Showing 69001 words to 72000 words out of 191594 words

Chapter 24 - MAKAHO NE COMPLETE

cewa.

"Ni

dai ban san wani laifi da ka yi mini ba."

"Na san na yi."

"A'a."

Ta girgiza kai.

"Komai bai faru ba."

"Don Allah ki daina haka."

"Haka kuma fa?"

"Kina magana kamar ba ke ba."

Ta miƙe tsaye.

"To ai ni ce."

Ta gyara zaman hijabinta.

"Ko akwai wat

a Nadra daban?"

Fahad ya bi ta da ido.

Yana jin yadda zuciyarsa ke ƙara nauyi.

"Nadra..."

Ta juya.

"Na'am, Ambassador?"

Yadda ta kira cikakken sunansa ya sa kirjinsa ya buga.

Tun bayan aurensu ba kasafai take kiransa da "Ambassador" ba.

Yawanci sai

sau ta ce Habibiz Ko Yaya Fahad."

Amma yau...

"Ambassador."

Wannan kalma ka

ɗ

ai ta nuna masa tazarar da ta saka a tsakaninsu.

Ya matso kusa.

"Ki daina kirana haka mana."

"To yaya zan kira ka?"

"Kamar yadda kika saba."

Ta yi kamar tana tunani.

"Na

manta."

Fahad ya lumshe ido. Sanan ya kira sunanta cikim sa

"Nadra..."

"Na'am?"

"Ki yi haƙuri."

Ta yi murmushi tama cewa

"Ka yi ta maimaita haƙuri. Amma ban san dalilin ba."

"Na yi miki rashin adalci."

"Da gaske?"

"Eh."

"Yaya?"

"Na saurari Far

ida ba tare da na saurare ki ba."

A wannan karon murmushinta ya

ɓ

ace.

Sai dai ba ta nuna rauninta ba.

Ta ce cikin natsuwa,

"Hakan ra'ayinka ne."

"A'a, gaskiya ce."

"To shikenan."

"Shikenan?"

"Eh."

"Kin yafe mini?"

Ta

ɗ

an yi shiru. Sannan ta ce,

"Idan mutum bai yi laifi ba, me zai sa wani ya yafe masa?"

Fahad ya dafe goshinsa.

Wallahi ya shiga uku.

Ya fi son ta yi masa fa

ɗ

a.

Ta yi kuka.

Ko ta yi masa masifa.

Amma wannan sanyin nata...

Shi yake ƙona zuciyarsa.

Ya kama hannunta.

Ta zare cik

in ladabi.

"Don Allah."

Ta fa

ɗ

a.

"Ina son in je kitchen."

Ba ya tsaya bin takansa ba nufi kitchen.

"Nadra..."

"Ina jin ma'aikata sun gama girki. Zan duba."

Ta juya ta nufi kitchen.

Fahad ya bi bayanta kamar ƙaramin yaro.

Da ta shiga kitchen, ma'a

ikatan suka gaishe ta.

Ta amsa cikin fara'a.Ta fara duba abincin dare.

Tana tambayar .Ko salad ya kammala.Ko dessert ya shiga fridge.

Duk tana magana da kowa...

Sai dai ko kallon Fahad ba ta yi.

Shi kuwa yana tsaye a bakin ƙofa.Yana kallonta.

Yana ji

n nauyin abin da ya aikata.

Daga ƙarshe ma'aikatan suka fahimci akwai wani abu.

Suka fara neman uzuri

ɗ

aya bayan

ɗ

aya.

Kitchen

ɗ

in ya rage su biyu.Fahad ya matso.

"Nadra."

Ta ci gaba da zuba miya cikin wani ƙaramin kwano.

"Na'am?"

"Ki dube ni mana."

Ta

ɗ

aga ido na daƙiƙa

ɗ

aya.

Sai ta maida kan aikinta tana cewa

"Na duba."

Ya saki ajiyar zuciya.

"Kin san abin da ya fi damuna?"

Ta girgiza kai.

"A'a."

"Cewa kin daina fa

ɗ

a da ni."

Ta

ɗ

an yi dariyar da ba ta fito daga zuciya ba.

"Fa

ɗ

a kuma?"

"E

h."

"Ba ni da dalilin fa

ɗ

a."

"Kin fi bani tsoro idan kika yi shiru."

Ta

ɗ

an juyo gare shi.

A karon farko idanunsu suka ha

ɗ

u sosai.

Ta ce a hankali,

"Wasu lokutan shiru yana fi kalmomi zafi, Fahad."

Kalaman suka shiga zuciyarsa kamar kibiya.

Ya sunk

uyar da kansa.

A yanzu ya fahim cewa ba wai ya

ɓ

ata ran matarsa kawai ba...

Ya karya amincewar da take da ita cewa kafin ya yanke hukunci a kanta, zai fara saurarenta.Kuma gyaran wannan kuskuren ba zai tsaya da kalmar "ki yi haƙuri" ka

ɗ

ai ba.

_

*Bayan

kwana uku*

Yau ne ranar da Jalaluddeen zai dawo,.kuma yau ne ranar da Mom za ta dawo daga Dubai wajen hada kayan lefen Ma'eesha da Yasmeen.

Kuma yau saura kwana biyu a yi bikin auren nasu .

Gidan ya cika da jama'a ana ta farin ciki da girke -girke.

_Ma'eesha ta yi kyau sosai ba kadan ba, an gyara ta ta dawo kamar wakar injin. Idan ta shiga waje sai wajen ya kwana bai daina ƙamshin jikinta. Ta yi ƙyalli da sheƙi.

Ma sha Allah ba wanda zai gane ta daga kallo

ɗ

aya.

Jama'a an fara taruwa saboda bikin

da aka shirya.

*Maman Ihsan ce*✍

🏻

09065327995

[7/21, 9:06 AM] +234 706 732 9840: *MAKAHO NE*

_Book 2_

Maman Ihsan ce ✍

🏻

JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

*LITTAFINA NA KUƊI NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI. NAIRA DUDU ƊAYA

NE KACAL. ZA KI TURA MANI KUƊIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2242538350 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 09065327995*

Page1





1





8





Har aka kwashe awa

ɗ

aya Ma'eesha na zaune kan kafarta. Wanda zuwa lokacin ƙafarta ta fara gajiyawa da zaman da ta yi

.

Motar Abbi ne ya shigo cikin gidan, bayan ya yi parking ya fito ya nufi shiga ciki.

Da sallama ya tura kofar falon ya shiga.

Ya tsaya a bakin ƙofar falon yana gyara hularsa kafin ya yi sallama cikin muryarsa mai cike da natsuwa.

"Assalamu alaikum."

Ma'eesha ta

ɗ

ago kanta da sauri duk da gajiyar da ta yi saboda zaman da ta yi na tsawon lokaci. Da sauri ta amsa cikin ladabi.

"Wa alaikumus salam wa rahmatullah, Abbi."

Ya amsa mata da murmushi mai taushi, amma murmushin ya shu

ɗ

e nan take da idanunsa su

ka sauka a kanta.

Har yanzu tana zaune a ƙasa.Mayafinta yana rufe jikinta.Kanta a sunkuye.Ba alamar an yi mata maraba.Ba alamar an ce mata ta shiga ciki.

Haka kuma Ba alamar an kula da ita.Ya

ɗ

an

ɗ

aure fuska.

"Ke ka

ɗ

ai ce a falon nan?"

Ma'eesha ta yi sh

iru na

ɗ

an lokaci kafin ta amsa a hankali.

"Eh... Abbi."

Ɗ

an jim ya yi na rashin jin da

ɗ

i kafin ya ce.

"Ina Ummeen?"

Ta nuna hanyar

ɗ

akin da yatsa sanan ta ce

"Tana ciki."

Abbi ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

"Subhanallah."

Ba tare da ya ƙara ce

wa komai ba ya nufi cikin gidan.

Ya tsaya a bakin ƙofar

ɗ

akin ya kira sunan ta

"Maryam."

Ba ta amsa ba. Kuma ba ta kalli kofar a ba

Ya sake kiran sunan nata a karo na biyu

"Maryam."

Sai daga ciki-ciki ya ji muryarta ta ce.

"Shigo."

Ya tura ƙofar

ya shiga.

Ummee na zaune bakin gado, hannayenta a ƙirji, fuskarta cike da tsananin

ɓ

acin rai.Ko kallonsa ba ta yi ba.

Abbi ya tsaya yana kallonta na wasu daƙiƙu kafin ya ce cikin murya mai nuni da takaici.

"Me ya sa kika bar yarinyar nan ita ka

ɗ

ai a fa

lo?"

Ba tare da ta

ɗ

ago ta kalle shi ba ba ta ce.

"To me kake so in yi?"

Abbi ya yi mamaki, ya girgiza kai cikin takaici ya ce.

"Maryam."

Ta katse shi da cewa .

"Ban son ganinta."

Kalmar ta fito kai tsaye.Ba tare da

ɓ

oye komai ba.Abbi ya yi shiru y

ana kallonta.Ita kuma ta ci gaba.

"Na gaya maka tun farko. Ba zan iya son yarinyar nan ba. Duk lokacin da na kalle ta sai na tuna abin da ya faru."

Abbi ya yi numfashi. Sanan ya ji magana .

"Abin da ya faru ba laifinta ba ne."

"Ban ce laifinta ba ne."

Ta yi magana tana jiyar da kai ƙauda kanta gefe .

"To me ya sa kike hukunta ta?"

Ummee ta miƙe tsaye. tana cika da batsewa ta ce.

"Saboda zuciyata ba ta kar

ɓ

e ta ba

Ta yi maganar a fusace. Sanan ta

ɗ

aura da cewa .

"Na yi burin wata daban ta zama mata

r Jalaluddeen.Na yi mafarkin Yasmeen.Na tsara rayuwa daban. Amma yau komai ya rushe."

Ta girgiza kai sanan ta

ɗ

aura da cewa.

"Kuma ba zan iya ganin yarinyar nan ina jin da

ɗ

i ba."

Abbi ya matso kusa da ita.

"Maryam, kina jin abin da kike fa

ɗ

a kuwa?"

Ta

juya masa baya sanna ta ce .

"Ina ji."

"Yarinyar nan fa amana ce Matar

ɗ

anki ce."

Shiru ta yi masa ba ta yi magana ba

"Kin bar ta sama da awa guda tana zaune a ƙasa kamar baƙuwa.?"

Har yanzu ba ta ce komai ba.Abbi ya ci gaba da cewa .

"Ko ba don ita

ba, ki yi don Jalaluddeen."

Nan take ta juya ta kalli Abbi ta ce

"Shi ne ya jawo min wannan ciwon."

Abbi ya

ɗ

aga gira ya kira sunan ta.

"Maryam!"

"Eh ina jin ka."

Ta amsa da ƙarfi.

"Shi Jalaluddeen ya ƙi bin abin da nake so. Shi ya za

ɓ

i wannan yar

inyar. Shi ya rusa duk wani buri na. Yanzu kuma yana so in rungume ta kamar na haife ta?"

Ta girgiza kai.

"Ba zan iya ba."

Abbi ya lumshe idanunsa.Ya fahimci zuciyarta ta yi tsauri matuƙa.Ya yi ƙoƙarin lallashinta.

"Ki saurare ni..."

Amma ta katse shi

.

"A'a, Wallahi ba zan iya ba.Idan kana son kai ta gidan mijinta, kai ta. Ni ba zan raka ta ba. Ba zan taka ƙafata zuwa gidan Jalaluddeen ba saboda ita."

Ta zauna bakin gadon tana share hawayen da suka cika idanunta ta cigaba da magana tana cewa.

"Ka ba

r ni kawai."

Abbi ya tsaya yana kallonta.Ya fahimci duk maganar da zai yi a wannan lokacin ba za ta canja komai ba.Ya sauke ajiyar zuciya.

"Allah Ya shirye ki, Maryam."

Bai jira amsa ba.Ya juya ya fita.

Da ya dawo falon, Ma'eesha har yanzu tana zaune

a yadda ya barta.Da jin takun sawunsa ta

ɗ

ago kai cikin girmamawa.Ya tsaya gabanta.

Fuskarsa cike da tausayi.

"Ma'eesha."

Ta

ɗ

ago da kai amma ba ta kalli idanunsa. A ta amsa da

"Na'am Abbi."

Ya yi shiru na

ɗ

an lokaci kamar yana neman kalmomin da suka

dace.

"Duk abin da ya faru..."

Ya sauke numfashi ya kasa karasa maganar dai zan yi

"ki yi haƙuri."

Ma'eesha ta yi saurin yagirgiza kai tana cewa

"Babu komai Abbi."

Ya yi murmushin takaici.

"Akwai komai.Amma ina roƙonki kada ki saka shi a ranki, K

ina ji ko?"

Ta gyada kai tare da cewa

"In sha Allah."

Ya sunkuya ka

ɗ

an yana dubanta irin kallon uba ga

ɗ

iya.

"Rayuwa tana da jarrabawa.Wani lokaci mutum ba ya samun kar

ɓ

uwa a rana

ɗ

aya..Amma da kyawawan halaye da haƙuri, zukata suna canzawa."

Ma'eesh

a ta runtse ido tana danne ƙwallarta.

"In sha Allah Abbi."

Abbi ya jinjina kai ya ce.

"Tashi, ƴata."

Ta

ɗ

an yi jinkiri saboda ƙafafunta sun yi mata sanyi da ciwo. Da hannun kujera da ta rike ta miƙe tsaye da kyar.

Da ta tsaya sai ta

ɗ

an karkace saboda

ƙafarta ta yi numb.

Abbi ya tare ta kafin ta fa

ɗ

i.

"A hankali."

Ta gyara tsayuwarta tana jin kunyar halin da take ciki.

"Yi haƙuri dan Allah."

"Ba ka yi min komai ba."

Ta yi maganar tana murmushi

Ya yi mata murmushi irin na uba.

"Sai mu tafi n ka

i ki gidan mijinki."

Kalmar gidan mijinki ta sa zuciyar Ma'eesha ta bugo da ƙarfi.Ta gyara mayafinta. Ta share hawayen da suka taru a gefen idanunta.Sannan ta bi bayan Abbi cikin nutsuwa.

Da suka isa bakin ƙofa, Abbi ya waiga ya kalli hanyar

ɗ

akin Ummee.

Ya tsaya na

ɗ

an lokaci.A zuciyarsa ya yi addu'a.

'Ya Allah, Ka cire ƙiyayya daga zuciyar Maryam. Ka ha

ɗ

a zukatansu cikin alheri.'

Sai ya bu

ɗ

e ƙofar suka fita zuwa harabar gidan, inda motar ke jiransu domin ya kai amanar

ɗ

ansa zuwa gidanta na gaskiya, g

idan Jalaluddeen.

_Umma_

Ammi na zaune a kan kujera tana jan tasbaha a hankali, amma duk da haka hankalinta ba ya kan abin da take yi. Sau da yawa idanunta kan sauka kan agogon bango, sannan ta sake kallon hanyar

ɗ

akin Sidra.

A gefe kuwa Umma ce zaun

e, hannunta riƙe da wayarta amma ba ta ma san abin da ke kan screen ba. Tun jiya zuciyarta take cike da fargaba saboda abin da ya faru da Sidra yayin cin abinci.

Can ta sauke wayar ta ce cikin ƙasa-ƙasa.

"Ammi... kina ganin dai ba wani babban abu ba ne?"

Ammi ta

ɗ

an yi shiru kafin ta amsa.

"Allah ne mafi sani."

"Sai dai ba na son zama muna zato."

"Shi ya sa na ce mu je asibiti kawai. Duk abin da yake damunta za a gano."

Umma ta gyada kai tare da cewa

"Hakan shi ne mafi alheri."

Dukansu suka sake y

in shiru.

Bayan wasu daƙiƙu...

A hankali Sidra ta fito daga

ɗ

akinta.

Ta yi wanka ta shirya cikin doguwar abaya mai launin ruwan madara, mayafinta ya rufe kanta da kyau. Sai dai fuskarta ta nuna kasala, idanunta kuma sun yi luhu-luhu kamar wadda ba ta ji

da

ɗ

in jikinta ba.

Da ta iso falon ta yi sallama.

"

Ammi ta yi mata murmushi.

"Kin shirya kenan?"

"Eh Ammi."

Sidra ta zauna kusa da Umma.

Ta lura yadda suke kallonta cikin kulawa.

JiSai ta

ɗ

an ha

ɗ

e gira cikin rashin jin dadin abinda suka yi ta ce

"Lafiya kuwa?"

Umma ta yi saurin yin murmushi.

"Lafiya kalau."

Ammi ta ce.

"Mun dai ga kamar ba ki da ƙwarin jiki, shi ya sa muka ce mu je asibiti a duba ki."

Sidra ta yi mamaki.

"Asibiti?"

"Eh."

"Amma Ammi ai yanzu na ji sauƙi."

Ammi ta girgiza

kai. Ta ce.

"Ko da kin ji sauƙi, ba laifi ba ne a tabbatar."

Sidra ta

ɗ

an yi murmushi.

"To shikenan."

Ba ta ƙara tambaya ba.

Ta miƙe ta

ɗ

auko hijabinta, sannan suka fita tare.

...

Bayan kusan rabin awa...

Motar ta tsaya a harabar wani babban asibit

i mai zaman kansa

Suka sauka.

Ammi ce a gaba.

Sidra da Umma na biye da ita. Da suka shiga reception, aka yi musu maraba cikin girmamawa.

Ammi ta yi rajista da sunan Sidra.

Bayan mintu ka

ɗ

an...

Nurse ta fito.

"Sidra."

Ta miƙe.

Ammi da Umma suka bi b

ayanta.

Suka shiga

ɗ

akin likita.

Likitan mutum ne mai shekaru kusan arba'in, cike da fara'a.

Ya yi musu sallama koSuka amsa.

Ya kalli Sidra.

"Me ke damunki?"

Sidra ta

ɗ

an yi tunani.

ya na yi amai."

"Ƙamshin abinci ne ya tayar min da zuciya."

"Kuma

ina jin kasala."

Likitan ya gyada kai yana rubuta bayananta.

"Kin da

ɗ

e kina jin haka?"

"A'a. Jiya ne kawai ya fara."Ya ci gaba da rubutu.

Sannan ya

ɗ

aga kai.

"To, za mu yi wasu gwaje-gwaje domin mu tabbatar da abin da yake damunki."

Ya rubuta takarda

ya miƙa wa nurse.

" kai ta laboratoryA laboratory An kar

ɓ

i jinin Sidra.

Sannan aka ba ta ƙaramin kwalba domin ta ba da fitsari don yin gwaji

Komai ya gudana cikin natsuwa.

Bayan an gama, aka ce su jira sakamako.

Sidra na zaune tana kallon mutanen da k

e shige da fice.

Ba ta da wani tunani illa ta san me yake damunta.

LlAmmi kuwa tasbaha kawai take ja Umma kuwa zuciyarta na bugawa ba tare da ta san dalili ba.Bayan kusan mintuna ashirin.Sakamakon ya fito.Ma'aikacin laboratory ya kai shi

ɗ

akin likita.

Li

kitan ya kar

ɓ

i takardar.Ya bu

ɗ

e file

ɗ

in.Idanunsa suka sauka kan sakamakon.

Na

ɗ

an lokaci ya sake dubawa kamar yana tabbatar da abin da ya gani.

Sai murmushi ya bayyana a fuskarsa.

Ya

ɗ

aga kai ya kalli Sidra ya ce.

"Alhamdulillah."Congratulations.Sidra

ta ha

ɗ

e gira.

Ba ta fahimci abin da yake nufi ba.

Likitan ya ci gaba da cewa cikin annashuwa.

"Gwajin ya nuna kina da ciki."

Shiru...

Wani irin shiru mai nauyi ya mamaye

ɗ

akin.

Sidra ta daskare tamkar an dasa ta a wurin.

Ammi ta zaro idanu.

Umma k

uwa ta kasa ko ƙiftawa.

Likitan bai lura da sauyin yanayinsu ba.Yana ci gaba da rubuce-rubuce a cikin file.Sai ya

ɗ

aga kai yana murmushi ya tambaya.

"To... ina mijinta?"

"Me ya sa bai zo tare da ita ba?"

A wannan karon ne Ammi da Umma suka kalli juna c

ikin firgici.Jinin jikinsu kamar ya daina gudana.

Umma ce ta fara magana cikin rawar murya ta ce.

"Doctor..."

"Me ka ce?"Likitan ya

ɗ

an yi mamaki.

Na farko ya

ɗ

auka ba su ji ba ne.Sai ya sake kallon sakamakon gwajin.

Ya tabbatar da abin da ke rubuce.Y

a sake

ɗ

aga kansa.

"Na ce... gwajin ya nuna tana da ciki.""Shi ya sa na tambaya ina mijinta.nAmmi ta miƙe tsaye ba tare da ta sani ba.

Fuskarta ta canza gaba

ɗ

aya."Haba Doctor..."

"Kana nufin... ciki?"

Likitan ya gyada kai cikin kwanciyar hankal ya f.

"Eh."

"Ciki ne.Gwajin ya fito positive."

Umma ta dafe baki da hannu Hawaye suka cika mata idanu.

"A'a, "Ba zai yiwu ba..."

Likitan ya ha

ɗ

e gira.

Ya fara fahimtar cewa akwai wani abu da bai sani ba.

Ya kalli Ammi.Sai ya kalli Umma.

Daga nan ya sake

mayar da dubansa kan Sidra, wadda har yanzu take zaune cak, idanunta ciki jru

ɗ

ani, kamar ita ma ba ta fahimci abin da ake fa

ɗ

a ba

*Maman ihdan ce*✍

🏻

09065327995

[7/21, 9:06 AM] +234 706 732 9840: *MAKAHO NE*

_Book 2_

Maman Ihsan ce ✍

🏻

JAJIRTA

TTU WRITERS ASSOCIATION

*LITTAFINA NA KUƊI NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI. NAIRA DUDU ƊAYA NE KACAL. ZA KI TURA MANI KUƊIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2242538350 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 09065327995*

Page1





1





9





Daga nan ya sake mayar da dubansa kan Sidra wacce har yanzu take zaune cak,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login