa ta nufi madubin dakin ta ja drawer ta dauko paper da biro, nan bakin gadon ta zauna tayi rubutu a ta

kardan ta miqawa Na'ima, miqewa zaune Na'ima tayi ta karba sai ta ga address ne rubuce ajiki, Nafisa na hawaye tace "Zamu koma Abuja qarshen satin nan, aikin da yakawo Abba Kano ya kammala, wannan shine address din gidanmu na can, I'll be waiting for you h

ar zuwa lokacin da zaki samu courage din barin wannan quntacciyar rayuwar Na'ima" fashewa da kuka Na'ima tayi tace "Nafisa ya zanyi, duk inda zanje sudin 'yan'uwana ne" itama tana kuka tace "Wallahi koda bahaushe yace hannunka baya rubewa ka yasar, saidai

beyi tsutsa ba Na'ima, dole ka yanke, ai bazance ki bar

'yan'uwan ki ba inda cikin lumana kuke zaune, yau inkin mutu ba damuwar kowa bane cikinsu, why can't you see that ke da babu duk daya ne a wajensu" kasa magana Na'ima tayi har sannan tana kuka, ganin

hakan yasa Nafisan miqewa ta fice daga dakin bata daina kukan ba itama..fita falon tayi tana goge idanun ta Al'ameen ya miqe yace "Ta samu baccin ne" Nafisa ta gyada kai tace "Eh mu tafi, Mami na ta kirana" da haka suka fice daga gidan har sannan Na'ima na

zaune kan gado tana kuka mai tsuma zuciya....

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 35

Sai da taji tashin motansu alamun sun tafi ta qara sautin kukan nata, sai ta kwanta a kan gadon ta dago hannun nata dake nannade cikin bandage tana k

allo bata daina kukan ba, Na'ima tayi kuka ta gode Allah wannan daren, dakyar ta tashi tayi sallah, bayan ta idar ta daga hannu sama cikin kuka tana roqon Allah ya kawo mata dauki cikin lamuranta, nan kan sallayan ta kwanta tana addu'an bacci yazo mata ko

zata samu sauqi a zuciyarta, shigowan motan Bilal cikin gidan taji sai ta rufe idonta..

Shikadai ya shigo falon dan a sannan ya nemawa Stella hotel dinda zata zauna kafin ta koma Lagos, dakyar ya lallabata ta amince zata koma din, dakin Na'ima ya bude ya

ganta nan kwance a qasa, yace "Bakiji na dawo bane", sanin ba damuwarsa bane ya mata illa yasa Na'ima ta miqe zaune, ahankali tace "Sannu da dawowa" tsuka yayi ya juya ya nufi dakinsa, Na'ima na nan zaune taji kiciniyar sa da akwatin Stella ya fice daga gi

dan, ranan be kwana a gidan ba, can hotel din shima ya kwana..

Washegari da sassafe Na'ima taji bugun qofan falo, tayi saurin yafa veil akan doguwar rigan jikinta ta sauqa falon, Mami tagani tsaye tareda Al'ameen da Abu, fuskan Mami cike da damuwa ta ri

nqa kallon hannun Na'iman, iso ta musu suka shigo, bayan sun zauna sai Na'iman ta zauna a kujeran dake nesa dasu, Mami ta dafa gefenta tace "Zo nan ki zauna Na'ima" cikin sanyin jiki ta koma kusada itan, sai ta kamo hannun nata tana gani tace "Sannu kinji,

a garin yaya kika yanke da langa langan haka" Abu ya dawo kusada Na'iman shima yana kallon hannun yace "Sannu Anty", hawaye Na'ima taji ya kawo idanunta sai ta duqar da kanta ta fara kuka, rungumota Mami tayi tace "It's okay, ki rinqa kula daughter, Allah

ya kare na gaba" shidai Al'ameen sai kallonta yake sanin ba haka zancen yake ba amma besan dalilin da ya sa itada nafisan suka boyewa Mamin ba, da Mamin ta saketa tace da Abu "Dauko flask dinnan a mota" ya gyada kai sannan ya fice, sai a lokacin Mami ta r

inqa bin falon da kallo tace "Megidan naki ba ya nan ne?" Na'ima ta amsa da "Eh ya fita", da Abu ya kawo flask din sai Mami ta sashi ya dauko plate, anan falon Mami ta zuba wa Na'ima papper soup din da ta taho mata dashi din, suna dan hira ta saka ta a gab

a tanaci kadan kadan, Karan shigowan motan Bilal suka jiyo sai Al'ameen ya juya yana kallon kofan falon dan son ganin mijin Na'iman, because he sense that something is wrong a rayuwan Na'ima, daya shigo falon dan stiff yayi ganin mutanen da bai sani ba, ma

dadin ya qarasa su gaisa sai ya wuce direct upstairs ko sannu bai ce musu ba, Mami ta bishi da kallo da dan mamaki, duqar da kai Na'ima tayi tanajin hawayen takaici

na zuwa mata, babu wanda yace komai acikinsu sai can Mami ta kalli Na'ima tace "Nafisa ta f

ada miki zamu koma Abuja?" Na'ima ta gyada kai kawai, Mami ta cigaba "Ai zaki rinqa kawo mana ziyara ko daughter" nan ma hawaye kawai Na'ima take ta gyada kai, sanyi jikin Mami yayi sai ta kwantar da murya tace "Ki daina kukan nan, zamu rinqa yin waya ai,

call me if you ever want to talk to someone kinji" sai sannan Na'ima ta bude baki tace "Toh Mami" da haka Mamin ta fara miqewa su Al'ameen ma haka, har bakin motan nasu ta rakasu, Mami ta sake hugging dinta kafin ta shiga motan, Al'ameen yace "Anty nima ki

nada number na ai ko" Na'ima tace "A'a amma zance Nafisa ta turamin" ya gyada ahankali yace "Allah ya kare na gaba" sannan ya shiga driver's seat, dago mata hannu Abu yayi itama ta daga nata tana murmushi, da haka Al'ameen ya ja motan suka tafi Na'ima naji

n zuciyarta na karyewa...

data koma falon sai da zuciyarta ta buga ganin Bilal tsaye, fuskar nan a hade yace "Su waye su?" muryarta na dan rawa tace "Maman Nafisa ce" ya nuna ta da yatsa yace "Idan na sake ganinsu a gidan nan ko banzar kawar kin nan, sai

na illataki Na'ima" ta gyada kai tareda cewa "Kayi hakuri", dan tsayawa kallon hannun nata yayi sannan ya juya rai a bace ya koma dakinsa...

Komawansu Nafisa Abuja ba qaramin ta ba lafiyan Na'ima yayi ba duk da tana waya dasu, bata da aiki sai kuka akai a

kai yanzu kuma, in ta tuna babu inda za taje taji sanyi nan ma sai kuka, gashi Bilal ya dawo mata da sabon uzzurawa, idan bai daketa yau ba to gobe tasani sai ya daketa, kiranta yake da mayya a duk sanda ya daketan, akwai ranar da har allura ya danneta yay

i mata dan kawai yasamu biyan buqatarsa, amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login