Showing 111001 words to 114000 words out of 191594 words
gudu, tana ficewa daga harabar gidan cikin matsanancin gaggawa, yayin da zuciyar kowa ke cike da fargabar abin da zai biyo baya.
-
_Jalaluddeen_
Bayan an shigar da Jalaludeen
ɗ
akin
tiyata, ƙofofin ƙarfen suka rufe da ƙarfi.
Ja hasken da ke saman ƙofar ya kunna, alamar ana aikin ceton rai.
Likitoci da ƙwararrun nas-nas suka shiga aiki ba tare da
ɓ
ata lokaci ba. Kowa ya san cewa daƙiƙa guda na iya zama bambanci tsakanin rayuwa da mut
uwa.
An cire harsashin da ya shiga ƙirjinsa cikin tsananin kulawa. An kuma dakatar da zubar jinin da ke cikin jikinsa. An gyara raunukan da tarkacen ƙarfe suka yi masa tare da daure ƙasusuwan da suka samu matsala.
Aikin ya
ɗ
auki sa'o'i masu tsawo.
A ƙar
she.
Babban likitan tiyatar ya cire safar hannunsa yana sauke numfashi ya ce
"Mun yi duk abin da za mu iya."
"Yanzu komai yana hannun Allah."
An kwantar da Jalaluddeen a
ɗ
akin kulawa ta musamman (ICU).
Na'urori da dama suna manne a jikinsa.
Ana sa ran
zai
ɗ
auki kwanaki kafin ya nuna wata alamar farfa
ɗ
owa saboda irin yawan jinin da ya rasa da kuma tsananin raunukan da ya samu.
Babban likitan ya ce da sauran likitocin,
"Ku ci gaba da sanya ido sosai."
"Idan ya tsallake awa ashirin da hu
ɗ
u masu zuwa, ak
wai fatan zai rayu ."
Kowa ya amince.
Ba wanda ya yi tunanin wani abin mamaki zai faru.
A waje kuwa
Oga yana zaune a bakin ƙofar ICU.
Idanunsa sun yi jajur saboda rashin barci da damuwa.
Tun lokacin da aka shigar da Jalaluddeen bai motsa daga wajen ba.
Sai addu'a yake yi.
"Ya Allah... ka ba shi lafiya."
_Deputy Director_
A gefe guda kuma...
Deputy Director yana tsaye cikin shiru.
Fuskarsa babu wata alamar farin ciki.
A zahiri yana nuna damuwa kamar kowa.
Amma a cikin zuciyarsa.
Wani irin baƙin cik
i ne yake ci.
Ya juya gefe yana tunani yana magana shi kadai.
"Da ace bai tsira ba.Da komai ya ƙare."
Ya matse haƙoransa ciki. Bakin ciki da takaci yake magana
.
"Me ya sa sai shi ya kamata a ce Jalaluddeen ya Mutu. Wanan akwai taurin rai wallahi .
Sai
dai babu wanda ya fahimci abin da yake
ɓ
oyewa
_Jalaluddeen_
Sa'o'i ka
ɗ
an bayan an kwantar da Jalaluddeen.
Wata nas ta shiga domin duba alamomin jikinsa.
Da ta duba na'urar bugun zuciya...
Sai ta
ɗ
an tsaya.
Ta sake dubawa.
Bugun zuciyarsa ya fara daid
aituwa.
Hawan jininsa ya fara hawa.
Numfashinsa ya fara ƙarfi fiye da da.
Ta yi mamaki ta kwala wa Doctor kira .
"Doctor..."
Likita ya ƙaraso.
Ya duba sakamakon na'urar.
Sai ya
ɗ
aga gira.
"This is impossible..."
Ya fa
ɗ
a cike da mamaki .
Ya sake yin gw
aje-gwaje.
Komai yana nuna ci gaba mai kyau.
"Ku sake gwada wa."
An sake gwadawa.
Sakamakon bai canja ba.
Likitan ya kira shugaban sashen.
Da ya zo ya duba...
Sai shi ma ya yi shiru.
"Wannan ba abin da muka yi tsammani ba ne."
"Cikin irin raunukan nan.
.."
"Ba haka ake samun sauƙi ba."
Har yanzu suna cikin mamaki...
Sai Jalaluddeen ya
ɗ
an motsa yatsunsa.
Nas
ɗ
in ta zaro ido tana. Kallon hannun cike da mamaki.
"Ya motsa!"
Likita ya matsa kusa.
A hankali Jalaluddeen ya motsa kansa.
La
ɓɓ
ansa suka
ɗ
an yi
rawa.
Numfashinsa ya ƙara ƙarfi.
Sai idanunsa suka fara bu
ɗ
ewa a hankali.
Fitilar
ɗ
akin ta bugi ƙwayoyin idanunsa.
Ya lumshe su.
Sannan ya sake bu
ɗ
ewa.
Likitoci suka kalli juna.
"Wai... ya farka?"
"Ba zai yiwu ba."
Babban likitan ya matsa kusa yana
sake mamakin wanan al'amari.
"Officer Jalaluddeen
Idan kana jina
Ka matsa hannunka."
Nan take...
Jalaluddeen ya
ɗ
an matsa yatsunsa.
Kowa ya yi shiru.
Likitan ya kasa
ɓ
oye mamakinsa.
"Subhanallah..."
"Wannan abin al'ajabi ne."
"Mun yi tsammanin ko ba
yan kwanaki da yawa ne zai dawo hayyacinsa."
"Amma ga shi..."
"Har ya fara fahimtar abin da ake fa
ɗ
a masa."
Nan take aka sanar da Oga.
Da gudu ya shigo cikin farin ciki yana cewa.
"Da gaske?"
Likitan ya yi
murmushi.
"Eh."
"Ya dawo hayyacinsa."
"Ko
da yake har yanzu yana buƙatar kulawa sosai."
"Amma wannan ci gaban ya wuce duk abin da muka zata."
Oga ya matsa bakin gadon.
Ya ga Jalaluddeen ya bu
ɗ
e idanunsa yana kallonsa cikin rauni.
Hawaye suka cika idanunsa.
Ya riƙe hannunsa ya ce.
"Officer..."
"Ka ba mu tsoro.'
Jalaluddeen ya yi ƙoƙarin yin murmushi.
Sai dai ciwon jikinsa ya hana shi.
Ya motsa la
ɓɓ
ansa a hankali.
"Alhamdulillah..."
Oga ya kasa riƙe hawayensa.
"Alhamdulillah."
"Na san kai ba mai saurin mika wuya ba ne."
Duk likitocin da k
e
ɗ
akin suna kallon abin da ya faru cikin mamaki.
Ɗ
aya daga cikin Doctor ya ce,
"A cikin shekaru na na aikin likitanci
Ban ta
ɓ
a ganin irin wannan saurin samun sauƙi ba."
"Wannan bai wuce ikon Allah ba."
Duk suka amsa da.
"Hakika."
A gefe guda kuwa...
Deputy Director ya samu labarin cewa Jalaluddeen ya farfa
ɗ
o.
Fuskarsa ta sauya nan take.
"Me ka ce?"
Jami'in ya amsa da
"Sir..."
"Officer Jalaluddeen ya dawo hayyacinsa.
"Kuma likitoci sun ce jikinsa yana samun sauƙi cikin sauri fiye da yadda suka z
ata."
Na
ɗ
an lokaci ya yi tsit.
Sai ya matse hannunsa da ƙarfi.
Idanunsa suka cika da takaici.
"To
Da alama Allah bai gama da shi ba."
Ya juya ya nufi ofishinsa cikin baƙin ciki, zuciyarsa cike da fargabar cewa idan Jalaluddeen ya ƙara samun ƙarfi, wata
ƙ
ila zai tuna duk abin da ya faru... kuma wannan na iya zama farkon fallasar wata babbar gaskiya da wasu ke ƙoƙarin
ɓ
oyewa.
*Maman Ihsan ce*✍
🏻
[7/26, 7:53 AM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Maman Ihsan ce✍
️
JAJIRTSTTU WRITERS ASSOCIATION
*LITTAFINA NA KUƊI NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI.NAIRA DUBU ƊAYA NE KACAL. ZA KI TURO MANI KUƊINNTA WANAM ACCOUNT NUMBER 2242538358 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAMBAR. 09065327995.*
Page1
️
⃣
3
️
⃣
6
️
⃣
Ya juya ya nufi offish
insa cikin baƙin ciki, zuciyarsa cike da fargabar cewa , Idan Jajaluddeen ya Kara samun karfi , watakila zai tuna abun da ya faru. Kuma wanan na iya zama farkin fallasar wata ba babbar gaskiya da wasu ke kolkarin
ɓ
oyewa
_Jalaluddeen_
mintuna bayan O
ga ya fito daga
ɗ
akin ICU, ya tsaya a bakin corridor yana kallon gilashin
ɗ
akin. Ya ga Jalaluddeen kwance, jikinsa manne da na'urori, amma bugun zuciyarsa ya fara daidaituwa. Ya sauke wani dogon numfashi.
Ya san akwai wani aiki mafi wahala da ke gabansa.
S
anar da iyalansa.
Ya ciro wayarsa daga aljihu, ya
ɗ
an yi shiru na wasu daƙiƙu kafin ya nemo lambar Dad. wayar ta shiga.
"Assalamu alaikum."
Muryar Dad ta fito cikin nutsuwa ya yu wa oga sallama
"Wa alaikumus salam. Oga, lafiya?"
Oga ya yi shiru na
ɗ
an
lokaci.
Wannan shirun ka
ɗ
ai ya sa zuciyar Dad ta fara bugawa.
"Lafiya dai ko?"
Oga ya ha
ɗ
iye miyau Yana tsinun yadda zai sanar da su wanan baban ala'amari.
"Alhaji..."
"Ina buƙatar ku zo garin Kaduna asibiti yanzu."
Dad ya mike tsaye daga kujerarsa.
"
Asibiti Me ya faru?"
Oga ya lumshe idanunsa. Kafin ya nufe yana cewa.
"Officer Jalaluddeen ya samu mummunan rauni yayin wani aiki."
Wayar ta yi shiru.
Na wasu daƙiƙu.Ba a ji komai ba.
Sai muryar Dad ta fito tana rawa.
"Rauni...?"
"Yaya yake?
Oga ya y
i saurin cewa,
"Alhamdulillah. yanzu
likitoci sun sam. nasarar ceton rayuwarsa."
aya wo hayyacinsa."
"Amma har yanzu yana cikin kulawa ta musamman."
Dad ya sauke numfashi mai nauyi.
Ya dafe ƙirjinsa.yams cews
"Alhamdulillah..."
Sai kuma ya tam
baya
cikin tashin hankali,
"Harbin aka yi masa?"
Oga ya amsa wa Dad fa cewa
"Eh."
"Kuma ya samu wasu munanan raunuka."
Kuu zo yanzu. Z a mu yi muku bayani idan kun iso."
Dad ya ce,
"In sha Allahu."
Wayar ta katse.
Dad ya juya da sauri.
Mom tana zaune a fa
lo tana karatun Al-Qur'ani.
Da ta ga yanayin fuskarsa sai zuciyarta ta buga.
Ta rufe Al-Qur'anin tana kallonsa ta ce.
"Lafiya?"
Dad ya kasa magana nan take Sai ya zauna a kujera.
Ya dafe kansa. Mom ta matsa kusa
"Me ya faru?"
Da ƙyar ya iya cewa,
"An
kira ni daga asibiti."
Mom ta zaro ido.
"Asibiti?"
"Wa ya shiga?"Dad ya
ɗ
aga kansa.
"Jalaluddeen."
Al-Qur'anin da ke hannun Mom ya zame ya fa
ɗ
i kan kujera.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Ta tashi tsaye.
"Me ya same shi?"
Dad ya yi saurin cewa,
"An ce ya samu mummunan rauni yayin aiki. Amma suna cewa yana raye. Sun ce ya dawo hayyacinsa."
Mom ta fashe da kuka tana cewa.
"Ya Allah.Na ce yau zuciyata ba ta kwanta ba."
Ta kama hannun mijinta tana cewa
"Mu tafi."
"Yanzu."
Dad ya girgiza kai.
"
Eh."
Amma kafin su fita...
Sai Mom ta tsaya.
"Dada fa Da Ma'eesha?"
Shiru ya biyo baya.
Dukansu sun san...
Idan Dada ta ji labarin haka kai tsaye...
Zai iya girgiza lafiyarta.
Dad ya ce cikin tunani,
"Bari mu fara je mu ga halin da yake ciki
Idan mun ta
bbatar da komai..."
"Sai mu dawo mu sanar da su."
Mom ta girgiza kai ta ce
"Hakan ya fi."
"Ba zan so su ji labari mai firgita su ba kafin mu san komai."
Cikin gaggawa suka fita zuwa asibitin.
A gidan Jalaluddeen kuwa...
Komai yana tafiya kamar yadda ak
a saba.
Dada tana zaune a kan sallayarta tana ja da tasbihi.
Bayan kowace addu'a...
Sai ta
ɗ
aga hannuwanta sama.
"Ya Allah."
"Ka tsare mini jikana
Ka dawo da shi lafiya."
A
ɗ
aya
ɓ
angaren gidan kuma...
Ma'eesha tana cikin
ɗ
akinsu.
Tun daga safiyar ran
ar zuciyarta take cike da wani irin tashin hankali.
Ba ta san dalili ba.
Ta yi ta kiran wayar Jalaluddeen sau da dama.
Amma a kashe.
Ta zauna bakin gado tana riƙe da wayarta.
Ta yi ƙoƙarin karanta wanilittafi.Ta kasa.
Ta kunna talabijin.
Ta sake kashewa.
Z
uciyarta ta kasa samun natsuwa.
Ta dafe ƙirjinta.
"Ya Allah..."
"Me yake damna ne haka?"
A lokaci guda kuma...
Dada ta shigo
ɗ
akin.
Da ta ga Ma'eesha zaune cikin damuwa sai ta yi murmushi.
"Har yanzu bai kira ki ba ko?"
Ma'eesha ta girgiza kai ta ce.
"A'a Dada.Tun jiya ban ji muryarsa ba."
Dada ta zauna kusa da ita. Ta ita tans rarrashinta.
"Ki kwantar da hankalinki.Kin san aikin Jalaluddeen.Wani lokaci ba ya samun damar amfani da waya."
Ma'eesha ta yi murmushin ƙarfin hali.
Amma zuciyarta ta ƙi ya
rda.
Ba tare da ta sani ba...
Wasu hawaye suka gangaro kan kumatunta.
Dada ta share mata su ta ce
"In sha Allahu ba zai da
ɗ
a an ba da jimawa ba zai shigo ya ce, 'Assalamu alaikum Dada,' kamar yadda ya saba."
Ma'eesha ta lumshe idanunta tana amsawa da,
"
In sha Allah."
Sai dai a can cikin zuciyarta...
Wata murya tana ci gaba da gaya mata cewa akwai wani babban abu da ya faru.
Kuma ba da da
ɗ
ewa ba...
Ƙ
arar motar Dad da Mom za ta tsaya a harabar gidan, tare da labarin da zai sauya yanayin gidan gaba
ɗ
aya.
, Zuciyar Ma'eesha ta sake bugawa da ƙarfi.
Ba tare da ta jira komai ba ta fito da sauri zuwa harabar gidan.
Mom ce ta fara fitowa daga motar.
Da zarar Ma'eesha ta kalli fuskarta, sai gabanta ya fa
ɗ
i.
Idanun Mom sun kumbura saboda kuka.
Dad ma ya fito, fus
karsa cike da damuwa.
Dada, wacce ke tsaye a bakin ƙofa, ta yi saurin takowa.
"Me ya faru?"
"Me ya sa fuskokinku suke haka?"
Babu wanda ya iya magana.
Mom ta zo kusa da Dada, amma da zarar ta ha
ɗ
a ido da ita, sai hawayenta suka sake zubowa.
Dada ta fara
girgiza kai tana cewa.
"A'a.Akwai wani abu.Ku fa
ɗ
a min."
Dad ya sauke numfashi mai nauyi.Ya kama hannun Dada.
"Dada.Ki yi haƙuri Kafin ki ji abin da zan fa
ɗ
a.Dada ta zaro ido.
"Jalaluddeen ne ko?"
Shiru.
Shirun ya fi kowace amsa nauyi.
Dada ta dafe
ƙ
irjinta tana cewa.
"Ku yi magana mana! Me ya sami jikana?"
Dad ya ha
ɗ
iye miyau.
"Jalaluddeen ya samu mummunan rauni yayin wani aikin DSS."
Dada ta yi baya cikin mamaki
"Rauni Wane irin rauni?"
Mom ta kasa ci gaba da
ɓ
oye abin.Ta fashe da kuka yana
fadin
"An harbe shi..."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Dada ta saki wata ƙara mai ban tausayi.
"Jalaluddeen!!"
A daidai wannan lokacin...
Ma'eesha ta fito daga falo.
Da ta ji sunan Jalaluddeen, ta tsaya cak.
Ta kalli fuskar Mom.
Ta kalli Dad.
S
annan ta kalli Dada.
Zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi.
"Me ya faru?"
Babu wanda ya amsa.
Ta sake tambaya cikin firgici.
"Don Allah ku gaya min.Me ya sami mijina?"
Mom ta matsa kusa da ita.
Ta riƙe hannunta.
"Ma'eesha..."
Ki yi haƙuri. Jalaluddeen ya
samu mummunan rauni."
Kalmar ta fa
ɗ
i ne a hankali...
Amma ta bugi zuciyar Ma'eesha kamar tsawa.
Ta girgiza kai.
"A'a Karya ne.Mijina ba zai..."
Mom ta katse ta cikin kuka ta ce
"An harbe shi.Yana asibiti yanzu."
Kafin ta ƙarasa magana...
Idanun Ma'ee
sha suka juya.
Jikinta ya yi laushi.
Ta fa
ɗ
i ƙasa sumammiya.
"Ma'eesha!!"
Mom ta yi saurin tare ta.
Dada ma ta durƙusa tana kiran sunanta.
"Ma'eesha! Ki bu
ɗ
e ido!"
Dad ya
ɗ
ebo ruwa da sauri.
Ya yayyafa mata a fuska.
Bayan wasu daƙiƙu...
Ta fara motsa y
atsunta.
Sannan ta bu
ɗ
e idanunta a hankali.
Da ta tuna abin da aka fa
ɗ
a mata...
Sai ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
"Mijina Ku kai ni wurinsa!"
Ta riƙe rigar Mom tana girgiza ta.
"Don Allah! Ba zan iya zama a nan ba.ina son ganinsa."
Mom t
a rungume ta tana kuka.
"Ki kwantar da hankalinki.Likitoci sun ce yana raye Har ya dawo hayyacinsa.,
Amma Ma'eesha ta ci gaba da girgiza kai.
"Ko yana raye...Ina son na gan shi."
"Don Allah ku kai ni Kaduna.
Dada ma ta share hawaye.
Ta ce da murya mai r
awa,
"Ni ma ba zan zauna a nan ba. Ina son ganin jikana.
Ko daga bayan gilashin ICU ne."
Dad ya yi ƙoƙarin lallashinsu.
"Ku saurara.Ba tafiya ce mai sauƙi ba."
Sai Ma'eesha ta katse shi.
"Dad...Don Allah.
Kar ku hana ni.Idan kuka tafi kuka bar ni a nan.
Zuciyata za ta buga."
Dada ta amsa.
"Ni ma haka.
Ko da me zai faru..."Zan je."
Dad ya kalli Mom.
Mom ta share hawayenta.
Ta ce cikin sanyin murya,
"Ba za mu iya hana su ba."
Mu tafi tare."
Dad ya sauke numfashi.
"Shikenan.Ku shirya.
Za mu tafi Kaduna
yanzu."
Ma'eesha ba ta jira a sake gaya mata ba.
Da gudu ta shiga
ɗ
akinta.
Ta
ɗ
auko hijabinta, wayarta da ƙaramin jaka.
Ko canza kaya ba ta yi ba.
Dada ma ta shiga
ɗ
akinta.
Ta
ɗ
auki tasbihinta da mayafinta kawai.
Mintuna ka
ɗ
an bayan haka...
Su hu
ɗ
u suka f
ito.
Dad ya dubi agogo.
Ya ce,
"Idan muka bi mota za ta
ɗ
auki lokaci."
Mom ta ce,
"Mu je filin jirgin sama. Wataƙila za mu samu jirgin da zai tashi yanzu."
Nan take suka nufi filin jirgin saman Abuja.
Bayan sun isa filin jirgin sama...
Dad ya nufi waje
n sayen tikiti cikin gaggawa.
Cikin ikon Allah...
Akwai jirgin da zai tashi zuwa Kaduna cikin
ɗ
an ƙanƙanin lokaci.
Da aka sanar da su haka...
Kowa ya yi godiya.
Ba tare da
ɓ
ata lokaci ba aka kammala dukkan matakan tafiya.
Ba da jimawa ba...
Aka yi sanarwar
shiga jirgi.
Ma'eesha tana tafiya cikin hawaye.
Dada kuwa tana jan tasbihi tana maimaita,
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel.Ya Allah
Ka tsare mini ya ya Jalaluddeen."
Bayan kowa ya zauna a kujerarsa...Jirgin ya fara motsi a hankali.
Daga bisani ya ƙara
gudu a kan titin tashinsa.
Cikin daƙiƙu ka
ɗ
an...
Ya
ɗ
aga sama daga filin jirgin saman Abuja, ya kama hanyar Kaduna.A cikin jirgin kuwa...
Babu mai magana.Sai sautin kukan Ma'eesha da take ƙoƙarin dannewa, yayin da ta rungume hoton Jalaluddeen da ke cikin
wayarta.
Dada kuma idanunta a rufe suke, hawaye na zuba ba tare da tsayawa ba, hannunta na ci gaba da jan tasbihi tare da addu'a guda
ɗ
aya..
"LlYa Allah... Ka dawo mini da Jalaluddeen lafiya."
Suna cikin jirgin Dad ya kalli Mom ya ce .
"Subhanahi ban Fa
ɗ
awa Ummee
ɗ
anta na lafiya ba, bari na sauka na kira ta."
Mom ta kalle shi ta ce .
"Yakamata kam. Ni ba ta
ɗ
aukar wayata ne. Idan na kira tana fushi da ni, shi ya sa ban kira ta ba. Sadik kuma na san idan na fada ma sa zai ce sai ya zo. Kuma ga aiki a as
ibiti Ni tun da ba ba nan shi ne zai maye gurbina a asibiti."
_Mamy_
gaggawa na asibitin. Tun kafin motar ta tsaya gaba
ɗ
aya, ya bu
ɗ
e ƙofar ya fito cikin sauri.
"Doctor! Nurse! Don Allah ku taimaka!"
Muryarsa ta cika harabar Emergency Department.
Likitoci da nas-nas biyu suka fito da gadon
ɗ
aukar marasa lafiya cikin gaggawa.
"Me ya same ta?"
Jamil ya yi saurin cewa,
"Ta fa
ɗ
i ne kwatsam. Bakin ya karkace, ba ta iya magana, hannunta na