Showing 30001 words to 33000 words out of 121625 words

Chapter 11 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

53

ne ai, jikina yana ciwo" da haka ta bude ta shiga ta bar Na'ima nan tsaye

bata shiga motan ba, Ahmad ya qaraso wajenta bayan ya gama saka kayan, a hankali yace mata "Ko zakiyi driving

din?" Na'ima ta kauda kai cikin sanyin murya tace "Ban iya ba" shidai kawai kallonta yake ganin kamar kyau ma ta qara yi cikin kwanaki dayawan da

bai ganta ba, ganin bazata juyo da kanta ba yasa ya bude mata front seat din ya tsaya yana jiran ta shiga, Nafisa na kallonsu ta cikin motan sai murmushi take lamarin nasu na sata nishadi, aranta tana ayyanawa wato "Mutune biyu ne marasa yawan magana suka

hadu guri daya sai ake gudanar da alaqan a aikace bada baki ba", hannu Nafisa takai ta dan kwankwasa glass din sai Na'ima ta farga da ashe tana kallonsu, ta danyi saurin shiga gaban motan Ahmad ya rufe ya zagaya ya shiga suka tafi..

Shiru motan yayi Naf

isa dake baya taqi cewa komai dan dama itace mai fara hira a motan to yau itama tayi shiru tana kallonsu, driving dinsa kawai Ahmad yake jefi jefi yana kallon Na'ima da tayi shiru itama tana facing window, can yadan juya kansa back seat yace "Bude muku abi

ncin nan Nafisa", dauko ledan gefenta Nafisa tayi ta bude ta dauki nata burger da ruwa sannan ta miqawa Na'iman tace "Mungode Yaya" baice komai ba, Na'ima ta ciro sai kuma ta miqo masa tace "Zakaci?" juyowa yayi ya kalleta da dan murmushi a fuskansa yace "

Rowa zaki min?" Na'ima tayi murmushi sannan ta girgiza kai tana qara miqo masa, kallon ta ya dan yi sai kuma ya maida hankalinsa kan tuqinsa yace "Naqoshi", itama bata ci sosai ba ta maida sauran burgern cikin box dinsa ta fara karkade hannunta, sai ya zar

o tissue daga ma'ajiyinsa ya miqa mata ta karba tareda muttering "Thanks" Nafisa dake baya tana kallonsu ta dan jijjaga kai tana murmushi ta miqo hannunta ta zari tissue din itama....

Saida suka ci rabin tafiyan sannan suka tsaya a wani gas station dake c

ikin wani town nan kan hanyan tafiyar tasu, fita Ahmad yayi zai qara mai a motan, sai Nafisa ta dan matso gurin Na'ima tace "Sis bari naje restroom" Na'ima tacire seatbelt dinta ta juyo tace "Bari na rakaki" girgiza kai Nafisan tayi tace "Kijiki sai kace w

ata yarinya, yi zamanki yanzu zan dawo, mezan siyo miki cikin restaurant din" Na'ima ta jijjaga kai tace "Naqoshi, Dan Allah karki dade" dan murmushi kawai Nafisa tayi ta fita daga motan, fadawa Ahmad dake tsaye yana filling motan inda zataje tayi, sai ya

gyada kai yana cigaba da abunda yakeyi.

Bayan yagama ya shigo motan ya zauna batareda ya rufe kofan ba, shiru sukayi Na'ima ta rasa abun da zata fada sai taga ya juyo gareta a nutse yace "How have you been?" dago kai tayi ta kallesa tace "I'm fine" ya sak

e cewa "Ya karatun ku" tace "Alhamdulillah" suka sake yin shiru, ahankali tace "I'm sorry " yana kallonta yace "What for?" ta dan sunkuyar da kanta tace "For what i said the other day" ta jira jin amsansa sai kuma taji baice komai ba, dago kanta ta sakeyi

suka hada ido tace "I didn't mean what i said" shima ahankali yace "I'm sorry too" bata kai ga tambayansa meyasa ba taji Nafisa ta bude kofan ta shigo, gyara zama Ahmad yayi ya rufo qofan shima ya tada motan suka tafi...

Isarsu gidan Anty Amnah suka samu

batanan taje asibiti, dayake sunsan pin din kofan yasa basu damu ba, Ahmad bai shiga gidan ba yace "ku gaisheta inta dawo" Nafisa tace "bazaka shigo ka sha ruwa ba" ya girgiza kai yace "No" yana kallon cikin idon Na'ima yace musu "Take care" Nafisa ta gyad

a tayi godiya, Na'ima tace "Mungode" itama, gyada kai yayi yakoma gun motarsa ya tayar yabarsu nan tsaye, Nafisa tabi baya motan da kallo tace "sai na karbo motan nan munje school da ita" Na'ima ta kalleta tace "Kije dai bandani, daga ganin mota kin gigice

Nafisa" tana dariya tace "Yarinya bakisan motan bane" jijjaga kai kawai Na'ima tayi suka wuce cikin gidan.

Sai yamma Anty Amnah tadawo tareda twins data biya school dinsu ta daukosu, zuwa lokacin su Na'ima sunyi sallah sun huta har sun dafa musu abinci

..

Suna zaune a falon ta shigo alamun gajiya bayyane jikinta tace "Yan makaranta kun iso?" basu kai ga amsawa ba twins suka buga tsalle sukayi kansu, dariya Na'ima ta fara bayan sun danneta tace "Oyoyo darlings" nan gurinsu Anty Amnah ta zauna tana kallon

Na'ima tace "Sai sun ballaki ai, kai ku sauqa daga kanta" Na'ima tayi dariya batace komai ba.

Gaisheta sukayi ta amsa tace da Nafisa "How far..ya jikin naki?" sai Nafisa ta gyara zama tace "Naji sauqi Anty, gidannan kamar da magic cikinsa, sai naji na wa

rware" dariya kawai Anty Amnah tayi sanin da hadin bakinta Nafisa tayi qaryan rashin lafiyan, tace "Toh Allah ya qara sauqi" Na'ima tace "Anty akawo muku abinci ko sai kun huta" ta dan girgiza kai tana murmushi tace "A'a daughter ki barshi zamuje muci, tha

nk you".

Itadai tun ranan farkon ganinta da Na'ima take sonta, zamansu da ita kuma ta sake fahimtan dayawa daga cikin halayen yarinyar wanda a lokaci da dama ta kanyi ta tunanin ta Ina yarinyar ta gaza da har abubuwa suka faru da ita haka?, kallon Na'iman

tarinqa yi wadda ke biyewa hiran twins batasan ma san tanayi ba, ganin zata dago kanta yasa Anty Amnah tashi ta wuce dakinta zuciyanta cike da tunani...

Da daddare suna having dinner tareda Uncle Yasir shima, yace "Kuyi zamanku anan ku qarasa karatun nak

u kunji" Anty Amnah tace "Nima haka nace fa" Na'ima tayi shiru tana jiran Nafisa ta basu hakuri akan zasu koma sai taji akasin haka dan Nafisa cewa tayi "Toh Uncle in sha Allah" dan dago kai tayi tana kallon Nafisan da take cin abincin ta hankali kwance, U

ncle yace "Yauwa ko ku fa, trains din yanzu suna gudu sosai dan within awa daya da rabi ma zakuga kun isa, ko ya kika ce Na'ima?" ya qarasa maganan yana kallon Na'ima, gyada kai tayi ahankali tace "Toh Uncle" yace "Ma sha Allah, ai kun fara dissertation di

nku ba?" Nafisa tace "A'a Uncle muna kan yin research akai ne" yace "Allah ya taimaka, hope kunada group mates" Nafisa tace "Eh Uncle" Anty Amnah ta sake tambayan Na'ima da "Kema kin samu group mate dinne daughter?" sai sannan Na'ima ta dago kanta tace "Eh

Anty akwai kawata da zamuyi research din tare" Anty Amnah tace "Ma Slsha Allah, Allah ya baku sa'a" suka amsa da Amin...

Bayan sun koma dakinsu basu yi magana ba, Na'ima ta shige toilet ta bar Nafisa na rage kayan jikinta, bayan ta fito tasamu har Nafisa

n ta kwanta, changing tayi itama cikin kayan bacci ta zo ta zauna bakin gado tace "Nafee we need to talk" sai Nafisa tadan yaye blanket din daga kanta ta dago tana gyara zama tace "Inajinki meya faru?" Na'ima na kallonta tace "Are you hiding something from

me?" Nafisa ta girgiza kai tace "Haba dai..A'a kam, me kika gani?" tace "Komai ma doesn't sit right with me Nafisa, all of a sudden kince kin samu sauqi ko magani baki sha ba sannan Uncle sunce mu zauna bikiyi protesting ba kai tsaye kika yarda, kamar ba

ke bace Nafisan da nasani batason zirga zirgan tsakanin Oxford da London, what happened to you ?" sai Nafisa ta dan yi murmushi tace "Kiji ki da wasu zance, dan na yarda mu zauna shine akwai abunda ke damuwa?" Na'ima bata ce komai ba ta qura mata Ido, dan

matsowa Nafisan tayi kusa da ita ta riqo hannunta tace "Haba mana sis, kinsan ban taba boye miki abu ba fah" dan jijjaga kai Na'ima tayi tace "Ai komai yanada mafari Nafisa, nasani ko kin fara boyemin abubuwan da suka shafeki" Nafisa ta sake damqe hannun N

a'iman tace "Babu abunda nake boye miki, for better for worse kinsani you're my best person in this world" Na'ima ta gyada kai tace "Nima haka, kawai banason changes din nan danake gani gurinki ne kwana

biyun nan, you look strange" Nafisa tayi dariya tace

"Bawani changes Bobo" itama Na'iman dan dariya tayi tace "Yanzu zamu zauna anan din kenan?" Nafisa tace "Eh..Amma in bakyaso sai mu koma" tadan ware ido tace "A'a ni bance banaso ba, ai nan yafi ma" da haka suka fara hiransu da suka saba Nafisa ta ware sun

a surutu, dan dama shiru shirun nata bana Allah da Annabi bane...

Kiran Mami neh yashigo wayar Nafisan, tadan dakata da magana suna kallon fuskan wayan itada Na'ima, bayan ta daga sun gaisa daga dayan bangaren Mami tace "Baby nayi waya da Maman twins tace

min kunzo saboda baki da lafiya" Nafisa tace "Eh Mami banajin dadi ne" sai tace "To kuma shine waninku bazai kira a fada mana ba, tun yaushe ne bakida lafiyan kuma me yake damunki?" ta amsa da "Kwana biyu dasuka wuce ne fa Mami kuma na dan ji sauqi ma yan

zu, dama ciwon kai ne sai kuma dan fever haka" Mami tace "Toh Allah ya qara sauqi, tace min zaku dan zauna anan gidanta tunda ba wani lectures kukeyi a school din ba" sai Nafisa ta gyada kai tace "Eh..yasu Abba fa?" Tace "Yana nan lafiya bana kusa dashi, I

na Habibti fa bata muyi magana" miqawa Na'iman wayan tayi, bayan sun gaisa Mami tace "Habibti shine kuka qi kira ku fada mana babu lafiya" Na'ima tace "kiyi hakuri Mami wallahi na zata ta fada muku ne shiyasa ban kira ba" Mami tace "Antyn kuce ta kira ta f

adamin, ya kuke toh, ba matsala ko" Na'ima tace "In Sha Allah Mami yasu Abba?" ta amsa da "lafiyansu kalau, kuyi zamanku nan gidan maman twins din tunda bakwa yawan shiga makarantan" tace "toh Mami in sha Allah" da haka sukayi sallama tace su kirata fa in

wani abun ya sake tasowa...

Basu je school ba washegari daya kasance Friday sai sukayi hutawan su a gidan suna taba karatun, dan Anty Amnah ma ta fice gurin aiki ita da mijinta haka zalika twins suma suna school....bacci Na'ima tayi mai dadi sannan ta tas

hi tayi brush da wanka ta shirya cikin qaramin riga da dogon straight skirt ta fice falon, Nafisa ta samu tana cin abinci taja kujera ta zauna tace "Shine baki tadani ba, inata bacci har yamin yawa" Nafisa ta zuba mata madara a cup ta miqa mata sannan tace

"Nima fa yanzu na tashi, masu gidan duk sun fice" gyada kai Na'ima tayi takai cup din baki ta kurba tace "Nafisa kaina yayi datti ki wankemin ko muje salon" Nafisa tace "Wallahi kanki akwai wahalan wankewa, danayi miki last time fa kince salon zamuje next

" Na'ima tace "Toh ai yanzun ma cewa nayi ko kimin ko muje salon" sai Nafisa ta dan harareta sanin Na'iman tafison wankewan a gida kawai fadan salon din take, dariya Na'ima ta farayi ta ajiye cup din tana kallon Nafisan tace "Dan Allah ki wankemin kinji si

si na" sai kuma itama Nafisan tafara murmushi tace "Toh zaki yarda ki rakani gidan Yaya Ahmad ranan Sunday" tsaf Na'ima ta dinke fuska tace "Ni narasa dalilinki na sai munje gidansa, kin fara maita ne bansani ba Nafisa?" sai Nafisa ta kwashe da dariya tace

"Bawani maita, ni nazata ma straight zaki amince ganin irin kallon da kukewa juna jiya" Na'ima ta harareta tace "Banaso Nafisa, ni yaushe na kalleshi?" Nafisa tadan ware Ido tace "Lallai ma yarinyar nan kin rainawa kanki hankali ba ni ba, iyeee..sannu Na'

ima" ta sake wani dariyan ta cigaba "Ku gama kallon juna cikin soyayyar a gabana shine yanzu zaki wani kawo min wata maganan" Na'ima ta ajiye bread din hannunta ta miqe tace "Barmin gashin nawa ya rube toh, soyayya kuma halan kin fara ganin komai a baibai

ne cikin lamuranki yanzu" ta qarasa maganan tana wucewa daki fuskanta dauke da alamun murmushin da Nafisan bata gani ba, sai Nafisa tayi wata dariyan tace "Muna tafe dai Na'ima"....

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 19

Ranan Sunday babu y

anda Nafisa batayi da Na'ima akan ta rakata suje gurin Lauren da ta shigo garin ba amma taqi, Na'ima tace "Nafisa da ban sanki bane sai in yarda dake" Nafisa na murmushi tace "Kinji na rantse ba gidan Yaya Ahmad zamuje ba, ai tunda bakya son zuwa kuma na h

akura" Na'ima ta jijjaga kai tana qara jawo laptop din gabanta batace komai ba, sai Nafisa ta zauna kusa da ita tasake cewa "Haba mana Na'ima" still bata kulata ba ta sake cewa "Na'imaa" still dai ko a jikinta, Nafisa bata hakura ba ta sake cewa "Na'ima Yu

suf Dabo" sai sannan ta dago kanta ta kalli Nafisan tace "Ita Lauren din kullum ne take zuwa London wai" Nafisa tace "Shikenan kar tayi yawo tana matsayin influencer" Na'ima tace "Toh ai yau batanan gobe bata can ne gashi tanason ku rinqa yawon tare" Nafis

a tace "Wallahi kam, tace wai muje Licester jibi ma, amma bazan samu zuwa ba munada group research ranan nida teammates dina" Na'ima ta girgiza kai  "Toh meyasa kike bin ta ne ma wani lokacin" tace "Ha'a shikenan bazanyi yawon ganin duniya ba Na'ima, batur

e fa yace all work without play make jack a dull boy, hausawa ma sunce taba kidi taba karatu" Na'ima ta cigaba da duba abunda take typing tace "Toh nidai bandani, in kinga nafita to sai gobe Monday zuwa school" Nafisa tace "Toh kizo muje daganan sai mu biy

a salon a wanke kai din" Na'ima najin haka ta amince dan dama ta gaji da kan nata babu wanki...bayan sun shirya suka ari motan Anty Amnah dan tasu sun barota can Oxford daman, dagasken kuma gurin Lauren din sukaje , sun sameta a wani restaurant babba, Laur

en tayi musu ordern abinci already, itada nafisa suka hau baza magana, itadai Na'ima sai bin abincin take da kallo taqi ci dan har zuwa wannan lokacin bata saba da ire iren abincin qasar ba, tana dai cin wasu amma batacin nama a kowanne restaurant gudun ab

ata haramtaccen nama...Lauren ce ta juyo ganin batacin abincin tace "what happen ne'ima?" Na'ima ta danyi murmushi tace "I can't eat this" ta qarasa maganan tana daga hannu a waiter, sake order tayi na simple dish "fish and chips" ...

Salon din sukaje aka

wanke musu kai harda Lauren din, tun kafin a fara wankewa Lauren din kai tafara video har qarshe, Rashin sabon ganin hakan a gurin Na'ima yasa ta dan kalli Lauren ta jijjaga kai tana dan murmushi da mamaki ganin komai nata yana media, Nafisa tunda ta samu

wayanta bata kula da batun surutun Lauren ba ma....Gashin Na'ima ba qaramin kyau yayi ba da ya sha gyara aka daure mata shi in a dough, ita aka fara gama wa gyaran dan Nafisa har da kitso za'a mata ita kuma Lauren za'a mata qari sosai..

Sai yamma suka ko

ma gida bayan sun yi sallama da Lauren tace zata kawo musu ziyara nan gidan Anty Amnahn.

Isarsu gidan suka samu motan Ahmad fake a kofar gidan, Nafisa ta kalli Na'ima tace "Iyee sai ga Yaya Ahmad ya dawo, shida yake wuyar ganuwa" Na'ima tace "Ba kince dan

'uwanku bane, ko dai banji da kyau bane lokacin da kikace cousin din ku ne" Nafisa ta fara dariya tace "Wallahi in zan kwana Ina fadawa mutane iya yanko baqar maganar ki baza'a yarda ba" sai Na'ima ta danyi murmushi tace "Ni me nace kuma" Nafisa ta nufi gi

dan tana dan dariya tace "Babu..Amma kinsan dai inason alaqan ku ko sis, like seriously kuna burgeni, the match was perfect, ke fara shi fari ke dogon hanci shima haka, ga kyau Allah ya baki shima haka....soyayyarku me shirun nan tana burgeni Na'ima" itada

i Na'ima tarasa me zatace a farko sai kuma a hankali tace "Nafisa bazan iya soyayya ba, besides Ahmad can't

handle a messed up person like me" Nafisa ta dan dafa kafadanta tace "Haba Na'ima...kiyi living rayuwanki, ki ajiye duk wani batun abun da ya faru a

baya ko wani auren da kika taba yi, idan anzo wannan ramin Ina tabbatar miki zaku tsallaka tare indai yana sonki, Yaya Ahmad mutumin kirki ne kuma kinsan shine the right person da zai iya standing up to mahaukaci irin Bilal dasu Hajiya" Na'ima ta jijjaga

kai hawaye na kawowa idonta tace "Kinsan na kasa yarda har yanzu baisan inda nake ba Nafisa, bansan me yake shiryamin ba kuma tunda yace duk inda naje sai yadawo dani gidansa" Nafisa tace "Wannan ne kuma bai isa ba, shidin banza, Allah ya fisa wallahi, ki

kwantar da hankalinki babu abunda zai faru" Na'ima tayi shiru tana kallon kofar gidan Anty Amnah, Nafisa ta riqo hannunta tace "Mu shiga sis, babu komai, shi bai isa ya hanaki son wanda kikeso ba wallahi" Na'ima ba biye da ita batace komai ba suka shiga gi

dan...

Zaune suka samu Ahmad shida Anty Amnah a falon ga twins a kusa dashi, suna hada Ido da Na'ima taga ya mata murmushi sai ta samu kanta da maida masa murmushin itama, zama sukayi nan falon suma suka gaishe sa ya amsa idonsa akan Na'ima da itama kallo

nsa take jefi jefi, twins ne suka bar jikin Ahmad suka dawo jikinta, Jafar ya miqa mata popcorn din hannunsa akan taci, diban biyu tayi takai baki, Anty Amnah tace "Anyi wankin kan?" suka amsa da Eh, hawa jikin Na'ima jabeer yayi ya ja gyalen abayan nata a

take gashinta ya bayyana yace "Anty muga naki" ta dan ware Ido zata karbi gyalen Jafar dake jikinta ya ja ribbon din shima yace "Anty naki yayi kyau", Anty Amnah tadan musu tsawa tana cewa "Wallahi zan saba muku in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login