Showing 15001 words to 18000 words out of 121625 words

Chapter 6 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

19

tana

quoting maganar Salman da hannunta, sai Nafisa tace "Banida lokacinki Salma". Na'ima tayi tsuru tsuru ganin fada zai kaure akanta, tadan kamo gefen skirt din jikin Nafisa alamun su bari.

Sanin masifa da rashin hakurin Husna da Nafisan yasa Salma juyawa t

a fice tana fadin "Kwaji dashi" Husna ta dan daga murya tace "Zamu hade ne, yar rainin hankali" sai ta maida hankalinta gurin Nafisa tace "Wallahi duk Laila ce take koya musu salon magana mai dauke da rainin nan, balle yanzu da tunda watan bikin ya kama su

ke sintirin yawo tare, idiots..." Nafisa tayi tsuka tace "Can gidansun zamuje daga nan, Mami harda min gargadin batason fada" Husna ta kyabe baki tace "Lailan ce sai kana mata zafi zafi" Nafisa tace "Ita tasa Salma ta fitar da wannan ankon mai kama dana 'y

an iska ko?" Husna tace "Eh mana, ba don Mamma tace sai nayi ba su sun isa su sani nayi wannan kayan ne" Nafisa ta sake yin tsuka jin ranta yana neman baci tace "Wace gulman kika kirani za kimin din jiya?" Husna tace "ke jiya Farha ta sake hotunan wanda ta

auran a insta" Nafee tace "Haba? Kice anata ruguntsumi babu ni kaddai" Husna tace "Kedai bari..5k comments a jiyan fa".

Cikin zumudi suka fara maganganunsu da ya shafi Instagram wanda Na'ima ba ganewa take yi ba dan duk ta qosa su tafi kuma, jitayi duk

ta taqura.

Bayan sunyi sallama dasu Mamma akan zasu tafi ta basu humra da turaren kabbasa sukayi godiya suka je wajen Anty itama, sama sama ta amsa musu, Husna ta rakasu suka fice, sun fito compound din gidan kenan suka hango Ahmad sunkuye cikin boot din

motarsa yana neman abu , Husna tace "Tabb ga yaya can" Nafisa tace "Bari muje mu gaisa" riqo hannun Nafisan Husna tayi tace "Mamma ta kai qarata jiya, kuzo mu wuce tun bai dago ya ganmu ba" Nafisa tace "To inya juyo fa, kinga Na'ima zo muje" ta qarasa maga

nan tana riqo hannun Na'ima itama, Na'ima ji tayi kamar ta cewa Nafisan "Bazai juyo bama" amma ganin Husna yasa bata fada ba, haka dai ranta babu dadi suka qarasa wajensa da har zuwa lokacin yana duqen bai gama abunda yake ba, Nafisa ce tafara magana tace

"Sannu yaya" sai ya dago ya rufe boot sannan ya juyo, idonsa bai sauqa kan komai ba sai Na'ima, suka sake hada Ido Na'ima tayi saurin kauda kanta ganin yau ma kallon ta yake yi, jitayi kafafunta na neman gagara daukanta gashi sai ta ganta wata qarama a qas

ansa dan Allah ya masa baiwar tsayi da qaqqarfan jiki, dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida hankalinsa wajen qannen nasa yana amsawa cikin muryarsa dake hana Na'ima nutsuwa yace "Yauwa sannu Nafisa, ya gida?" Nafisa ta amsa, cikin sanyin murya Na'ima t

ace "Ina wuni" tana kallon everywhere but not his face, dan motsa lips dinsa yayi wanda inba lura kayi ba baza kace murmushi yayi ba, yana nazarin yadda take escaping kallon fuskansa, a nutse ya amsa mata da "Lafiya" Husa tace "'Yar'uwarsu Nafisa ce Yaya,

sunanta Na'ima..." sai ya sake kallon Na'iman yana nanata sunanta a zuciyarsa, a fili yace "I know" Na'ima ta dan juya ta kallesa ganin ya maida kallonsa wajen qannensa, within sakannin da basu wuce sha biyar ba ta gama kallon fuskansa a sace sannan tayi s

aurin kauda kanta kar ya juyo, Nafisa ce ta tambayesa "Yaya Adam yana nan kuwa Yaya?" ya dan gyada kansa yace "Yana falo" hanyar bangarensu Ahmad din suka nufa,

yadan bi bayan Na'ima da kallon gefen Ido kafin ya shiga motarsa ya tayar.

Sun tadda Adam yan

a Shirin fitan shima yana maqala link jikin hannun rigarsa, suka gaisa yace musu fita zasuyi shida Ahmad shima, tare suka fito ya musu sallama ya wuce gurin motan da Ahmad yake ciki yaja suka fice, suma tasu motar suka shiga suka bar gidan Husna na nan tsa

ye a compound ta daga musu hannu.

Isarsu gidan Daddy basu samu kowa a falo ba, sai basuyi azarbabin bin Mummy part dinta ba Nafisa tasa sukayi zamansu nan falon, basu jima da zama ba Mummy ta sauqo cikin shiga ta alfarma cike da qasaita ta qaraso ta zauna

tace "Sannunku" suka gaisheta kan Na'ima na qasa dan tunda Mummy ta shigo taji kwata kwata Aura din matar bai mata ba sam, suna gama gaisawa Mummy ta dan kwala kira wata mai aiki ta shigo sai ta umarceta da ta kawo musu refreshments, sunanan zaune shiru b

abu me magana Mummy ta kalli Na'ima sannan tace da Nafisa "Ina kika samo wannan fa? Kawarkice?" Nafisa ta amsa da "A'a yar uwar muce" Mummy ta qarewa Na'ima kallo sannan tace "To sannu"

Laila ce ta fito daga wani qofa alamun kitchen ne a gurin, ta qaraso

cikin falon ta zauna gefen Mummy tana kallonsu sama sama tace "Sannu fa" sai Nafisa ta dan juyo itama sama sama tace "Sannu" Na'ima ta dago kai ta kalli Laila zata gaisheta atake ta rasa me zata fada, ganin attachment da nails din da suke jikin Lailan yayi

triggering wasu memories acikin brain dinta, tayi saurin sauqe idonta, Laila da kyawun Na'ima took her by surprise ta kalli Nafisa tace "Wannan fa, daga Ina?" Nafisa na jinta kuma bata kulata ba ta cigaba da kallon Tv kamar bada ita Lailan ke magana ba, M

ummy ce ta amsawa Lailan tace "Nima yanzu nake tambayanta, wai 'yar'uwarsu ce, Inaga sai dai ta fannin Mamin tasu daga Nijar"

Laila ta sake tambayan Nafisan tace "Daga gidan baba kuke ne?, Salma tananan?" Sai lokacin Nafisa ta juyo ta amsa coldly da "Eh"

Laila tace "Yaya Ahmad fa?" Nafisa tace "Bansani ba nima" tasake juyawa tana kallon Tv, Na'ima dai kamar ta arce daga falon haka takeji, the atmosphere become toxic to her, daga Mummyn har Lailan tuna mata suke da wasu mutane a rayuwan ta da bata son tuna

su kwata kwata yanzu. Jin Laila na tambayan Ahmad yasa Mummy tace "Ba kince zaki kirasa ba" cikin rashin da'a Lailan ta amsawa Mummy da "Toh na kirasa bai dauka ba ya zanyi Mummy, ni zuwa kawai zanyi da kaina in kaimasa cakes din, tunda bai dauki kiran ba"

ta miqe tana turo baki ta sake tsuka ta wuce stairs su Nafisa na bin ta da kallo, Mummy tace "Ke kika sani ai" ta sake kwala kiran me aiki tace mata "Ki dan debo musu snacks din da Lailan tayi" ta amsa da Toh ta koma kitchen din bata jima ba ta dawo dauke

da different shape of small pieces of cakes ta ajiye gabansu, basu ko taba plate din ba Nafisa ta fara miqewa tareda cewa "Mummy zamu wuce gida" Na'ima ta miqe itama tana mata sallama sai Mummy tace "Toh a gaida gida" da haka suka fice, isarsu wajen motan

su afili Nafisa tace "Shegiya" juyowa Na'ima tayi zagin yayi tooking dinta by surprise tace "Haba Nafee" adan fusace Nafisa tace "Ke bakiga yanda shegiyar ke mana magana bane, wallah badan Mami ta gargadeni akan fada da Laila ba da watarana sai na zubar ma

ta da haqora tas" Na'ima tadan ware Ido tace "Toh ba gashi har mun gaisa mun fito ba, komai dan haquri ne ai, keda ba wani haduwa kukeyi bama" Nafisa tayi tsuka suka shiga motan suka bar gidan tana mitan sai sun koyawa Laila hankali itada Husna, itadai Na'

ima Allah Allah take su qarasa gida ta huta da wannan tunanin da suka zo ranta tun safiyar yau har zuwa barinsu gidansu Laila.

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa





Chapter 12

Isarsu gida suka samu Anty Amnah tazo, sunzo saboda bikin itada 'ya'y

anta twins, ihun murna twins suka fara ganinsu Na'iman sai suka nufesu da gudu Na'ima na ware musu hannunta suka maqalqaleta, Nafisa na kallonsu tace "Yarannan kun gama yayi na wato" Mami da Anty Amnah dake zaune a falon sukayi dariya Anty Amnah tace "Boys

babu amana" zama sukayi nan falon bayan sun gaisa Anty Amnah take tsokalan Na'ima wai tayi qiba, tayi dariya tana jin duk wani tunani da ta kwaso gidansu Laila yana washewa.

Har dare Anty Amnah na gidan sai da sukayi sallah sukayi dinner sannan ta kira d

river ya maida ita gidanta dake nan Abujan wanda suke sauqa in sunzo qasar.

Daren ranan bayan Na'ima ta gama shirin bacci cikin riga da wando dogo ta saka hula akanta ta fice zuwa falon Mami sanin cewa mazan gidan basa gurinta by now, bata samu Mami a fal

on ba ta qarasa cikin dakin ta ganta a duqe gaban bedside drawer tana bincikawa, qarasowa cikin dakin Na'ima tayi tace "Barka da dare Mami"

Mami tadan dago tace "Habibti, bakiyi bacci ba?" Na'ima ta amsa da "Eh" ta zauna bakin gadon Mamin ta sake cewa "Ab

u kike nema ne Mami" sai Mami tace "Wai fa nayi ajiya ne na manta specifically inda nayi ajiyan" ta qara da "Lantana ta qara soya muku gyadan ku yananan a kitchen" Na'ima ta gyada kai tace "Har munci ma"

Tananan zaune Mamin ta miqe ta wuce toilet sai Naf

isa ta shigo tace "Nan kikayo?"  ta gyada kai, Nafisan ta zauna kan gadon itama ta zubawa Na'ima chocolates masu dan yawa akan cinyanta, ware Idanu tayi za tayi magana kenan Mami ta fito daga toilet idanunta suka sauqa kan chocolates din, Nafisa da batayi

expecting ganin Mami a dakin ba ta ware idanu tace "Laaa Mami ashe kinanan, nazata kina kitchen fa"

Mami ta harareta tace "Shiyasa kika shigo da abunda na hanaku sha din kenan" Na'ima ta juya kanta dariya na taho mata, sai Nafisa ta fara dariya tace "Wall

ahi Mami tun safe bamu sha ba sai yanzu" Mami ta wuce gurin wardrobe zata dauki abu tace "Ya muku kyau, ku cigaba" Atare suka bata hakuri bata kulasu ba ta fita daga dakin. Nafisa ta juya ta daka duka a cinyan Na'ima, sosa gurin Naima tayi tana dariya tace

"Auchh..to ai zan miki magana naga ta fito daga toilet din".

Hiransu suka zauna nan dakin Mamin sunayi, Nafisa na pressing wayanta, can tayi wani tsuka mai karfi tana kallon wayanta tace "Ni na taba kallon yarinya mara zuciya da aji irin yarinyar nan k

uwa" Na'ima na kallonta tace "Me kuma ya faru?" Nafisa ta miqe zaune ta miqo mata wayan a fuska tace "Laila mana, kiga post dinda tayi a IG, ke yanzu wannan yabmiki kama da hannun Yaya Ahmad dan Allah" shiru Na'ima tayi tana kallon wayan wanda hoton hannun

mace da namiji ne sarqe cikin na juna dan ba sanin hannun Ahmad din tayi ba, sai tace "Nafisa ni kuma Ina nasan yanda hannunsa yake?" Nafisa tace "Nidai ko kaffara bazanyi ba wannan ba hannunsa bane,byaushe ma ya dauki kiranta balle har ya kai da riqe han

nunta" Na'ima tace "To ke me ruwanki in ma hanunsa ne, ba budurwarsa bace, meye na rantsuwan" Nafisa ta dan harareta tace "Waa? Yaya Ahmad din? lallai

bakisan wannan ba, anfada miki yanada lokacinta ne...ke har matan ma in general, harkan kudade kawai yasa

ni wannan kowama yasan haka" Na'ima tadan kyabe baki tanajin wani iri aranta batace komai ba Nafisa ta cigaba da maganan tace "Har da wani love caption, Eh lallai Laila" ta qarasa tana dan dariya ta sake miqa wayan fuskan Na'ima tace "Kiga caption din har

da hashtagging din sunan Yayan fa" Na'ima ta kauda idonta daga kallon wayan jin ranta na dan baci babu dalili tace "Amfanin me kallon zemun, kinada problem wallahi Nafisa" Ta juya ta jawo blanket din kan gadon Mamin tayi kwanciyarta, ganin abunda tayin lik

e she's not interested in the talk yasa nafisa daukan pillow ta kwada mata, fashewa da dariya Na'ima tayi tace "Allah kedin ce ai Nafee, hiran is not productive,bI don't see why kike tada jijiyan wuya" sai Nafisa ta sauqa daga gadon tace "Bazaki gane bane"

ta qarasa maganan tana fita daga dakin Na'ima ta bita da kallo tana tunani aranta kan meyasa ma zataji wani abu a ranta game da hiran to, after all batada hadi da kowanne cikin mutane biyun, bata dade da fara bacci ba Nafisan ta dawo ta kwanta, nan dakin

Mamin suka kwana ranan.

Lokacin bikin yana ta matsowa and Na'ima is not even interested in it, itadai ta dawo gida domin ta ga su Mami ne daman bawai bikin wata Salma can da bata santa ba.

Da bikin ya zama saura kwanaki kadan Meerah ta aiko musu da kay

an nasu, kaya sunyi kyau har Abba saida aka nunawa

Nafisa ta kaisu salon akayi musu qunshi aka yiwa Nafisa kitso while Na'ima tace bata so aka gyara mata gashin kawai.

Cikin week din bikin Nafisa tace suje can gidan bikin Na'ima ta jijjaga kai tareda c

ewa "A'a bazanje ba Nafee sai ranan auren" kuma Mami ta yarda da hakan a lokacin da Nafisa ta kai qaran Na'iman wajenta.

Haka Na'ima na gani Mami suke zuwa gidan bikin tace ita sai ranar auren zata je..Ana gobe auren duk 'yan gidan sun tafi can gurin even

t aka bar Na'ima ita kadai da Lantana, girki suka yi bayan sun gama Na'ima ta wuce dakin Mami ta debo kayan ta na laundry sannan ta shiga dakin Nafisa ta debo nata ta wanke su tas a washing machine

Har dakin Abubakar ta shiga dake nan falon downstairs ta

gyara masa ko ina, she kept herself busy sunata hira da Lantana.

Sai dare Faruk ya dawo dasu Mamin, sun shigo lokacin tana sallah a dakinta bayan ta idar ne ta tafi gurinsu nan falon Mami suna zaune, shiganta dakin Mami tace "Habibti ya zaman shiru" ta qa

raso ta zauna gefen Mamin tace "Sannu da dawowa Mami"

Mami ta amsa da Yauwa, Nafisa dake gefe azaune kan kujera itada Faruk bayan ta chanja kaya, tace "Husna tace in bakije ba gobe dakanta za tazo daukanki" Faruk yayi murmushi yace "Meyayi zafi, kamar ab

un dole" ya kalli Na'ima yace "Habibtin Mami kiyi zamanki ma in goben bakyason zuwan" Na'ima tayi murmushi tace "Toh Yaya" ta qarasa maganan tana dan ware Ido ma Nafisan alamun "To dai kinji" Nafisa tace "Wallahi baki isa ba sai kinje, in ban ciccibeki na

kaiki ba" Mami da faruk sukayi yar dariya tace "To fah" ta juya tana kallon Na'ima tace "Habibti kinci abinci dai ko" Na'ima na dariyan Nafisan ta gyada kai tace "Eh Mami, akwai naku a dining ko a kawo muku nan" Mami tace "barshi mu huta tukunna"

Faruk s

ai kallon Na'ima yake ganin she was openly herself these days, harda tsokala wanda a farkon zuwanta gidan she can go days batayi ko da murmushi ba.

Ranan ba'ayi hira a falon Abba ba, kowa ya tafi makwancinsa da wuri a huta gajiya.

Washegari da sassafen

Mami ta tafi gidan bikin ta barsu suna bacci, Na'ima bata tashi ba sai almost nine shima yunwa ce ta tada ita ta sauqa yin breakfast sanye cikin purple color din kayan bacci mai laushi kamar cutton a jikinta, hularta tayi baya kwantaccen gashin goshinta d

uk ya bayyana, kitchen ta shiga tana tsaye bakin fridge Nafisa ta shigo itama da kayan baccin ajikinta tana miqa alamun itama tashinta daga bacci kenan, zuba madara Na'ima tayi a cup ta miqa mata, Nafisa ta karba tana kaiwa baki tace "Yaushe zamu shirya mu

tafi, Husna called me" Na'ima tayi hanyar fita daga kichen din hannunta riqe da kofin madaran tana cewa "Nafee mu dan bari anjima mana, it's too early" Nafisa ta bita suka fita tace "Kinsan fa za muje wurin makeup dinnan" zama sukayi a nan dining zasuci a

bincin.

Basuyi nisa da fara cin abincin ba Faruk ya shigo, on a normal circumstances Na'ima ba wani damuwa tayi ba dan babu hijab a jikinta sanin cewa tana zama da normal kaya ko a gabansa ne dan kamar Yaya na jini ta dauki Faruk kuma shima bai damu ba,

Amma ganin wanda ke biye dashine yasa ta daskare a wurin ta kasa kai cokalin abincin bakin ta aranta tana cewa "Yau kuma me wannan mutumin yazo yi da safe haka" because tunda ta fara rayuwa a gidan bata taba ganinsa ba sai kwanannan.

Qarasowa dining d

in Ahmad yayi yana dan kauda idonshi daga kallonta ganin yanayin kayan jikinta.

Sanye yake cikin white polo shirt da blue jean shima in a casual way, ganinsu yasa nafisa cewa "Yaya, good morning" Ahmad ya zauna yace "Nafisa, kin tashi lafiya" Nafisa ta am

sa tareda gaisheda Faruk sannan ta miqe ta fara serving dinsu abincin, sai Na'ima ta ajiye cokalin hannunta ta dan fara gyara hulanta da jelan gashinta masu tsayi suka qi komawa duka, tace "Ina kwananku" Faruk dake kallonta ganin how cute she looks, yace "

Lafiya Na'ima, I thought kun tafi gidan bikin fa" Na'ima ta dan jijjaga kai tace "Sai anjima" Ahmad ya kasa jurewa sai da ya dago ya kalleta amma Na'ima taqi kallon gefensa,  murmushinsa na yau saida ya dan bayyana ganin still dai she can't look at him kum

a baisan meyasa ba yake bidan ta kalleshin .

Hira sukeyi sama sama suna cin abincin, Nafisa tace "Yaya anan ka kwana ne?" Ya dan jijjaga kai hankalinsa na kan abincin da yake ci kadan kadan, anutse yace "A'a can gidana na kwana" Faruk yace "Gidan baba wa

s crowded i don't know how Yaya Adam is cooping" Ahmad ya dan gyada kafada yace "Wannan jama'a basa damun baccinsa ai" Nafisa da faruk suka danyi dariya.

Na'ima dake jinta so uncomfortable under his Eyes yasa tun dazun idonta ke kan plate din gabanta bat

a dago ba aranta tana ayyana meyasa wannan bawan Allahn ke sa mata rashin nutsuwa ne, samun kanta tayi da dan dagowa tana kallon hannunsa hoton rannan da Nafisa ta nuna mata yana fado mata arai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login