Showing 1 words to 3000 words out of 132482 words
[10/10, 9:57 PM] Gambosy: ♥♥♥♥
*XAXXAFAN SO*
(Guba ne)
*The broken*
*heart story*
💔💔
🌟
STARS WRITERS ASSO
🌟🖊
✨
(Home of special and extraordinary writers)
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(H
ajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to: Unique In Your Love Heart Members*
*بسم الله الرحمن الرحيم و صلى الله على النبي الكريم*
📄
*1*
Durkushe take a gaban mahaifinta wanda yake xaune akan daya daga cikin kujerun dake dakin,hannunshi rike da ja
rida akwai glass fari akan fuskarshi hankalinshi akan Jaridar.. kusan minti 3 tana xaune sannan ya ajiye jaridar kan wani dan table dake gabanshi y dubeta fuskarshi babu yabo babu Fallasa ya miko hannu
"Bani takardar"
Ya fada cikin muryar bayyana takaici
.
Hannu biyu ta saka ta mika mishi a sanyaye.
Ya karba da sauri ya warware ya fara dubawa.. Wajen mintuna biyar yana nazarin takardar sannan ya dago ya kalleta,tayi sauri ta sunkuyar da kai jikinta sai bari yake. Ita kanta tasan batayi abin kirki ba aj
arabawar.. ya d'an ja fasali sannan ya fara magana ahankali
"Bansan me yake damunki ba hafsat, Allah ya gani ina iyakacin k'ok'arina kan karatunki amma kink'i ki mayar da hankali".. "Kayi haquri abba" ta fada tana hawaye. "Ba kuka nace ki min ba, na dai
fada miki ki gyara kafin in fara nuna bacin raina akanki. Ya dace a hankalce ke da kike daukar 1st position amma duba fa bata biyu ba,ba ta uku bama har ta biyar koh? To yayi kyau"
"Kayi haquri Abba" ta kuma fada.. "Hmm tashi kibani guri" tayi xumbur kama
r kan qaya take sum sum sum ta nufi kofa "zo ki tafi da takardarki"
ta dawo jiki a sanyaye ta karba ta wuce kamar wacce kwai ya fashewa aciki.
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken*
*heart s
tory*
💔💔
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to :Unique in Your Love Heart members.*
📄
*2*
Dakinta ta nufa wanda ita kadai ce mamallakiyar dakin sai 'yar qaramar qanwarta ta hudu, Mu
feedah. Ta tura qofar dakin a hankali ta shiga, ta tarar da mufeedah tana bacci kan dan qaramin gadonta, kasancewar dare ne. Nata gadon ta nufa tayi cilli da report sheet d'in a qasa ta fada kan gadon tayi shiru cikin rashin sanin tunin da ya dace tayi,ta
dafe kanta kawai da hannayenta biyu..
Wayarta ce ta shiga ruri wacce ke cikin drawer ta kayanta. A hanxarce ta mike don ta manta bata sanya wayar a shiru ba (silent). Ta nufi drawer ta bude ta dakko wayar.
Ba wata babbar waya bace Samsung ce mara memory
'yar qarama, wacce ko radio bata da shi *"DEAR"*
shine akan screen din wayar ta lumshe Idonta hadi dayin ajiyar xuciya ganin wanda ya kira wayar, ta danna 'Green' (mab'allin amsa waya)
Ahankali tace "Hello"
"Ya akayi ne 'yan matana?"
"Humm!!
Tayi aj
iyar zuciya ta nufi gadon ta dan kashingida.
Daga can akace
Me ya faru ne baby naji kinyi wani ajiyar heart? ".. Uhum?
ta dan girgiza kai..
"Bbu komai fa"
"Are u sure? "
"Yess"
"Ban yarda ba fa!
"Me yasa?"
"Haka kawai dai may be kina boyemin
wani abu ne Koh? "
"No, I just missed your sweet voice throughout today..am shine yasa.."
"Hmm dagaske kinyi kewa d'ina baby? "
Ya fada da wata irin hausarshi kamar bai K'ware a hausar ba.
Ta juya kwanciyar ta zuwa rub da ciki "ka daina mamaki"
Ok na
gode yaune ina busy baby, mum ce ta sanyani wani aiki wai don rigima ni nayi driving enta xuwa meeting,then ta wani sanya ni na xauna jiranta tun3 12pm har 4:30pm sannan muka bar wajen."
"Dear"
Na,am
Mommynsu ce kake cewa tana rigima?
Hahh Kijiki kema
baby so what's this in ba rigima ba? Ni duk ta tare min schedule ena na yau, hmm mum akwai rigima fa
"Tom shikenan!
Ta tak'aita hirar saboda bata son yana fadan irin wannan kalaman ga iyayen shi, amma shi kamar bai dauki hakan wani abu ba.
"Baby me zan
samu ne Uhum"?
Motsi taji kamar za,a bude k'ofar d'akin don haka tace "Am sorry bacci nakeji"
"Ok kin gaji dani Koh? "
Kafin tace wani abu ya katse wayar.
Daidai lokacin Mamansu ta shigo dakin
"wacce irin kwanciya ce wannan?
Tayi sauri ta tashi
zaune. Mama ta Kalli wayar dake gefenta, "waya kike koh"?
"A,a" ta fad'a a d'an tsorace tana girgiza kai.
"Yayi miki kyau, kinyi sallah ne "?
"Yanzu zanyi"
"Yayi kyau"
ta d'an Kalli wasu sashi na d'akin sannan ta juya ta fita.
Hafsa kuma ya mik'e
ta nufi band'akin dake cikin d'akin don yin alwala.
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥
️
♥
️
♥
️
♥
️
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken*
*heart story*
💔💔
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to: Unique In Your Love Heart Members*
*بسم الله الرحمن الرحيم و صلى الله على النبي الكريم*
📄
*1*
Durkushe take a gaban mahaifinta wanda yake xaune akan daya daga cikin kujerun dake dakin,hannunshi rike da jarida akwai glass far
i akan fuskarshi hankalinshi akan Jaridar.. kusan minti 3 tana xaune sannan ya ajiye jaridar kan wani dan table dake gabanshi y dubeta fuskarshi babu yabo babu Fallasa ya miko hannu
"Bani takardar"
Ya fada cikin muryar bayyana takaici.
Hannu biyu ta sa
ka ta mika mishi a sanyaye.
Ya karba da sauri ya warware ya fara dubawa.. Wajen mintuna biyar yana nazarin takardar sannan ya dago ya kalleta,tayi sauri ta sunkuyar da kai jikinta sai bari yake. Ita kanta tasan batayi abin kirki ba ajarabawar.. ya d'an j
a fasali sannan ya fara magana ahankali
"Bansan me yake damunki ba hafsat, Allah ya gani ina iyakacin k'ok'arina kan karatunki amma kink'i ki mayar da hankali".. "Kayi haquri abba" ta fada tana hawaye. "Ba kuka nace ki min ba, na dai fada miki ki gyara k
afin in fara nuna bacin raina akanki. Ya dace a hankalce ke da kike daukar 1st position amma duba fa bata biyu ba,ba ta uku bama har ta biyar koh? To yayi kyau"
"Kayi haquri Abba" ta kuma fada.. "Hmm tashi kibani guri" tayi xumbur kamar kan qaya take sum
sum sum ta nufi kofa "zo ki tafi da takardarki"
ta dawo jiki a sanyaye ta karba ta wuce kamar wacce kwai ya fashewa aciki..
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*The broken*
*heart story*
💔💔
Story and wr
iting by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to*
*Unique In Your Love Heart group Members.*
📄
*3*
*Tana* idar da sallar ta miqe ta nufi drawer ta dakko wata doguwar riga, ta bacci ta saka, ta kashe fitilar dakin,
sannan ta kwanta..
Ita kanta tasan tana buqatar ta nutsu tayi tunani,amma ji takeyi gaba daya xuciyarta a jagule ba xata iya yin wani tunani ba,duk da da akwai buqatar tayi naxarin abubuwa da dama wanda suka faru ayau din.
Misali; yaune akayi musu hutun
makaranta kuma aka basu sakamakon jarrabawarsu wanda ya dad'e tana d'aukar na d'aya ko na biyu,sai gashi ta tsallaka har mataki na biyar,wanda tun kafin araba musu result d'in da kwana biyar, tasan matsayinta. Malamin ajinsu shiya kirata yake mata fad'a a
ranar.
"Hafsat H Hamid. me yasa kike wasa da karatunki ne yanxu? Na lura gaba d'aya yanxu hankalinki baya kan karatu.ke yarinya ce yanxu kike tasowa ya dace ki bawa karatunki muhimmanci fiye da komai hakanne xai gina miki rayuwarki ta gaba."Ki cire shirm
e da shashanci sannan ki daina batawa kanki lokaci kan soyayyar banxa.."
Tayi saurin dagowa ta kalleshi..
Yayi murmushi "yes abinda yake damunki kenan, kin dauka bana gane duk halin samarin kuke ciki. Don Allah ina baki shawara amatsayina na kamar mahaif
inki ki dauka yanxu lokacine na kiyi karatu ba soyayya ba.soyayya a gurinki a yanxu bata lokaci ne, ko kina ganin ba abin kunya ne ace kin mik'a wa mahaifinki 5th position naki ba a wannan term d'in."?
Ta waro ido "Sir 5th kuma?"
Ya d'an hade rai "yes, w
a ya miki exam d'in?"
A hankali tace "Nice "
"To tashi kije ,amma kiyi tunani kada ki dinga bari yara suna miki wasa da xuciya."
"Thank you sir"
Ta fad'a a k'agauce.
Ba wai nasiharshi ce bata d'auka ba,amma ta yaya zaice wai tabar soyayya?!
*Hafsah d
a dad'i wallahi kicigaba*☺
Na biyu kuma fadan da abbansu yai mata yau d'in, wanda ya zamo na farko a tarihinta.Ita yabo kawai ta sani a al,amran karatunta, amma yau gashi Abba da kanshi ya kushe k'ok'arinta?
🤔
na uku kuma wayar da sukayi da yusuf d'axu.
Duk ciki shine taji zata iya yin tunani a kai,ba wai fad'an abba ko tunanin gyara akan karatunta wanda amma yi musu dogon hutu har na sati hud'u ayau.
Ta mik'a Hannu ta d'akko wayarta ta danna numbobinshi sannan ta kira.
wanna Karon sunan daya bayyana sh
ine 'My dream'
ba,a d'aga wayar a kira na farko, sai a Kira nabiyu wanda aka d'aga wayar sannan akayi shiru daga can b'angaren (ba,ayi magana ba)
Ita ce ma tace "Dear am sorry kaji!?
(sai yanxu yaga damar yin magana)
"For what "? ba kedai baki da time
ena ba,? "Nima Yanzun am busy doing something important than receiving your call."sai anjima kinji? "
yayi saurin katse wayar.
"Oh my God!
"Me yasa haka yusuf?
Tama rasa abinyi, ita dai tana cutuwa da wannan saurin fushi na yusuf, shi dai kome yakes
o shi za,ayi mishi.
Ta tsorata da fushinshi na yanzu, don haka ta kuma danna kiranshi har tagama ringing ba,a d'aga ba,amma karo na biyu kuma da ta sake kira yai rejecting d'in kiran..
Tayi cilli da wayar tayi shiru, wani zafi zuciyar ta ke mata.
tana t
a hura iska daga bakinta a hankali, ta fad'a a fili "Am so sorry my yusuf bana son b'acin ranka, me yasa kake fushi da nine..?
Ta kuma daukar wayar dole ne ya mishi text na ban hak'uri don tasanshi fushinshi zai iya d'aukansu wani lokaci mai tsaho, idan
batayi da gaske ba.
"U mean everything for me kasan kuma you're my only one..
I can't sleep bayan kana fushi da ni.
am sorry ba ina nufin b'ata ranka bane. d'axun mama ce ta kirani.
kayi haquri please!"
Tana gama typing d'in ta tura mishi ko k'ara ka
rantawa ba tayi ba.
kusan mintuna biyar sannan delivered message ya shigo.Tayi ajiyar xuciya bata saka ran reply ba don tasan bazaiyi ba...Amma taji sanyi aranta, sai yanxu takejin zata iya yin bacci...
*"Hmm Hafsah kenan er Soyaya*
😜
[1/11, 12:09 AM]
Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken*
*heart story*
💔💔
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to:*
*Unique In Your Love Heart Members*
📄
*4*
*Wanene yu
suf ne da Hafsah ta damu akanshi haka*??
Yusuf Aminu kyakykyawan matashin saurayi ne d'an kimanin Shekara 27 yaro ne dangata wanda ya taso cikin gata gaba da baya.
Mahaifinshi professor ne wanda yake kan ganiyar shi,bayan yayi aiki a Nigeria na en shek
aru, sannan ya sami aiki a k'asashen waje inda yake lecturing a jam'i,ar akasar 'California'.
Mutum ne shi daya zaga k'asashen duniya k'asashen ma irin na turawa, saboda haka al,adunsu sun zauna mishi sosai, hatta shigarshi yafi yin irin tasu, fiye da iri
n ta 'hausawa'.
Ya hadu da Matar shine Layla a k'asar Canada..lokacin tana qoqarin hada digirinta a fannin 'business' wato (kasuwanci).Budurwace ita y'ar kimanin shekara 27, a lokacin.
Ta taso cikin gatan mahaifiyarta,wacce Itace ke daukar duka nauyins
u ita da k'anwarta kasancewar mahaifinsu ya rasu tun bata fi shekara goma ba a duniya. Koyarwa mahaifiyar tata keyi,Wanda da wannan albashin suka dogara.sai tallafi da takan samu daga 'yan uwa da kuma zawarawanta. Bayan layla ta kammala karatune sukayi aur
en ita da professor lokacin ya dawo Nigeria daga Canada, babu jimawa kuma,suka tafi london, inda acan aka haifi yusuf daga baya kuma suka dawo California.kafin su dawo Nigeria gaba d'aya bisa umarnin mahaifiyarshi na 'ya zauna cikin danginshi kusa da ita.'
tunda shi kada'i ta mallaka.
Yusuf ya taso cikin gata domin shi kad'aine iyayenshi suka mallaka, ya samu gogewa da dabi,un turawa, domin acikinsu ya taso.
Mahaifiyarshi sam bata kwabarshi,aganinta abar yaro yayi abinda ranshi keso shine 'Yanci'.
Ta ba
ngaren ilimin addini kuwa a iya cewa yusuf bai wani abu sami abin azo a gani ba. Shima bayan dawowarsu Nigeria ne 'Dada' wato kakarshi ta wajan Mahaifinshi ta matsa suka kaishi wata islamiyya.sannan ta ta kan matsa mishi da tambayoyi akan addini kuma tana
koya mishi wadansu abubuwan.
Bayan dawowarsu Nigeria ne da shekara uku Allah Yaiwa kakar tashi rasuwa.alokacin kuma yusuf ya kammala karatunshi na secondary. Yusuf yasan yayi rashi sosai, domin duk sanda aka musu hutun makaranta wajanta yake xuwa inda ta
sanya shi dole yake xuwa makarantar dare.A wajanta yusuf ya koyi wadansu daga cikin al,adun hausawa kamar gaisuwa,da kuma yanayin shigarmu (ta hausawa) yakanyi ne saboda sha,awar hakan.
Bayan wasu watanni ne kuma aka samar mishi gurbin karatu a jami,ar C
alifornia inda zai karanta engineering.
*yusuf a sauka Lpia*
✈
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken*
*heart story*
💔💔
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to:*
*Unique In Your Love Heart Members.*
📄
*5*
*Sun* hadu da Hafsah ne da a rana wata litinin d'in watan August wacce ta kama daya ga wata. A safiyar ranar anyi ruwa sosai kafin xuwa hantsi ya dauke.
Su hafsat sun sami dama
r xuwa makaranta a ranar wanda driver (Nura) wanda babansu ya ajye musu yake kaisu makarantar a wata motarsa data d'an kwana biyu HONDA CARINA.
Uzurin daya tare driver ga barin xuwa d'aukar su yasa hafsat jan hannun k'annenta. Bashir da Zainab wa'yenda su
ke 'Secondary' wanda ya samu yaxo daukar Amira (k'anwarsu) wacce take a primary kuma ana riga tashinsu.
A jere suke a bakin titi suna jiran su tsayar da 'adaidaita sahu' su hau. Duk yunwa ta damesu, ga gajiya, ga kayan Jaka da suka goya da iyayen littatt
afai a ciki.
Hafsah taja tsaki "Mts" sannan tace Bashir niko mutafi a k'afa ne?
Bashir ya kalleta "yaya a k'afa kuma ?
Eh mana na gaji kuma yunwa nakeji"
Bashir yace nima haka wallahi,amma ai da nisa koh?
Ya Kalli Zainab yace "wai muje a k'afa"? Ta cu
no baki "A,a ni dai gsky."
Suna cikin haka wata mota taxo ta wuce ta gabansu. Har tayi gaba sai aka dawo, daidai saitin Hafsah aka tsaya aka zuge glass d'in motar wani matashin saurayi ne aciki wanda baxai wuce shekara 26 zuwa 27 ba. Ya dan lek'o yace "ki
nga wa kuke jira ne?
Hafsah ta Kalle shi ta kau da kai. Ya kuma cewa "Haba dake fa nake kika yi min shiru". Yana rufe baki Zainab tace "kaga mota muke jira, driver baixo daukar mu... Hafsah taja hannunta sukai gaba tana cewa "ina ruwanki da shi"? Ya kuma
matsowa dai dai saitin su yace "kunga kuzo in kaiku"
Ta d'an daure fuska tace "A,a mungode" sai suka had'a baki ita da bashir wajan fad'ar hakan,wanda sai alokacin shi yayi magana.A daidai lokacin kuma bashir ya tsare musu wani daidaita suka shige da sau
ri...
Shima ko baiyi wata -wata ba yaja motar shi ya bi bayan abin hawan da suka shiga .kofar d'an wani madaidaicin gida aka sauke su. Anyi wa gidan
k'awa da adon fulawoyi a gefenshi sai farin gate da ya haska gidan ga futulun kwai masu kyau wadanda suke
walwali da dare sun k'awata bangon gidan. Hafsah ta mik'a mishi kud'inshi tun kafin su fito, suna fitowa sukayi wuf suka shige ciki basu lura da wani na shirin yin parking a k'ofar gidansu ba.
A parlour suka cillar da jakunkunan su cike da yunwa da gajiya
.suna mitar yau Nura ya shanya su.
Mamansu tace "A,a ku bazakuyi wa mutum uzuri ba? Yanzu da kuka dawo mai ya sameku? Kuzo kuci abinci kuyi sallah ku tafi islamiyya."
A k'ofar gida saurayin murmushi ya saki bayan sun shige zuciyar shi cike da murmushi,
da alama gidan babu maigadi da ya mishi wata tambaya.
Ya gyada kai yaja motar shi yayi gaba.
*WASHEGARIN*
*RANAR*
*DA YAMMA*
misalin k'arfe shida na yamma dawowarsu Hafsah kenan daga islamiyya sunzo zasu shiga gida. Mufida har ta tura gate sukaj
i anyi musu horn.
Hafsah ta juya mota ce a gefensu, suka share zata shige kenan taga ya taho yana nufo ta. Chak ta tsaya yayin da k'annenta tuni sun shige gida.
*Ni ko nace Hafsah meye na tsayawa kuma*
😅
Cikin wata irin tafiya yake takowa, wacce baz
akace sauri yake ko kuma yanga ba.
Ta k'ara gyara zaman jakar dake kafadar ta. Sai lokacin taga rashin alfanun tsayawarta.
"Ashe harma ya iso wajenta..
🤔
"Sannunki Koh?
Shine ya tabbatar mata isowarshi kusa da ita.
Ad'an daburce tace "Am um yawwa"
Y
a matso daf da ita wanda sai da numfashinta yai sama ya sauka.
"Nine yusuf. Am kuma na ganku ne jiya lokacin kuna cikin uniform har nayi miki magana amma kika yi ignoring me"
Ta dan yi shiru tana wasa da yatsun hannunta. Ba wai nasiharshi kasa tuna jiyan
bane, sai