Showing 102001 words to 105000 words out of 121625 words

Chapter 35 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

23

Na'ima to the point that bata iya tafiya" sai Ahmad ya dunqule hannu yakai bakinsa, shiru yayi ganin haka Nafisa ta cigaba da bashi la

barin tana hawaye, Ahmad sai kallon pool din yake ransa na zafi, da ta fada masa kisan da Stella taso yiwa Na'iman sai da ya rufe fuskansa da tafin hannunsa, aransa ya dinga fadin duk addu'an da tazo bakinsa, kafin Nafisa takai masa qarshen labarin sai da

duk wata jijiya ta tashi a fuskan Ahmad, abunka da farin mutum sai fuskan tayi jaaa, Nafisa na kuka tace "Komawa tayi kamar me ciwon kwakwalwa Yaya, she was depressed to the point that neman mutuwa take a lokacin, karfe biyun dare ta iso Abuja ranan fa, ci

kin bodin Daf Yaya, babu inda babu ciwo a fuskanta, ko gani batayi da ido daya, wallahi kasheta ya so yi Allah beyi ba dan tabon da suka yiwa Na'ima tun daga bayanta har kafanta bazasu qirgu ba" sai sannan Ahmad ya bude baki a hankali yace "He's an animal,

ko me nayi masa bazan huce ba Nafisa, ko me na musu dukansu bazan taba jin dadi ba" itama tace "Sun cuci Na'ima a rayuwa, har yau nakasa kwatanto rumuwan da zeyi daidai da abunda suka aikata mata Yaya" sai sannan ya kalleta amma bece komai ba, aransa yana

ayyana how little she knows about the world, acikin maganganunta yaji cewan Bilal yana yi wa Na'ima alluran bacci awasu daren, does that means raping Na'ima yakeyi in her sleep kenan, Hasbunallah, sai ya daga kai yana kallon sama zuciyarsa na dacii, , a z

uciya yace 'Ya Allah, give me strength' dan wani irin ciwo yakeji a zuciyarsa, irin wannan abubuwan suna ta faruwa da Na'ima a lokacin da ita da shi suke mabanbantan guri a duniyar, then his biggest regret in life shine rashin kulata da yayi ranar da ya fa

ra ganinta a Kano, rashin bibiyar rayuwarta da yayi a wannan lokacin shi yafi komai yi masa ciwo yanzu, bai dena kallon sky din ba ya sake wani maganan zucin 'Ya Allah kabani juriya akan lamarin Na'eemah', sai Nafisa ta sake cewa "I was meaning to tell you

everything amma Na'ima taqi bari inyi hakan, har nan qasar ya sake biyota, and he beat her again a ranan da kaje daukan mu a school, she was afraid in kasan asalinta ko kasan ta bar gida alaqanku zai chanja" yana kallon Nafisan yace "Ni nake tsoron ta cha

nja min saboda abunda namiji ya mata a rayuwa Nafisa" tace "Tana sonka Yaya,i know her and i see it in her eyes, nasan at first she was reluctant about it but not now, not now wallahi, Bilal was all in the past" sai yace "Not for me Nafisa, i only know him

now so he is my present" sai ya sauqe numfashi ya sake cewa "He is in cell right now, and don't even speak of it to her" sai sannan Nafisa tayi murmushi tace "Toh Yaya, dan Allah ka barshi yayi rotten a cell dinnan" sai yace "Cell is a good place Nafisa,

i won't mind letting him go free now, dan komai yanada lokacinsa" ya juya yana kallon pool din sannan ya sake cewa "Komaii"..

Da Nafisa ta tashi tafiya sai da ta biya kitchen din sa ta dauki coke mai sanyi a fridge, tana kurba ta nufi parking lot wani nut

suwa na shiganta, tasan lokacin da Bilal zeyi kuka in return ya kusa, dan a iya sanin da suka yiwa Ahmad a familyn su, gwara yabi abu cikin gaggawa akan yace zai bisa a sannu, tashin nakiya yake yiwa abun a lokacin da ba'a yi tsammani ba...Har motan Nafisa

n ya fita daga gidan Ahmad yana nan zaune a bakin pool din, cikin sanyin jiki ya miqe tareda nufan cikin gidan nasa, alwala yayo ya fara sallah anan falon, da ya idar sai ya nufi stairs da nufin ya je yayi wanka a dakinsa amma beep din wayansa da ke kujera

n falon ya katse sa, dawowa yayi ya dauka sai ya ga hotunan Bilal din ne Micheal ya turo masa, hotunane gasunan kala kala wani Bilal din yana zaune wani kuma gashinan kwance kan dandaran qasa acikin cell din, ahankali yakai hannu yana zooming fuskan Bilal

din abubuwa dayawa na zuwa masa arai, tuna wannan mahaukacin, wannan mashayin yayi sharing same bed da Na'ima

yasashi juyawa yayi wurgi da wayan, da karfin gaske ta daki gini sannan ta tarwatse anan falon, cikin huci ya zauna a kujera ya kama kanshi da duk

a hannunwansa yana jin komai nasa na masa ciwo, wani radadi yake ji a zuciyar sa me dacin gaske...And he know har ya mutu bazai dena jin tsanan Bilal a zuciya ba....

Har dare Na'ima ta kasa bacci dalilin rashin ganin kiran Ahmad, ta juya tana kallon Nafis

a dake bacci a gefenta hankali kwance, sai taji kamar ta tasheta ta fada mata abunda ya faru tsakaninta da Ahmad a Oxford ranan, gashi kuma har sannan bai kirata ba, tana nan zaune jingine da gadon tana tunani sai ta kasa jurewa kawai ta dauko wayanta ta d

anna masa kira, cikin ringing na ukun ya dauka sai yayi shiru, ahankali Na'ima tace "Are you there?" sai taji muryansa ahankali shima yace "Babe i'm sorry ban kiraki ba" tace "No it's okay, I'm just checking on you" yace "Uzuri ne ya riqeni, but I'll come

tomorrow kinji" tayi saurin cewa "No it's fine, good night" ahankali yace "Good night" ta gyada kai tana gyara kwanciya zatayi bacci, da haka Ahmad ya kashe wayan, sai ya juya yana kallon likitan da ke tsaye kansa yana hada allura ga Lamin zaune shima a ge

fen gadon yana kallonsa, Lamin bai ce komai ba sai da likitan ya gama yiwa Ahmad alluran sukayi sallama ya fice sannan ya kalli Ahmad yace "Does this has to do with her?" shiru Ahmad yayi bai amsa ba ya kai yatsunsa yana danne audugan hannunsa dake gurbin

alluran, da dan bacin rai Lamin ya sake cewa "Ahmad what is wrong with you these days?, you're not yourself" Ahmad dake jin zazzabin jikinsa na tsumashi ya dago kai rai a bace yace "Just leave me be Al'amin, dan Allah kabarni da abunda nakeji, just go plea

se" miqewa Lamin yayi ganin yanayin abokin nasa, sai yace "Sorry Man, Allah ya baka lafiya" Ahmad ya jawo white duvet a jikinsa sai ya rufe idanunsa ya jingina kansa da fuskan gadon baice komai ba, juyawa Al'ameen yayi zai fita sai ya dan tsaya kallon hoto

n Na'ima dake dakin yaqara juyowa yana kallon Ahmad din da har sannan be bude idanunsa ba, ahankali yace "Saida safe" da haka ya fice daga dakin abubuwa dayawa suna zuwa ransa..Sai karfe ukun dare bacci ya dauki Ahmad ranan, bayan yayi sallahn asuba yana k

wance kira ya shigo dayan wayansa dake kusada bedside lamp, sunan Mahaifinsa ya gani akan wayan sai yayi saurin dauka tareda sallama, daga daya bangaren kamilin mahaifin nasan yace "Wa'alaikumussalam babban mutum" duk yanda Ahmad ke jin yanayinsa sai da ya

yi murmushi yace "Ina kwana Baba" yace "Ka tashi lafiya?" Ya amsa da Alhamdulillah sannan Baba yace "Ya ayyukan kuma?, London ta riqeka dayawa" Ahmad bai bar murmushin ba ya sake cewa "Alhamdulillah" a nutse Baban ya fara magana "Adam ya samoni da maganan

ayyukan jiya, you have to be there tomorrow for the shareholders meeting, they'll be expecting you there as their Head, kana da pending meetings da ayyuka har haka kuma kake zaune a London har yanzu Babana" cikin ladabi Ahmad yace "In sha Allah za'a gyara"

sai Baban yace "Yauwa dai, I'll be there tomorrow nima" da haka sukayi sallama Ahmad ya sake danna kira a line din mahaifiyarsa, yana shiga ta dauka da sallama, bayan sun gaisa sai yaji kaman tana kitchen dalilin sounds din da yake jiyowa, sai yace "Kina

aiki ne?" fita Mamma tayi daga kitchen cikin kwantar da murya tace "Baka da lafiya ne naji muryanka haka?" yace "I'm fine Mamma, it's just headache" ta sauqe numfashi tace "Ka rinqa sararawa kanka da aikin nan da Allah, dazu mahaifinka ya fadamin zakuyi ma

ganan zuwan ka Lagos, in ka gama ka dawo nan gida ka dan huta tukunna" murmushi Ahmad yayi yace "In sha Allah zanyi yanda kika ce din" tace "Allah ya baka Lafiya, Allah yayi albarka" ya amsa da Amin sukayi sallama, nan ya hau neman available flight na safi

yar ranan, economy class ticket ya samu ya siya saboda late booking

din, miqewa yayi jikin sa babu qarfi ya nufi toilet kansa na juya masa, da ya gama shirin cikin riga da wando masu tsadan gaske sai ya dauko farin jacket ya dora akai tareda saka farin fac

ing cap sannan ya dauki jakansa ya fice yana texting me kula da gidan nasa wanda ya kasance drivernsa shima anan basement din gidan yake zama..

Sai da Ahmad ya zauna a cikin jirgin sannan ya turawa Na'ima text na tafiyan nashi, daga daya bangaren Na'ima n

a kitchen tana hada breakfast dan Anty Amnah zasu fita da wuri ranan, daukan wayan tayi ta karanto saqon nashi.

'Babe i'm sorry i can't come today, I'm heading to Lagos right now but I'll call you the moment we land Okay, take care'

Jikinta ne yayi sanyi

bayan ta gama karantawa, sai ta tura masa da saqon Addu'an isa lafiya sannan ta cigaba da abunda takeyi...

Da safiyar ranan Bilal ya fito daga cikin police station din a jikkace yayi wani wujiga wujiga dashi, jacket dinsa dake hannunsa ya saka sannan y

a ciro wayansa da aka bashi yau din daga aljihu ya kunna, sai yayi sa'a akwai sauran chargy aciki, nan messages din Hajiya da Alhaji suka rinqa shigowa amma na Hajiya sunkai talatin, sharesu yayi sannan ya danna kira a wani abokinsa me suna Anas da ya sauq

a gurinsa a qasar, har ta gama ringing ba'a dauka ba, qarasa wa bakin street din yayi ya tari uber yanajin ransa na suya, lallai daga Na'ima har wanda suke zaman iskancin tare a qasar zasu gane shi suka kulle, wato riqanta har ya kai ta saka abokin zaman d

adiron nata ya masa wannan wulaqancin, da ya isa gidan abokin nasa dake Dulwich, kansa tsaye ya shiga gidan, aikuwa nan kan kujeran falon ya samu Anas yana badalarsa da karuwarsa jikinsu duk babu kaya, sai ya miqe yana kare gabansa yace "Shit man, ya zaka

shigo wa mutane babu sallama Bilal" dauke kai Bilal din yayi ko kulasa beyi ba ya nufi dakin da ya sauqa, shi bata su yake ba, abunda ke cin zuciyarsa yafi gaban wannan, da ya shiga dakin sai ga kiran Hajiya ya shigo wayansa yana cire kayansa, da kamar baz

e dauka ba sai yayi qaramin tsuka ya dauka, daga daya bangaren Hajiya kamar zatayi kuka tace "Ayya Babana so kake in mutu kawai ka huta kenan, Ina ka shiga cikin satikan nan dan Allah?" Yace "Ina London fa" tace "Me ya kaika can kaida ga aikinka ya dawo ka

no kuma" cikin karyewan zuciya yace "Naganta, Naga Na'ima Hajiya" ai daga can miqewa Hajiya tayi tace "A London ta ke barikin kuma, Bilal in kana yiwa Allah ka rabu da yarinyar nan, me zaka cewa Alhajin in ka dawo da ita, ta ina zaka fara kare kanka akan a

bubuwan da kayi" zuciyar sa na quna yace "Sai na dawo da ita Hajiya, Na'ima mata ta ce ni kadai, babu wanda zai aureta ina raye, har wanda tasa ya kullenin bazan barshi ba" Hajiya da ta hangame baki tana shirin magana Bilal ya kashe wayan, yana gani tana s

ake kira amma bai dauka ba, message notification yagani a saman wayansa da baquwar number sai ya shiga ya karanta content din..

'This is my first warning to you, don't let me see you near her again'

Bilal ji yayi kamar yayi ta dukan gini ko zaiji dad

i a wannan lokacin, ransa in yayi dubu ya lalace, yau shine wani banza zai kullesa sannan ya bashi warning akan Na'ima, lallai sai ya nuna masa shima qwaro ne...sai da yayi wanka ya cire kayan jikinsa da suke wari sannan ya sake dauko wayansa yayi sliding

Dm din Nafisa dake Instagram....

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 43

A week Later...

Zuwa sannan yazama saura kwana hudu su Na'ima suyi graduation ceremony na gama Msc dinsu a inda Na'ima zata gama a fannin Data science while Nafisa

kuma information management, a wannan ranan suna apartment dinsu sai harhade kayansu sukeyi guri daya wanda zasu koma gida dashi, Na'ima na tsugunne gaban wardrobe tana saka kaya a akwatin nasu Nafisa ta shigo hannunta riqe da wasu books manya, ta dago kai

tana kallonta tace "Nafee zo ki zauna muyi magana" da Nafisan ta zauna a bakin gado sai tace "Na miki wani abunne da yasa bakyason fadamin alaqarki da Lamin?" da sauri Nafisa sauqo qasa tana ware Ido tace "Meyasa zakiyi tunanin haka Na'ima?" cikin sanyin

murya tace "Toh naga kuna waya kuma kinqi fadamin komai" Nafisa tace "Wallahi ba boye miki komai nake ba, har yanzu muna stage din fahimtan juna ne sis, kuma Ina jira inga step din da zai dauka akan relationship din namu in na koma Nigeria ne" Na'ima ta gy

ada kai tace "In sha Allah komai zai daidaita a tsakanin ku" sai takai hannunta ta dafa Nafisan tace "Inason inga kina cikin steady relationship sis, I'll give everything to see you happy with the man you love Nafee" sai Nafisa tayi murmushi tace "Kamar ke

da Yaya Ahmad" murmushin itama tayi ta kauda kai tana fadin "Ni nace miki muna dating?" Nafisa ta kwashe da dariya tace "Toh wallahi kanki kika rainawa wayo bani ba, Eh lallai" Na'ima bata daina murmushi ba ta cigaba da ciro kayan wardrobe din, sai Nafisa

takai hannu ta dauko wani kaya tana kallo tace "Dama har yanzu kayan nan suna nan? dasu kika taho qasar nan daman?" Na'ima na kallon kayan Nurse Aminan itama, ahankali tace "Ina ajiyansu ne har zuwa ranan da Allah zai bani ikon maida mata su tareda kudin

da ta aramin" sanyi jikin Nafisa yayi tace "In sha Allah tare zamuje in ga baiwar Allah'n nan, she is truly kind, Allah ya biyata da mafificin Alkhairy" Na'ima ta gyada kai tana jin zuciyarta na karyewa tuna abunda ya faru da ita ranan da aka bata kayan, s

hiru Nafisa tayi tana kallonta sai takejin kamar ta fada mata yanda sukayi da Ahmad da abunda Bilal ya turo mata a Instagram, amma sai ta fasa, ta miqe zata debo toiletries din Na'ima dake bandaki kiran Husna ya shigo wayanta, a hand free ta saka bayan ta

dauka sai Husna tace "Nafisa na barwa duniya ke, na yafe ki kawai" Nafisa na dariya tace "Wallahi baki isa ba, ina maqale dake har duniya ta tashi" sai Na'ima tayi murmushi tana girgiza kai sanin draman mutane biyun nan, Husna ce tace "Dan rashin mutunci h

ar zakuyi graduation amma baki kirani kin fada min ba sai yanzu nakeji a bakin Yaya yana fada wa Mamma akan muzo nida ita da Anty fatima, Bobo yaushe ma yasan kuna karatun da har ze rigani sanin gamawanku" Nafisa tace "Anty Husna ta aminiya ta yau fa nake

shirin kiranki" Husna na dariya tace "Karyaaa, sai kace ban sanki ba, yanzu dai ba wannan ba, labari naji gurin Salma wai Laila tabi Yaya har nan qasar" Nafisa ta amsa da "Tazo three weeks dasuka wuce, har dambe munyi amma na mata duka" sai da Na'ima ta ba

r abunda takeyi tana jin ikon Allah, dariya sukayi dukansu kafin Husna tace "Zamu zo in sha Allahu bakina da maganganu nima, yar banzan wai ance sai rashin lafiya takeh mommyn ta sai sintiri take zuwa gurin Mamma, da safen nan kuma sai gata tazo gidan nan

qalau da ita takawo wa Yaya snacks" Jin abunda tace yasa Nafisa kallon Na'ima, ganin ta kauda kai tana zipping box yasa ta cewa "Ke hakura zatayi fa dan Yaya Ahmad ya daidaita da matar da zai aura anan qasar ma" Husna tace "Ke

habaaa?..har ina cewa zan mik

i magana ki san yanda zakiyi ki hadasa da kawarkin nan Na'ima, Allah ya gani tana burgeni sosai" sai Nafisa tayi murmushi tace "In na fada miki wacece sai kinfi kowa farin ciki toh, kedai Allah ya kawoku lafiya" Na'ima yi tayi kamar ba maganan ta suke ba t

ana cigaba da abun gabanta, amma aranta sai da taji wani zafi najin Laila taje gurin Ahmad din, ranta ne taji yana baci, kawai ta miqe ta fice daga dakin tana nufan kitchen zata tattare musu wasu utensils din...

Har washegarin ranan Na'ima na kallon kiran

Ahmad a wayanta amma taqi dauka, gashi dai tanajin zuciyarta wani iri amma batason yarda cewa kishin Ahmad ne yake damun ta, haka ta wuni har yamma zuciyarta babu dadi, gashi Nafisa bata nan ranan sai yamma ta dawo, lokacin suna kitchen itada Anty Amnah N

afisan ta shigo tana musu sannu da aiki, sai da suka gama ta ja hannun Na'iman suka shiga daki tace "Bobo bakisan Ya Ahmad yadawo babu lafiya bane?" sai Na'ima ta tsaya kallon ta takasa magana, ganin hakan Nafisan ta sake cewa "Ashe da rashin lafiya ya taf

i last week ma, yanzu ma ya dawo da shi, ina gidansu Lauren, Lamin ya kirani yake fadamin da yazo daukana, har munje na dubasa ma" sai Na'ima ta kauda kai tace "Allah ya bashi lafiya" da haka ta kwanta a gadon, zama Nafisa tayi tace "Me yake damunki ne Na'

ima, rashin lafiya yake fa" sai ta dago kai tace "Ayya Nafisa yazanyi toh in ba addu'an zan masa ba" Nafisa tace "Kije ki dubasa, that's it" sanyi jikin Na'ima yayi, ganin haka sai Nafisan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login