Showing 90001 words to 93000 words out of 121625 words

Chapter 31 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

32

sallan ta

daga hannu zatayi addua taji kuka yazo mata, har ta gama ta koma gadon ta zauna bata daina hawaye ba dan ganin Bilal din da tayi yau din ya tada mata abubuwa da dama da tayi tsammanin sun wuce a rayuwanta, wani kiran Ahmad din ne ya sake shigowa wayan nata

, sai sannan ta dauka takai kunne, shiru sukayi..daga daya bangaren Ahmad na tsaye bakin pool din gidansa sanye da Pj's hannunsa riqe da glass cup me dauke da champagne yana kurba kadan kadan, shiru sukayi na tsahon seconds kafin yace "Ya kan naki fa?" aha

nkali tace "Yayi sauqi" cikin nutsuwa shima yace "Sorry dear" bata amsa ba, ya sake cewa "Bakiyi bacci ba, ko na tadake?" tace "Uhm uhm" suka sakeyin shiru, cikin sanyin murya ta sake cewa "I want to tell you something" Jin yayi shiru yasata cewa "I'm sorr

y i didn't tell y.." bata qarasa ba taji yace "Shhhh, get some sleep now okay, we'll talk tomorrow" da sanyin jiki tace "Toh" yace "Allah ya baki lafiya" da haka sukayi sallama, ta bangaren Ahmad bayan ya kashe wayan sai ya tsaya nan riqe da cup din yana k

allon cikin pool din like he was lost in thoughts.....

Washegari da sassafe sai ga kiran wayan shi lokacin da Na'iman ta shiga toilet, data fito sai taga Nafisan na miqo mata wayan tace "He's calling" karba tayi ta kai kunne bayan ta amsa kiran, bayan ya

amsa gaisuwan ta yace "I'm outside, I'll be waiting for you" shiru tayi sai ya sake kwantar da murya yace "Babe" tace "Toh", shiryawa tayi cikin riga da wando me fadi sai ta saka dogon jacket daya wuce gwiwanta sannan tayi rolling veil, Nafisa na kwance ka

n gadon tana danna wayanta, sai da Na'iman tace mata zata fitan sannan ta miqe zaune tace "Please Na'ima try and tell him what he needs to know, bance sai kin fada masa komai ba tunda baki shirya hakan ba, but i know Yaya Ahmad will be ready to cross that

river with you when the time comes" gyada kai Na'ima tayi tareda cewa "Toh" sannan ta fita, babu wanda ya tashi a gidan dan har Hajiya Laila tana can guest room tana bacci har sannan itama, tun fitowanta Ahmad dake jingine da motan yake kallonta har ta qar

asa ta tsaya nan gabansa, sai taga ya bude mata front seat, bata ja ba ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga, cikin twenty minutes Ahmad yayi parking motan a arean Westminster bridge, kallon gurin Na'iman ta rinqa yi tanajin fresh view din na saka mata

nutsuwa, saida Ahmad ya dauko packet din da ya taho dashi na hot coffee sannan suka fara takawa asannu, tafiyan suke a sannun

cikin shiru, sai can Ahmad yace "This is one of my favorite places in London" Na'ima na kallon yanda boats suke wucewa akan ruwan

tace "It's beautiful" tsayawa sukayi jikin rail na bridge din yace "I always come here when i needed some 'alone time' for myself", coffee yaciro ya miqa mata ta karba amma bata sha ba, tana kallonsa tace "I'm sorry for how i acted yesterday" yana kallonta

shima yace "Babe, me yake damunki?" sai ta juya ta kalli river'n, cikin kwantar da murya Ahmad ya sake cewa "You can tell me" bata kallesan ba cikin sanyin murya tace "I was married before"...jin yayi shiru yasata juyowa ta kallesa sai taga kallon ruwan y

ake kamar me tunani, ta sake cewa "Ba daga nijar nazo ba, ni 'yar asalin qauyen Adamawa ce amma na rayu a Kano" sai sannan taga ya kalleta wanda hakan yasa ta kasa jure kallon idonsa ta sauqe idonta, a nutse yace "Na'eemah look at me" bata dago kan nata ba

sai ya kai yatsansa ya dago habarta ta kallesa idonta na kawowan hawaye, bai bar kallontan ba yace "Were you afraid to tell me this?" ahankali ta gyada kai sai ya kamo hannunta ya damqe cikin nashi, dan stiff Na'ima tayi Jin haduwan hannun nasu kamar an j

ona mata electric wire, yana riqe da hannun nata yace "Even if you had to marry a hundred times, I'd choose you a thousand times Na'eemah" ji tayi zuciyarta na melting da wani irin feelings a lokacin, sai ga hawaye na fitowa daga idonta, ya kai hannu yana

share mata su, yana dan murmushi yace "You're a cry baby Na'eemah, how do you even survived in marriage da wannan kukan naki" murmushi ta fara idonta da hawayen batace komai ba, coffee din suka fara sha suna kallon ruwan sai can yace "Did he hurt you?" da

sauri ta kallesa takasa cewa komai, sai ya kalleta yace "Shi ya yanka miki hannu?" nan ma da sauri ta girgiza kai tace "A'a, yankewa nayi" sai Ahmad ya gyada kai, ganin ya fara mata tambayoyi yasa Na'iman cewa "Ya akayi accent dinka yazama haka?" yayi murm

ushi yana kallonta yace "A Canada na tashi, iyayena sunyi zama acan tun ina yaro" ta gyada kai sai ya sake cewa "Na taba ganinki a Kano" ta ware Ido da dan mamaki tace "Anya ni ka gani, ban taba saninka a baya ba" dan duqawa yayi ya jingina da rail din bri

dge din, yana kallonta yace "I never forget a face, more especially naki, kinje gidan Abba ranan" ta gyada kai tana qoqarin tunowa amma ta kasa, yace "Kinada auren a lokacin?" cikin sanyin jiki ta sake gyada kai, yana kallon cikin idonta yace "Daga wannan

ranan zuwa yanzu shekara daya kenan, da wata takwas da kwana uku Na'eemah, Astaghfirullah, but you've been on my mind since that day".......

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 38

Kallon sa ta rinqa yi tanajin zuciyarta na bugu, sh

ima bai daina kallonta cikin ido ba, sunkai 5 secs a haka kafin ta juya kanta tana dan gyaran murya, murmushi Ahmad yayi yana kallonta ganin irin kunyanta, sai ya juya ya kalli river'n shima yayi sipping coffee din hannunsa still be daina murmushin ba, bec

ause he likes it when he made her uncomfortable, hakan na qara tabbatar masa da yana samun guri cikin zuciyarta kamar yanda yake

bida, Na'ima ji tayi atmosphere din na saka wa zuciyarta wani irin yanayin, sai tace "Ya kamata mu koma kafin su tashi daga bac

ci" Ahmad yace "Zaki barni in shiga gidan tare dake yau?" sai tayi murmushi cikin sanyin murya tace "You'll still bail on me ko na hanaka" murmushi me fadi Ahmad yayi sannan yace "Inason kowa ya ganni tare dake Na'eemah" wani murmushin tayi dan har ga Alla

h duk wasu kalamai da Ahmad din yake fada mata direct suke samun waje cikin zuciyarta, she's new to it, bata taba jin haka akan kowa ba sai akansa shima bai taba jin haka akan kowacce mace ba sai itan...

Da Ahmad ya nemi yakaita nearby cafe suyi breakfast

qi tayi, tace su tafi gida suyi breakfast din acan, babu yanda ya iya haka suka fara wani tafiyan zasu koma gurin motansa, a wani public dustin yayi dumping robber cups din coffee din nasu sannan suka shiga motan sa, cikin shiru suke tafe a motan jefi jef

i suke juyawa su kalli juna, sai da yayi parking a qofar gidan Anty Amnah ya juyo yace "Yaushe ne graduation dinku?" Na'ima ta amsa da "In a month in sha Allah" yace "Ma Sha Allah, i'll be going to Italy for a work this week and in na dawo inason komawa La

gos" ahankali tace "Allah ya taimaka" cikin kwantar da murya ya sake cewa "Babe i hope after graduation din zaku koma Abuja" sai ta gyada kai idonta a qasa, ya dan matso yace "Then i'll transfer all my work back to Abuja kinji" sai sannan ta kallesa itama

a hankali tace "I'll be waiting" da haka ta juya tareda da bude motan fuskanta dauke da murmushi, tanajin duk wani damuwan da ta shiga jiya akan Bilal din yana washewa daga zuciyarta, tare suka jera suka nufi shiga gidan, Na'ima ce farkon shiga falon, agai

n yau ma Lailan ta fara gani tana tahowa cikin falo daga dakinta, Anty Amnah da Abban twins sannan Nafisa suna zaune a dining area having their breakfast, Ahmad da ya shigo bayan Na'iman ko kallon Lailan beyi ba ya nufi su Anty Amnah, itama Na'iman sai ta

bi bayansa dan har ga Allah ita mantawa take da wata Laila ma a gidan, kasa motsawa Lailan tayi daga inda take tsaye sai Anty Amnah ta kalleta tace "Kin fasa cin abincin ne ko me?" Nafisa ta tabe baki sannan ta miqe tafara serving Ahmad dake zaune kusa da

Na'iman yana magana da Abban twins kamar bai san da wata Laila a gurin ba, juyawa Laila tayi ta koma guest room din nasu, cikin bacin rai ta fara bincika akwatin ta, wani kwalba ta dauko me dauke da wani ruwa acikinsa, shafawa tarinqayi a tafin hannunta ha

r jikinta kamar yanda mommy'nta ta umarce ta dayi sannan ta tafi falon, ganin Na'ima a gefen Ahmad din ba qaramin tsaya mata arai hakan yayi ba, sai taja kujeran dake facing din Ahmad ta zauna, itadai Na'ima kanta a qasa tana cin abincin ahankali bata ma s

auraron hiran dasu Ahmad din ke yi sama sama da Abban twins..

Ahmad sai cin abincin sa yake cikin kwanciyar hankali, can ya juya ya kalli Na'iman dake cakulan abincin sama sama, kasa cin abincin Laila tayi tana kallon su ranta na baci, ita dai Nafisa sai

kallonsu take tana danne murmushi, sai da Na'ima takai cup bakinta tana sipping tea din ta hada ido da Nafisan dake kallonta tana murmushi, kwaruwa tayi da tea din ta dan fara tari, da hanzari Ahmad ya zuba ruwa a cup ya miqa mata tareda cewa "Sorry" daga

Anty Amnah har Abban kallonsu suka tsaya yi, gyada kai Na'ima tayi ta karbi cup din sai ya miqa hannu ya ciro tissue dake gurin still ya miqa mata bai ma lura da kallon da mutanen gurin ke masa ba, kadan ya hana Nafisa kwashewa da dariya ganin yanda Laila

ta daskare a zaune tana kallon Ahmad, sai da Na'ima ta gama shan ruwan Anty Amnah tace "Sannu Na'ima" Abba ma yace "Sannu" gyada kai tayi sai ta miqe Ahmad na kallonta zata bar gurin, Anty Amnah ta sake cewa "Har kin qoshi daughter" tace "Uhm Anty"

da hak

a ta nufi hanyar dakinsu, Nafisa da ta kasa shiru ta kalli Laila tace "Ke ma kin qoshi ne" sai ta juya tana wani irin kallo a Nafisan...Bayan sun gama Ahmad ya miqe tareda fada musu zai wuce office shima, yana fita Lailan ta bi bayansa su Anty Amnah suka b

ita da kallo suna ganin ikon Allah, a gurin motansa ta idda sa rai a bace tace "Yaya" ya juyo yana kallonta bai amsa ba sai ta tsaya nan gabansa tace "Jiya naje gidanka nasamu ka chanja gate pin din ka fa" ya dan daga kafada yace "Yes.. meya faru?" ranta a

dan bace tace "Sai abu ya faru ne zanje gidan ka Yaya?" bai amsa ta ba ya tsaya yana kallonta fuskansa a dinke kamar be taba dariya ba, ganin haka sai ta sassauta bacin ran nata ta shagwabe fuska tareda matsowa zata kamo hannunsa, kauda hannun nasa yayi a

nutse yace "Why are you even here? fadamin me kikazo yi a London" tace "Shikenan sai bazan zo gurin 'yan uwana ba, naga har bare ma suna zama a gurinsu" bai ce komai ba ya cigaba da kallonta coldly yana jin ransa ya fara baci kuma, nan tasha jinin jikinta

tace "Hutu fa nazo yi gurin Anty Amnah" sai sannan yace "Pack your things and go back home before i loose my temper with you Laila" kuka ta fara tace "Yaya ga bare ma tana zama a gidan 'yan uwan mu sai nice zakace in tafi, wallahi nikam a'a" juyawa Ahmad y

ayi ya bude front seat na motan zai shiga sai Lailan ta matso zata kama hannunsa yayi baya yace "Kika tabani sai na saba miki, bazan maimaita abunda nace miki ba, in kinga dama ki bari in sake dawowa in sameki" Tananan tsaye ya ja motansa ya bar street din

sai ta juya rai a bace ta koma cikin gidan tana fadin "Babu inda zanje wallahi, saidai sh*giyar nan tabar gidan"

Bayan su Anty Amnah sun gama breakfast din suka shige part dinsu ita da mijin nata yayi shirin fita aiki dan ita sai night, saida Nafisa ta g

ama tattare gurin takai kitchen zata wanke Na'ima ta shigo, basu ce komai ba suka fada cleansing plates din, saida suka koma daki Nafisan ta tambaye ta yanda sukayi da Ahmad din, a sannu ta fada mata yanda sukayi dashi, sai Nafisa takai hannu baki tana blu

shing tace "Ya Allah" Na'ima na murmushi itama batace komai ba, kafin Nafisan tayi magana Laila ta turo kofan tareda shigowa da babban akwatinta, miqewa Nafisa tayi tace "Meya haka ke kuma" Laila tace "Me kuwa..zama zanyi anan ita baren sai ta tafi guest r

oom" da dan mamaki Nafisa ta bude baki tace "Laila anya lafiyan ki, na rantse bazaki zauna a dakin nan ba" cikin bacin rai tace "Toh naga abunda zai hanani wallahi" ta kalli Na'ima tace "Ke wai baki da dangi ne sai nawa" Nafisa bata san lokacin da ta mulmu

lo zagi a Lailan ba ta qara da "Idan ban gaura miki mari ba kin canja min suna" cikin daga murya ta cigaba "ki fita daga dakin nan Laila" Na'ima ta miqe tace "Nafee muje guest room din" cikin bacin rai Laila ta handakata tareda cewa "You don't get to say a

nything tunda ba gidan uw*rki bane nan din" nan Nafisan ta handaka Lailan itama suka fara dambe a dakin Na'ima na rabasu, da sauri Anty Amnah ta shigo dakin tana fadin "subahanallahi bakuda hankali ne" sai da ta musu tsawa suka rabu kowacce na maida numfas

hi Nafisa tace "Kuma wallahi sai kin bar London gaba daya bama gidan nan kadai ba" Laila tace "Ke kin isa, waccan mara galihun ce zata bar qasar wallahi, yar matsiyata kawai" cikin tsawa Anty Amnah tace "Sai naci ub*nku zaku nutsu tukunna?" shiru sukayi Na

'ima tayi tsuru tsuru sanin fadan dan ita akeyi, neman ba'asin fadan Anty tayi, Nafisa tayi saurin fara fadin yanda akayi har da qarawa da "Wai sai tayi sanadin barin Na'ima garin nan bata gama karatu ba" dan kallon ta Na'iman tayi tana mamaki, Laila tace

"Qarya take wallahi" Anty Amnah ta daga mata hannu tace "Duk naji, meyasa ke komai sai kinyi rashin da'a ne Laila, da kika zo nan din wato neman fada kikazo kenan, in hakane to ki hada kayanki anjima zan siya miki ticket ki koma

gida bazaku sakamin ciwon k

ai ba da giramanku, kema Nafisa sai na saba miki wallahi, shashasha kawai, da ta fadi hakan sai bazaki fadamin ba kawai ku hau dambe ke gaki uwar masifa, toh duk ku kama kanku a gidan nan kuna jina" Laila ta juya fuu ta fice daga dakin ko akwatin nata bata

dauka ba, Nafisa tace "Kiyi hakuri Anty" bata ce komai ba ta fita ranta a bace, Na'ima na kallon Nafisa tace "Yaushe tace haka Nafee" da masifa Nafisan tace "Ke bakisan Laila bane, in ba tafiya tayi ba bazata bari mu huta ba" ta qarasa maganan tareda dauk

an kiran Mami da ya shigo wayanta...Aikuwa tun kafin Anty Amnah ta siyawa Lailan ticket ta siya da kanta, jirgin su zai tashi da dare, ko mummynta bata kira ba ta hada sauran kayanta ta fito janye da akwatin ta, duk suna zaune a falon tace da Anty Amnah "N

a tafi" sai jikin Antyn yayi sanyi kuma tace "Daughter fushi kikayi, toh ki koma nawa dakin da kwana tunda bancika kwana cikinsa ba" dauke kai Lailan tayi tace "Flight din anjima ne" ta yi maganan tareda nufan fita, miqewa Anty Amnah tayi ta bi bayan ta, N

afisa ta tabe baki ta juya tana kallon Na'iman da duk jikin ta yayi sanyi itama....

A washegarin ranan driver'n Ahmad ne ya kaisu makaranta suyi submitting dissertation dinsu, tare Na'ima taje ko ina da Nafisa ranan, tana sane Nafisan tayi haka ne gudun

kar ta qara haduwa da Bilal, suna fitowa daga office din supervisor din Nafisan sai taga tayi tsalle tace "Finally, atmosphere din qasar nan ya fara isata" Na'ima tayi murmushi tace "Ki jira mu ga score din mu tukunna" tace "Ai ko na fadi dai na gama scho

ol din nan" Kiran Mami ne ya shigo wayan Na'iman ta dauka, bayan sun gaisa tace "Habibti kunyi submitting din" ta amsa da "Eh" sai Mami tace "Ma Sha Allah, may your graduation mark the beginning of a beautiful new chapter in your life Habibti" har ranta ta

ji addu'an, tana murmushi tace "Amin, thank you Mami" tace "Wane kalan kaya kikeson sawa a graduation ceremony din?, Baby tace fitted kuma nasan fada tayi babu shawararki" dan kallon Nafisan tayi taga tana mata dariya, tace "ko wanne ma" Mami tace "No ki k

ira Meerah kuyi magana, zata turomin bill din" amsawa tayi sukayi sallama, sai da suka dauko motan su daga gurin ajiya sannan suka dauki hanyar komawa har sannan ba wanda yayi maganan zuwa apartment din nasu....

Laila ce zaune a falon gidansu, fuskan na

n tayi jajir tana hawaye, Mummy dake gefenta ma rai a bace tace "Ita yarinyar me ya kaita gidan Amnah'n" Laila tace "Tare suke zama da Nafisa a gidan, Mummy har fita fa takeyi tareda Yaya Ahmad din" sai Mummy tace "Baki goga abunda na bakin bane?" tana sha

re hawaye tace "Baya kulani fa Mummy, cewa yayi in bar gidan Anty Amnahn ma" cikin masifa Mummy tace "A matsayin gidan ub*nsa kenan, duk dani suke zancen, sha kurumin ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login