Showing 132001 words to 135000 words out of 191594 words
biyu kuma na z
agaye harabar.
A bayan gidan ma ba a bar komai a sake ba.
Wasu jami'an DSS suna sintiri cikin natsuwa tsakanin bishiyoyi da shingen baya, yayin da wasu ke cikin motar sintiri da ke zagayawa a wajen gidan lokaci zuwa lokaci.
Duk wanda zai shigo ko fita sai
an tantance shi ta hanyar na'urar tantance shaidar aiki da kuma izini daga cibiyar tsaro
.
Har ma da sararin samaniyar yankin, ana sa ido ta hanyar kyamarori masu hangen nesa da aka girka a wurare daban-daban.
Gidan ya yi shiru, amma shiru ne da ke nuna c
ikakken tsaro.
Ma'eesha ta fito ta tsaya a bayansa.
Ta rungume shi daga baya, ta
ɗ
ora kanta a kafa
ɗ
arsa.
"Yanzu na fara jin zuciyata ta kwanta."
Jalaluddeen ya lumshe ido yana kallon lambun da ke gabansa.
"Ni ma."
Ya riƙe hannayenta cikin nasa.
"In sha
Allah, wannan zai zama farkon sabuwar rayuwarmu."
Ma'eesha ta yi murmushi mai cike da bege.
"Amin... Allah Ya sa wannan shi ne ƙarshen duk wata fitina."
Jalaluddeen ya kalli sararin samaniya na
ɗ
an lokaci kafin ya ce cikin nutsuwa,
"Ba mu san abin da
gobe ta ƙunsa ba... amma muddin kina tare da ni, zan fuskanci komai ba tare da tsoro ba."
Ma'eesha ta matso ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, yana shafa gefen fuskarta yana murmushi yayin da a waje jami'an DSS ke ci gaba da tsayuwa cikin shiri da cikakken
tsaro, suna tabbatar da cewa ko tsuntsu ba zai kusanci wannan gida ba tare da an sani ba. Sai dai a cikin zuciyar Jalaluddeen yana shirya yadda zai yi aikinsa na karshe akan Ta'addacin Daula da kuma ma su mara masa baya . Ya da a ransa cewa fitar da zai y
i na karshe akan daula ya zo wanda zai rusa shafe Tarihinsa ya
ɗ
auki matarsa su tafi yawon Honeymoon.
_Daula_
Daren ya yi nisa.A cikin wani tsohon rumbun ajiya da ke wajen gari, duhu ya mamaye ko'ina. Fitila guda ce kawai ke rataye a saman rufin
ɗ
akin,
tana walƙiya lokaci zuwa lokaci kamar za ta mutu.
Mutane masu
ɗ
auke da makamai suna sintiri a wajen, yayin da wasu ke tsaye bakin ƙofa suna sa ido.
A tsakiyar
ɗ
akin kuwa...
Daula ya zauna a kan wata kujera mai fa
ɗ
i, fuskarsa cike da baƙin ciki da
ɓ
acin ra
i. A gabansa akwai tebur, amma bai ta
ɓ
a abin da ke kansa ba. Yatsunsa kawai yake bugawa a saman tebur cikin alamar rashin haƙuri.
Ƙ
ofar
ɗ
akin aka bu
ɗ
e.
Deputy Director ya shigo cikin nutsuwa.
Daula bai ma ce ya zauna ba.
Sai ya ci gaba da kallonsa da idan
un da suka cika da fushi.
"Ka zo kenan?"
Deputy Director ya
ɗ
an sunkuyar da kai.
" Eh Na zo."
Shiru ya mamaye
ɗ
akin na
ɗ
an lokaci.
Sai Daula ya buga tafin hannunsa a kan tebur da ƙarfi.
"Ka gaza!"
Muryarsa ta amsa kuwwa a cikin
ɗ
akin.
"Gaba
ɗ
aya wan
nan shirin da muka yi ya rushe. Mutanenmu sun mutu, wasu an kama su, amma Jalaluddeen yana raye!"
Deputy Director ya yi shiru.
Daula ya miƙe tsaye.
Ya fara kai-komo cikin
ɗ
akin.
"Ka tabbatar mini cewa wannan karon ba zai tsira ba."
Ya juya ya nuna shi d
a yatsa ya ce.
"Amma yau ana cewa an sallame shi daga asibiti."
Deputy Director ya sauke numfashi ya ce .
"Lamarin ya sauya."
Daula ya yi wata gajeriyar dariya mai cike da takaici.
"Ya sauya?"
Ya matsa gabansa ya ce .
"Ko kana so ka gaya mini cewa m
utum
ɗ
aya ya fi ƙarfin dukkan shirye-shiryenmu?"
Deputy Director ya girgiza kai.
"A'a."
"To me ya hana ka gama aikin?"
Deputy Director ya
ɗ
an yi shiru kafin ya ce cikin natsuwa kafin ya ce.
"Saboda yanzu ba mutum ne kawai ba."
Daula ya
ɗ
aga gira.
"M
e kake nufi?"
"Yana ƙarƙashin cikakken tsaro."
Daula ya yi tsaki ya ce.
"Tsaro?"
Deputy Director ya gyada kai.
"An kai shi wani wuri da ba kowa ya san inda yake ba. Tsaro yana kewaye da shi dare da rana. Duk wani motsi ana sa ido a kansa."
Daula ya h
a
ɗ
e hannuwansa
.
"Saboda haka kana nufin ka kasa?"
Deputy Director ya kalli idanunsa ya ce .
"Ba na cewa na kasa."
"To?"
"Ina cewa wannan ba lokacin gaggawa ba ne."
Daula ya yi shiru.
Deputy Director ya ci gaba da cewa.
"Idan muka yi yunƙurin sake ka
i hari yanzu, za mu tona kanmu. Za mu rasa abin da ya rage mana."
Ya
ɗ
an dakata.
"Abin da ake buƙata yanzu shi ne haƙuri."
Daula ya yi dariyar raini.
"Haƙuri?"
Deputy Director ya gyada kai
.
"Tsaro ba ya zama iri
ɗ
aya har abada. Lokaci yana sauya koma
i."
Daula ya tsaya yana kallonsa na wasu daƙiƙu.
Fushinsa bai ragu ba.
Amma ya fahimci abin da ake nufi.Ya juya baya.
"Ka sani..."
Muryarsa ta yi ƙasa.
"Na da
ɗ
e ina aiki. Kuma abu
ɗ
aya nake ƙi."
Deputy Director ya saurara.
"Rashin cika alƙawari."
Ya
sake juyowa.
"Kada ka sa na rasa amincewa da kai."
Deputy Director ya gyara tsayuwarsa ya ce.
"Ba zan bari hakan ta faru ba."
Daula ya yi shiru na
ɗ
an lokaci, sannan ya nuna masa ƙofa.
"Ka tafi."
Deputy Director ya
ɗ
an sunkuyar da kai cikin girmamaw
a ya ce.
"Na ji."
Ba tare da ƙara magana ba, ya juya ya fita daga
ɗ
akin.
Da ƙofar ta rufe, Daula ya tsaya shi ka
ɗ
ai cikin duhun
ɗ
akin, idanunsa cike da tunani. A hankali ya matse tafin hannunsa, yana nuna yadda rashin nasarar shirin ya ci masa tuwo a ƙwa
rya, yayin da a wani
ɓ
angaren birnin, Jalaluddeen ke ci gaba da samun kariya a ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.
_Jabeer_
Jabeer har yanzu yana zaune a ƙasa a bakin corridor
ɗ
in Emergency, kansa riƙe cikin tafukan hannayensa. Hawaye na zuba ba tare d
a tsayawa ba, yayin da kalaman likitan ke ci gaba da amsa kuwwa a cikin kunnuwansa.
"Mun kasa ceton jaririn..."
"Ta yi miscarriage..."
Ya runtse idanunsa da ƙarfi. Sai dai duk da irin baƙin cikin da yake ciki, sai wata magana ta fa
ɗ
o masa.
Abban Sidra.
Da sauri ya ciro wayarsa daga aljihu. Hannunsa na rawa har ya kusa zubar da wayar. Ya nemo lambar Abba, sannan ya danna kira.
Bayan ringing biyu...
Abba ya
ɗ
aga.
"Assalamu alaikum."
Jabeer ya ha
ɗ
iye wani irin ƙwallo da ya tsaya masa a maƙoshi ya amsa
da.
"Wa alaikumus salam, Abba."
Abba ya gane muryarsa don haka ya ce.
"Jabeer? Lafiya?"
Jabeer ya rasa ta inda zai fara.
"Abba... don Allah..."
"Me ya faru?"
Muryar Abba ta sauya cikin damuwa. Jabeer ya lumshe idanunsa.
"Sidra tana asibiti."
Abba
ya yi shiru na daƙiƙa guda.
"Me kake nufi da tana asibiti?"
"Na same ta a kwance cikin bathroom... tana zubar da jini... na kawo ta Emergency."
Numfashin Abba ya tsaya.
"Subhanallah!"
Jabeer ya ci gaba da magana cikin kuka.
"Likitoci sun yi iya ƙoƙa
rinsu sun ceci rayuwarta..."
Ya kasa ci gaba.
Abba ya
ɗ
aga murya.
"Jabeer! Fa
ɗ
i abin da ya faru!"
Jabeer ya share hawayensa.
"An rasa cikin."
Shiru ya mamaye layin.
Na wasu daƙiƙu babu wanda ya iya magana.
Daga ƙarshe Abba ya ce cikin murya mai nau
yi.
"Wane asibiti kuke?"
Jabeer ya fa
ɗ
i sunan asibitin.
"In sha Allah muna zuwa yanzu."
Ya katse wayar.
A lokacin kuwa...
Abba, Umma da Ammi suna cikin motarsu suna dawowa daga ta'aziyyar
ɗ
an abokin Abba da Allah Ya yi wa rasuwa.
Tun a hanya suke t
attauna mutuwa da yadda rayuwa take.
Sai wayar Abba ta yi ƙara.
Bayan ya gama wayar, fuskarsa ta sauya gaba
ɗ
aya.
Umma ta kalle shi cikin firgici.
"Lafiya?"
Abba ya kunna motar da sauri.
"Sidra tana asibiti."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
A
mmi ta dafe ƙirji ta ce.
"Me ya same ta?"
Abba ya girgiza kai.
"Ban sani ba sosai... amma Jabeer ya ce tana Emergency."
Nan take yanayin motar ya sauya.Ba wanda ya sake magana.
Umma kuwa ta
ɗ
aga hannayenta sama tana ta addu'a.
"Ya Allah Ka kare mana
ita... Ya Allah Ka ba ta lafiya..."
Bayan mintuna ka
ɗ
an...
Motarsu ta tsaya a harabar asibitin. Pp Ko ba su tsaya da kyau ba, suka fito da sauri suka nufi Emergency.
Tun daga nesa Jabeer ya hangosu.Ya miƙe tsaye.
Da suka ƙaraso gabansa, bai iya kallon
idon Abba ba.
Kai tsaye ya durƙusa.
"Abba..."
Hawayensa suka sake zuba.
"Ka yi haƙuri..."
Abba ya
ɗ
aga shi da hannunsa.
"Yanzu ba lokacin wannan ba."Ina Sidra?"
"Tana nan?"
"Kuna cikin lokaci."
Kafin Jabeer ya amsa, ƙofar Emergency ta bu
ɗ
e.
Likitan
da ya kula da Sidra ya fito.Ya kalli mutanen da ke tsaye.
"Waye danginta?"
Abba ya matsa gaba.
"Ni ne mahaifinta."
Likitan ya gyada kai ya ce.
"Alhamdulillah... kun iso."
Abba ya tambaya cikin tashin hankali.
"Yaya take?"
Likitan ya sauke numfashi
.
"Da farko muna gode wa Allah Da ba a kawo ta cikin gaggawa ba, da akwai yiwuwar mu rasa rayuwarta saboda yawan jinin da ta rasa."
Umma ta dafe baki Tana hawaye .
Likitan ya ci gaba da cewa
"Amma Alhamdulillah, mun samu damar tsayar da zubar jinin."
"Yanzu lafiyarta tana cikin kwanciyar hankali."
Abba ya lumshe idanunsa tare da furta kalmar
"Alhamdulillah..."
Kalmar ta fito daga bakinsa cike da godiya.Sai likitan ya
ɗ
an yi shiru kafin ya ce,
"Amma..."
Zuciyar kowa ta sake bugawa.
"Mun yi iya ƙ
oƙarinmu wajen ceton cikin..."
Ya girgiza kai cikin tausayawa.
"Allah bai ƙaddara ba.An rasa jaririn."
Umma ta fashe da kuka.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..."
Ammi ta jingina da bango tana share hawaye.Abba ya runtse idanunsa. Na wasu daƙiƙu ba
i ce komai ba.
Sai daga ƙarshe ya
ɗ
aga kansa sama.
"Alhamdulillah ala kulli hal."
"Duk abin da Allah Ya ƙaddara, shi ne mafi alheri."
Likitan ya gyada kai cikin girmamawa.
"Za ku iya ganinta, amma kada ku dame ta sosai. Tana buƙatar hutawa."
Ya juya
ya koma ciki.
Abba ya juyo ya kalli Jabeer.
Jabeer kansa a ƙasa yake, hawaye na ci gaba da zuba.
Cikin murya mai cike da nadama ya ce,
"Abba... na yi kuskure..."
"Ban san yadda zan nemi gafararku ba."
Abba ya matso kusa da shi.
Ya
ɗ
ora hannunsa a ka
fa
ɗ
arsa ya ce .
"Jabeer."
Jabeer ya
ɗ
aga kansa da ƙyar.
Abba ya ce cikin nutsuwa,
"Duk abin da ya faru, Allah ne Ya ƙaddara."
Ya sauke ajiyar zuciya.
"Saboda haka... na gode maka da ka kawo ta asibitin a cikin lokaci.
Jabeer ya zaro ido cikin mamak
i.
"Abba..."
Abba ya gyada kai.
"Na gode da ka ceci rayuwar 'yata."
"Jaririn ya tafi, kuma wannan hukuncin Allah ne. Amma rayuwar Sidra ta fi komai muhimmanci."
Jabeer ya sake fashewa da kuka.
Ya sunkuyar da kansa yana jin nauyin kalaman Abban Sidra,
yayin da Umma da Ammi suka nufi
ɗ
akin da Sidra take domin su gan ta bayan ta tsallake wannan mawuyacin hali.
*Maman Ihsan ce*✍
️
[7/30, 11:00 PM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Maman Ihsan ce✍
️
JAJIRTSTTU WRITERS ASSOCIATION
*LITTAFI
NA NA KUƊI NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI.NAIRA DUBU ƊAYA NE KACAL. ZA KI TURO MANI KUƊINNTA WANAM ACCOUNT NUMBER 2242538358 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAMBAR. 09065327995.*
Page1
️
⃣
4
️
⃣
6
️
⃣
Ya sunkuyar da kansa yana jin nauyi
n kalaman Abban Sidra, yayin da Umma da Ammi suka.nufi
ɗ
akin da Sidra take domin su gan ta bayan ta tsallake wannan mawuyacin hali.
Tana barci suka same ta ana yi ma ta karin jini. Cike da tausayin ta Umma take kallon ta.
_Ma'eesha_
Bayan sallar Is
ha'i ta shiga kitchen ta ha
ɗ
a wa Jalaluddeen fruit salad. Ta fito da shi a hannunta.
Yana zaune kan kujerar ya jingina bayansa da kujerar. Idanunsa a lumshe kamar mai barci amma ba barci yake yi ba.
"Assalamu alaikum."
Bude idanunsa ya yi tare da sakar
mata murmushi kafin ha amsa sallamar da ta yi .
"Wa'alaiki salam warahmatullah."
Zama ta yi gefensa tana rike da bowl na fruit salad din .
"Na gode."
Ya ce hana kokarin karbar bowl din.
Girgiza kai ta yi tana murmushi.
"No ba zan baka ba, da kaina za
n ciyar da kaina."
Ta yi maganar tana kai masa yankan Apple a bakinsa
Sai da ta ci rabi sannan ya ce ma ya ya koshi.
Girgiza kai ta ga yi tana maraice fuska ta ce .
"Please ka shanye duka ka ga ba abinci ka ci ba."
Murmushi ya yi tare da cewa .
"
To ai ba na jin zan iya cin abincin ne?'
Dole ta bar shi haka nan, sanan ta
ɗ
auko magungunansa ta ba shi ya sha kamar yadda likita ya rubuta.
Wani kallo ta lura yana yi ma ga wanda ba ta gane kansa ba.
Idanunsa suka sauya kala zuwa ja. Wanda hakan ya
haifar wa Ma'eesha faduwar gaba. Cikin damuwa da tausaya wa ta ce.
"Sorry jikin ne ya dame ka ko?"
Kai ya girgiza mata alamar a'a.
"To ko akwai abun da kake so ne?"
Kai ya jinjina mata alamar akwai.
"To Me kake so mijina."
"Matata nake bukatar."
Da
sauri ta kalle shi don ta yi mamakin maganar tasa.
"Amma na ga ba ka warke ba , kada ka janyo ma kanka wata matsala."
"Kada ki damu da ni, zan iya."
Ya yi maganar tana janyo ta zuwa jikinsa, ita kuma ta saki baki tana kallon sa da mamakin ganin yanayins
a.
_Sidra_
Bayan wannan dare mai cike da tashin hankali, asibitin ya ci gaba da zama tamkar gida ga kowa. A hankali rayuwa ta fara komawa daidai, duk da cewa zuciyoyin wa
ɗ
anda ke ƙaunar Sidra ba su daina
ɗ
auke da ra
ɗ
a
ɗ
in rashin jaririn ba.
Likitoci
sun mayar da Sidra zuwa
ɗ
akin kwanciya na musamman bayan sun tabbatar cewa zubar jinin ya tsaya gaba
ɗ
aya. An saka mata ruwan jiki da magunguna, sannan aka umarce ta da kada ta yi wani yunƙuri na motsi sai da taimakon ma'aikatan jinya.
A cikin kwanaki bi
yun nan, Jabeer bai kusan barin asibitin ba.
Ko gida bai koma ba.A wani kujerar da ke gefen gadon Sidra yake kwana, idan barci ya
ɗ
auke shi ma na
ɗ
an lokaci ne kawai. Da zarar ya farka, idonsa kan Sidra yake.
Idan nurse ta zo ba shi ne ke miƙewa ya taima
ka ba.
Idan likita ya zo dubata, shi ne na farko wajen saurarensa.
Idan magani ya ƙare, shi ne ke garzayawa pharmacy.
Abba ya yi ta kallonsa cikin mamaki.
Sau da dama idan ya shigo
ɗ
akin da sassafe, zai tarar da Jabeer ya jingina da kujerar yana baci.
A rana ta farko bayan faruwar lamarin, Sidra ta fara bu
ɗ
e idanunta sosai.
Da farko ta ga farin silin
ɗ
akin.Sai ƙamshin magunguna.Sannan ta ji wani abu mai
ɗ
umi ya riƙe tafin hannunta.
A hankali ta juya kanta. Jabeer ne.Kansa yana kwance gefen gadonta, y
ana bacci cikin gajiya.Fuskarsa ta rame.
Idanunsa sun kumbura saboda kuka da rashin barci.
Gemunsa ya fara fitowa saboda kwanaki biyu bai kula da kansa ba.
Sidra ta da
ɗ
e tana kallonsa.
Ba ta ta
ɓ
a ganin Jabeer cikin wannan hali ba.
Kafin ta ce komai, Ja
beer ya motsa.Idanunsa suka bu
ɗ
e.
Da ya ga ita tana kallonsa, ya miƙe da sauri.
"Sidra..."
Muryarsa ta cika da farin ciki ya ce.
"Kin farka?"
Sidra ta
ɗ
an gyada kai.Ba ta da ƙarfin magana.
Jabeer ya kira nurse cikin sauri.Nurse ta zo ta duba alamunta
.Ta yi murmushi.
"Alhamdulillah... tana samun sauƙi sosai."
Da wannan labari ne aka kira Abba da Umma.
Ba su wuce mintuna ka
ɗ
an ba suka shigo
ɗ
akin.
Umma na ganin Sidra ta bu
ɗ
e idanu ta fashe da kuka.
Ta zauna bakin gadon tana shafa kanta.
"'Yata..."
Sidra ta riƙe hannunta cikin rauni ta ce.
"Umma..."
Abba kuwa ya tsaya yana kallonta kawai.
Sai ya
ɗ
aga hannuwansa sama yana cewa .
"Alhamdulillahi Rabbil Aalameen."
"Na gode Ya Allah."
A wannan rana ne kuma Papa da Mimi iyayen Jabeer suka iso as
ibitin.
Tun kafin su shiga
ɗ
akin, Mimi ta fara yi kamar za ta yi kuka
Da ta shiga ta ga Sidra kwance a gadon jinya, ta ƙarasa gare ta cikin tausayawa.
Ta kamo hannunta.
"'Yata..."
"Ki yi haƙuri. Duk abin da ya same ki ya ƙare da yardar Allah. Allah Y
a maye miki da mafi alheri."
Sidra ta yi murmushi mai rauni.
"Nagode, Mimi."
Papa kuwa ya tsaya kusa da Abba.
Ya ha
ɗ
a hannayensa cikin kunya.
"Alhaji..."
"Ban san ta inda zan fara neman afuwarku ba."
Abba ya girgiza kai tare da cewa
"Wannan lokaci
ba lokacin zargin juna ba ne."
"Mu gode wa Allah da Ya bar mana Sidra."
Papa ya sauke ajiyar zuciya.
"Hakika."
"Dukiya da yara da komai ba su kai darajar rai ba.Ya juya ya kalli
ɗ
ansa.
Jabeer kuwa yana tsaye can gefe cikin shiru.
Papa ya ce,
"Na yi
alfahari da abin da ka yi."
"Da ba ka yi gaggawar kawota ba.Ya kasa ƙarasa maganar.
Kowa ya fahimci abin da yake nufi.
Jabeer kuwa ya sunkuyar da kansa.
"Ni ne sanadin