Showing 12001 words to 15000 words out of 121625 words

Chapter 5 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

18

Na'ima ta lura da wata baquwar mota, wata sleek ride dake fak

e nan parking space din, atare suka fito Nafisa ma da ta lura da motan tace "Su Yaya Ahmad sun zo kenan" Na'ima na kallon motan ta rufe cab din gefenta suka wuce cikin gidan hannun Nafisa riqe da ledan kayan da suka siyo.

Shigarsu falon sai Na'ima ta hang

o Mami zaune da wasu maza biyu zaune kan kujera sunyi backing dinsu, dayan yana having conversation da Mami while dayan yana riqe da waya a hannunsa yana kallonsu Mamin, qarasawa sukayi cikin falon Nafisa na gaba, mai maganan ya dan dago ya kallesu yace "N

afisa" ta amsa da "Yah Adam sannunku da zuwa" yace "Yauwa" Mami tace "Baby kundawo" Nafisa tace "Eh Mami" suka qarasa Nafisa ta ajiye kayan hannunta a gaban Mami sannan suka zauna kan kujera kan Na'ima na qasa, Nafisa ta sake cewa "Yaya sannunku da zuwa, I

na wuninku" Ahmad ya dago kansa, a nutse yace "Lafiya Nafisa" husky voice dinsa na shiga kunnen Na'ima, sai shima Adam ya amsa gaisuwan, cikin sanyin murya Na'ima tace "Ina wuni" tadai ji Adam ya amsa amma mai deep voice din da ake kira da Ahmad dinne bata

ji ya amsa ba, sai tadan dago kanta ta kalleshi, Caraf idanunta suka shiga cikin nasa yana nazarinta.

Kauda idonta tayi da sauri ta maida kallonta kan Tv dake falon tana jin bugun zuciyarta acikin kunnenta, Tunda take bata taba ganin idanun da suka mata k

aifi ta kasa jure kallonsu kaman na bawan Allahn nan ba. Shima Ahmad dauke idonsa yayi ya cigaba da danna wayarsa, Mami tace "Ka dai ce bazaka dawo gida ba Ahmad, ka riqe Lagos dinnan har dawowa yana maka wahala" Ahmad ya juya ya kalli Mami a nutse yace "A

kwai wasu abubuwan danake son nayi settling ne acan mami" sai Mami tace "Ai zamanka dai anan din yafi, tunda can din bawai iyali ka ajiye ba" ta cigaba da maganan tareda juya wa tana kallon Adam tace "Kaima Adam baka fada masa gaskiya ko" sai Adam yayi dar

iya yace "Nima gajiya nayi da fada masa gaskiya, may be yanzu zeji taku Mami" Mami ta maida hankalinta kan Ahmad din tace "Ai

Mamma tace min kunyi maganan kuma har yanzu baka dawo ba" Ahmad yadan shafa kanshi yace "In Sha Allah za'ayi yanda kuka ce din Mam

i"

Itadai Na'ima duk ta taqure acikin falon kaman ace cass ta arce, Adam ya juyo yana kallonsu yace "Nafeen Mami yaushe kika dawo?" Nafisa da tunda ta gaishesu ta maida hankalinta kan waya ta dago kanta tana murmushi tace "For a week now Yaya" yace "Ma S

ha Allah, kin kusa gamawa amma" ta gyada kai tace "Eh saura 4 to 5 months haka" yace "Allah ya bada sa'a" yana kallon Na'ima da tun dazu idonta ke kan Tv bata juyo ba yace "Mami baquwa kukayi ne" ta amsa da "Eh 'yar dan'uwana ce dake can Nijar, tare suke k

aratun da Nafisan ma" Adam yace "Allah sarki" sai Mami tace "Zo ku miqamin kayan nan sama in na shigo zan waresu" Na'ima ce farkon miqewa kamar wanda falon ke mintsinta, sai Ahmad yadan dago ya sake kallonta ta qarasa ta karbi kayan, Nafisa ta miqe itama t

ace "To yaya sai anjimanku" suka amsa da Toh, tabi bayan Na'ima da har ta isa stairs, suna shiga falon Mamin Nafisa tace "Ke yanzu naga texts din mutumin bari kiga" Na'ima da taji duk kafafunta a sanyaye ta nemi kujera ta zauna anan falon tana tuna idanun

wannan bawan Allah data baro a falo, Nafisa ta qaraso kusa da ita tana nuna mata wayan tace "Kiji wai yanzu ma yana hanya zaizo" cikin sanyin murya Na'ima tace "Kibarshi yazo sis, you have to settle fadan nan naku once and for all" sai Nafisa tace "Allah k

o?" Na'ima ta gyada kai, shiru Nafisan tayi kamar me nazarin wani abu sannan ta miqe ta tafi dakinta, diban kayan Na'ima tayi ta dorasu kan table din dake nan falon sannan ta fice tana ture duk wani tunani daga ranta.

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa





Chapter 10

Daren ranan after maghrib suna zaune falon Mami itada Nafisa, ipad ne a hannunta tana game don tunda suka dawo gidan bata bude wayanta dake ajiye cikin box dinta ba, Hira sukeyi jefi jefi da Mami dake zaune itama tana kallon hiran da akeyi

cikin Tv a tashar BBC, Mami tace da nafisa "Baby kina jira sai nace kije ku gaisa da iyalan uncles dinki ko?" Nafisa ta dago kanta daga danna wayan da take yi kwance a kujera tace "Mami I thought tunda za'ayi bikin nan basai naje bafa" Mami na kallonta tac

e "Ke tunaninki bazai baki kije ku gaisa kafin ku hadu a gurin bikin ba ko, for a week now na zuba miki Ido ai" sai Nafisa tayi shiru batace komai ba Mami ta cigaba "Gobe ki shirya kuje tareda Na'ima ku gaishe su and that's final" ta amsa da "Yes Mami"

S

ai Mami ta maida hankalinta kan Na'ima da ta ajiye ipad din nata jin Mamin na magana, tace "Habibti, gobe kuje gidansu Baba ku gaishesu" cikin sanyi Na'ima ta amsa da "toh Mami in Sha Allah" bayan sunyi sallahn ishansu nan falon tareda Mami suka sauqa down

stairs suka bar Mamin a side dinta.

Zama sukayi anan falon Nafisa na turo baki ita a dole abunda Mami ta sa suyi bai mata dadi ba, Na'ima ta kasa shiru tana murmushi dan yanayin Nafisan dariya ma ya bata tace "Nafee it's just ziyara fa, what's the harm in

that? Beside, ba kince yayun Abba bane su din" Nafisa ta bata rai tace "Eh..amma Mami ce take taqurawa sai munje alhalin su ba wani zuwa gidan nan suke ba,

tunda muka dawo kinga yaran gidan sunzo gaisheta ne?.." Na'ima batace komai ba, Nafisa ta cigaba

"Har gwara ma su yaya Adam da Anty Fatima sai

dan dama dama Husna, Amma 'ya'yan Anty da Mummy fa ba wanda yake zuwa gaishe da Mami" Na'ima da bawai saninsu tayi ba, tana dai jin labarin su wani lokaci a bakin Nafisan, sai ta dan gyara zama tace "Yaran Anty

sune twins da Salman da za'ayi bikin nata ko?"

Ganin Na'ima ba wani saninsu tayi ba yasa Nafisan cewa "Kinga yaya Ahmad, wanda sukazo rannan to shine babba a gidan Baba, forget it bari na miki dalla dalla, su Abba su hudu iyayensu suka haifa that is Bab

ba sai Abba sannan Daddy and last dinsu Anty Amnah, to gidan baba yana da mata biyu da Mamma sannan Anty, yaran Mamma sune yaya Ahmad, Anty Fatima, Husna sannan Ummi sai kuma yaran Anty wanda Salma itace fari sannan twins Safiyya da Sumayya" Na'ima ta gyad

a kai alamun fahimta at the same time idanun Ahmad neh suka fado mata arai ta dan yi stiff tana tuna yanda yake kallonta dazu.

Nafisa ta cigaba "Sai gidan Daddy kuma, kinga yaya Adam shine babba wanda shi mahaifiyarsa ta rasu so practically he was raised

by Mamma tareda yaya Ahmad, Mummy ce matar Daddyn ita kadai, ita kuma yaranta akwai Anty Murja, Anty Ummi sannan Laila ce autarsu, to anty Amnah kam kin santa ai" Na'ima ta gyada kai tace "Nagane" Nafisa tace "Mami itadai kayi ta zuwa gaishesu kamar wa'end

a akayiwa mutuwa" sai Na'ima tayi murmushi tace "To ai 'Yan'uwan ku ne Nafisa, ya zama dole" Nafisa tace "Ni ba gidan Baba bane banason zuwa, gidan Daddy ne, Mummyn ce ba sauqi a lamarinta" yar dariya Na'ima tayi tace "Kijiki sai kace wata sa'arki" Dariya

itama Nafisan tayi tace "Bazaki gane bane".

Abba ne ya shigo tareda samarin gidan dawowansu daga masallaci kenan su Na'ima suka gaishesu, nan kowa ya nufi dinning dan yin dinner Mami ta sauqo itama, Na'ima ce tayi serving dinsu, dan tun farkon zuwanta gid

an Mami kan sata itama tayi serving a table din so that she could feel at home, hakan yazame musu al'ada ko ita ko Nafisa sune servers in an zauna cin abinci, Abubakar ne ya  bubbude flask din ganin babu tuwo yace "Anty yau ba'ayi mutuminki tuwo ba" Na'ima

data koma ta zauna tayi murmushi tace "Abu tsokala ko" Abba yana fara'a yace "Tuwo abunso ne ai Abu" Abubakar yace "Inaaa, Abba munfi gane yaren shinkafah" akayi dariya gaba daya.

Bayan sun gama cin abinci aka koma main falon ana hira, su Na'ima suka ta

ttare kwanikan suka wankesu a kitchen sannan suka koma falon aka cigaba da hiran dasu, Al'adan gidan ne yawanci dare ana zama ayi hira in ba dai ranan da Abba ya gaji ba ko kuma yana da wani muhimmin uzuri ba, Morning ne dai ba'a cika haduwa ba dan kowa ya

na da lokacin tashinsa, so breakfast ma kowa da lokacin yin nasa.

Washegari...

Na'ima ta fito daga wanka ta zauna kan stool nan gaban madubi, cire hulan wankan nata tayi tafara taje gashinta da ya kasance mai santsi da laushi, har wani curls yakeyi gas

hin nata tsabar laushinsa. Taje gashin take while tana kallon kanta cikin madubin, idonta ne yakai kan bakin wani tabo a gefen kafadanta gashinta ya dan rufeshi, ta qurawa gurin ido acikin mirror takai hannu tana tattare gashinta daya sauqa kafadunta har z

uwa bayanta, wani babban tabo ne ya bayyana sosai a gurin mai kama da yanka anyi dinki, takai hannu ta shafa kanshi tana tuna dalilin jin ciwon, komai yana dawo mata cikin brain dinta kamar yanzu glass din da aka jefon ya yanketa a wajen, idanunta ne suka

ciko da hawaye takai hannu ta sharesu still wasu ma suka sake gangarowa.

Tana cikin share idanunta Mami ta shigo dakin, sai tayi saurin kauda kanta gefe tana goge idanun nata, qarasowa Mami tayi ta dafata, ahankali

tace "Na'ima" juyowa Na'iman tayi ta cig

aba da share hawayenta , Mami tayi shiru tana kallonta sai kuma ta kama hannunta ta jata suka zauna bakin gado, cikin kwantar da murya Mami tace "Na'ima fadamin meke damunki?" Muryan ta na dan rawa tace "Babu komai Mami" shiru Mamin tayi tana kallonta sai

kuma ta sake cewa "Kinason komawa wajensu ne?"  da sauri Na'ima ta jijjaga kai tace "A'a Mami" sai kuma ga wasu hawayen, Mami ta  dan rungumota tana shafa dogon gashinta tace "It's okay dear, it's alright..... everything is going to be fine kinji" tana ji

kin Mamin ta gyada kanta, Mami tacigaba "I won't let things be repeated again in sha Allah, we will do anything to protect you, ki kwantar da hankalinki kiyi karatun ki kinji, this is your home too..talk to me duk lokacin da kike buqatan someone to talk to

" Na'ima ta dago daga jikin Mami tana gyada kanta sai Mami tace "Now wipe those tears, you had so much ahead to live for in sha Allah, stop wasting your tears kinji" Na'ima ta sake gyada kanta tace "Toh Mami" sai Mami tace "In bakyason fitan ma kiyi zamank

i ki huta" tayi murmushi tace "A'a Mami zanje"

Mami ta shafa kanta tace "Toh tashi ki shirya" miqewa tayi ta nufi wardrobe dinta Mamin ta bita da kallo zuciyanta na karyewa ta miqe ta fita daga dakin.

Na'ima na cikin saka kayanta Nafisa ta shigo cikin s

hirinta tace "Har yanzu wai baki shirya ba?" Na'ima ta kalleta tace "Gashi fa inayi"  sai Nafee ta zauna kan gadon tana kunna wayanta, bayan Na'ima ta gama saka kayan ta fara neman veil din da zata yafa jikin light blue doguwar rigan jikinta na atamfa daya

sha beadwork, ta bincika bata samu wanda ya dace ba acikin jerin veils dinta na cikin wardrobe din sai kawai ta jawo babban box dinta da ta dawo dashi daga England tafara bincikawa aciki, idon nafisa ne yakai kan wayar Na'iman dake cikin kayan, ta miqa ha

nnu ta dauka tace "Bobo ni lafiyanki kuwa da baza kiyi amfani da wayarki ba" Na'ima dake abun gabanta tace "Nafee to wa zan kira?" Shiru Nafisan tayi sai kuma tace "To ai ba kira kadai akeyi da waya ba akwai abubuwa da dama" Na'ima na rufe box din tace "Du

k ina yinsu da Ipad plus laptop dina ai" bayan ta mayar da box din ma'ajiyansa ta qaraso ta karbi wayar nata dake hannun Nafisan ta jawo bedside drawer ta jefa Nafisa na bin ta da kallo.

Sun fito zasu tafi Nafisa ta jefawa Na'iman key tace "Kiyi driving d

inmu yau kema" sai Na'ima tayi dariya tace "kinfa sani hannuna bai gama fadawa ba" Nafisa ta bude side din mai zaman banza sannan tace "Ai sai kinayin a hankali zaki qware din"  da haka Na'ima ta bude driver seat ta shige itama, haka tayi driving din Nafis

a na qara nuna mata yanda zatayi, kuma balaifi ta iya din.

Isarsu gidan Baba bayan maigadin ya bude musu gate din babban mansion din Na'ima tayi parking, ta fito tana dan bin gidan da kallo ganin yafi nasu Mami girma, shigansu babban falon gidan suka sa

mu babu kowa sai mai aiki dake faman goge goge suka gaisa da ita sai Nafisa ta tambayeta ko su Mamma na nan, ta amsa da Eh tana sashinta.

A falonta suka samu Mamman, Na'ima ta dan tsurawa kamilan Matar Ido ganin kamarta daya da Ahmad, bayan sun gaisheta t

a amsa da "Lafiya nafisa, yakuka baro Mamin ?" Nafisa ta amsa da "Lafiya, tace agaisheki" Mamma ta amsa tana kallon Na'ima tace "Yarinyar wajen Mamin naku ce wannan ko"  Nafisa tace "Eh Mamma itace, sunanta Na'ima" sai Mamma tace "Ma sha Allah sannu Na'ima

,ya zaman qasar tamu, ba kamar nijar ba ko?" Na'ima ta dan sunkuyar da kanta tana jin yanayin ta wani iri aduk lokacin da aka dangantata da Nijar, gurin da bata ma taba sanin inda yake ba balle taje,

murmushi tayi tace "Alhamdulillah" bayan Mamma tasa an k

awo musu drinks da snacks suka dan taba hira game da karatunsu sannan suka miqe Nafisa tace "Mamma zamu je gurin Anty" tace "Toh Nafisa" sai Nafisan ta sake cewa "Husna tananan kuwa?" tace "Bansani ba ku duba dakinta , dan dazu tace min zata je gidansu cou

rse mate dinta" Nafisa ta amsa da Toh sannan tayi gaba Na'ima na biye da ita suka fice daga falon Mamma. Bayan sun fito daga part din Anty wacce suka gaisa da ita sama sama dan mace ce wadda nukurci ya cinye mata zuciya bata cika fara'a ba, batasan Na'ima

ba kuma bata damu da tambaya ba har suka fice, dakin Husna suka shiga suka sameta kwance kan babban gadonta, tana ganinsu ta miqe ta danyi ihun murna sannan ta riqo hannun Nafisa.

Nafisa ta fusge hannunta tace "Dalla sakeni bayan kinsan nadawo amma ko kiz

o"

Husna tace "Bobo Dan Allah kiyi hakuri school ne ta riqeni amma kina raina wallahi" Na'ima ta dan kalli Husna jin kalman "Bobo" a bakinta, dama Nafisa ta fada mata sunan dasuke kiran juna ne itada Husna.

sai Nafisa ta kyabe baki tace "Bawani nan" dar

iya Husna tayi ta juya tana kallon Na'ima tace "Sannunki da zuwa" Na'ima tace "Yauwa sannu" ta qarasa zata zauna kan resting sofa da ta gani a dakin Husna ta riqo ta tace "Mu qarasa gadon yafi dadin zama" sai Na'ima ta girgiza kai zata zauna Husna ta riqe

hannunta ta jata kan gadon da Nafisa ta hakimce akai ta miqe kafafu harda cire gyale. Bayan sun gaisa Husna ta kawo musu yogurt me sanyi babu cups haka ta miqawa kowannensu a hannu ta hau gadon itama riqe da guda daya, tana kallon Na'ima ganin itadai bata

santa ba ta juya tadan taba Nafisa tana mata sign da Ido alamun "Wacece wannan?" a fili Nafisa tace "Na'ima ce fa wadda na baki labarin muna tare a Oxford" Husna tace "Ohhh cousin dinki dinnan?" sai Na'ima ta hada Ido da Nafisa, waskewa Nafisan tayi tace "

Eh ita" Husa tace "Ma Sha Allah, she's so beautiful" ta juya ya kalli Na'ima ta sake cewa "Sis, you're so beautiful" Na'ima ta sauke idanunta tana dan murmushin kunya batace komai ba, sai Nafisa ta dan daki kafadan Husna tace "Dalla kina sa ta kunya" Husna

tayi dariya tace "Aiiii...sorry" .

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa





Chapter 11

Suna cikin hira Husna ta tambayi Nafisa "Sis meya faru jiya na kiraki zan miki gulma naji wayanki a kashe?" Nafisa tace "Na kashe ne dan nasan Umar zai kirani" sa

i Husna ta jijjaga kai tace "Kai..keda guy dinnan dai bansan yanda zanyi defining kalan taku matsalar ba wallahi" Na'ima batasan lokacin da tafara yar dariya ba suka juya suna kallonta Husna na dariya tace "Allah kuwa, yanda kikasan numfashinsu ne ajikin n

a juna, su basu rabu ba, kuma matsalar taqi qarewa" Na'ima ta girgiza kai tace "Karma ace sai sun rabun, dan banason su rabu but it's high time su fahimci a ina matsalarsu take" Nafisa tace "Bazaku gane bane" Husna tace "Toh fahimtar damu yanda zamu gane d

in, guy dinnan kunason juna amma kullum matsalar yau daban ta gobe daban, Bobo get a break please" Nafisa bata amsa ba ta cigaba da shan yogurt dinta, Salma ce ta shigo dakin Na'ima ta dan kalleta ganin bazata wuce mate dinsu ba, ta qaraso bakin

gadon ta t

saya tace "Sannunku" suka amsa Nafisa na cewa "Amarsu kinsha qamshi" Salma tayi yar dariya sannan ta cewa Husna "Dazu Yaya Adam ya shigo yana neman ki bakyanan" Husna tace "Eh munyi waya dashi ai" sai Salma ta juya tana kallon Na'ima tace "Wannan fa, daga

Ina?" tsuka mai karfi Husna tayi tace "Kefa matsalata dake kenan, meye hakan kuma?" Nafisa ma ta juyo tana hararan Salma, sai Salma tace "Ha'a daga tambaya" cikin fusata Husna tace "Dalla to haka ake tambayan? Ji rainin wayo wai 'daga ina' " ta qarasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login