Showing 189001 words to 191594 words out of 191594 words
suka gaida Mom, sanan suka gaida Jalaludden tare da
yi ma sa barka.
Gadon da Babys
ɗ
in suke kowa ya
ɗ
auki guda
ɗ
aya.
Mom ta kalli Sadik ta ce
"Dama yanzu muke shirin wucewa gida, dan daga ita har Babys
ɗ
in ba su da wata matsala."
"Alhamdulillah."
Sadik ya furta yana kallon baby girl din da ke hannunsa
.
"Okay, Mom Amma ba za ku yi breakfast a nan ba?"
"Gara mu je gida. Amma ita mai jego ita sai ta sha saboda karfin jikinta."
"Ni na fi son mu tafi yanzu, zan yi breakfast a gida."
A tare suka juya suna kallon Ma'eeha dan ba su san cewa ya farka ba.
"Sorry Daughter, ya jikin naki?"
Mom ta tambaye ta cike da kulawa.
"Da sauki Mom."
"Ba abun da take yi maki ciwo dai ko?"
"Kina jin wani wuri na yj maku ciwo?"
Kai ta girgiza alamar a'a. Do. Haka Suka fara shirin tafiya.
Jalaludden da Sadik suka fit
a da da kayan su. Yayin da Mom ta rike dayan baby Yasmeen na rike da daya. Ma'eeha na tafiya da kanta a hankali. Sauran nurse na ta yi masu Barka da Allan ya raya.
Mom da moatarta ta tafi da Ma'eesha da Babys
ɗ
in, Sadik ya dauki matarsa a motarsa. Jalalud
den kuma ya shiga motarsa shi ka
ɗ
ai.
Suka bar harabar Asibitin.
Jalaludden ne a gabansu, kai tsaye sai ya nufi hanyar gidansa.
Bayan ya yi parking motarsa ne ya tsaya yana jiran shigowar Motar Mom Amma shiru.
Hakan ya saka shi daukar waya ya kira lamb
ar Mom.
Daga cikin sakin wayar ya ji Muryarta tana cewa .
"Ya aka yi ne angon jego?"
"Mom har yanzu ba ki iso ba lafiya?"
"Isowa zuwa ina? Bayan ga mu a gida a cikin
ɗ
aki?"
Da mamaki ya ce .
"Wani dakin kuka Mom, bayan ko gidan ba ku iso ba?"
"Way
e ya fada maka a gidanka za ta zauna? Ai ita da gidanka sai ta yi watanni biyu ko uku."
"Subhanallah!"
"Lallai haka za'ayi, yara biyu ba wasa ba, kuma haihuwar fari ce, dole tana bukatar kula da saka idanunu."
"To ko annan gidan ba sai a dinga zuwa ana
kila da ita da yaraan ba?"
"To ba za ta dawo ba sai ta yi watanni da na fa
ɗ
a, duk siyayyan kayan Babys na nata kayan ja tattaro su ka zuba a Mota ka ka
wo su nan ina jiran ka."
Yana shirin yin magana ta katse kiran wayar
Kamar ya yi kuka haka yake ji .
Bai da wani zabi. Da ya wuce yin abin da Ta saka shi.
Sai da ya cika Mota guda da kayan Babys da na shi kayan .
Bayan ya kai masu kayan ne aka jida su a dakin Mom. Nan ya tarar da Ummee ta zo ganin babys.
Ta dauki yaran cike da so da kauna. Tana dar
iya, amma ko kallon inda Ma'eesha take ba ta yi ba. Yasmeen kuwa ita ke ta hidima da Ma'eesha ita take yi mata komai. Danya kamata. An sanar da mutanen Katsina su Dada, an kira mutanen Kaduna an sanar da su. Daddy ya yi farin ciki sosai. Yake sanar wa mata
rsa Inno ta yi murna , ita ke sanar wa Jamil da Laila. Kowa ya yi farin ciki.
Inda Ma'eesha ke samun kulawar da ta dace .
Yasmeen ma kullum idan Sadik zai tafi office sa sau ya zai koma gida sai ya biyo ya dauke ta su tafi gidan .
Ana saura kwana biyu
suna jama'a suka fara cika gidan. Mutanen Katsina su Dada da Hajiya safiya da Hajiya Saratu suka suka zo . Har da Lubna da Jamila. Daga Kaduna ma ga Matar Daddy Inno ta zo tare da Laila. Sai kuma Hajiya Turai. Ƙawar Ma'eesha Nasreen ma ta zo.
*Ranar s
una*
Da sassafe aka wayi gari gidan ya cika da wani irin annashuwa da ba a iya kwatanta shi. Yaran an rada masu suna. Namijin aka saka masa Sunan Dad suna masa lakabi da Adil. Sai mace aka saka mata sunan Ummee ana yi mata lakabi da Noor.
Tun kafin has
ken rana ya gama watsuwa a sararin Abuja, gidan Jalaluddeen ya riga ya sauya salo. An kawata harabar gidan da fitilu da kayan ado masu kyau, an shimfi
ɗ
a manyan tabarma a wuraren da aka tanada domin baƙi, wani gefen kuma aka jera kujeru da rumfuna, yayin d
a maza da mata suka samu nasu
ɓ
angaren.
Hayaniyar masu girki ta cika bayan gida. Ana yanka nama, ana juyawa a manyan tukwane, ana shirya abinci iri-iri. Kamshin kayan miya da nama ya ratsa ko'ina.
A gefe guda kuma, an shirya wurin taron yara da kayan ado
masu launuka masu kyau. An rubuta manyan kalmomi a jikin bangon:
“BARKA DA ZUWA Kabir (AdIL) & Maryam (NOOR.”)
A cikin
ɗ
akin Ma'eesha kuwa, komai ya kasance cikin nutsuwa.
Ma'eesha tana zaune a kan kujera mai kyau, jikinta cikin wata doguwar atamfa m
ai kyau wadda aka yi mata kwalliya ta musamman domin ranar. Fuskar ta cika da farin ciki.
A hannunta tana riƙe da
ɗ
aya daga cikin tagwayen.
Ƙ
aramin yaron namiji yana sanye da farar kaya, ƙaramin hula a kansa, yayin da aka
ɗ
aura masa ƙaramin
ɗ
an zare a wu
yansa.
A gefen Ma'eesha kuma Noor tana kwance cikin shimfi
ɗ
arta, sanye da kayan jaririya masu kyau.
Ma'eesha ta kalli yaran biyu, murmushi ya bayyana a fuskarta.
“Alhamdulillah...” ta furta a hankali.
Ta shafa fuskar Adil da yatsanta.
“Allah ya raya k
u cikin imani da lafiya.”
Sai ta juya wajen Noor.
“Ke kuma Allah ya sa ki zama mace mai albarka, Noor.”
A wannan lokacin ƙofar
ɗ
akin ta bu
ɗ
e.
Jalaluddeen ya shigo.
Yana sanye da babbar riga mai kyau da aka yi mata aiki na musamman. A fuskarsa cike da
farin ciki da ba ya iya
ɓ
oyewa.
Da ya ga Ma'eesha da yaran, sai ya tsaya na
ɗ
an lokaci yana kallonsu.
Ma'eesha ta
ɗ
aga ido ta kalle shi.
“Ka zo?”
Jalaluddeen ya yi murmushi.
“Na zo ne in ga iyalina.”
Ya nufi wajen yaran.
Ya
ɗ
auki Adili a hankali, ya
na kallonsa kamar wanda har yanzu yake mamakin yadda Allah Ya ba shi wannan ni'imar.
“Ɗana...” ya furta.
Daga nan ya kalli Ma'eesha.
“Kin san sunan da muka yanke masa?”
Ma'eesha ta yi murmushi.
“Na sani.”
Jalaluddeen ya kalli yaron.
“Sunansa Kabeer.
”
Sai ya
ɗ
an yi shiru kafin ya ƙara da:
“Amma za mu riƙa kiransa da Adili.”
Ma'eesha ta yi murmushi.
“Allah ya raya Adil”
Jalaluddeen ya juya wajen yarinyar.
Ya
ɗ
auke Noor a hankali.
“Ke kuma sunanki Ummee.”
Ma'eesha ta
ɗ
an kalle shi.
“Ummee?”
Ya
gyada kai.
“Eh. Mun saka mata sunan Ummee, saboda matar da ya kasance uwa gare ni, wanda ta kula da ni, ta raine ni, ylta kasance tare da ni a lokacin da nake buƙatarta.”
Idanunsa suka yi wani nauyi
“Amma za mu riƙa kiranta da Noor.”
Ma'eesha ta yi
murmushi mai cike da hawaye.
“Noor...”
Ta maimaita sunan a hankali.
“Allah ya raya muku Adili da Noor.”
Jalaluddeen ya zaunar da Noor kusa da Adili.
Ya kalli yaran biyu.
“Allah ya sa ku zama haske a rayuwarmu.”
Ganin Inno ta shigo dakin ne ita da L
aila da Nasreen ya sa Jalaludden ya fita ya bar
ɗ
akin.
Bayan an idar da addu'o'i da karatun da ya dace, aka fara shagalin suna.
Gidan ya cika da mutane.
Maza suna gefe guda, mata kuma a nasu
ɓ
angaren. Ana ta taya iyaye murna, ana addu'a, ana rabon ab
inci da kayan ciye-ciye.
Masu taya Ma'eesha murna suna ta shigowa suna fitowa.
“Allah ya raya su!”
“Amin!”
“Allah ya sa su zama masu albarka!”
“Amin!”
“Allah ya ba su tsawon rai!”
“Amin!”
Ma'eesha ta zauna cikin natsuwa, yayin da ake kawo mata kyau
tuttuka iri-iri.
Akwatuna cike da kayan jarirai.
Turare.
Kayan sawa.
Kayan kwalliya.
Kudi.
Zobe.
Sarkoki.
Akwatunan kayan yara masu tsada.
Ma'eesha ta kasa boye farin cikinta. Ganin kyaututtukan da take samu.
Wata daga cikin manyan mata kawayen M
om ta zo ta rungume ta.
“Lallai kin samu tagwaye, kin samu ni'ima.”
Ma'eesha ta yi murmushi an ta ce.
“Alhamdulillah.”
Daga baya Mom
ɗ
in Jalaluddeen, ta tashi. An ta riƙe wani babban akwati da aka lullube shi da kyau.Kowa ya juya ya kalle ta.
Ta n
ufi inda yaran suke.
Ta zauna kusa da Ma'eesha.
“Wannan kyautar ba tawa ba ce kawai.”
Ta kalli Adili da Noor.
“Kyauta ce daga kakarsu.”
Ta bu
ɗ
e akwatin.
A ciki akwai manyan kayan zinariya da aka yi wa yara na musamman, tare da wasu kyaututtuka masu d
araja da kyau da tsada.
Kowa ya yi mamaki.
“Subhanallah!”
Mom ta
ɗ
auki
ɗ
aya daga cikin kayan ta nuna wa Ma'eesha.
“Wannan na Adili.”
Sai ta nuna
ɗ
ayan.
“Wannan kuma na Noor.”
Ma'eesha ta kasa magana na
ɗ
an lokaci.
“Mom...”
Mom ta riƙe hannunta.
“
Ki kar
ɓ
a. Yaran nan sun cancanci komai na alheri.”
Ta sumbaci goshin Noor.Sannan ta sumbaci Adili.
“Allah ya raya min jikoki.”
-
SCENE: KYAUTAR DAD
Bayan Mom ta zauna, Dad ma ya tashi.
Jalaluddeen ya yi murmushi.
Mom ta miƙa mata wata kyauta da ak
a shirya.
“Wannan na Aili da Noor ne. Inji Dad kansu ya ce na ba su.
"Mom wanan wahalar ta yi yawa."
“Ba wahala ba ce. Farin ciki ne.”
Ummee ma ta nufi Ma'eesha ba yabo ba fallasa, ta ba wa takwararta kyautar
ɗ
an kunnen gold da warwaro da zobe masu
kyau.
Daga baya Jalaluddeen ya nemi Ma'eesha ta zo tare da shi.
“Zo.”
Ma'eesha ta kalle shi cikin mamaki.
“Ina?”
“Ki zo kawai.”
Ya kama hannunta.
Suka fita zuwa harabar gidan.
A wajen akwai wani babban farin akwati da aka lullube shi.
Ma'eesha ta
tsaya.
“Menene wannan?”
Jalaluddeen bai amsa ba.
Sai ya
ɗ
aga hannunsa.
Ma'aikaci ya cire abin da aka rufe.
Sai ga wata sabuwar mota kyakkyawa.
Ma'eesha ta zaro ido.
“Yaya Jalal!”
Ya yi murmushi.
“Na ce dole ne ranar sunan yaranmu ta zama ranar da
ba za ki manta ba.”
Ta kalle shi cikin mamaki.
“Motar fa?”
“Ta ki ce.”
“Ni?”
“Ke.”
Ma'eesha ta kasa magana.Jalaluddeen ya matso kusa da ita.
“Kin yi min komai. Kin haifa min Adili da Noor. Kin jure abubuwa da yawa. Wannan ba zai iya biyan komai ba.
”
Idanun Ma'eesha suka cika da hawaye.
“Jalal...”
Ya goge mata hawaye.
“Ba wannan ka
ɗ
ai ba.”
Ma'eesha ta kalle shi.
“Me kuma?”
Jalaluddeen ya yi murmushi. Ya mika mata wani takardar gida.
Ta tsaya cak.
“Wannan fa?”
Jalaluddeen ya ce:
“Gidan ki
ne mallakinki na siya maki, na san zai burge ki baban gida Meta."
Ma'eesha ta rufe bakinta da hannunta.
“Ya Jalaluddeen...”
“Na saya miki shi ne domin ki samu wurin da za ki ce wannan nawa ne.”
Hawayen farin ciki suka zubo daga idonta.
Ta rungume shi
sosai. Jalaluddeen ya rungume ta.
“Na gode,” ta furta cikin kuka.
Ya amsa:
“Ni ne ya kamata in ce na gode.”
A cikin gidan kuma, shagalin ya ci gaba.
Ana ta dariya, ana rabon abinci, ana
ɗ
aukar hotuna.
A ranar, Ma'eesha ta samu kyaututtuka da yawa da
ga dangi da abokai. Dad ma kyautar gida ya bata a Kaduna .
Amma a cikin dukkan kyaututtukan da ta samu, akwai guda biyu da zuciyarta ta fi riƙe da su:
Adli da Noor.
Tagwayen da suka zama sabuwar rayuwa a gare ta. Jalaluddeen ya tsaya yana kallonsu daga
nesa.
Adili yana hannun Dad.
Noor kuma tana hannun Ummee
Ma'eesha tana tsaye kusa da mijinta.
Ya kama hannunta.
“Kin ga yadda gidanmu ya zama?”
Ma'eesha ta kalle shi.
“Ya zama cike.”
Jalaluddeen ya yi murmushi.
“Ba gidan ba kawai.”
Ya kalli yar
an.
“Rayuwarmu ce ta cika.”
Ma'eesha ta jingina kanta a kafadarsa.
Suka tsaya suna kallon Adili da Noor, yayin da hayaniyar murna da addu'o'in jama'a ke cika gidan.
Ranar suna ta zama ranar da iyalin Jalaluddeen ba za su ta
ɓ
a mantawa da ita ba.
Asili
— Kabeer.
Noor — Ummee.
Tagwaye biyu, albarkar gida
ɗ
aya.
*Bayan wata uku.*
Har lokacin Ma'eesha na gidan Mom, don Mom.ta ce sai ta je Kaduna da Katsina ta gaifa dangi sanan ta koma gidan mijinta. Haka kuwa aka yi, suka je Kaduna suka yi sati Daya
sanan suka je Katsina suka yi sati daya,.sanan suka dawo Abuja. Zuwa lokacin ana shirin bikin auren Yusuf dan wajen Ummee da ƙanwar Jalaludden wato Sadika. Saboda suna son juna ba wanda ya hadu su har suka fahimci juna.
Jalaludden ya gaji da jiran matar
sa, don haka wata rana daddare ya bar motarsa a wajen gidan mahaifinsa.
Kasancewar tambaye Ma'eesha ina Mom ke kwana ta sanar da shi cewa Mom ba kullum dare take tare da su ba. Kasancewar yaran ba sa da kuka. Idan sun kwanta daddare sai asuba suke farkaw
a. Dan haka a bangaren Dad take kwana .
Jalaludden ya yi amfani da wanan damar ya shigo ba tare da sanin kowa ba sai security.
Dakin Mom ya nufa. Zuwa lokacin Ma'eeha ta yi barci, babys na jan gadon su.
Ya karasa wajan ta, kasancewar barcin bai yi nisa
ba ta farka sakamakon jin kamshin turarensa.
Da mamaki take kallonsa yadda ya shigo cikin daren nan. Kan gadon ya haura tana kokarin sauka ya danne ta ya sakar mata nauyin jikinsa. Cikin tsoro ta ce .
"Mom za ta shigo da."
Bai saurare ta ba. Ya cigaba
da kwanciya a jikinta.
"Za ta iya shigowa da Mom ba ta kwan..."
Kafin ta rufe baki ya fara kissing nata daidai lokacin Mom ta shigo, abun da ta gani ya sa ta juya ta koma.
Hankalin Ma'eeha ya tashi ta saka masa kuka, dole ya barta ya fito daga dakin
, a falo ya ga Mom tana danna wayarta ba ta .
Kai a sunkuye ya bar gidan saboda kunya da ya ji
Sai da aka gama bikin Saddika Yusuf sannan aka mayar da Ma'eesha damunta bayan ayi mata gyaran jiki. Aka nema mata dattijuwa da yake taya ta raino.
Sidra
ta haifi
ɗ
a namiji. Wanda suka saka masu suna Ahmad.
Yasmeen ta haifi ya mace mau suna A'isha takwarar Mom ita ma an yi shagali sosai .
Nadra ta koma America tana zaune tare da mijinta. Lafiya cikin so da kauna.
Gabadaya rayuwar iyalan cikin farin c
iki da ƙaunar juna suke gudanar da ita. Sai sambarka.
*Tammat bihandulillah, littafi ya cika da godiyar Allah. Kuskuren da na yi Allah ya yafe Mani. Fatan darasin dake ciki Allah ya sa ya amfani al'ummar musulmi.*
*Godiya ta musamman gare ku yan paid g
roup na MAKAHO NE. domin ku ne Maman Ihsan, da bazar ku nake rawa. Ida ba dan ku ba da ban kai nan ba. Na gode sosai ALLAH ya saka da alheri ya bar ƙauna much love
😘😘😘
*
*Mu hadu a sabon littafina mai suna KAMA DA WANE (Bata wane)*
🤗
Maman Ihsan ce
✍
️
09065327995