Showing 90001 words to 93000 words out of 191594 words
lafiya ba. Na san ba za ki zauna da ni a matsayin mijinki ba. Don haka ba zan tauy
e ki ba idan ba ki so na ba dole a shirye nake da na sake ki, sai ki..."
"Yaya Sadik."
"Na'am."
Ya amsa yana kallon ta.
"Mu yi addu'ar Allah ya sanya alkhairi a cikin zaman auren mu mana."
Da mamaki yake kallon ta kafin ya ce .
"Amin ya Allah."
Shir
u ne ya biyo baya, kafin ya kalle ta ya ce .
"Kin ci abinci.?"
Kai ta jinjina alamar a'a
"Okay bari na je na nema maki abun da za ki ci ko?"
"Kada ka wahalar da kanka Doctor. Bari na shiga kitchen na duba, ko tea ne zan iya sha."
Tana fadar haka ta n
ufi hanyar kitchen. Da ido ya bi ta har ta
ɓ
acewa ganinsa. Har za ta shafe kitchen din sai ta dawo ta ce .
"Ko na ha
ɗ
o da kai ne?"
Dama shi ma yunwar yake ji, don haka ya jinjina ma ta kai alamar eh.
Ta wuce ya yi murmushi yana daukar wayarsa.
Yana na
n zaune har ta zo da faranti da kofin tea guda biyu, sai bread da soyayyen ƙwai.
Kafin ta karaso ya tare ta yana karbar farantin dake hannun ta.
"Yau ga amarya a daren aurenta ta shiga kitchen ta yi girki madadin ango ya kawo ma ta tsarabar kazar amarci.
"
Dariya sosai ta yi .
"Na ciri tuta kenan tun da na ko na ce na yi daban a cikin mata."
"Ƙwarai kuwa kin yi daban, domin ke ba gamagarin mace ba ce, ke ta daban ce a cikin mata."
Dariya sosai ta .
"Kada ka yi Mani dadin baki ina bin ka bashin kazar a
marci, gobe za ka kawo mani."
Dariya ya yi yana shafa gefen fuskarsa.
"Ba damuwa yanzu ma ban yi tunanin za'a kar
ɓ
e ni a matsayin ango ba, shi ya sa na shigo haka nan ban siyo kazar ba. Amma yanzu tun da kin ce kina bi na bashi to zan biya ba shi gobe,
ke ma ki shirya biyan bashin kazar da za ki ci."
"Ban gane ba."
Ta fa
ɗ
a tana son gane inda bayanin sa ya dosa.
"Ai kazar amarci bashi ne idan kika ci sai kin biya."
Da sauri ta sa hannu ta rufe bakinta da mamaki.
"To ba zan ci kazar ba na fasa."
"Ai
baki isa ba sai kin ci."
Dariya suka yi a tare. Suka sha tea din a tare . Bayan sun gama ta kwana Kayan. Kowa ya nufi
ɗ
akinsa ya kwanta.
_Jalaluddeen_
Har ya shirya zai bar gidan da yammacin ranar sai ya nufi dakin Ma'eesha.
Da sallama ya shiga ciki
Suna zaune ita da Dada. Dada na zaune a saman sofa Ma'eesha na zaune bakin gado suna fira.
A tare suka amsa masa sallamar.
Kusa da Dada ya zauna, ba ta nuna masa komai ba, sai sai ta ƙudiri niyyar ba za ta ta
ɓ
a barin su ya kebe su biyu a daki ba. Har sai
ta warke.
A tare suka dinga fira duk da idanunsa na kam Ma'eesha.
Kiran sallar Magrib ne ya sa ga tashi ya nufi masallaci. Su kuma suka yi sallar a daki.
Sai da aka yi sallar isha'i ya dawo .
Suna zaune a falon. A tare suka ci abinci da ma su aiki su
ka girka.
Sanan suka cigaba da fira Ma'eesha na ba Dada labarin zaman da suka yi da Khalifa Makaho a Kaduna.
Dada ta jinjina ma ta suna ta dariyar rainin hankali irin na Jalaluddeen.
Dada tana kallon tashar labarai, yayin da Ma’eesha ke kallon Jalal
uddeen yana zaune a kujerar da yake zaune suna yi wa juna murmushi.
Sai wayarsa ta fara ringing.
Da farko bai
ɗ
aga ba. Amma da ya ga lambar, zuciyarsa ta buga da ƙarfi. Hannunsa ya
ɗ
an yi rawa kafin ya
ɗ
aga kiran ya yi sallama
“Assalamu alaikum.”
Mury
ar da ta fito daga
ɗ
ayan
ɓ
angaren ta kasance ƙasa-ƙasa amma cike da gaggawa.
“Officer Jalaluddeen, muna cikin matsala. An samu sauyi a operation
ɗ
in. Wanda muke nema ya motsa daga inda yake, kuma muna buƙatar ka iso cikin dare.”
Fuskar Jalaluddeen ta sau
ya gaba
ɗ
aya. Idanun Ma’eesha suka
tsaya a kansa. Ta lura yadda ya mike zaune kamar wanda aka tsikare.
“Yanzu?”
ya tambaya cikin muryar da ke nuna damuwa.
Daga cikin wayar aka ce.
“Yanzu nan take. Ba za mu iya ci gaba ba tare da kai ba. Ka san wannan
aikin kai ka fara shi.”
Jalaluddeen ya yi shiru na
ɗ
an lokaci. Sai ya lumshe idanunsa kamar mai tunani mai nauyi.
“Ina zuwa,”
Ya fa
ɗ
a a hankali, sannan ya kashe wayar.
Falon ya yi tsit.
Dada ce ta fara magana.
“Lafiya dai ko, Jalal?”
Ya
ɗ
an gyara
zamansa kafin ya amsa cikin natsuwa.
“Eh Dada… amma an kira ni daga ofis. Akwai wata matsala da ta taso a aikin da na bari tun kafin na dawo gida.”
Ma’eesha ta
ɗ
an matsa kusa da shi. Ta san akwai wani abu mai girma saboda yadda numfashinsa ke fita da sau
ri.
“Yanzu za ka tafi?”
Ta tambaya cikin damuwa.
Ya juya fuskarsa zuwa gare ta, duk da cewa yana ci gaba da taka rawar makaho.
“Ban so tafiyar ta zo a haka ba. Amma idan ban je ba, aikin zai iya lalacewa.”
Dada ta ajiye remote
ɗ
in hannunta.
“To amma
Jikana, ka fa dawo ne kwanan nan. Ba za su bari ka huta ba?”
Ya yi murmushi mai rauni.
“Dada, wasu ayyuka ba sa jiran hutu. Idan matsala ta taso, dole a tashi a magance ta kafin ta ƙara girma.”
Ya miƙa hannu ya
ɗ
auki sandarsa, sannan ya tashi tsaye a h
ankali. Ma’eesha ta lura cewa duk da tashin hankalin da yake ciki, yana ƙoƙarin ya
ɓ
oye komai.
“Ma’eesha,” ya kira sunanta a tausashe.
“Na’am.”
“Ki taimaka min ki ha
ɗ
a min ƙananan kaya. Ba zan da
ɗ
e ba in sha Allah.”
Ta gyada kai, amma zuciyarta ta cika
da fargaba. Ta bi bayansa zuwa
ɗ
akinsa
Da suka shiga
ɗ
akin, ta rufe ƙofar a hankali. Jalaluddeen ya tsaya cak na wasu daƙiƙu, sannan ya cire ya shafa fuskarsa. Wannan shi ne karo na farko da Ma’eesha ta ga tsantsar damuwa a fuskarsa.
“Me ya faru ne?”
ta tambaya cikin ra
ɗ
a.
Ya sauke numfashi.
“Aikin da na bari bai ƙare ba. Mun kusa kama wani mutum mai ha
ɗ
ari, amma yau an samu bayanin cewa yana shirin tserewa. Idan hakan ta faru, duk wahalar da muka yi za ta tafi a banza.”
“Shin tafiyar tana da ha
ɗ
ari
?”
Ya kalle ta da idanunsa na gaskiya, ba irin kallon da yake yi idan yana cikin basaja ba.
“Aikin DSS ba ya rasa ha
ɗ
ari. Amma zan yi iya ƙoƙarina in dawo lafiya.”
Maganar ta sa idanunta suka cika da hawaye.
“Ka yi min alƙawari za ka kula da kanka.”
Y
a matsa kusa da ita ya kama hannunta.
“Na yi miki alƙawari. Kuma ki tuna, babu wanda ya san komai a garinn nan. Har yanzu dole ne a ci gaba da basajar nan.”
Ta gyada kai cikin fahimta.
Suka fara ha
ɗ
a kayan cikin sauri. Ta saka masa wasu kaya, wayoyi,
takardu, da abin da zai buƙata. Shi kuma yana duba agogo lokaci-lokaci.
Bayan sun fito daga
ɗ
akin, Dada na tsaye a tsakiyar falon tana jiran sa.
“Jalal, zo nan.”
Ya ƙarasa kusa da ita.
Ta
ɗ
ora hannunta a kansa.
“Allah Ya tsare ka, Ya ba ka sa’a, Ya da
wo da kai lafiya. Duk inda za ka je, ka tuna akwai mutanen da ke maka addu’a a gida.”
Jalaluddeen ya kama hannunta ya sumbata.
“Amin Dada. Addu’arki ita ce ƙarfina.”
Dada ta ce, “Ka kira mu idan ka isa.”
“In sha Allah zan kira.”
Ma’eesha ta kawo masa
ƙ
aramin jakar tafiya. Hannayensu suka ha
ɗ
u na
ɗ
an lokaci, amma babu wanda ya ce komai saboda Dada na kallonsu.
Da ya fita daga gidan, ya yi tafiya ka
ɗ
an a hankali. Da zarar ya tabbatar babu mai kallonsa daga tagar falon, sai ya tsaya. Ya miƙe tsaye gaba
ɗ
aya, ya cire tabarau, ya riƙe sandar a hannu ba tare da amfani da ita ba.
A can ƙarshen titi wata baƙar mota ta tsaya. Fitilunta suka kashe.
Ƙ
ofar baya ta bu
ɗ
e.
Wani jami’i cikin ƙananan kaya ya ce, “Officer Jalaluddeen, mun makara.”
Jalaluddeen ya j
uya ya kalli gidan na
ɗ
an lokaci. Ya san Ma’eesha na kallon labulen
ɗ
aki tana yi masa addu’a, Dada kuma na ci gaba da ambaton sunan Allah a falon.
Sai ya shiga motar.
Motar ta ja cikin dare da sauri, yayin da fuskarsa ta koma ta jami’in DSS mai shirin ko
mawa fagen aikin da bai gama ba.
*Maman Ihsan ce*✍
🏻
[7/24, 9:07 AM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Maman Ihsan ce ✍
🏻
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
*LITTAFINA NA KUƊI NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI. NAIRA DUDU ƊA
YA NE KACAL. ZA KI TURA MANI KUƊIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2242538350 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 09065327995*
Page1
️
⃣
2
️
⃣
8
️
⃣
Motar ta ja cikin dare da sauri, yayin da fuskarsa ta koma ta Jami'an DSS mai shirin komawa fagen aikin da bai
gama ba
Daren ya ƙara yin duhu yayin da baƙar motar DSS ke ratsawa cikin titunan birnin. Babu hayaniya sai ƙarar tayoyin motar da kuma sautin walkie-talkie na jami’an da ke ciki.
Jalaluddeen ya zauna a kujerar baya, fuskarsa ta koma ta jami’in tsaro ma
i cike da ƙwarewa. Tabarau baƙin ya cire, sandar kuma ya ajiye a gefe. Duk wani yanayin makaho da yake nunawa a gida ya
ɓ
ace gaba
ɗ
aya.
Jami’in da ke gaba ya juya ka
ɗ
an.
“Sir,
MDD Barde yana jiranka a Kaduna Command. An riga an sanar masa kana hanya.”
Jalaluddeen ya
ɗ
aga kai. Ya tambaye shi
“Yaushe aka samu sabon bayanin?”
“Mintuna talatin da suka wuce. Wata majiya daga cikin mutanen Daula ta tabbatar cewa an shirya jigilar makamai daga wani rumbun a Rigachikun kafin asuba.”
Fuskar Jalaluddeen ta
ɗ
a
n
ɗ
aure, amma duk da haka ya ce .
“Rigachikun kenan… idan haka ne, ba ƙaramin motsi suka yi ba.”
Motar ta ci gaba da tafiya cikin gudu har suka isa wata tashar DSS da ke wajen gari. A nan aka sauya mota zuwa wata Toyota Land Cruiser mai lambar gwamnati
ta musamman.
Bayan kusan awa biyu da rabi suna tafiya, suka shiga cikin Kaduna. Titunan sun yi tsit saboda dare ya riga ya tsala.
A ƙofar Kaduna State Command na DSS, jami’an tsaro suka bu
ɗ
e musu gate ba tare da
ɓ
ata lokaci ba. Da motar ta tsaya, Jalalud
deen ya fito cikin ƙwarewa, ya rataye jakarsa a kafa
ɗ
a.
Wani jami’i ya yi sauri ya yi masa sallama. Tare da cewa
“Barka da zuwa, Senior Intelligence Officer.”
“Barka,”
Jalaluddeen ya amsa a taƙaice.
Aka raka shi zuwa bene na biyu, inda ofishin Deput
y Director Ibrahim S. Barde yake.
Ƙ
ofar ofishin na bu
ɗ
e. DD Barde mutum ne mai shekaru kusan hamsin da biyar, dogo, mai cikakken gashin baki da fuskar da ke nuna tsananin aiki. Yana tsaye gaban babban allon taswira lokacin da Jalaluddeen ya shiga.
Ya juy
a ya ce:
“Jalal, ka iso a kan lokaci.”
Jalaluddeen ya yi sallama cikin girmamawa ya ce .
“Sir.”
DD Barde ya nuna masa kujera tare da cewa
“Zauna. Wannan aikin ya fi yadda muka zata rikitarwa.”
Jalaluddeen ya zauna, amma hankalinsa gaba
ɗ
aya yana kan
taswirar da aka manna a bango.
Akwai hotunan wasu mutane, lambobin motoci, da layukan da ke ha
ɗ
a wurare daban-daban daga Kaduna zuwa Katsina da kuma iyakar Nijar.
DD Barde ya
ɗ
auki wani fayil mai kauri ya miƙa masa. Ya ce .
“Ka sake duba wannan.”
Jala
luddeen ya bu
ɗ
e fayil
ɗ
in. A saman takardar an rubuta:
TARGET: ALHAJI DAULA.
Hoton wani dattijo mai shekaru kusan sittin ya bayyana. Sanye yake da babbar riga da hula, fuskar nan ta attajiri mai mutunci.
DD Barde ya fara bayani.
“Sunansa na gaskiya Al
haji Nasir Daula, amma kowa ya fi saninsa da Alhaji Daula. A idon jama’a
ɗ
an kasuwa ne mai harkar shigo da kayan masarufi. Yana da kamfanoni uku a Kaduna da Kano, sannan yana yawan yin ayyukan alheri.”
Jalaluddeen ya
ɗ
aga ido.
“Amma a bayan fage?”
DD B
arde ya matsa kusa da taswirar.
“A bayan fage shi ne babban mai ha
ɗ
a hanyar safarar makamai daga yankin Sahel zuwa cikin Najeriya. Ba ya ta
ɓ
a
ɗ
aukar makami da kansa, kuma ba ya magana ta waya kai tsaye. Yana amfani da mutane uku na kusa da shi.”
Ya nuna
hotunan da ke manne a jikin taswirar sanan ya ce .
“Wannan Musa Garkuwa ne, tsohon direbansa. Shi ke kula da jigilar kaya. Wannan kuma Rabi’u Chindo, ƙwararren mai canza lambar mota. Sai wannan na ƙarshe…”
Ya dakata ka
ɗ
an.
“Usman Dan Hanya. Shi ne mai h
a
ɗ
a Daula da ƙungiyoyin da ke sayen makaman.”
Jalaluddeen ya lumshe ido yana nazari. Yana tuna tsamar da ta masu da Daula a baya,.sai sai ba fadawa kowa ba.
“Har yanzu ba mu da shaidar da za ta
ɗ
aure Daula kai tsaye a kotu, ko?”
DD Barde ya girgiza kai
tare da cewa.
“Wannan shi ne matsalar. Duk lokacin da muka kama wani daga cikin mutanensa, shaidun suna
ɓ
acewa ko kuma a tsoratar da wanda zai ba da shaida.”
Ya juyo ya kalli Jalaluddeen kai tsaye.
“Amma kai ka ta
ɓ
a shiga cikin cibiyarsu lokutan baya d
a suka wuce. Kai ne ka fi kowa sanin yadda suke aiki.”
Jalaluddeen ya tuna lokacin da ya yi watanni yana aiki a
ɓ
oye a matsayin Makaho. Daula ya ta
ɓ
a yarda da shi har ya kai shi wasu rumbum
“Sir, idan ya motsa daga rumbun Rigachikun, akwai yiwuwar zai n
ufi hanyar Birnin Gwari kafin a fitar da kayan zuwa iyaka.”
DD Barde ya yi murmushin gamsuwa.
“Daidai. Wannan shi ne abin da nake son ji daga gare ka.”
Sai ya danna wani maballi. Wani ƙaramin allo ya haska, aka nuna hoton drone na wani babban gida mai k
atanga a wajen Rigachikun ya de
“Wannan shi ne sabon rumbun da muka gano yau da yamma. Muna zargin akwai akwatunan bindigogi ƙirar AK da kuma harsasai masu yawa a ciki.”
Jalaluddeen ya matsa gaba. San
“Shin an tabbatar Daula yana ciki?”
“Ba a tabbatar
ba. Amma an ga motarsa ta shiga wajen da ƙarfe goma sha
ɗ
aya na dare.”
Daga nan DD Barde ya bu
ɗ
e wani siririn fayil ja.
“Wannan aikin yanzu an
ɗ
ora maka jagoranci.”
Jalaluddeen ya
ɗ
an yi shiru. Kafin yq de jure
“Ni, Sir?”
“Kai ne Senior Intelligence
Officer mafi kusa da bayanan Daula. Zan ba ka cikakken iko na field operation. Duk jami’an tactical da surveillance za su yi aiki ƙarƙashinka.”
Kalmar ta sauka a kansa da nauyi. Ya san wannan ba ƙaramin aiki ba ne.
“Menene manufar operation
ɗ
in?” ya tam
baya.
DD Barde ya amsa cikin ƙarfi: yana cewa
“Abu uku ne. Na farko, a gano inda makaman suke. Na biyu, a kama mutanmen da ke jigilar su. Na uku kuma, wanda ya fi muhimmanci… a kama Alhaji Daula da rai.”
“Da rai?” Jalaluddeen ya maimaita.
“Eh. Muna so
n ya yi magana. Akwai manyan sunaye a bayansa, kuma muna buƙatar sanin su.”
Sai DD Barde ya rage Murya ya de
“Jalal, ka sani wannan aikin ba kawai na Kaduna ba ne. Hedikwatar Abuja na sa ido kai tsaye. Idan muka yi nasara, za mu karya babbar hanyar saf
arar makamai a Arewa.”
Jalaluddeen ya rufe fayil
ɗ
in a hankali.
“Yaushe za mu fara motsi?”
“Karfe biyu na dare za ka yi briefing da tawagarka. Karfe uku za ku fita zuwa Rigachikun. Kuma ka sani…”
Ya
ɗ
an dakata sanan ya ce cigaba da cewa
“Daula mutum
ne mai wayo sosai. Idan ya gane kana cikin operation, zai iya amfani da tsohuwar alaƙar da kuka ta
ɓ
a yi domin ya rikitar da kai.”
Jalaluddeen ya miƙe tsaye.
“Sir, a wajen aiki babu abota.”
DD Barde ya kalle shiy ya yi na
ɗ
an lokaci, sannan ya gyada kai
cikin gamsuwa ya ce
“Wannan shi ne dalilin da ya sa na amince da kai.”
Ya miƙa masa hannu yana cewa .
“Allah Ya kiyaye ka, Senior Intelligence Officer Jalaluddeen.”
Jalaluddeen ya kar
ɓ
i hannun.
“Amin, Sir.”
Yana fita daga ofishin, wani jami’i ya miƙ
a masa sabon ID na operation da makamin hannu. Ya saka ID
ɗ
in a aljihu, ya
ɗ
auki makamin, sannan ya nufi
ɗ
akin briefing.
A zuciyarsa kuwa tunanin gida ya
ɗ
an ratsa shi.
Ya tuna da addu’ar Dada.
Ya tuna da hannun Ma’eesha cikin nasa lokacin da take ba sh
i jakar tafiya.
Sai ya
ɗ
aga kai ya mayar da hankalinsa kan aikin.
A daren nan, Jalaluddeen ba mijin Ma’eesha ba ne kawai.
Shi ne Senior Intelligence Officer Jalaluddeen, jagoran operation
ɗ
in da zai iya