Showing 42001 words to 45000 words out of 121625 words
ya zauna, Nafisa tace "Yaya amma ka chanja interior na gidan?" ya dan bi falon da kallo yace "Eh Nafisa" tace "Yayi kyau
sosai, can i take a tour?" Ya gyada kai "Sure, go ahead" sai ta miqe ta nufi stairs tafara hawa sai kuma ta juyo fuskanta da fara'a tace "Yaya yau inason mutafi da jeep dinnan please" ya sake cewa "Ba damuwa, key din yana cikin bedside drawer na" ta gyada
kai sannan ta cigaba da hawa stairs din zuwa sama.
Juyowa yayi ya kalli Na'ima dake zaune har sannan batace komai ba, sai ya miqe yadawo nan gefenta a hankali yace "Yau ma bazaki kulani ba" itama cikin sanyin murya tace "Mun gaisa fa" sai ya rinqa kallon
ta fuskansa da murmushi baice komai, ganin haka sai ta fara wasa da bakin gyalenta, jin beyi magana ba tace "Me kakason ince to?" yace "Tell me how you missed me Na'eemah" dago kai tayi tana kallonsa shima haka sai taji idanunsa sun mata nauyi nan da nan t
a kauda kai tana dan gyaran murya tace "Ka daina kallona irin haka" sai yayi dan dariya yace "Fadamin ya nake kallon naki?" batace komai ba sunanan zaune Nafisa tadawo falon hannunta riqe da key tace "Yaya wannan ne ba" ya daga kai yana kallon key din yace
"Eh shine" zama tayi ta zuba musu juice din da yakawo musu dazun ta miqawa Na'ima sannan suka fara hira itada Ahmad din jefi jefi, kiransa akayi a waya ya miqe yana cewa "Sorry i have to take this" sannan yayi hanyar fita waje.
Juyawa tayi ta cewa Na'ima
"Bobo muje sama in nuna miki wani abu" sai Na'ima ta girgiza kai tace "A'a Nafee"
Nafisa ta taso tafara Jan hannunta tace "Dan Allah kizo muje, kawai wani abu zaki gani sai mu dawo" haka Nafisa ta jata suka je side dinsa da ke nan saman, sai taga sun w
uce falo da study room dinsa Nafisan zata jata wani daki tace "Nafisa is not proper in shiga masa daki dai" tace "Meye wani proper, da'alla kizo mu shiga" shigansu dakin Nafisa ta jata gurin master bed, itadai Na'ima sai bin gadon da kallo ganin girmanshi,
sai da suka tsaya daidai setin gadon sannan Nafisa ta kamo kafadunta ta juyar da ita suka kalli ginin dake facing gadon.
Hannu Na'ima takai bakinta tsabar mamaki tana kallon katon hoton ta da akayi framing anan jikin ginin, hoton ya kusa cinye gurin dan
girma, dariya takeyi acikin hoton bazata manta ba ranar da sukaje gurin sport dinnan ne domin kayan ne ajikinta cikin hoton..sunanan tsaye Nafisa bakinta kamar ze yanke dan murmushi tace "Yaya Ahmad is Finished" sai kuma tayi dariya tace "Na'ima..I'm truly
happy for you, for all of you..this is clean" itadai Na'ima takasa cewa komai sai hawayen da ya kawo idonta tunani iri iri a ranta, janta Nafisa ta sakeyi suka koma falon qasa nan suka samu Ahmad kishingide a sofa yana danna wayarsa, dagowa yayi yana kall
onsu Nafisa tace "Yaya zamu tafi" yace "So soon?" Na'ima sai kallonsa take tana jin zuciyarta wani iri, Nafisa ta sake cewa "Eh Yaya, yauwa yanzu ya zamuyi da motan Anty Amnah, inason mu koma acikin taka" ya danyi murmushi yace "Ba damuwa Nafisa, zan aika
mata anjima" sai ya sake cewa "I've ordered food, ku tsaya akawo tukunna" Nafisa tace "A'a Yaya a qoshe muke mukam" jakansu dake nan kan kujera Nafisa ta dauka suka fara nufan hanyan fita, shima miqewa yayi yabi bayansu har nan parking space, bakin Nafisa
yaqi rufuwa dan itadai Allah yasa mata son motan, duk yanda yaso Na'ima ta kallesa taqi gashi kuma
taqiyin magana, shigewa motan tayi itama Nafisa ta tada suka fice yananan tsaye....Ranan da dare da ya kirata ma baigane kanta ba duk tayi wani irin sanyi, h
aka dai yayi ta magana tana amsawa sama sama, ita jin ranta takeyi duk a hargitse ma tarasa me zata fara tunani guda daya, what if yazo ya san ta taba aure? , what if yasan tushenta? , what if yasan su waye mutanen da ta rayu cikinsu?.. dakyar bacci ya kwa
sheta daren ranan tsabar tunani..
Ranan wata laraba sun wayi gari da shirin zasu kai project papers dinsu gurin supervisors dinsu, da wuri suka shirya ko breakfast ma basuyi ba dan zuwan wuri sukeson suyi, bayan sunyi sallama da Anty Amnah suka fice , f
itowan su kofar gidan zasu nufi gurin motan Ahmad dake nan fake sukaga wata Uber tayi parking dan nesa dasu,
Tsayawa kallon Laila data fito daga bayan motan sukayi dukansu, drivern ya fito yafara ciro mata akwatin ta daga bayan motan..Nafisa da ke gefen N
a'ima tace "A'uzubillahi minash shaidanir'rajim..ji wani mummunan gani da farar safiyar nan" duk yanda Na'ima takai da Jin ranta babu dadi saida ta kusa fashewa da dariya.
Sunanan tsaye babu wanda yayi gigin tayata kama akwatin data ke ja da kyar, dan tsa
yawa Laila tayi tana kallon motan Ahmad dake fake a kofar gidan sannan ta qaraso gurin su Nafisan.
Nafisa tace "Ke kuma sauqan yaushe da safiyar nan" Laila na mata kallon banza tace "Ban sani ba" Nafisa tace "Hattara dai Laila, babu wanda nake shakka kaf
London, da dutse zan miki gugan baki wallahi" sai Laila tayi wani tsuka me qarfi tana hararan Na'ima da taqi kallonta, wucewa tayi har tana dan bangaje kafadan Na'iman tayi cikin gidan Anty Amnah'n janye da akwati suna binta da kallo, sai kuma Nafisa ta da
ga hannu sama afili tace "Allah ka yafemun zanyin abunda uwata ta haneni da yi"..
A hanyarsu na tafiyan ne Na'ima ta juya ta kalli Nafisa tace "Sis ko zamu koma namu apartment din tunda kin samu sauqi" Nafisa ta dan harareta tace "Wa? Akan Laila tazo kena
n, wallahi bazamu bar gidan ba saidai ita ta bari, tsoronta ma mukeji kenan" Na'ima ta girgiza kai tace "Banason tashin hankali Nafee" Nafisa tace "babu abunda zai faru dai sis, kema kinsan Anty Amnah ai, bazata dauki nonsense ba" shiru Na'ima tayi batace
komai ba sai Nafisa tasake cewa "Ki kwantar da hankalinki dan Allah, ba wani abu"...
Na'ima ce zaune akan wani rest bench cikin school premises din itada zarah hannunsu riqe da ice coffee, hira sukeyi kiran Ahmad ya shigo wayanta, bayan sun gaisa a nuts
e ya tambayeta "Babe where are you?" Ta amsa da "Ina school" ya sake cewa "I'm on my way now" sanin daga London ya kamo hanya yasata cewa "Allah ya kawoka lafiya" ya amsa da Amin sannan ta sake cewa "Zanje apartment dinmu dauko mana wasu kayan" daga can ba
ngaren Ahmad ya amsa da "Okay zanje can din daukanki" sannan sukayi sallama ya kashe wayan, tashi tayi sannan tayi sallama da zarahn akan zata tafi, saida ta tari cab anan bustling street na bakin makarantan sannan ta shiga suka wuce, a hanya ta kira Nafis
a bata dauki kiran ba kawai ta maida wayan jaka...
Isarta apartment din nasu ta fito daga elevator anan corridor din nasu taga wani kamar delivery man a tsaye a bakin kofan dake gefen nasu apartment din, wuce sa tayi bata ga fuskansa ba dan sanye yake d
a facing cap har da face mask, saida ta tsaya daidai kofar su ta saka door pin din ta bude zata shiga taji an hankadota da karfin gaske ta fada cikin gidan
nasu, kifewa tayi anan falon zuciyarta yayi wani bugawa da qarfi har tanajin bugawan a kunnuwanta sa
nin mutum daya ne zai iya mata haka a kaf duniya, ta juyo daga kwance tana kallon sa, rufo kofan yayi yacire face mask din yana kallonta cikin wani irin kallo dayake kada 'ya'yan hajinta tun fi azal, fari ne guy din kamar Na'ima amma babu ta inda suke kama
da juna sannan yanada dan kakkauran jiki, qarasowa yayi falon cikin muryansa me kaifi yace "Yaushe na fara wasa dake Na'ima" baya tafarayi tana dan jijjaga kai, isowarsa gurinta beyi wata wata yakai mata hari da kafansa akan cikinta, Na'ima tayi wani qara
tana kama cikin nata, sai da yayi mata harbin sau uku cikin tsawa yana cewa "Tell me...yaushe na fara wasa dake" sai ta fara rarrafawa tana dosan gurin kujera tana hawaye ya kamo gashinta ta bata ya dagota, hannu takai tana kama gashin nata da ya riqe taf
ara wani irin kuka, dagota yayi ya bugata nan jikin kujeran ta sakeyin wani ihu, yana huci yace "Har zan bada saqo gurin banzar kawarki sannan kiqi complying, who are you Na'ima?" kuka take bata ce komai ba har sannan, sai ta miqe zaune tana kallon cikin i
donsa, yana kallonta shima ya sake cewa "I warned you haduwan mu bazatayi kyau, dan haka ki tashi ki wuce daki ki debo kayanki mu tafi gida, and i mean NOW before i wound you"
Na'ima dake kallonsa tanajin zuciyarta tana bushewa for the first time, a hanka
li tace "Bazanje ba" tsayawa kallonta Bilal yayi with shock written all over his face.. tana kallonsa idonta na zuban hawaye ta sake cewa "Bazanje ko ina ba Bilal" ta qarasa maganan itama tana mamakin irin qarfin gwiwan data samu a karo na farko na tsawon
rayuwanta tareda Bilal, tunda ta mallaki hankalin kanta a rayuwa take tsoron Bilal da duk abunda ya shafesa..
Miqewa tayi still yana kallonta tace "Wallahi ko zaka kash.." bata qarasa ba ya dauke ta da mari bata farfado ba ya sake kai mata wani, baya tayi
zata gudu ya kamota ya bugata da bango tana ihu, yana huci yace "Maimaita abunda kikace" ta fara jijjaga kai zata kwace kanta kawai ya hau kai mata mari tana tarewa da hannunta, burinta daya a wannan lokacin shine takai ga zuwa kitchen ko zata samu wuqa,
dakyar ta kwace ta nufi hanyar kitchen din ya kamota ya sake bugata da kofan dakinta, Jin kofa a bayanta yasa ta bugawa ta fada dakin yana biye da ita, hannu takai ta daki mirror da karfi ya tarwatse a nan dakin ta dauki babban yanka guda daya ta juyo tana
nuna Bilal din dashi, jikinta na rawa tace "Ko ka fita ko muyi mutuwar kasko" yana kallonta bai motsa ba ta sake matsowa tana taka fasassun mirro'n daya zube nan qasan dakin, cikin ihu tace "Ka fita Bilal, ko in kasheka nima in kashe kaina"
Bilal ya shig
a shock sosai a wannan lokacin ganin yanda Na'iman daya sani ta rikide ta koma wata daban, sai yayi qasa da murya yace "Na'ima you've tasted freedom, is this really you?" Ta fara dosowa gurinsa yadanyi baya ganin da gasken zata iya caka masa, tace "Wallahi
ko ka fita daga gidan nan ko in kasheka" baya yafari suka fito daga dakin yace "Na'ima listen to m.." cikin ihu tace "I'm done, I'm done Bilal" sai kuka yazo mata kuma, tasake cewa "Ka barni nayi rayuwata, kabarni hakanan" Ya daga hannun sa alamun surrend
er yace "Alright zan fita, ki ajiye abun hannun naki tukunna" ta girgiza kai gashinta duk yayi daddaya tana zare masa idanu ta cigaba da doso sa da mirro'n hannunta yana jini, da baya da baya Bilal ya fita daga kofan, tana ganin ya fitan ta jawo kofan ta r
ufe da qarfi ta jingina bayanta nan jikin kofan tana fashewa da kuka me karfi, yardar da abun hannun nata tayi ta tsugunna nan bakin kofan ta cigaba kuka tana dafe hannunta a setin zuciyanta...
Qarar wayarta ta Jiyo anan kan sofa ta miqe dakyar ta isa gur
in, sunan Ahmad tagani rubuce a fuskan wayan, sai lokacin ta tuna ashe ya fada mata zaizo daukanta, daukan wayan tayi bata daga kiran ba sai ta nufi gurin balcony tadan leqa kanta..
Numfashinta ne taji ta tsaya a wannan lokacin ganin Ahmad a tsaye jikin m
otansa waya a kare kunnensa, daga gefensa a nan street din kuma Bilal ne tsaye shima da alamun yana jiran abun hawa, dukansu kusa suke tsaye da juna batareda daya yasan daya ba.. Na'ima ta dago wayan tana kallo ganin Ahmad ya sake mata wani kiran, kallon
su ta rinqa yi tananan tsaye in idonta ya kalli Ahmad sai ta kalli Bilal shima dake nan gefe........
Shin wai wacece Na'ima?, Menene asalin alaqarta da Bilal?, Shin ya kuke ganin wannan lamarin zai qare a tsakanin wa'innan mutane?..
Kudai ku biyoni da
n Jin labarin Na'ima da abubuwan da rayuwarta ya qunsa ......
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 22
Tushe Gandun Labari..
Asalin Na'ima Yusuf Dabo......
Na'ima jika ce a cikin Ahalin Malam Hamisu Dabo dake cikin garin Mayo-Belwa, Ad
amawa state, Malam Hamisu ya taso cikin nema sosai na sana'ar gwari kuma da ita Allah ya rufa masa asiri yake daukan nauyin 'yan'uwa da kuma iyalinsa, Matar sa daya mai suna Habiba wadda ta kasance bahaushiya yar garin kano suna rayuwa cikin rufin asiri, h
aihuwar Habiba biyar suna komawa babu rai wanda hakan ba qaramin tashin hankali yake sa musu ba, Habiba tasha tsangwana gurin dangin hamisu wanda har 'yan uwanta sun shaida hakan, rigima akayi sosai tsakanin danginta da na hamisu saboda har maita sun jingi
na mata akan hakan, 'yan uwanta sun shigo cikin lamarin gurin neman magani har daga qarshe suka rugumi dangana da hakuri, kuma sai Allah ya dubesu da rahama ya bawa Habiba wani cikin wanda ya kasance na shida kenan, cikin ikon Allah ta haifo danta namiji r
anar suna yaro yaci Abdullahi, Hamisu sun raini dansu na tsahon shekara kafin Habiba ta koma ga Allah, sanadin ciwon jeji da yayi mata mummunan kamu, mutuwanta ya jijjaga Malam Hamisu da 'yan'uwanta sosai amma haka suka rungumi kaddara sukayi hakuri, ranar
da 'yan'uwan habiba suka tashi komawa bayan zaman makokin ita Habiban, sun nemi abasu Abdullahi su koma garinsu dashi amma Malam Hamisu Sam yace "A'a" abar masa dansa zai kula dashi, danginsa da ba wani son Habiban suke ba tun can asali, basu nuna damuwar
su akan hakan ba, dakyar Malam ya yarda wata qanwar Habiba dake zama anan garin kano ta karbi Abdullahi dan itama a lokacin tana kan renon danta qarami wanda zeyi sa'an Abdullahi shima..
An dauki shekaru kafin Malam Hamisu ya sake wani aure, Kuma wani rag
on azanci sai be bibiyi bayan dansa ba 'ance dan Adam ajizi' , daga baya ya auri wata ana kiranta lantana me kai musu tallan nono gurin sana'arsa, sunyi zaman lafiya da lantana kuma a wannan karon sun samu haihuwa har yara hudu, babban cikin sunansa Ayuba,
Nasiru, Yusuf sannan lubabatu data
kasance kurma, acikin yaran Malam Hamisu babu wanda bai kama sana'ar gwarin ba, amma sai yazamo Yusuf ya hada tasa sana'ar da boko...
Yusuf ya taso daban cikin 'yan'uwansa tayanda daga kan halayyarsa har zuwa hazaqarsa
daban take, ga nutsuwa da rashin hayaniya, babu yanda Malam Hamisu beyi dashi akan ya kama sana'ar sa kawai ya ajiye boko ba amma abun yaci tura, su Ayuba da Nasiru kam dama 'ina zakuje? Kudi.. daga Ina kuke? Kudi.....' sai zafin neman kudi, kuma sunqi tar
uwa kamar wa'inda akayiwa baki, ta bangaren Yusuf kuma Allah ya rufa masa asiri daidai gwargwado, a iya karatun secondary din da yayi ya samu aka daukesa aiki anan makarantar primary na gwamnati dake cikin garinsu,
Ana tafe bayan wasu shekaru kowa yakai
ga gacin aure acikinsu, Lubabatu ce tafara aure aka miqata wani qauye dake nan kusada garin nasu, Ayuba da Nasiru kusan tare ma sukayi nasu auren, zuwa wannan lokacin sunyi neman kudin har fita ci rani zuwa manyan gari sunyi amma kudi sunqi zuwa kaman abun
masifa...
A lokacin da Yusuf ya tashi aure shikuma yadanyi kwari a fannin aikinsa da kuma sana'arsa dayake tabawa, wata yar maqotansu yagani yanaso sunanta Binta wadda afarko dai kyawunta ne abunda yafara rinjayarsa gareta, asannu asannu suka kuma daidai
ta ganin halayenta abunso, gashi mahaifiyarsa tana sonta, Binta ta taso gaban kakarta ne tareda qanwarta Halima, iyayensu sun rasu sai zama ya dawo dasu itada qanwar tata gurin kakarsu ta wajen Uba kuma se ya kasance ba wani dangin azo agani garesu ba, All
ah ne gatansu sai kakarsu da ta tsaya musu akan komai nasu..Aure akayi na so da qauna tsakanin Yusuf da Binta yarinya mai hakuri da kawaici, sai ta hadu da Yusuf shima mara hayaniya da kuma nutsuwa, anan cikin unguwa Yusuf ya fulaste gidansa daya siya me d
auke da daki biyu aka kai masa Bintarsa..Zama sukayi na so da tattalin juna, Yusuf na matuqar son Matarsa, Binta bata rufa shekara ba ciki ya bayyana jikinta, murna wajen Yusuf ba'a cewa komai, haka suka rinqa tattalin cikin tare gwanin sha'awa har Allah y
a kawo ranan haihuwar Binta suka samu diyarsu mace inda taci suna NA'IMA, yarinya son kowa gurin kyau da haiba, gashi Allah ya zubawa Yusuf son 'yarsa kamar ya maidata ciki, bini bini yake yawo da abarsa akan keke, abu kuma indai Na'ima tace tanaso a gidan
nan to sai an mata shi, dayawan lokuta hakan baya yiwa Binta dadi sanin me rayuwa ta qunsa yau mune gobe ba muba, Yusuf yakance "Tunda muna rayen, kuma Allah ya bamu iko sai muyi mata" Binta takan jijjaga kai kawai sanin kome zata ce masa bazai fahimta ba
saboda son 'yarsa ya rufe masa ido, 'yan'uwa da dangi kowa ya shaida Yusuf yana son 'yarsa Na'ima dan baya iya boye hakan agaban kowa..
Na'ima na datawa mahaifinta ya sakata nan makarantar da yake koyarwa, aka sakata a primary, tare suke tafiya da mahaif
in nata kuma tare suke dawowa gida a kekensa, kuma har zuwa lokacin Allah bai qara basu wata haihuwan ba, hakan kuma bai taba damun Yusuf ba sanin cewa komai na Allah ne, Binta ce ma mai saka damuwan hakan a ranta wani sa'in..
Babu dalilin hawa balle na s
auqa kawu Ayuba ya fara mitan wai Yusuf ya saka 'yarsa a makarantar