Showing 39001 words to 42000 words out of 191594 words

Chapter 14 - MAKAHO NE COMPLETE

/>
"Dole ne."

"Kin san abin da kike fa

ɗ

a?"

"Eh."

Abbi ya girgiza kai.

"Ba zan tilasta wa

ɗ

ana zama da mata biyu ba idan ba zai iya musu adalci ba."

Ummee ta ce cikin ƙarfi,

"Zai iya."

"Wane hujja kike da it

a?"

"Ni ce na raina shi."

Abbi ya yi murmushi mai ciwo.

"Kin raina shi."

"Amma yau da kika gani ya kasa adalci tsakanin mace guda da wata kafin ma su shiga gidansa."

Ummee ta yi shiru.

Ya ci gaba.

"Yau Yasmeen ce ta ji kunya."

"Gobe kuma?"

"Wa zai tabbatar

mini cewa ba Ma'eesha ba ce za ta ji irin wannan?"

Ummee ta ce,

"Na fi damuwa da Yasmeen."

Abbi ya ce,

"Ni kuma ina damuwa da su duka."

Shiru.

Sai iska daga tagar falon.

Ummee ta sauke numfashi.

"Ba zan yarda a ce mutane sun yi mana dariya ba."

Abbi ya ce

,

"Mutane?"

Ta gyada kai.

"Eh."

"Sun riga sun fara magana."

Abbi ya

ɗ

an matsa kusa da ita.

"Ummee."

"Kada ki yanke hukunci saboda tsoron abin da mutane za su ce."

"Ki yanke shi saboda abin da Allah zai tambaye ki."

Kalmar ta sa ta yi shiru.

Ya ci gaba.

"Id

an Ma'eesha matarsa ce."

"Ba za mu iya gogewa da baki mu ce ba ita ba ce."

"Idan kuma ba matarsa ba ce."

"Sai mu tabbatar."

"Sannan mu yanke hukunci."

Ummee ta ce cikin damuwa,

"Amma Yasmeen ba za ta zauna da kishiya ba."

Abbi ya gyada kai.

"Shi ya sa zan

nemi ra'ayinta."

Ta kalle shi.

"Ra'ayinta?"

"Eh."

"Da kuma na Jalaluddeen."

Ummee ta fusata.

"Ra'ayin me kuma?"

Abbi ya ce cikin hikima,

"Aure rayuwarsu ne."

"Ba tamu ba."

"Ba za mu iya raya musu rayuwa da ƙarfinmu ba."

Ummee ta ce,

"Ni kam ba zan bari Yas

meen ta fita daga gidan nan ba."

Abbi ya tambaya a hankali,

"Ko da Jalaluddeen bai sonta?"

Ta yi saurin cewa,

"Zai so ta."

"Ta yaya?"

"Da lokaci."

Abbi ya girgiza kai.

"Soyayya ba umarni ba ce."

"Ba za ki iya tilasta zuciya ba."

Ummee ta

ɗ

an yi shiru, sann

an ta ce cikin murya mai rawa,

"Na ga yadda Yasmeen take kallonsa."

"Na san irin ƙaunar da take masa."

"Ba zan iya kallonta tana dawowa gidan iyayenta da tabon wannan abin ba."

Hawaye suka cika idanunta.

"Na yi mata alkawari."

"Na ce ba za ta ta

ɓ

a yin nada

mar shigowa gidanmu ba."

Abbi ya sauke numfashi mai nauyi.

"Ni ma ban so ta yi nadama ba."

"Amma abin da ya fi muni shi ne mu tilasta ta shiga rayuwar da za ta ci gaba da zubar mata da hawaye."

Falon ya sake yin tsit.

Ummee ta zauna a hankali.

Ta rasa abin

cewa.

Abbi ya miƙa hannu ya

ɗ

auki carbin da ke gabanta ya mayar mata.

Ya ce cikin taushin murya,

"Yanzu ba lokacin yanke hukunci da fushi ba ne."

"Lokacin neman gaskiya ne."

Ya miƙe tsaye.

"Kuma na rantse."

"Ba zan zalunci Yasmeen ba."

"Ba zan zalunci Ma'

eesha ba."

"Ba kuma zan zalunci Jalaluddeen ba."

"Sai gaskiya ta bayyana."

Ummee ta

ɗ

aga kai a hankali.

Ta san mijinta idan ya yanke hukunci cikin irin wannan natsuwar, ba abu ne mai sauƙin sauyawa ba.

Amma ita ma ta riga ta rantse a zuciyarta.

Ko da duniy

a za ta juye, ba za ta bari Yasmeen ta rasa matsayinta a gidan nan ba.

A karo na farko cikin shekaru masu yawa na aurensu, ra'ayin Abbi da na Ummee suka tsaya kishiyar juna.

_Jalaluddeen_

Jalaluddeen yana cikin motarsa.

Hannunsa riƙe da sitiyari, amma

zuciyarsa ba ta kan tuƙin da yake yi.

Wayarsa ta yi ƙara.

Ya

ɗ

aga kai ya duba screen

ɗ

in.

Sunan da ya bayyana ya sa ya

ɗ

an lumshe idanunsa.

Ummee Calling...

Ya kalli wayar na wasu daƙiƙu.

Sai daga ƙarshe ya

ɗ

auka.

"Assalamu alaikum."

Muryar Ummee ta fito

a raunane.

"Wa alaikumus salam..."

"Jalal..."

Ya amsa cikin girmamawa.

"Na'am Ummee."

Shiru ya biyo baya.

Can kuma ta ce,

"Ka yi haƙuri..."

Jalaluddeen ya runtse idanunsa.

A yau ne karo na farko da ya ji kalmar nan daga bakinta.

Sai dai duk da hakan...

Rau

nin da ke zuciyarsa bai gama warkewa ba.

Ya sauke numfashi a hankali.

"Allah Ya yafe mana baki

ɗ

aya Ummee."

Kalma ka

ɗ

ai ya fa

ɗ

a.

Amma kalmar ta sa hawayen Ummee suka zubo.

Ta fahimci cewa

ɗ

anta bai yi fushi da ita ba...

Sai dai zuciyarsa ta ji ciwon da zai



ɗ

auki lokaci kafin ya warke.

"To ina bukatar ka dawo guda yau din nan, kada ka sake kwana a wani wajen matukar ba gidan la da ka tare da iyalinka ba ne, sanan ga Yasmeen ta shiga damuwa , na yi rarrashinta amma ta ki saurare na. Don Allah ka zo ka rarra

she ta na gaji wallahi.

Shiru ya yi na wani dan lokaci.

"To Ummeen zan zo?"

"Wani lokaci?"

"Anjima."

"Ka dawo yanzu ko zan samu sukuni da nutsuwa, ga matsalar rashin ka a gida ga na Yasmeen, sai kuka take yi har da zazza

ɓ

i gabadaya ma ta kasa cin abi

nci, tun jiya ga ta can sai jinya take yi ."

"Ummeen ki lallabata ta ci abinci ya sha magani."

"Na ji iya yi na, kai ka san ta fi jin maganar ka fiye da nawa"

"Ga ni nan zuwa ."

Ya juya akalar motar zuwa gidansu.

A can cikin

ɗ

akinta kuwa, Ma'eesha na

ci gaba da kuka...

Ba ta san cewa a daidai wannan lokacin ba Jalaluddeen yana fafutukar gyara alaƙarsa da iyalinsa.

Ita kuwa zuciyarta ta ci gaba da raya mata cewa...

Wataƙila yanzu yana hannun amaryarsa... kuma ta rasa shi har abada.

*Maman Ihsan ce*✍

09065327995

[7/10, 6:57 AM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*

_Book 2_

*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*

Page1





0





5





Watakila yanzu yana hanyar Amaryarsa ... Kuma ta rasa shi har abada.

_Nadra_

Ita da Fahad sun je yi wa Umma da Abba salla

ma akan cewa yau za su tafi America.

Abba da Umma suka ta yi wa Fahad da Nadra nasihohi.

"Ku ji tsoron Allah a duk inda kuka je," Umma ta ce cikin tausasawa.

"Ku kula da junanku, ku kuma riƙa tuna da gida."

"Amin, Umma,"

Nadra ta amsa tana share ƙw

allar farin cikin rabuwa da gida.

Bayan sun gama sallama da Abba, Umma , Ammi.

Nadra ta nufi

ɗ

akin Sidra. Ta tsaya bakin ƙofa ta yi sallama.

"Assalamu alaikum."

Sidra ta

ɗ

ago kai a hankali, fuskarta babu walwala. Ta amsa sallamar ba tare da murmushi ba.

Nadra ta zauna kusa da ita.

"Yaya, na zo in yi miki sallama. Yau za mu tafi America ni da Fahad. Ki yi mana addu'a."

Sidra ta yi wani

ɗ

an murmushi mai cike da takaici.

"Addu'a? Wacce addu'a kike so in yi miki? Wadda za ta sa ki ci gaba da rayuwa da mijin d

a ba naki ba ne tun farko?"

Nadra ta sunkuyar da kanta.

"Yaya, don Allah kada ki sake bu

ɗ

e wannan maganar. Abin da ya faru ƙaddara ce."

Sidra ta yi dariya mai ciwo.

"Ƙaddara? Da ba na guduwa ranar auren, da yau ni ce zan zauna a matsayin matar Fahad, ba ke

ba."

Nadra ta ce cikin sanyin murya, "Amma yanzu ya zama mijina ne bisa aure na shari'a. Ina roƙonki, kada ki bari wannan al'amari ya raba zumuncinmu."

Sidra ta kawar da kai.

"Ki tafi ki more rayuwarki. Amma ki sani, zuciya ba ta manta cikin sauƙi."

Nadra

ta miƙe idanunta cike da hawaye. Ta kalli yayarta na

ɗ

an lokaci kafin ta juya ta fita daga

ɗ

akin.

A bakin ƙofa, Fahad yana tsaye yana jiranta. Da ya ga yanayin fuskarta, ya fahimci ba a rabu lafiya ba.

"Lafiya?" ya tambaya.

Nadra ta yi ƙoƙarin murmushi.

"

Mu tafi, jirgi ba ya jira."

Fahad ya kalli ƙofar

ɗ

akin Sidra na

ɗ

an lokaci. Ya san har yanzu zuciyarta na cike da ciwo, amma ya riga ya bi yanke shawarar rungumar ƙaddararsa. Ya kama hannun Nadra cikin nutsuwa, suka fice daga gidan domin fara sabon babin r

ayuwarsu.

fitarsu daga gidan, kowa ya raka su zuwa mota. Umma ta sake rungume Nadra tana share mata hawaye.

"Allah Ya kiyaye hanya, Ya sanya alheri a duk inda za ku je."

"Amin, Umma," Nadra ta amsa cikin rawar murya.

Abba ya dafa kafadar Fahad.

"Ka kula

da amanar da Allah Ya ba ka. Ka zama miji nagari."

"In shaa Allah, Abba."

Motar ta fara tafiya a hankali. Nadra ta juyo tana kallon gidan da ta taso a cikinsa har sai da ya

ɓ

ace daga gani. Wani irin kewa ya lullu

ɓ

e ta, amma kasancewar Fahad yana riƙe da ha

nnunta ya ba ta kwanciyar hankali.

"Kina tunani ne?" Fahad ya tambaya.

Ta yi murmushi a hankali.

"Ina tunanin gida... da kuma Yaya Sidra. Ina fata wata rana za ta yafe mana."

Fahad ya sauke numfashi.

"Ni ma haka nake fata. Ban ta

ɓ

a son abin ya kasance haka

ba."

Bayan tafiyar tasu, gidan ya yi shiru fiye da yadda aka saba.

Umma ta shiga

ɗ

akin Sidra. Ta same ta zaune gefen gado tana kallon taga.

"Sidra."

Ta

ɗ

ago kai.

"Na'am, Umma."

"Har yaushe za ki ci gaba da

ɗ

aukar wannan baƙin cikin? Abin da Allah Ya ƙadda

ra ba wanda zai iya canjawa."

Sidra ta lumshe ido.

"Na san haka, Umma. Amma duk lokacin da na ga su tare, sai na tuna da abin da na rasa."

Umma ta zauna kusa da ita.

"Ba Fahad kika rasa ba, Sidra. Kin rasa damar da kika bari ta wuce. Bambanci akwai. Kuma A

llah yana iya maye miki da abin da ya fi shi alheri."

Sidra ta yi shiru. Maganar ta shiga zuciyarta, amma ciwon bai gushe ba.

Bayan sa'o'i da dama na tafiya, jirginsu ya sauka lafiya a Amurka.

Komai ya kasance sabo a idanun Nadra. Manyan gine-gine, fitilu

masu kyalli, da yanayin da ba ta ta

ɓ

a gani ba.

Ta matso kusa da Fahad.

"Gaskiya komai daban yake."

Fahad ya yi murmushi.

"Sabo ne kawai. Da lokaci za ki saba."

Suna fitowa daga filin jirgin sama, wani saurayi ya daga hannu yana musu nuni.

"Fahad!"

Fahad ya

yi murmushi ya rungume shi.

"Yusuf! Kai ne ka zo

ɗ

auka ta?"

"Eh mana. Barkan da zuwa."

Yusuf ya juya ya kalli Nadra.

"Assalamu alaikum. Ke ce Hajiya Nadra?"

"Wa alaikumus salam," ta amsa cikin kunya.

"Barkan da zuwa. Fahad ya dade yana ba mu labarinki."

N

adra ta yi murmushi, zuciyarta ta fara samun natsuwa.

A wannan daren, bayan sun sauka a sabon gidansu, Nadra ta bu

ɗ

e akwatin kayanta. Sai ta hango wani ƙaramin kunshi da ba ta san da shi ba.

Ta bu

ɗ

e a hankali.

A ciki akwai

ɗ

an zoben azurfa da kuma wata tak

arda.

Rubutun ya kasance da hannun Sidra.

"Nadra, ban san ko zan iya yafe komai cikin gaggawa ba. Amma ke ƙanwata ce, kuma ba na son ki tafi kina tunanin ina miki ƙiyayya har abada. Ki kula da Fahad, ki kula da kanki. Ina roƙon Allah Ya ba ku zaman lafiya.

Wata rana, watakila zuciyata za ta warke."

Hawaye suka cika idanun Nadra.

Ta miƙa takardar ga Fahad.

Da ya karanta, ya yi shiru na

ɗ

an lokaci.

Daga bisani ya ce cikin taushi, "Wannan shi ne mataki na farko na sulhu."

Nadra ta

ɗ

aga kai tana murmushi cikin

hawaye.

"In shaa Allah... wata rana za mu dawo gida, mu tarar da zuciyar Yaya ta sami salama."

A can nesa, cikin

ɗ

akinta, Sidra ta

ɗ

aga hannu bayan sallar isha'i.

"Ya Allah, idan alheri ne a gare su, Ka sanya musu albarka. Idan kuma akwai alheri da Ka tana

da a gare ni, Ka ba ni haƙurin jira."

A karon farko tun bayan wannan al'amari, ta ji zuciyarta ta

ɗ

an yi sanyi, kamar ƙofar sabon fata ta fara bu

ɗ

ewa.

Bayan ha

ɗɗ

iyar motar Jalaluddeen ta yi parking a harabar gidan, injin motar ya ci gaba da ƙara na ƴan

daƙiƙu kafin ya kashe shi. Ya jingina bayansa da kujerar direba, idanunsa a lumshe tamkar wanda yake ƙoƙarin tattara ƙarfin zuciya. Numfashi ya sauke a hankali, ya shafi goshinsa da tafin hannunsa. Zuciyarsa cike take da nauyin abubuwan da suka faru cikin

kwanakin nan. Bai san ta yaya zai fuskanci Yasmeen ba, bayan labarin da ya san ya riga ya ragargaza zuciyarta.

Daga ƙarshe ya bu

ɗ

e ƙofar motar ya fito. Iskar yamma ta ka

ɗ

a gefen babbar rigarsa, amma ko ka

ɗ

an bai ji da

ɗ

inta ba. Da takunsa masu nauyi ya nufi

cikin gidan.

Da shigarsa falon, ya tarar da Ummee zaune kan kujera, tasbaha na yawo a hannunta, amma a fili take cewa hankalinta ba ya kan zikrin da take yi. Da ta

ɗ

ago ta gan shi, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

"Ka zo, Jalaluddeen."

Ya ƙarasa kusa da

ita ya gaishe ta cikin ladabi, sannan ya zauna.

"Lafiya Ummee?"

Ta girgiza kai a hankali.

"Lafiya dai... amma ba cikakkiya ba."

Ya zura mata ido.

"Me ya faru?"

Ta

ɗ

an yi shiru kafin ta ce,

"Yasmeen."

Sunan ka

ɗ

ai ya isa ya sa ƙirjinsa ya buga.

"Tun jiya da

aka sanar da ita an fasa maganar aurenku, ta shiga

ɗ

akinta. Ta ƙi fitowa. Ta ƙi cin komai. Ko ruwa sai da aka roƙe ta ta sha amma ta ƙi. Mun yi magiya, ni, Khadija, har ma da Hajiya, amma ta ce ba ta jin yunwa."

Jalaluddeen ya runtse ido na

ɗ

an lokaci.

"In

a jin tsoron lafiyarta. Ka shiga ka dubata. Wataƙila kai za ta saurara."

Bai ce komai ba. Ya miƙe a hankali ya nufi hanyar

ɗ

akinta.

...

Da ya isa ƙofar

ɗ

akin, ya tsaya na

ɗ

an lokaci. Ya

ɗ

aga hannu zai buga ƙofa, amma ya sake sauke shi. A ƙarshe ya buga sau

biyu a hankali.

Shiru.

Ya sake bugawa.

Har yanzu babu amsa.

A hankali ya mur

ɗ

a ƙofar. A bu

ɗ

e take.

Ya shiga.

Hasken

ɗ

akin a dusashe yake. Labulen tagogi a rufe suke. Yasmeen na zaune bakin gado, ta ha

ɗ

a guiwoyinta da ƙirjinta, ta jingina kanta a jikinsu.

Gashin kanta ya watse, idanunta sun kumbura saboda yawan kuka.

Da ta ji motsin ƙofar, ta

ɗ

ago kai.

Idanunsu suka ha

ɗ

u.

Na

ɗ

an lokaci ba wanda ya iya magana.

Sai kawai ta miƙe tsaye cikin sauri, ta ƙarasa gare shi da gudu.

"Jalal..."

Kafin ya ankara, ta fa

ɗ

a jikinsa ta rungume shi gam, tana fashewa da kuka mai ra

ɗ

a

ɗ

i.

"Don Allah kada ka tafi... Don Allah kada ka bar ni..."

Kalaman nata suna fita tsakanin shessheƙar kukanta.

Jalaluddeen ya tsaya cak. Hannuwansa suna gefe. Ya lumshe ido.

A hankali ya

ɗ

ora hann

unsa kan kafa

ɗ

unta, ya

ɗ

an matsar da ita daga jikinsa ba tare da tsawa ko ƙarfi ba.

"Yasmeen..."

Ta girgiza kai.

"A'a... kada ka ce komai. Ka ce min ƙarya ce. Ka ce ba gaskiya ba ne. Ka ce har yanzu za ka aure ni."

Hawayenta suka ci gaba da zuba.

"Na yi ma

farkin ranar aurenmu sau ba adadi. Na shirya komai a raina. Me ya sa aka yi min haka?"

Jalaluddeen ya sauke numfashi.

"Ki zauna, Yasmeen."

"A'a."

"Don Allah."

Ta kalle shi cikin jajayen idanunta kafin ta zauna a bakin gadon. Shi ma ya ja kujera ya zauna ku

sa da ita.

Ya miƙa mata tissue.

Ta kar

ɓ

a ba tare da ta goge hawayen ba.

"Kin ci wani abu?"

Ta girgiza kai.

"Bana jin yunwa."

"Kin sha ruwa?"

"Bana so."

"Yasmeen..."

Ta katse shi.

"Mene ne amfanin ci da sha idan duk abin da nake so ya tafi?"

Ya yi shiru na

ɗ

an lokaci.

"Rayuwa ba ta tsaya kan abu

ɗ

aya ba."

"Amma zuciyata ta tsaya a kanka."

Kalmar ta bugi zuciyarsa.

Ya kau da kai na

ɗ

an lokaci kafin ya dawo ya kalle ta.

"Ki saurare ni. Kina da muhimmanci fiye da yadda kike tunani. Ba zan so ki cutar da kanki s

aboda wannan ba. Rashin cin abinci ba zai canja abin da ya faru ba, sai dai ya cutar da lafiyarki."

Ta share hawaye.

"To me zan yi?"

"Ki kasance mai haƙuri. Ki ba Allah al'amarinki. Wani lokaci abin da muke ganin shi ne mafi alheri ba shi ne Allah Ya rubut

a mana ba."

Ta yi shiru.

Ya miƙe tsaye.

"Sai ki fara da cin wani abu."

"Bana so."

"Saboda ni."

Ta

ɗ

ago ta kalle shi.

"Saboda kai?"

"Eh. Idan kina girmama maganata, ki ci ko ka

ɗ

an."

Ta yi shiru na wasu daƙiƙu.

Daga ƙarshe ta gyada kai a hankali.

Ya fito ya

sanar da Ummee a kawo mata abinci. Cikin mintuna ka

ɗ

an aka kawo faranti da ruwa. Jalaluddeen ne ya matsa kusa da ita.

"Ko cokali uku ne kawai."

Ta

ɗ

auki cokalin da hannu mai rawa. Ta ci ka

ɗ

an, ta tsaya.

Ya yi murmushi mai taushi.

"Haka nake so."

Ta sake ci

.

Bayan ta gama ka

ɗ

an, ya miƙa mata kofin ruwa.

Ta kalle shi kafin ta kar

ɓ

a.

Saboda shi, ta

ɗ

aga kofin zuwa bakinta ta sha ruwa a hankali.

Ummee, wadda take tsaye daga bakin ƙofa tana kallonsu, ta sauke ajiyar zuciya. Wannan ne karon farko cikin kusan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login