Showing 18001 words to 21000 words out of 121625 words

Chapter 7 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

14

/>
Koda su Na'iman suka gama yin breakfast din bata tashi ba h

ar seda Ahmad ya tashi suka nufi falon Abba sannan ta miqe tafara taya Nafisa tattare wajen.

Bayan sunyi wanka suke shirya cikin simple attire, Nafisa ta saka musu kayansu cikin bag suka wuce gurin makeup din.

Sunyi kyau sosai bayan angama make up din

barinma Na'ima kamar ka sace ta, ankon daya kasance na lace ba qaramin haskata yayi ba.

Isarsu gidan bikin bayan sun gaisa da mutanen da suka idda a main falon gidan sai suka wuce part din Mamma dan Nafisa tasan acan zasu samu Mami, aikuwa ta na zaune tar

eda wasu yan'uwansu manyan mata, bayan sun gaisa dasu, Nafisa ta jasu dakin Salma

suka samu 'yan mata a dakin kowacce na yauqin ta isa, Husna da Salma basa dakin sai Laila da qawayenta sun hakimce kan gadon Salman, Nafisa na kallonta tace "Sannunku..Lail

a Ina Husna?" ta amsa dakyar "Bansani ba" zama suka yi kan tsabtacaccen carpet din dake shimfide a dakin, Na'ima daman bata kulasu ba tayi zamanta ko kallonsu batayi ba.

Laila ta kallate sannan tace da Nafisa "Yar zaman gidan naku bata tafi ba kenan" Nafi

sa ta juyo tana dan hararanta tace "Bangane ba, what do you mean?" sai Laila ta kyabe baki tace "Wannan ta kusa da ke din mana" Nafisa tace "First of all sunanta Na'ima and secondly, I'm in good spirits yau dinnan Laila karki batamin rai dan banida lokacin

ki" kafin Lailan ta amsa Luba dake zaune gefenta tace "Ha'a taga bare a cikinku ai dole tayi magana" a fusace Nafisa tace "Sannu Lubabatu, sannu 'yar'uwarmu ta jini, kinga idan ina magana ta hankali ki daina tsomamun baki, ke asuwa?" sanin masifan Nafisa y

asa Luba juyawa tana tsuka me qarfi, cike da tsiwa Laila tace "An fada din bare, dan wannan farin nata ba ta inda kuka hada jini da ita" Nafisa ta miqe Na'ima tayi saurin riqo gyalenta, ranta ya sosu da wannan maganar da suka fada har hakan saida ya nuna a

kan fuskanta amma ta danne tace da Nafisa "Mu fita Nafee" ganin yanda bacin ranta ya fito fili yasa Nafisa batayi musu ba ta jira miqewan Na'iman suka nufi hanyar fita daga dakin, 'yan matan dakin da suka tsaya kallon draman suka bisu da kallo, Laila tayi

tsuka tace "Gwara ku fitan dan nima banida lokacinku" wata qawarsu tace "To ke Laila me farar yarinyar ta miki?" Laila ta kalleta a fusace tace "Babu ruwanki".

Haka na'ima tayi wunin gidan bikin ranta duk babu dadi dan Nafisa ta zage itada Husna sai bid

irinsu sukeyi, Na'ima ta qi binsu haraban gidan da ake taro ta na zaune a main falon gidan riqe da yarinyar Anty Fatima immediate sistern Ahmad, sai wasa yarinyar take da dankunnen Na'iman.

Bayan ankai amarya tare dasu can gidanta dake cikin wata shahar

arriyar unguwa cikin Abujan, suna zaune cikin Mini falon amaryan Na'ima tace "Nafisa ki tashi mu tafi" Husna tace "A'a ku bari ango suzo mana" sai Na'ima ta dan bata rai sai kuma a hankali tace "Har sai mun jirasu?" kafin Husna tayi magana Nafisa tace mata

"Kinsan jaraban Na'ima kuwa, muje naji anty Amnah tace zasu tafi yanzu dan har ta kira za'a zo  daukansu" Miqewa Na'ima tayi jin haka dan duk a taqure take a gidan gashi ta gaji, gurin su Anty Amnah Nafisa ta kaita, Anty amnah tace "Gaskiyarki Na'ima bari

mutafi tare, barsu su gama rawan kansu" Nafisa tayi dariya tace da Na'ima "To sai na dawo" da haka ta koma upstairs.

Sunanan zaune aka kira Anty Amnah, bayan tabgama magana dana dayan bangaren ta kashe wayan tace "Tashi muje Na'ima mai daukanmu yazo" ta

qarasa tana fadawa wata mace dake gefenta, miqewa sukayi Anty Amnah ta sake cewa "bari muyi sallama da amarya" sannan suka wuce upstairs, Hanyan waje Na'ima ta nufa akan zata jirasu can gurin motan, fitanta ta hango wata black mota a haraban gidan ga light

dinta a kunne, qarasawa tayi tadan tsaya ba daf da motan ba, nacikin motan ya bude ya fito yana kallonta, dan riqe numfashinta tayi kadan ganin Ahmad.

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 13

Rufe cab din motan Ahmad yayi bayan ya fito, y

a jingina jikin motan hannuwansa cikin aljihun kayan jiikinsa yana kallonta, kauda kai Na'ima tayi daga kallonsa Jin zuciyarta ta fara bugawa kamar yanda takeyi aduk lokacin da suka hadu, dan sunkuyar da kansa yayi yana dan murmushi sannan ya dago ya cigab

a da kallonta baya ko kifta ido, sunanan tsaye babu me magana ya dan gyara tsayuwa zai fara takawa gurinta Laila ta fito daga gidan, sai ya dauke kai daga kallon Na'iman ya juya ya kalli Lailan, tuni ya dinke fuskarshi kamar bashi yake murmushi yanzu ba, t

unkarosa Laila tayi sai ta dan yi wani irin kallo a Na'ima sannan ta qarasa wajensa tana murmushi kamar bakin ta zai yanke tace "Yaya..Ashe kazo, Ina wuni" babu yabo babu fallasa yace "Lafiya" tace "Ko inzo mu koma gidan tare" yadan kalleta yace "Tare mu

kazo ne?" Laila batasan lokacin da ta juya ta kalli Na'ima da ta juya kanta ba, ta sake juyawa tana kallon Ahmad tana jin kunyan tsinka ta da yayi a gaban Na'iman, ta sake cewa "Kaiii Yaya" coldly Ahmad yace "Su anty Amnah nazo dauka" kafin ta amsa sai ga

Anty Amnah ta fito daga gidan itada wasu wata guda biyu, qarasowa sukayi gurin motan daya daga cikin matan tace "Laila kema dake zamu koma kenan" Anty Amnah ta riga Laila amsawa da "A'a haba dai, ai Salma baza taji dadi ba, bayan ga 'yan uwanta can suma su

na jiran ango da abokansa" matar tace "Gaskiya dai, ki jira abokan angon suzo su maidaku tukun" Shidai Ahmad tuni ya bude motan ya shiga, Laila ta matsa musu zasu bude kofan motan, sai Anty Amnah ta juya ta kalli Na'ima dake shirin shiga back seat tace "Zo

Na'ima ki shiga gaba, mu saimu shiga bayan" Na'ima ba don ranta yaso ba ta bude gaban motan ahankali ta shiga, Laila sai hararanta take tana jin kamar ta maketa.

Shigan Na'ima cikin motan qamshin turaren Ahmad mai sanyi wanda ya rikide dana motan ya buge

ta, Jin proximity dinsu yayi kusa yasa ta jin kamar ta fice daga motan amma haka ta dake idanunta na kallon gabanta, bayan su Anty Amnah sun shiga Ahmad ya tada motan suka wuce aka bar Laila nan tsaye kaman ta fashe....

Shiru Na'ima tayi kamar bata cikin

motan, su Anty Amnah sai hiransu suke, sun dan yi nisa da tafiyan Anty Amnah tace "Habibtin Mami yaushe hutun naku zai qare" cikin nutsuwa da sanyinta daya zame mata jiki Na'ima ta amsa da "Next week in sha Allah Anty" Anty Amnah tace "Mu zuwa Monday zamu

koma gaskiya" daya daga cikin matan tace "itama a England din take zama ne?"

Anty Amnah ta amsa da "Eh suna makaranta acan tareda Nafisa, yarinyar Mami ce itama" matan suka amsa da "Ma sha Allah...Allah ya taimaka" ciki ciki Na'ima ta amsa da Amin, Ahmad

ya dan juyo ya kalleta sannan ya maida hankalinsa kan tuqinsa.

Isarsu gidan Mamin sun fito dukansu Anty Amnah ke tambayan Na'ima "Anan zaki kwana ne kema" Na'ima ta dan jijjaga kai tace "Yaya Faruk zaizo mu wuce, zan dauki jakan mu a dakin Husna ne" An

ty tace "Toh"

Wuce su tayi tabarsu nan suna magana da Ahmad din daya fito shima ya tsaya.

Shigarta falon ta tadda Mamma ta fito daga kitchen din dake nan downstairs hannunta riqe da wasu ledoji, ta qarasa zata tayata riqe wasu, sai Mamma tayi murmushi t

ace "No, kibarshi daughter i can manage" duk da haka saida ta karba suka fara tafiya zasu wuce upstairs su Anty Amnah suka shigo, Mamma ta juyo tace "kun dawo" a gajiye su Anty Amnah suka zube akan kujeru anan falon tace "Mun dawo Mamma, Ahmad ne ya kawomu

, kinganshi can waje wai bazai shigo ba da mutane gidan" murmushi Mamma tayi tace "Nima sai asuba yake shigomin tunda aka fara hidiman bikin nan" ta qarasa magana ta na maida hankali kan Na'ima dake tsaye tana jiran su gama magana tace "Muje daughter" da h

aka suka wuce part din Mamma, sai da na'ima ta taya ta ajiye ledojin inda yakamata sannan ta mata sallama nan ta bata abubuwan bikin masu yawa a leda tayi godiya sannan ta wuce dakin Husna dauko jakarsu, wasu 'yammata ta samu a dakin kwance kan gadon kowac

ce na danna waya, dagowa sukayi suna kallonta sai Na'ima ta wuce gurin wardrobe din Husna ta dauko kayan nasu ko kallon gefen 'yammatan batayi ba, daya daga cikinsu tana kallonta tace "Kema a garin nan kike ne?" Na'ima tace "Eh" suka sake tambayanta "Ke ya

r'uwar su Nafisa ce?" wannan karon gyada kai kawai Na'ima tayi ta fice daga dakin aranta tana mitan "Kamar ita kadai ce aka gani baquwar fuska a taron bikin, sai tambaya ake mata kaman wadda taje gidan jarida"

Tana sauqa stairs kiran Faruk ya shigo wayan

ta ta tsaya ta dauka, daga dayan bangaren yace "Na'ima kinanan gidan Baban ne?" tace "Eh yaya" yace "To ki fito compound ki jirani ganinan na kusa qarasowa" ta amsa da "Toh" sannan ta qarasa sauqa tayi sallama da su Anty Amnah dake nan falon basu tashi ba,

sukace ta gaishe dasu Mami ta amsa da "Toh" sannan ta fice daga falon.

Fitanta wajen ta ganshi tsaye jikin motan hannunsa daya cikin aljihu dayan kuma yana danna wayanshi, jin takun mutum yasa shi dago kai ya kalleta, sai Na'ima ta danyi stiff a tsaye ga

nin Ahmad aranta tana tunanin "Daman bai tafi ba"

Gyara tsayuwa yayi yana kallonta yace "Let me drop you" bata bashi amsa ba ta tsaya kallonsa, sai da taga ya bude front seat sannan ta fara magana "Daman Yaya Faruk yace...uh..uh..munyi waya.." Zuba mata i

danu Ahmad yayi batasan lokacin da ta fara takowa gurinsa ba, miqa hannu yayi ya karbi jakan dake saqale a kafadanta sai ta sake masa, ya zagaya ya saka a booth sannan ya dawo wajenta ya jira ta shiga motan ya rufe mata kofan sannan ya shiga driver seat, s

higansa motan sai ta dan gyara zamanta ta juya tana kallon window jin motan kamar ya mata matsi Ita dashi kadai aciki, bai kalleta ba ya tada motan suka fice daga gidan, sun fito daga street din gidan Baban Na'ima ta hango motan Faruk zai shiga street din

shikuma, juyawa tayi ta kalli Ahmad da hankalinsa na ga tuqinsa, dan juyowa yayi, sai tayi saurin kauda kanta..Saida sukayi nisa Na'ima taji yace "Did i got something on my face?" Na'ima ta dan juyo batareda ta kalli fuskansa tace "Na'am?" parking motan ya

yi a gefen street, Na'ima batasan lokacin da ta dan ware idanu ta juya ta kalleshin ba, hada idanu sukayi yadan duqo kanshi kusada ita yana kallonta, Ji tayi isakan motan ya mata kadan kamar ta bude motan ta fice.. Ahmad na kallonta yayi qasa da murya yac

e "Meyasa bakyason kallona?" sai ta kauda kanta tana kallon titi bata amsa ba, ji take muryanshi na karya mata duk wasu gabobi na jikinta, sai ya sake kwantar da murya yace "Look at me Na'eemah" sai ta dan juyo bata kalleshin ba cikin sanyin murya tace "Me

yasa zan kalleka.." still yana kallonta shima cikin qanqan da murya yace "Because i want to see your eyes" batasan lokacin da ta juya kanta tana kallon window ba tana dan murmushi, shima murmushin yayi yace

"Na'eemah kin maida ni sirikinki ko" ta jijjaga k

anta tana cigaba da murmushin, shidai Ahmad duk ya lalace wajen kallonta, baisan meyasa yarinyar takeda wani effect me karfi akansa ba, ganin ba kallonsan zatayi ba yasa ya tada motan yana fadin "Shikenan, I'll have to try harder then."

Babu wanda ya s

ake cewa komai a cikin su, Ahmad yana driving din jefi jefi zai juya ya kalli Na'iman da har lokacin kallon window take, amma zuciyoyinsu are aware of each other, wani irin yanayi suke shiga dukansu biyun aduk lokacin da sukayi gamo da juna and it seems li

ke zuciyar kowannensu is reaching out to one another.

Bayan Ahmad yayi parking a kofar gidan Abban, Na'ima ta bude qofan zata fita taji muryasa cikin sanyi yace "Gidan Anty Amnah kuke zama a England din?" Na'ima ta dan juyo tace "A Oxford muke" ya sake

cewa "When are you going back?" sai ta dan dago ta kalleshi kadan tace "Sai next week thursday" bata jira jin abunda zaice ba ta bude kofan ta fice, fita shima Ahmad yayi ya zagaya booth ya ciro mata jakan sannan ya qaraso gabanta ya miqa mata, karba tayi

cikin sanyinta tace "Thanks for the lift" ya dan gyada kai yace "Take care of yourself Okay" sai ta gyada kai alaman Toh sannan ta juya ta shige gate din gidan yana binta da kallo.

Shigan Na'ima falon ta samu Mami da samarin gidan suna hira, Mami tace

"Sannu habibti, kun dawo?" ta qarasa ta zauna kujeran kusa da Mami tace "Eh Mami" Mami tace "Faruk dinne ya dawo daku? dan daga nan ya fita yace zaije daukoku" Na'ima tace "A'a..Yaya Ahmad ne" sai Mami tace "Ya kyauta kuwa, shine bai shigo ba" Na'ima tayi

shiru batace komai ba, sai Abubakar ya tambayeta "Ina Anty Nafisan?" tace "Su zasu jira abokan ango" dan dariya sukayi Al'ameen yace "Ai abokan angon ma sun shigo uku a hannun su Anty Nafisa" Mami tadan kada kai tana dan dariyan itama tace "Ai baby sai god

iyan Allah" Abubakar yace "Anty Nafisa ba sauqi, sai sun jira sunyi cash out tukunna, suyi draining abokan angon tas" suka sake kwashewa da dariya shida Al'ameen, Na'ima na kallonsu tana murmushi ta jijjaga kai sannan tace "Wannan maganan kamar a kunnenta"

Abubakar ya dan ware idanu yace "Haba Anty" Al'ameen bai fasa dariyan ba, Mami tace "Rabu dasu, kije ki dan watsa ruwa ki huta tukunna" amsawa tayi da "Toh" sannan ta miqe tana daukan jakarsu ta nufi upstairs.

Shiganta dakin ta jefa jakan akan gado ta

cire veil dinta sannan ta danyi qaramin tsalle ta kife akan gadon tana sauke numfashin gajiya, tunanin moment dinta da Ahmad tafara, his eyes..his voice... Ta tambayi kanta, why is she luring herself into another trap? as if her past didn't teach her enou

gh to stay away from any man, gamuwanta dashi baifi 'yan satittika ba, amma why is her heart reaching out to him aduk lokacin da suka gamu?..Ya kamata ta farka daga wannan mafarkin da ta fara, ya kamata ta gina katanga tsakaninta da Ahmad dan this is not t

he right time for it.

Tananan kwance taji anfara knocking door din dakin nata, miqewa tayi ta bude, sai tayi Ido hudu da Faruk dake kallonta yace "Na'ima naje daukoki Anty Amnah tace kin fita kina jirana kuma banganki ba" Na'ima ta dan kauda idonta daga k

allonsa tace "Eh nafito...uhm..shine Yaya ya dawo dani" yana kallonta yace "Wani Yayan?" ahankali tace "Yaya Ahmad" kallonta ya tsaya yi baice komai ba, Jin shiru yasa Na'ima dagowa ta

kalleshi, sai ya kauda idonsa yace "Okay, saida safe" ta amsa da "Toh Y

aya" ta mayar da qofan ta rufe.

Wanka tayi ta saka doguwan riga na cutton mara nauyi ta fice downstairs dan neman abunda zataci, su Mamin still tasamu a falon suna hira Mami tace "Habibti ga abinci can na ajiye muku a kitchen" ta amsa da "Toh" ta wuce k

itchen ta debo abinci ta dawo tazauna nan aka cigaba da hiran da ita, sunanan zaune Faruk ya sake shigowa shima ya samu wuri ya zauna alamun shima yayi changing, tambayansa Na'ima tayi ko zata kawo masa abincin yace "Eh" sai ta miqe ta je ta debo masa shim

a, Abba ne yashigo falon yace "Yau kun yiwa falona yaji kenan" suka yi dariya gaba daya, ya samu guri ya zauna aka cigaba da hiran dashi.

Sai qarfe tara Nafisa suka shigo gidan itada Husna, duk mutan falon suka dago kai suna kallonsu, qarasowa sukayi a ga

jiye Nafisa ta zube kusada Mami, Al'ameen yace "Sannu uwar bikin gaba daya" sukayi dariya, Gaisheda Abba sukayi yace "'Yar'uwarku ta dawo tun dazu shine bazaku biyota ku dawo baki daya ba, me kuka tsayayi can gidan Salman daren nan?" Nafisa ta marairaice t

ace "Abba itafa Na'ima cewa tayi bazata jira rakiyan abokan angon ba" Abba yace "Menene shidin?" Abubakar yace "Charges dinsu suka tsaya karba Abba" Al'ameen ya buge masa kafada suna dan dariya, Nafisa ta juya tana hararansu, Na'ima dai jijjaga kai tayi ta

na murmushi, sai Husa tace "Abba daman ana jiran abokan ango suzo sai su maida kawayen amaryan gida" Abba ya sake cewa "Toh from henceforth, banason ku sake yin dare haka a ko'ina" suka amsa da "Toh Abba, kayi hakuri" can Husna ta miqe tace "Mami akwai abi

nci" Mami tace "Kije gashi can a kitchen din" Nan suka zauna cin abincin Nafisan da Husna sukayi ta fayyace musu yanda suka wanki abokan angon millions of money su Faruk dasu Al'ameen na murmushi sanin sai anyi haka, Na'ima na mamakin yanda wasu basa jin n

auyin cire kudi a familyn su Nafisan.

A daren Na'ima tazo kwanciya su Nafisan suka shigo dakinta, hayewa kan gadonta sukayi Nafisa na cewa "Bobo wani abu ya sake hadoki da Laila ne" sai Naima ta miqe zaune ta jingina jikin fuskan gadon tace "Nafee me ya t

aba hadoni da ita nikuma" Husna tace "Kema dai Nafisa kinsan wannan yarinya mara setin ko ba'a mata abu ba haka take" sai Na'ima tace "Wani abu ya faru ne?" Nafisa ta girgiza kai tace "Babu komai".

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 14

D

an gajeran hutun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login