Showing 6001 words to 9000 words out of 191594 words
ta yi kuka.
"Dan dai na rana daya meye a ciki?"
"Ummee kin mance
cewa yana da tsanani akan fita cikin shigar da na na rufe jiki ba. Kalli fa kayan lefen da ya siyo ma ni duk Abaya sun fi yawa sanan ga wasu manyan mayafai da hijabai da ya saka mun ."
"Yanzu ki mance da wannan zancen idan ya ce ki cire kayan ki kira ni z
an yi ma sa magana ."
Cikin farin ciki ta ce
"To Ummee na gode.
Nan suka dings duba kayan da suke so a kawo ma su har da sarƙa da takami komai suka ga ya ma su za ce suna buka.
"Yau yana hanya idan ya zo shi zai biya kudin kayan ko Ummee?"
"Eh shi zai
biya ma na, ba amaryarsa ba ce ?"
"Murmushi kawai Yasmeen ta yi tana addu'a Allah ya sa wanan karon ma kada a ce za'a sake
ɗ
aga bikin nan."
Yusuf ne ya shigo yana cewa
"Ummee jirgin Yaya Jalal ya sauka bari na je na
ɗ
auko shi ."
"To ka hanzarta kada
ya yi ta jira."
"Ummee ko na bi shi mu je tare mu tarbo shi ."
"Dalla gafara mara aji kawai. Daga zuwa ke za ki je tarbo shi ko? To bari ki ji ke da saka shi a idanunki sai bayan an daura auren."
*Maman Ihsan ce*✍
️
09065327995
[7/4, 9:53 PM] Antysa
lima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
*NA*
Maman Ihsan ce✍
️
*LITTAFINA NA KUƊI NE KI BIYA KUƊINKI KAFIN KI KARANTA, KADA KI KARANTA MA NI LITTAFI BA TARE DA KIN BIYA NI HAKKINA NA BA. ZA KI TURA KUƊINKI NAIRA DUBU ƊAYA 1K TA WANAN ACCOUNT NUMBER 22425
38358 ZAINAB ABDULLAHI UBA BANK. IDAN KUMA KIMA KARANTA NA BAR KI DA ALLAH.*
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪
𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐
𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍
'
𝙎
𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾
𝙄
𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪
✍
️
(
𝙅
.
𝙒
.
𝘼
)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏
️
Page8
️
⃣
9
️
⃣
Dalla gafara mara aji kawai. Daga zuwa ke za ki je tarbo shi ko? To bari ki j
i ke da saka shi a idanunki sai bayan daura auren."
Da sauri ta kalli Mahaifiyarta tana ganin ta tsawwala mata ne.
"Haba Mamy wata al'ada ce ta haramta ma ni ganinsa?"
"Ba al'ada ba ce, amma haka na tsara kuma hakan za'ayi."
*To Ummee idan shi ne ya ki
ra ni fa?"
"Na san ma ba kiran da zai yi maki, in dai Jalal ne."
"Ummee ina son magana da shi fa, za mu yi wasu tsare-tsaren."
"Ai sai ki yi kuma ."
"Cewar Ummee tana barin wajen .
"Yaya Yusuf don Allah za ka tafi da ni?"
"Ba ki ji me take cewa ba n
e? Saboda ba ta isa dake b shi ne sai kin je?"
Ya fice daga falon ya bar ta tana
ɓ
ata rai.
_Nadra_
Haka kawai ta tsinci kanta cikin yanayin damuwa sakamakon jin cewa wai da Farida za su je America.
"Idan kuma ba ki amince ba zan fa
ɗ
awa Aunty Jummai ta
yi hakuri ta sauka a wani wajen."
Murmushi ta ƙakalo tana cewa
"Akan me za ta kwana a wani wurin, bayan ga ka nan. Tana da in da ya fi wajen da kake ne? Ki kuma tana da wanda ya fi ka a ƙasar ne?"
"Amma kin san cewa ba na son abun da zai bata maki rai
ko?"
"Haka ba wani abun da zai
ɓ
ata Mani rai, yar Uwarka ce fa ƙanwarka."
"Na sani ai, amma hakan ba yana..."
"Mu bar maganar don Allah, mu yi addu'a Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi."
"Amin ya Allah."
Ya amsa yana sumbatar goshinta.
_Ma'eesha_
Bayan sun fita sun bar ma ta dakin ne ta duba breakfast da aka kawo mata ta fara shan tea.
Ta sha sosai amma ba ta ci komai ba, ko bemread ma ba ta ci ba.
Bayan mintuna ashirin sai ga Haidar ya shigo da sallama.
"Sister kin gama shiri?"
"Eh ns gama Ya
ya."
"To ki fito muna jiranki,."
Daga haka ya fita daga cikin dakin . Ba abun da ta zo da shi shi, don haka kayan sakawar da ta ta zo da su a jikinsa ba sai kayan barcin da Haidar ya ya siya mata.
Kayan ta zuba cikin jakar kayan da ya siyo ma ta sanna
n ta fito daga
ɗ
akin.
Tana fitowa ta hange su suna jiran fitowar ta.
Da sallama ta karasa wajan da suke ta sake gaishe su.
A tare suka fito zuwa wajen motarsu.
Ma'eeha da Alhaji Sulaiman suka zauna bayan motar, yayin da shi kuma Haidar yana wajen me za
man banza yayin da Kabeer ke mazaunin direba.
Da alama shi ne zai yi tuƙin motar.
Key ya yi wa motar ya ja ta suka bar wajan.
Hanayar Katsina suka kama , Ma'eesha dai duk da Alhajin Sulaiman na mata fira don ta saki jiki da shi amma ba ta saki jiki da sh
i ba.
Kasancewar Kabeer na gudu idan yana driving ne ya sa Mahaifinsa yi ma sa magana ya rage gudun da yake yi.
Cikin ikon Allah suka sauka garin Katsina lafiya.
Suka dauki hanyar gida, horn suka yi maigadin gidan ya wangale ma su gate.
Ma'eeha ta fi
to tana kallon babban gidan, kafin ta ankare sai ta ji an rungume ta gaba da baya. Sau sautin dariyar jama'ar gidan take ji.
Lubna ta rungume ta ta gaba yayin da Jamila ta rungume ta ta baya. Ga Hajiya Saratu da Hajiya Safiya suna nurmushi, Dada ta fito
ta a tafiya tana cewa ..
"Ina jikar tawa take ne?"
"Ga ta nan Dada, ai da kin zauna yanzu za ta shigo ciki ta same ki?"
Kowa ya matsa ya ba ta wuri don ta ga ma'eesha sosai .
Ganin yadda take hawaye ga jikinsa na rawa kamar zata fadi ne ya saka Ma'eesh
a saurin karasa wa inda gane t rungume ta, ita ma kukan ta saka ita ma tana rungume da wanan tsohuwar, wacce ko baya fa
ɗ
a mata ba ta san cewa ita ce ta haifi Mummy. Domin kallo
ɗ
aya Ma'eesha ta yi wa tsohuwar sai ta ga kamar an tsaga kara kamannin nasu ya
yi yawa . Sai dai wanan tsohuwar ta nuna wa Mummy shekaru.
"Allah sarki baiwar Allah ki daina kuka wahalar ki ta kare in sha Allah. Duk mai son ganin kin wulakanta rayuwar ku ta
ɗ
aidaice in sha Allah su ne rayuwar su za ta lalace. Ki yi hakuri da gwagwarm
ayar rayuwa wata rana sai labari ."
Hannunta ta kama suka shiga ciki. A falo suka zauna yayin da Dada ta bada umarni a kawo ma ta abun sha da abinci.
Ruwa kawai ta sha, tana kallon mutane. Cike da burgewa take kallonsu ganin yadda kowa na gidin ke kall
onta yana murmushi wanda babu algus a ciki.
"Ku bar ta ta shiga ciki ta yi wanka ta huta ko?"
Cwaer Kabeer yana nufar upstairs don zuwa
ɗ
akinsa.j
_Jb_
Suna zaune shi da mahaifinsa yana cin abinci .
"Meke damuwanka Son?"
". Komai ma Papa ya faru."
"Subhanallah me ya same ka da kake cewa komai ya faru ne, waye ga taba Ni. Kai yanzu ya ga
ɓ
acin raina."
"Kar ka damu b wata matsala ai ."
"Ka tabbatar ?"
"Eh Papa.".
"Yauwa kafin na tafi ƙasar Pakistan ka yi ma ni maganar cewa za ka bar kasar nan kan
a bukatar hutawa ko?"
"Eh haka ne Papa."
"To wace ƙasa da wace ƙasa za ka taf?i."
Tabbas a baya ma so tafiya papa, amma yanzu saboda kusantowar wani babban al'amari gare ni ya sa na fasa tafiyar da nake da niyyar yi ."
"Ka tabbatar?"
"Eh na tabbata."
"Na ce ba."
"Ina jin ka Papa.."
"Bani satar amsa mana."
"Na me zan baka satar amsa?"
"Na abun da yake da mahimmanci da har ya haka shalelena zuwa in da ya saka rai yana son zuwa . Domin na sha shalelena akwai bin magana ta, amma meye tasirin abun da y
a sa ka fasa zuwa waje,,?
"Papa wannan karon ba xan fa
ɗ
a Mala gaskiya ba ka yi hakuri ,domin idan na fa
ɗ
a ma ka gaskiya za ka iya tsana ta ne Papa.".
"Idan ma wani ya sanar da akwai laifin da Z ka aikata na tsane ka karya ne? Sai suka na yi maka fa
ɗ
a na
baka shawara ."
Murmushi ya yi ya san Papa sarai ba zai tsane shi ba, amma kuma baya jin zai iya sanar da mahaifinsa cewa yi wa wata yarinya fya
ɗ
e .
"Papa idan ta yi tsami z ka ji."
"Okay my son idan tq fashe zan ji tun da wannan karon ka fara
ɓ
oye
Mani komai ."
Dariya ya yana barin Papa zaune a wajen.
"Take care of yourself."
Ya fa
ɗ
a yana kallon Ɗansa cike da so da ƙauna har ya
ɓ
acewa ganinsa.
"I love you my papa."
Ya fa
ɗ
a yana dariya y shine
ɗ
akinsa
Zubewa kan makeken gadonsa ya yi yana cewa
.
"Sidra, ko ya jikin nata yake oho. Ko ina zan ganki oho. Matsalar kada na ji gidanki ne ban san me zan ce ma ki ba. Ina fatan dai abun da ya faru a tsakanin mu iyayenki ba za su gane ba. Me yiwuwa idan suka gane sai kin fuskanci tsanani na san da wann
an ."
Shafa kansa ya yi yana cusa hannu cikin sumar kansa.
"Sidra ki rabu da Sady baby ba kaunarki take yi ba, kura ce kulluñe da fatar akuya."
_Jalaluddeen_
Ko fa ya ƙaraso wajen motat Yusuf ba walwala a fuskarsa. Kallo
ɗ
aya Yusuf ya yi masa ya gan
e yana cikin damuwa .
Rungume shi ya yi yana murmushi.
",Big bro ya kake ne ya aiki?"
"Alhamdulillah."
"Ma sha Allah."
Gefen wajen me zaman banza ga bude ma sa , ya shiga ya zauna ransa babu dadi.,"
""Lafiya kuwa naga kamar kana cikin damuwa a matsay
in ka na ango me jiran gado."
Bai ma san me Yusuf yake fa
ɗ
a ba, hankalin sa na can wajan tunanin Ma'eeha.
Dafa kafadarsa ya yi sanan ya ce.
"Are you okay?"
Jingina masa kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai.
"Akwai damuwa a tattare da kai. Sai dai
ba za ka fa
ɗ
a ba."
Yusuf be sake cewa komai. A har suka isa gidan
Ya yi parking sannan ya fito ya nufi in da Jalal yake da niyyar bude masa nasa murfin motar .
Sai dai kafin ya kai gMmi Jalaluddeen ya fito
"
Sai dai bai fito daga cikin motar ba yana z
aune ciki ƙafarsa na waje.
"Sai ka huta zaka fito ne?"
Kafin ya yi magana masu aikin da suka ga dawowaraa suka dinga gaishe shi yana amsawa ta hanyar daga masu hannu. Ganin za su sake saka masa damuwa ga shi bayan son magana.
Cikin gidan ya nufa yana ta
fiya kamar baya so. Da kallo Yusuf ya b shi har ya
ɓ
acewa ganinsa.
"Allah kadai ya san meke damunsa."
Yana shiga fakon ya hangi Ummee a dinning room tana kera abici a dinning table. Ya San abincin tarbonsa ne ta yi ba komai ba.
Ummee ta bar dinning are
a ta ƙaraso falon tana murna .
"Oyoyo yaron Ummeensa ya iso."
"Ummeena na ƙaraso.,"
Ya fa
ɗ
a yana aro murmushi yana
ɗ
orawa fuskarsa.
Durƙusa wa ya yi ya gaishe ta.
Ta dafa kansa tana ma sa Barka da dawowa.
"Ka shiga ciki ka yi wanka sai ka fito ga abi
nci nam na dafa na ka su kala+kala wanda ja san cewa kana so."
"Na gode Ummeena."
Ya fa
ɗ
a yana nufar
ɗ
ajinsa m, ya san Ummee n son sa fiye da sauran yaran da ta haifa a cikinta . Koda ace ba haka ba to ita kam.ba ta nuna waata alama ba. Kowa ya san ir
in son da Ummee ke yi wa Jalaluddeen.
Ɗ
akinsa ya shiga ya zube a kan gadon yana kallon saman
ɗ
akin pop
ɗ
akin .
Kusan mintuna talatin bai motsa daga inda yake ba, har bai tashi ba.
Knocking ƙofar aka yi, wanda hakan ya sa ya dawo daga duniyar tunanin da
ya fa
ɗ
a.
Izinin shiga ya bayar. Ummee ce ta shigo . Da mamaki take kallonsa ganin yadda ya kwanta da alama ko wanka bai yi ba.
"Son lafiya kuwa ko wanka ba ka yi ba ballantana ka ci abinci."
Tashi ya yi ya nufi bathroom ta bi shi da kallo wanda ta fahim
ci akwai damuwa tare da shi.
Fitowa ta yi daga cikin
ɗ
akin tana mamaki na sauyi da ta gani a tare da yaron nata.
Falonta ta koma ta zauna tana jiran fitowarasa.
Bayan ya fito daga wanka sai ya
ɗ
auki man shafawarsa ya shafa. Sannan ya shafa turaren jiki
ya saka ƙananan kaya, tsadadden slippers
ɗ
in sa ya saka, sanan ya
ɗ
auki
ɗ
aya daga cikin wayoyinsa ya bar
ɗ
akin.
Falo ya nufa in da ya samu Ummee zaune a falo tana jiransa.
"Barka da hutawa Ummeena."
Murmushi ta yi tana cewa .
"Barka dai son ya gajiya?
"
"Ba gajiya ?"
"Alhamdulillah."
Ya zauna saman kujerar dake fuskantar Ummee .
"Ya za ka zauna a nan bayan ga abincinka can a dinning table."
Yamutse fuska ya yi kafin ya fara magana .
"Ummee ki bar abincin nan kawai na ƙoshi."
"Akan me za ka ce kan
ƙoshi bayan baka ci komai ba.?"
Zuba masa idanu ta yi sosai tana karantar yanayinsa.
"Na ga ka rame kuma akwai damuwa a tattare da kai."
"Ba wani damuwa Ummee kawai dai ina jin jikina ba da
ɗ
i ne."
"Amma ka sha magani ko kuma ka ga likit"
"A'a ban je
asibiti ba."
"To yanzu ka daure ka ci abinci tukuna, sannan sai ka tafi asibitinku sai Mom
ɗ
in ka ko Sadik su duba ka."
"Okay ."
Ya amsa ba wai don yana da niyyar zuwa ba, amma ga mamakin sa sai jim ya yi Ummee na waya da Mom.
"Hello Dr ya kike ya aik
i?"
Daga can
ɓ
angaren Mom dake zaune a office din ta ne ta amsa
"Alhamdulillah Ummeen yara ya shirye-shiryen?"
"Alhamdulillah, naku?"
"Lafiya lau, ai ke ce mai shirye-shirye. Uwar ango uwar amarya duka a gidanki suke, kin ga kuwa ke ce mai shirye-shir
ye."
"To ga yarona ya dawo bai da lafiya ."
"Wani yaron Jalaluddeen kike magana?"
"Eh shi nake nufi, Yanzu bari ya ci abinci zai zo asibiti a duba mani shi."
Murmushi kawai Mom kawai ta yi.
"Allah ya kawo shi lafiya ."
Amin ya Allah."
Sallama suka y
i ya kashe wayar.
Tashi mu tafi ."
Ta yi maganar tana kifar dinning area bai da zabi dole yabi bayanta.
Zama ya yi a daya daga cikin kujerun da ke dinning area din, za ta zuba masa abinci ya ce.
"Ummeena ba zan iya cin komai ba."
Da kyar ta matsa masa
ya
ɗ
an ci cokali biyu na abici ga ce ya ƙoshi.
"Ban ga Yasmeen ba ko ba ta gidan ne?"
Murmushi Ummee ta yi sai yanzu ta ji dad'i, sabida rashin tambayar ta ya nuna bai damu da ita ba ne, amma yanzu hakan na nuna tana ransa. Shi ma a nasa bangaren ganin
yadda Ummee ke nuna masa so bai kamata ya nuna ko in kula akan ƴarta ba. Kuma ko ba komai hakan zai sa Ummee ta yi farin ciki.
"Yasmeen ba ta gidan nan tana can ana ma ta gyaran jiki."
"Okay."
"Dama akwai abubuwa da ake bukatar ka bayar da kudi ayi."
"Ba damuwa kamar nawa kuke bukata."
"Eh to suna da yawa, ga abincin da za'a ci ba biki har kwana biyu, ga nama da abun sha da kudin gyaran jiki."
"To Ummee miliyan biyar za ta isa ?"
"Eh za ta isa Allah ya saka da alheri."
"Amin bari na tura maki."
T
ake ya tura ma ta ku
ɗ
in sannan ta ba shi umurnin zuwa wajan Mom ta duba shi. Doreban gidan ne ya kai shi asibiti.
Kai tsaye office din mahaifiyarsa ya nuna bayan ya nemi azinin ganin ta, sai da ta sallama patien da take dubawa sannan ya shiga.
Ko da ya
shiga tana waya da alama ita da Yayanta ne take waya tana cewa.
"Ba zan iya hakuri ba Yaya, zan zo gobe na ganta, ina son na ha gudan jinin ƴar uwata. Gobe in sha Allah za mu zo ni fa Jalaluddeen da Sadik da Saddiƙa. Kwana
ɗ
aya za mu yi saboda bikin Jala
l da ya gabato."
Sallama suka yi ta kashe wayar.
Gaishe da mahaifiyar tasa ya yi masa Barka da dawowa.
"Kai da za mu yi tafiya zuwa gobe shi ne ba ka da lafiya. Kodayake tun da ba kwance kake ba haka za ka daure mu je ku ga ƙanwarku da aka gano ta. Musa
mman kai da ka dade ba ka je garin ba."
*Maman Ihsan ce*✍
️
[7/4, 9:53 PM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
Page 9
️
⃣
0
️
⃣
Dafe kansa ya yi sakamakon jin furicin mahaifiyarsa. Dan shi har ga Allah baya son wa
ta tafiya a yanzu haka, ya Fi son ya ka
ɗ
aice kansa ya ji da damuwar da yake ciki.
Gada
ɗ
aya ya yi zurfi cikin tunanin halin