Showing 24001 words to 27000 words out of 121625 words

Chapter 9 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

17

a jikinta qamshin rigan na cika mata hanci, ahaka bacci ya dauke ta zuciyarta na saqa mata abubuwa daban daban...

Sai shida saura jirginsu ya isa London, bayan

anyi announcing fitan su, Na'ima ta sauqe jacket din daga jikinta ta miqa kan cinyan Nafisa tafara shirin miqewa, dan ware Ido Nafisa tayi tafara dariya tace "lallai ma yarinyar nan, ni na lulluba dashi ne?" Na'ima ta miqe tana gyara squeezing din riganta

tace "Ke kika karba daga hannun wadda ta kawo ai" kawai dariya Nafisa tayi ta dan gyada kanta...Fitarsu basu gamu da Ahmad ba suka fara tafiya Nafisa nata waige waigen inda zata hangoshi suka shiga cikin Airport din, saida suka wuce arrivals Nafisa ta cir

o wayanta daga jaka ta fara kiransa, bayan ya dauka sun gama magana Nafisa tace da Na'ima "Muje sis" .

A wajen airport din suka samesa tsaye da jaka a rataye cikin white t-shirt mai dan kauri, jacket dinsa dake rataye hannun Nafisa ta miqa masa tace "Gash

i Yaya mungode" karba yayi ya kalli Na'ima dake tsaye, bude bakinta tayi a hankali tace "Thank you"  ya gyada kansa yace musu "The driver is on his way"  sannan yafara saka jacket din a jikinsa, Nafisa tace "Toh Yaya"

Dayake spring season ya danyi nisa s

ai ya zamto garin babu wani sanyi sosai....suna nan tsaye wata sleek ride tayi parking a gabansu wani bature yafito yana gaisheda da Ahmad ya amsa masa, sai drivern ya gaisa dasu Nafisa sannan yafara diban kayansu yana sakawa a booth Ahmad din na tayashi..

bayan sunyi settling acikin motan Ahmad na gaba ya fadawa drivern unguwar Anty Amnah suka dauki hanya.

Isarsu gidan Anty Amnah bayan driver ya sauqo musu da kayan nasu suka wuce bakin entrance din Nafisa ta danna door bell din, basu jima anan tsaye ba A

nty Amnah ta bude, cikin fara'a tayi hugging dinsu tace "Oyoyo 'yan makaranta sun dawo" ta jasu suka shige cikin gidan nata mai kyau

dake screaming luxury, twins basa nan suntafi makaranta shikuma Abbansu yana asibiti, kafin su zauna Nafisa ta wuce gurin d

ining area ta dauko musu bottle water data gani a gurin ta dawo falon tana miqawa Na'iman daya tace "Anty tare muke da Yaya Ahmad fa" sai Anty Amnah ta dan ware ido kafin tayi magana taji an danna door bell din again, miqewa tayi ta je ta bude Ahmad yace "

Momma kin rufeni a waje" tayi dariya tareda riqo hannunsa suka shigo cikin gidan tana cewa "Na isa son, kaida ganinka yayi tsada a London ma" zama shima yayi nan falon Anty Amnah tasake cewa "Kasan ban kawo araina tare kuke bane wallahi" Ahmad yadanyi murm

ushi kawai..miqewa Anty Amnah tayi ta debo musu drinks harda snacks, da kuma abinci tace "Za kuci yanzu ko sai kun huta?" Na'ima batace komai ba sai Nafisa ce tace "A'a Anty zamu huta tukunna, sai munyi changing ma" sai Anty Amnah tace "Toh" Nafisa ta juya

gurin Na'ima tace "Muje sis" suka miqe tare suka nufi dakinsu dasuke sauqa in sunzo gidan suka bar Anty Amnah ta miqa refreshments din nan gaban Ahmad.

Bayan su Na'ima sunyi wanka sun dan nutsu, komawa sukayi falon amma basu tadda Ahmad ba Anty Amnah t

ace musu ya wuce gidansa, dining area suka nufa suka fara cin abinci, bayan sun gama ne suka dawo falon sannan suka fara hira da anty Amnah.

Haka su Na'ima sukayi zamansu nan gidan Anty Amnah suna hutawa akan sai Sunday zasu koma Oxford, Kuma sun fada m

ata hakan ta amince.

Ranan Saturday da safe Nafisa tayi waya da kawarta Lauren akan tashigo London, haka ta shirya akan zasu hadu a wani Cafe tace da Na'ima suje amma tace baza taje ba..

Wunin ranan Na'ima da twins tayi sa dan su Anty Amnah da Mijinta

ma basanan sunje asibiti sunada shift, ta tafi kitchen da twins ta hau yi musu cake, dan Nafisa ce ta koya mata yanda akeyin cake din farkon zuwansu Oxford harta koya sosai, twins sai hira suke mata tana biye musu, sunyi having fun sosai dan twins suna son

ta sosai indai tazo gidan kuma sunanan to bini bini duk inda Na'ima tasa qafa suna biye da ita kaman dama tun can sun santa tun tashinsu.

Daren ranan Na'ima na zaune dakinsu ta jingina bayanta da fuskan gadon tana kallo a laptop dinta, gefenta plate ne

dauke da sauran cake dinta tayi, kwance Jafar yake a dayan gefenta yayi bacci shima...Nafisa ce ta shigo dakin Na'ima ta dan dago ta kalleta, Nafisa tace "Sannu uwar twins, sudai yafe mamansu suke yi ma in kika zo" Na'ima tayi murmushi tayi pausing kallon

nata tace "Kin dawo?" zama Nafisa tayi a bakin gadon ta dauki cake daya dake plate nan kusa da Na'iman takai baki tace "Duk na gaji ma" sai Na'ima tace "Ina da Ina kuka je haka?" ta amsa da "Ashe housewarming party Lauren tazo attending garinnan da kuma y

in content akan gurin partyn....sis akwai masu kudi a London, waiii.." Na'ima tayi murmushi tace "Kijiki sai kace bakisan kudi ba" Nafisa tadan ware Ido tace "Banda irin wannan kudin Bobo" sai Na'ima ta dan jijjaga kai tayi playing kallonta, Nafisa ta dan

gyara zama ta cigaba da magana "Guy dinda ya sayi Mansion din ashe cousin din Lauren ne....kawai sai gani ga Yaya Ahmad, na zagaya wajen pool din gidan naganshi zaune da wasu friends dinsa" Na'ima ta dan dago ta kalleta tace "Allah sarki" Nafisa dake lura

da expression din Na'iman tace "Kinsan ya tambayeni yakike" maida idonta kan kallon Na'ima tayi cikin sanyin murya tace "Ayya, ya yake shima?" sai Nafisa tace "Lafiyansa lau, narasa ina yake haduwa da friends irin

wa'inda nagansu tare yau, they all scream

money" Na'ima bata ce komai ba Nafisa ta sake cewa "Kinsan Yaya Ahmad yasha creating apps da sukayi gaining global reach" sai sannan Na'ima ta dago kanta tace "He's a programmer?" Nafisa ta amsa da "Babba ma kuwa, bayan aikinsa na company da Baba ya dora s

hi Head ai yana programing manya manyan Apps, zuwansa da yayi this time ma maqasudin zuwan ashe saida wata App din yazo yi gurin investors, ina tsaye kusa dasu naji yana maganan da wani white friend dinsa" sai Na'ima ta gyada kai kawai batace komai ba, Naf

isa dake son cusa mata maganan Ahmad din ta sake cewa "Dan dai ba shaquwa nayi dashi bane, saboda sai nayi shekara abu bai hadoni dashi ba kuma shi bayason arinqa shige masa cikin al'amuransa kai tsaye, dana jaki watarana munje gidansa dake nan London" Na'

ima tace "To ma tayaya zamu kwashi kafa muje gidansa Nafisa..akan wane dalili?" miqewa Nafisa tayi tafara rage kayan jikinta tace "Ha'a muda yayanmu..yanada kirki fa kawai ba komai zaki gansa yasa kansa aciki ba kamar Yaya Adam" Na'ima jijjaga kai tace "Ai

bance baida kirki ba kawai bazan je bane" cikin son kawar da zancen yasa ta sake cewa "Bayan celebrities dinda Lauren din keyin content akansu, yanzu ta koma yi har a gurin housewarming party ne? Ko bada ita kukaje yin content gurin movie premiere ba kwan

aki?" Nafisa tace "Wannan babu inda bata tabawa indai akazo batun content, da celebrities din, Entrepreneurs, business tycoons duka ko ina ma" Na'ima ta gyada kai sannan ta cigaba da kallonta.

Washegari Sunday ya kasance ranar komawarsu Oxford, da wuri

suka shirya komai nasu bayan sun idar da sallan safe, sannan suka tafi kitchen girka nasu breakfast din dan yau Sunday su Anty Amnah yawanci suna yin dogon bacci na hutu.

Bayan sun gama hada komai nan dining sannan suka zauna suka fara ci, Anty Amnah ce t

afito sanye cikin long pajamas, gaisheta sukayi ta amsa sannan taja kujera ta zauna tace "Sannunku...kun gama shirya kayan naku dai ko" Nafisa tace "tun tashinmu" Na'ima na sipping tea din hannunta tace "Twins basu tashi bane Anty?" madadin Anty Amnah ta a

msa sai tace "Meya samu muryanki daughter? Mura ne?" sai Na'ima tayi gyaran murya kadan tace "Nadan tashi da tari ne Anty" Anty Amnah tace "Sannu dear, akwai magani a cikin first aid box, zaki gani a study room din Abbansu, ko bari idan natashi zan dauko m

iki" Na'ima ta gyada kai tace "Toh Anty nagode"

Nan sukayi breakfast din da Anty Amnah suna hiransu, bayan sun gama suka koma daki sukayi wanka suna cikin shirin Anty Amnah ta shigo dakin tace musu "Ku fito yayanku yazo daukanku" sannan ta fita.

Na'ima t

a juya ta kalli Nafee tace "Wani Yayan?" Nafisa na zipping riganta ta danyi murmushi tace "Yaya Ahmad mana, I told him yesterday akan yau zamu koma da safe" sai Na'ima ta dan tsaya kallonta can kuma ta juya ta cigaba da saka kananun kayayyakinta a qaramin

jakanta batace komai ba.

Fito da kayansu suka fara yi Abban twins ya tayasu daukan wasu ya fita waje dasu, bin bayansa su Na'ima sukayi dauke da wasu kayan a hannunsu Anty Amnah ma haka.

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 16

Tsaye Na'ima

taga Ahmad bayan motansa suna saka kayan nasu shida Abban twins at the same time suna magana, qarasawa sukayi gurinsu Anty Amnah tace "Son mun tado ka da sassafe ko, ai da ka turo driver ya kaisu bakomai" rufe booth din Ahmad yayi yana murmushi ya matso ya

karbi ledan hannunta yace "Bakomai Anty..ina kwana" ta amsa masa su Na'ima suka miqa nasu kayan back seat suma, Nafisa ce ta fara gaishesa ya amsa sannan ya kalli Na'ima, gaishe sa tayi cikin sanyin murya sai kuma tari ya dan zo mata ta fara yi kadan kada

n, dan qura mata Ido Ahmad yayi sai kuma ya kauda kansa yayi sallama dasu Anty tareda bude mota, sallama suma sukayi dasu Anty Amnah, tayi hugging dinsu tace "Sai na ganku on weekends kuma" Abban twins yana murmushi yace "Bayan sun koyi qin zuwa akai akai

yanzu" Nafisa tayi dariya tace "Uncle hanyan ne akwai gajiya wani lokaci, amma upper week zamuzo" ya gyada kai yana murmushi yace "Allah ya nuna mana" Na'ima tace "Anty in twins suka tashi ki gaishesu" gyada kai Anty Amnah tayi tana murmushi tace "Toh daug

hter, safe journey".

Da haka sukayi sallama, Na'ima tayi saurin bude back seat ta shige, Nafisa na dan dariya ta zagaya ta shiga front seat Ahmad ya tada motan suka wuce aka bar su Anty Amnah tsaye suna daga musu hannu alamun Bye.

Shiru sukayi while Ahma

d yana driving, can Nafisa tayi breaking silence din tace "Yaya baka taba zuwa gidan da muke zama a Oxford ba ko?" Ahmad ya gyada kai idonshi na kallon titi yace "Nadade ban shigo England ba Nafisa.... bedsides, ai daga baya ma naji labarin tahowanki nan k

aratun" sai Nafisa ta gyada tace "Hakane...kuma har yanzu kana living a gidanka dinnan dana sani?" Ya amsa da "Eh inanan Nafisa, zakije ne?" Tana murmushi tace "Eh Yaya zamu kai maka ziyara nida Na'ima in Sha Allah..ai zaka dade kafin ka koma ba" yadan kai

yatsantsa yana sosa girarsa kadan yace "I don't know, ina tunanin zuwa New York ne next week" Nafeesa na kallonsa ta gyada kai, ya cigaba "But ba damuwa, ku kirani time din da kuka shirya zuwan i may be around" idon Na'ima kaman ya zazzago dan hararan Naf

isa, ita ta rasa meyasa Nafisan ke son suje gidan Ahmad din all of a sudden, hada Ido tayi dashi yana kallonta ta mirror din gaban motan, tayi saurin kauda kai ta koma daf da window tana kallon titi, tana jinsu suka cigaba da hira sama sama har bacci ya da

uketa....

Shigarsu cikin town din Ahmad yayi parking gaban wani babban store yace "I'm coming" sannan ya fita ya shige ciki, bai wani dau lokaci ba ya fito da wata qaramar leda a hannu ya shiga motan suka tafi, basu kai ga isa arean su ba ya sake tsayawa

a gaban wani restaurant nan ma ya shiga bai dade ba yafito hannunsa riqe da takeouts, miqa package din yayi gurin Nafisa ta karba ta ajiye kan cinyanta, sannan ya zagaya ya shiga motan..

Bayan sun isa haka Ahmad ya tayasu diban kayan nasu suka shiga el

evator da zai kaisu floor dinsu

Shigansu apartment din Ahmad ya dan bi middle space din nasu da kallo sannan ya wuce gurin mini dining area din nasu ya ajiye su takeouts din hannusa da car key dinsa, Na'ima ce ta fara daukan kayan dake nan falon tana kaiw

a dakinta ba tareda ta kalli inda yake ba, ruwa Nafisa ta dauko daga kitchen takawo masa ya karba, yace "Ina duster?" Ta koma ta dauko sai ta fara goge masa kujeran dining din, bayan ta gama yace "Thank you" sannan ya zauna ya ciro wayansa ya fara dannawa,

fara bude takeout din Nafisa tayi yace mata "Kunada kayan shayi Nafisa" ta gyada kai tace "Eh akwai Yaya, in hada maka ne?" ya miqe yace "No, zo kibani" shigewa kitchen din sukayi tare Ahmad zai dora shayin

Itadai Na'ima tunda ta gama shigo da kayansu

daki bata sake fita ba, ta cire dankwalinta da ribbon din da ta daure timilin gashinta sannan ta nemi waje nan bakin gado ta zauna tana jin wani iri sanin presence din wanda ke cikin apartment din nasu...

Tananan zaune tana jiyo hiransa da Nafisan jefi je

fi can kuma sai ga Nafisa ta shigo ta juya ta rufe kofan sannan ta qaraso gurin Na'ima cikin qasa da murya tace "Meye hakan kuma Na'ima mutum ya kawo mu tun daga London amma kin wani shigo daki kin barsa a falo" Na'ima na kallonta tace "Ba gashi kuna hiran

ba Nafee, me zance masa in na fitan" sai Nafisa tace "A'a Na'ima, Yayanmu ne fa, sai kace wani baqo, at least show your care mana, shida ba wani dadewa zeyi ba yanzu zakiji yace zai tafi ma" sai Na'ima ta gyada kai tace "To ganinan fitowan" Nafisa ta miqe

tace "Yauwa ko kefa" sannan ta fice..Shiru Na'ima tayi sai can kuma ta dauki ribbon din nata ta sake daure gashinta ta dau veil din tamayar jikinta kafin ta fice falon, zaune ta gansa shi kadai a falon yana danna wayansa, ya dago kai suka hada ido tayi sa

urin sauqe nata idon, rasa abunda zatace masa tayi sai kawai ta nufi kitchen a tunanin ta Nafisa na can, Ahmad ya dan bi bayanta da kallo sai ya danyi qaramin murmushi baice komai ba.

Bata samu Nafisan a kitchen ba sai taga takeouts din nasu anan kan kitc

hen island, qarasowa tayi ta fara budewa da daddaya takai hannu ta dauki chip daya tafara ci, Ahmad ne ya shigo kitchen din ta dan kallesa ta dauke kai, shima wucewa yayi gurin gas ya duba tea din, sauqewa yayi ya dauki cup  ya dauraye a pampo sannan ya ju

ye shayin ya juya gurin ta nan tsaye, Yana kallonta ya miqo mata shayin yace "Here..drink this" dan kallon shayin Na'ima tayi ta kuma kallonsa taga idonsa akanta, sai ta miqa hannu ta amshi shayin takai baki, ya juya ya fita sai gashi ya dawo da ledan abun

da ya siya a store dazu, dan tari Na'ima tafara kadan, ahankali yace "Sorry" ta gyada kanta kawai, bude ledan yayi ya ciro wasu magunguna na mura da tari ya balli daya ya dan kalleta yace "Dauko ruwa" ta ajiye tea din ta dauko bottle water a fridge sannan

ya miqo mata maganin yace "Here..sha wannan" itadai Na'ima batace komai ba ta miqa hannunta, bude tafin hannunta tayi da nufin ya saka mata maganin sai taga shiru bai bata ba, dan dagowa tayi ta kalleshi sai taga kallon tafin hannun yake baya ko kifta ido,

kafin ta dauke hannun taga ya sa dayan hannunsa yana riqo tafin hannun yace "What's this?" Ji tayi kamar an jona mata electric wire sai tayi saurin kwace hannunta, ranta adan bace tace "Don't touch me" ajiye maganin yayi yana kallonta cikin kwantar da mur

ya yace "Meye wannan a hannunki? tabon menene?" tayi shiru batace komai ba ya sake qanqan da murya yace "Na'eemah" dagowa tayi ranta yana dan baci akan tamabayar da yayi mata wanda a ganinta ba abunda ya shafesa bane, sai tace "Karka sake tabani" shidai ya

na kallonta ya gyada kai alaman "Toh" sai kuma ya sake cewa "What's that on your hand Na'eemah?" ta hade rai tace "Ciwo naji..but wait, why are you even here? all of these" tayi maganan tana nuna su takeouts da shayin sannan ta dago ta kallesa tace "All th

is caring..nasan zakace don mu qannenka ne shiyasa but all of these are making me uncomfortable, you're making me uncomfortable har Nafisan ma" Tsayawa kallonta kawai Ahmad yayi ta kasa jure kallonsa ta kauda kanta ta cigaba da cewa "We are fine on ourselv

es for more than half a year now please stop making us uncomfortable".

Ahmad bai daina kallontan ba, can kuma ya gyada kai baice komai ba ya juya ya fara takawa ya fice daga kitchen din ya barta nan tsaye tana jin wani iri kuma..

Tananan tsaye taji fitan

sa daga apartment din, a wannan moment dinne kuma taji duk wani qunci ya daure mata zuciya, dana sani ya fara shiganta sai

kuma ta dago tafin hannunta tana kallon katon tabon dake cikinsa, kawai hawaye ya fara fita daga idonta tana sharewa...

Takasa motsa

wa daga inda take tsaye a kitchen din, tanata kallon shayin da magungunan tunani iri iri suna mata yawo a cikin zuciya, Nafisa ce ta shigo kitchen din tace "Sis naji kamar an fita, Yayan ne ya tafi?" Na'ima ta dago ta kalleta tace "Bansani ba nima" sai Naf

isa takai hannu tafara duba magungunan tace "Allah sarki maganin mura ashe ya siyo miki, toh ina ya tafi kuma babu sallama" nan ma Na'ima bata amsa ba, Nafisa ta juya ta fice daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login