Showing 3001 words to 6000 words out of 121625 words
a BUK suke tare, yanzu haka yana aiki a central bank. Ganin Na'ima na dariya yasa Nafisa cewa "kinsan Allah, this time around idan nayi bl
ocking dinshi bazan bude ba mun rabu kenan" sai Na'ima ta dan bude ido tace "toh fah, abun har yakai haka?" ta amsa da "I'm serious this time"
Na'ima tace "toh yanzu dai bari mujira idan kikayi blocking dinshi dagasken sai mu cigaba da wannan maganar" kaw
ai Nafisa ta ajiye alayyahun hannunta data tara ta dauki roban gabanta dayake kan kitchen island din zata buga mata tana dariya, baya Na'ima tayi tana dariyan itama tace "gaskiya ne ai, maganar blocking dinnan har nagaji da jinta kuma anjima zan jiku kuna
waya kina kashe murya" Nafisa tace "zan baki mamaki kuwa, zaki gani" Na'ima ta dawo wajen girkin nata tana fadin "aikuwa zansha mamaki randa hakan ya faru" dan har ta gaji da bawa nafisan hakuri karta rabu da guy din.
A haka suka gama girkin suna hira cik
in walwala, bayan sunci sunyi sallahn la'asar kowacce ta tafi nata dakin yin wanka suka shirya suka fita yawon yamma, Walking through the street of the town zasuje Cafe , suna tafe suna hira sai Nafisa ta tsaida su a gefe tayi wa Na'iman hoto tana murmushi
, ta sake dauka musu tare sannan ta bawa Na'ima wayan ta dauka mata ita kadai, sai da rana ta fadi suka koma gida hannunsu riqe da ledan snacks din da nafisa ta sa suka siya a wani supermarket kamar ba jiya suka yo siyayya ba.
Bayan sun koma gida sukayi s
allah suka zube nan falon, Na'ima ta dauko laptop dinta ta cigaba da essay dinta while nafisa kuma tanata danna wayanta, sai da ta zabi hotunan da sukayi tare da wanda tayi wa na'ima ita kadai ta turawa Mami sannan ta zabi wanda ta dauka ita kadai banda Na
'ima tayi posting a Instagram handle dinta sannan ta tashi ta dauko nata laptop din don duba school work dinta itama.
Washegaria Monday zasu je school, Na'ima da wuri ta tashi zata hada musu breakfast dan tafi ganewa tayi musu if not nafisa toast da te
a kawai zata musu
Tana kitchen din tana kada kwai bayan ta gama chips Nafisan ta shigo hannunta riqe da ipad sai lumshe Ido take alamun bacci bai isheta ba ta
miqawa Na'ima ipad din, karba tayi taga fuskan Mami akan wayan tana mata murmushi tace "Habibti
ina kika baro wayanki inata kira"
Na'ima na murmushi ta amsa "yana daki ne, ina kwana Mami" tace "lafiya lau Na'ima,kun tashi lafiya" kafin ta amsa Abubakar dan autan Mamin ya sako kanshi ta bayanta yana gaisheta, ta amsa tana murmushi tace "Abu yau bakaj
e school bane" yace "jiya muka gama Waec Anty" sai Nafisa ta matso ta leqo kanta tace "Kai dalla ka bawa Mami wayan su gaisa" Gwalo Abubakar ya mata , Na'ima tayi dariya sanin draman da suke kwasa a tsakaninsu tace "rabu da ita,saura Neco yanzu ko" yace "E
h" tace "Allah ya baku sa'a" ya amsa da Amin yana matsawa fuskan Mami ya shigo tace "daughter ba wani matsala ko?" Na'ima tace " A'a babu komai"
"Ma Sha Allah,ku rinqa karatu fa kunji" ta amsa da "toh Mami in Sha Allah" Mami tace "Allah ya taimaka yayi al
barka" bayan ta amsa sukayi sallama ta miqawa nafisa itama sukayi sallaman.
Bayan Na'ima ta gama hada musu breakfast sunaci anan kitchen din dayake akwai kujerun zama jikin kitchen island din nafisa tace "yau zamuje wajen taron movie premiere a London"
Na'ima bata dago kai ba tace "Really?..wane movie ne" tace "British movie ne, Lauren ta siya mana tickets ashe tun last week" hankalin Na'ima na kan plate din abincinta tace "then me zakujeyi awajen toh?" nafisa tace "ita zataje for her content nima dai so
rt of that, kizo muje it'll be fun" sai Na'ima ta juya ta kalleta tana dan ware ido tace "Waaa?..school zan tafi yanzu ma ina gama cin abincin nan" Nafisa tace "muma fa sai mun gama morning lecture tukunna, it'll be fun I'm telling you" Na'ima ta girgiza k
anta tace "Bazan je ba"
Tuesday..
Tsaye Na'ima take a balcony na apartment din nasu dake 4th floor cikin 10-story building. Bayan tadawo daga school kadaici ya dameta a gidan ta fito nan don tasha iska, tana tsaye daga inda take tana hango wucewan muta
ne da dama a street din nasu, Most at times batason zaman shiru sosai in Nafisa batanan, takan nemi wani abu da zeyi keeping dinta busy to abstain herself from thinking.
Tananan tsaye ta hango wasu couple suna tafiya suna dariya, sai ta bisu da kallo har
suka wuce, ta dago hannunta tana kallon wani tabo dake tafin hannunta, qurawa tabon ido tayi tanajin zuciyarta na karyewa abubuwa da dama suna dawo mata cikin kanta , digar hawayenta akan tafin hannunta ne yasa tayi saurin goge idonta tabar balconyn takoma
cikin falo, kitchen dinsu ta nufa ta dauko mopper nan ta fara tattare gidan tana goge kowane lungu da saqo.
Ranar har bandakin nafisa saida ta wanke, ta sake rearranging din wardrobe dinta dana nafisan ta koma kitchen ta dafa musu rice and stew tareda ho
memade juice, kuma duka ayyukan nan din tayi ne don kawai tasamu something to keep her mind off, something that will abstain her from thinking too much.
Ranar juma'a suna zaune a falo da safe su biyunsu suna hira jefi jefi sun saka skin face mask, Na'im
a tana karatu a ipad dinta aka kira Nafisa, tashi zaune Nafisan tayi daga kwanciyar da tayi kan kujeran a fili tace "Yah faruk" sai Na'ima ta bar abunda take ta juyo, amsa kiran Nafisa tayi suka gaisa sai kuma ta miqe da sauri ta leqa balcony, ihun da tayi
ne yasa Na'ima ajiye ipad din hannunta da sauri ta bita balconyn itama tana duban street din, Yah Faruk ta hango sanye da qananan kaya ya jingina a
jikin mota a gefen street din maqale da waya a kunne yana dago musu hannu, ware idanu Na'ima tayi ta rufe b
akinta da hannu saboda mamaki, buga kafa Nafisa tafara yi tana ihun murna batareda damuwan mutane na dago kai suna kallonsu ba, Yana dariya ya matsar da wayan daga kunnenshi jin tana ihu, da gudu Nafisan ta koma falo tayi hanyan fita kayan da bacci a jikin
ta me dogon hannu da dogon wando ta fice da sauri.
sai Na'ima ta dawo falon ta tsaya tana murmushi don har ga Allah itama tayi murnan zuwansa don Yah faruk mutuminsu ne kuma yayansu....An investment banker sannan first born a gidansu nafisa, shine wanda n
afisa take bi, daga ita sai Al'ameen da yake makaranta a Toronto Canada sannan last born dinsu Abubakar. 'Ya'ya hudu yan gata wajen Mami da Abba sai Na'ima da suka hada ta zama cikon ta biyar acikinsu.
Tananan tsaye a falon taji beep din door pin alamun s
una kokarin shigowa, da sauri ta juya ta koma daki don dauko hijab itama kayan baccin ne jikinta dan tunda sukayi sallahn asuba suka koma bacci nan falon, tashinsu ne bayan sunyi brush sunyi breakfast Nafisa ta tsiro musu da saka face mask kafin suyi wanka
.
Bayan ta sako hijab din tacire face mask din ta dawo falon, samunsu tayi suna zaune nafisa sai zuba take kamar gyada, ta qaraso ta zauna kanta a qasa ta fara gaisheshi tana murmushi, amsawa yayi shima yana murmushin sai kallonta yake ganin duk ta chanja
from the broken girl he once knew, cikin tsokana yace "Habibtin Mami" miqewa tayi tana sunne kai cikin kunya ta wuce kitchen don kawo masa abun sha
Nafisa tace "Ya faruk I thought direct flight to Abuja ko Lagos zaka bi daga can Paris din fah" ya juyo y
ana kallonta yace "What's that on your face?" sai lokacin Nafisa ta tuna da abunda ke fuskanta ta fara dariya tana cirewa.
Na'ima bata jima ba ta dawo falon riqe da plate with snacks, drinks and bottle water ta jawo table zuwa gabansa ta dora akai sannan
ta zauna suka qara gaisawa yana tambayansu karatunsu.
Hira sukasha sosai nan falon cikin raha, a dan zaman da tayi can gidansu nafisan ta fahimci Yah faruk mutum ne mai kirki da son 'yanuwan sa sosai, ga kyauta da fara'a, shekara shida ya basu itada naf
isan ayanzu da suke cikin shekarunsu na ashirin da hudu.
Ganin hiran taqi qarewa especially yanda nafisa take ta zuba yace "toh yanzu dai ku shirya zan koma London tare daku, Anty Amnah tace in taho mata daku" nafisa tace "dama fa gobe muke shirin zuwa" y
ace "Naah..ku shirya mutafi yanzu dan nima goben nakeson wucewa gida" Nafisa ta turo baki "Haba Yaya, kabari sai sunday mana" yace "A'a ai nazo naga lafiyarku" ya juya yana kallon Na'ima yace "ko habibtin Mami" tayi yar dariya tana kauda idonta tace "kayi
kokari Yaya mungode sosai" yace "yauwa...ku tashi ku shirya karku dau lokaci please" da haka suka miqe kowacce tayi nata dakin suka barshi nan falon ya miqe yafara kashe kayan wuta na gidan.
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 04
Basu wani dau
lokaci ba suka Isa London, suka dau hanyar gidan Anty Amnah dake arean Kensington.
Anty Amnah ta kasance likita ce kuma tana auren babban likita mazaunin London da yaransu twins maza 'yan kimanin shekaru bakwai. Sunyi murnan ganinsu sosai, twins sai tsa
llen murna suke suna maqalqalesu Na'ima na dariyansu, bayan sun huta Anty Amnah tayi serving dinsu abincin da ta girka musu sunaci ana hira har suka gama.
Daren ranan suna bisa kan gado cikin dakinsu wanda suke sauka idan sunzo gidan, Na'ima na zaune ta
miqe kafanta hannunta riqe da ipad dinta twins suna kwance jikinta suna game tare while Nafisa kuma na kwance gefensu tana chat a wayanta, Kiran Abba ne yashigo wayan Na'ima ta dauka da sallama tana gaisheshi, amsawa Abba yayi ta dayan bangaren tareda tam
bayanta ya karatu, tace "Alhamdulillah Abba" yace "Hope babu wani matsala" ta amsa da "Eh" yace "Ma Sha Allah, ku dage da karatu Na'ima, banason wasa" tace "in Sha Allah, nagode Abba" da haka yace "Ina Nafisan?" ta amsa da "Gatanan" tareda miqawa Nafisa
wayan, bayan sun gama gaisawa da Abban taji Nafisan na tambayan ina Mami,
Suna cikin maganan dinki da Mamin sai Nafisa ta sake miqo mata wayan bayan ta saka a handsfree, bayan sun gaisa Mami tace "Na'ima ga kayanku nan ansiyo wanda zaku saka a bikin, ina
son aika muku wajen me dinkin Nafisan amma bansan wani kalan dinki kike so ba kuma" cikin sanyin murya Na'ima tace "kowanne kalla yayi" Mami tace "A'a badai kowanne kala ba, saka wayan a handsfree" Nafisa dake gefe tace "a handsfree yake fa Mami" sai Mamin
tace "Yauwa kinaji Nafisa, ta fada miki kalan wanda takeso din sai ki turawa Meerahn, nidai zan aika kayan gobe sai ku gama maganan a tsakaninku" Nafisa tace "toh Mami zanyi magana da ita a WhatsApp" da haka sukayi sallama Nafisa na kallonta tace "Meerah
never disappoint, zansa ta turomin latest one's sai mu zaba"
Na'ima bata amsa mata ba ta karbi wayan nata ta miqawa jabeer dake kusa da ita ya cigaba da game dinda sukeyi.
Suna nan zaune anty Amnah ta shigo dakin tace "sun hanaku bacci ko" Na'ima tayi m
urmushi tace "A'a game ai mukeyi" Nafisa tace "Anty, Ya faruk bai dawo ba?" tace "A'a" don tunda yakawo su nafisa aka taba hira dashi ya sake ficewa akan akwai gurin da zaije daga nan ya wuce masauqinsa kuma.
Anty Amnah na tsaye tayi clapping hannunta kad
an tace "Boys, it's time for bed" jabeer yafara kukan shagwaba akan shifa a wajensu na'ima sai kwana, hararansa tayi tace "My friend get down from that bed" Na'ima tace "Anty kibarsu mu kwana anan din" tace "A'a zasu takuraku, oya muje" Haka ta tusa kansu
suka bar dakin tana musu saida safe.
Washegari suna breakfast gaba dayansu, Nafisa ta saka Faruk a gaba da roqon sai yayi rescheduling flight dinsa Anty Amnah ma na tayata , mijinta da yake gurin yace "What if he has something to do back home?" Anty Amn
ah tace " babu ma...beside, it's weekend. work can wait till Monday, right son?" faruk ya danyi dariya yace "Zan duba available flight for Monday then" Nafisa tayi saurin cewa "zaka samu in Sha Allah" mijin Anty dasuke kira Uncle Yasir yayi murmushi yace "
Su nafisa qorafi ya fara karbuwa" dariya tayi tace "zai samu Uncle"
Itadai Na'ima tayi shiru tanacin abincin dake gabanta sannan tana sauraronsu, Faruk ya amsawa Nafisa da "I'm not sure yet" sai ya dauki wayanshi dake kan table din zai duba.
Nafisa ta
juya ta kalli Na'ima tareda kai mata qaramin bugu a kafada tace "kinaji inata faman roqo ko ki tayani" Na'ima tayi murmurshi batace komai ba tacigaba da shafawa jafar nutella a jikin bread, sai Faruk ya dago
kansa yace "Habibtin Mami ko in tafi?" dariya ta
yi kadan tace "A'a Yah Faruk" Anty Amnah tace "Itama batason ka tafin ai, kawai nafisa tafita baki ne"
Faruk ya gama rescheduling flight din ya ajiye wayan yace "There... it's done, saiku shirya anjima mu tafi park" Nafisa ta ajiye tea din hannunta tayi
masa thumb up tace "You're the best" twins ma sai sannan suka fara ihun murna jin an ambato zuwa park.
Zuwa 11 o'clock suka tattara aka tafi park Anty Amnah ta hada musu lunches dinsu suka saka a booth dan ita da Abban twins sunce baza suje ba zasu huta
a gida kasancewan weekend ne.
Wunin ranan a park sukayi, acan sukayi sallolinsu suka ci abinci, Faruk yasasu sun hau different wheels yana musu video sannan sunyi games kala kala shima har Nafisa ta ciyo kyautan teddies ma twins, sunci banza sunci wofi d
ai sannan suka koma gida da yamma duk a gajiye.
Washegari wayewar sunday yakamata su na'ima su koma Oxford don school, amma tunda suka tashi Nafisa take mitan itafa ta gaji, bayan sun idar da sallah ta cigaba da mitan, Na'ima na jinta batace komai ba ta
miqe tana linke sallaya.
Ganin Na'ima bata kulata ba sai tace "Sis ko mubari sai gobe mu koma?" Na'ima tayi murmushi tace "Allah ya kaimu toh" dan tasan qarshenta hakan ce zata faru daman, Nafisa tace "Kinga dama bawani lectures muke ba dama, it's not a
big deal" Na'ima ta koma kan gadon ta kwanta tace "hakane Anty Nafisa" itama tana dariya ta hau gadon dan sake komawa wani baccin.
A gurin breakfast Nafisa ta fadawa su Anty Amnah bazasu koma school ba acewarta basuda wani active school activity ranan Mon
day din" Faruk ya juya yana kallon Na'ima yace "Dagasken take?" ta gyada kai tace "Eh" baice komai ba Anty Amnah tasake tambayanta "Na'ima are you sure?" ta sake amsawa da "Eh dagaske ne Anty" Nafisa na murmushi tace "Bafa karya muke ba" Faruk yace "Ai nas
anki ne Nafisa" Anty Amnah tace "Toh shikenan sai ku huta sosai, nima zanje hospital anjima kadan akwai patient dina dazan duba she's under my care" Faruk yace "Ina uncle fa?" tace "Yana bacci tukunna, yayi night surgery jiya".
Yammacin ranan sai ga Far
uk da tickets na football match da za'ayi da dare cikin Chelsea stadium, one of the most known stadiums in London, tsalle Nafisa ta rinqa yi kamar ba ita tayita mitan gajiya ba, itadai Na'ima nata fara'a dan batasan komai gameda ball ba amma tanason zuwa t
aron itama dan she's curious to see the match in person.
Dawuri Faruk ya kaisu stadium din dan 8:00 pm za'a fara match din, bayan yayi parking a gurin da yayi booking suka fito zasu taka zuwa cikin stadium din babu Anty amnah, dan tace batason shiga hay
aniya kanta yana ciwo kuma ta gaji twins ma sun barosu a gida, shigansu cikin stadium din Faruk yayi gaba suna binsa a baya yana neman seat numbernsu, sai Nafisa ta juyo tana kallon Na'ima tace "Nice huh?" Na'ima na murmushi sai bin ko'ina da kallo take, t
ace "It's beautiful..so beautiful" bayan sun samu gurin zamansu basu jima ba aka fara match din Faruk ya miqe yace "I'm coming" sai ya fara kutsawa cikin mutane zai fita daga stadium din, bai jimaba yadawo hannayensa riqe da popcorn da drinks ya rungumosu
a qirjinsa, zama yayi tareda miqawa kowaccensu yace da Nafisa "What did i missed?" Idonta na kan field din ta amsa da "Not much" tana kai popcorn bakinta.
At first Na'ima bata gane yanda wasan yake tafiya ba sai Nafisa ke kwatanta mata kasancewar ita ta
taso cikin maza a gidansu suna yawan kallon football match sosai.
Cheering din mutane da ihun Nafisa dake gefenta ne yafara sa mata interest sosai akan wasan, aqarshe dai da ita aka miqe ana ihu a stadium din, ba qaramin nishadi match dinnan ya sanya wa N
a'ima ba, bakinta har kunne dan fara'a, Faruk ya sunkuyo kusa da ita yana dan daga murya yace "Do you like it?" Ta gyada kai cikin yar dariya tace "Sosai" shima yayi murmushi kawai.
Ranan taga football celebrities dinda ko a mafarki bata taba tsammanin ga
ninsu face to face ba, it's one of the nights that Na'ima bazata manta ba.
Bayan an tashi daga match din suna hanyan komawa gida ta tambayi Faruk "Kuma yanzu shikenan an kori dayan team din kenan?" yana dariya ya amsa da "Eh" ganin she's new to it, Nafisa
ta juyo daga front seat tace "BoBo zan siya mana tickets muje next match tunda kinaso" Na'ima tace "Ai da dadi ne, bansan haka ball din yake da dadi ba" sai Nafisa ta juya tana kallon Faruk sukayi dariya tare sannan ta sake juyowa gurin Na'ima tace "Welco
me to the team girl" .
KUNCIN ZUCI
📖📚