Showing 18001 words to 21000 words out of 191594 words
zumunta suna ci gaba da nuna yadda taron ke gudana.
Ba a jima ba, hotuna da gajerun bidiyoyi suka fara bayyana a shafuk
an sada zumunta. Social media
A cikin mintuna ka
ɗ
an, mutane suka fara yin sharhi. (Comments) Tun daga kan Facebook, twitter, Instagram, TikTok har ma da YouTube videos
ɗ
in ke tashi.
"Kai, wannan birthday ya ha
ɗ
u."
"Duba yadda Khalid da Jalaluddeen suke
mutunta juna."
"Kyautar agogon nan ta yi matuƙar kyau."
"Ba wai dukiya ce kawai ba, akwai tarbiyya."
"Ina son yadda Jalaluddeen bai nuna girman kai ba duk da matsayin da yake da shi."
Wasu suka yi anfani da hoton nasu biyu suka rubuta:
"*Friendship i
sn't measured by words, but by loyalty and respect.*
"
Bidiyon lokacin da suka ha
ɗ
a hannu suka yanka cake kuwa shi ne ya fi
ɗ
aukar hankali. Cikin
ɗ
an lokaci ya fara yawo a shafuka daban-daban, mutane suna yaba da tsari, tarbiyya da kuma kyakkyawar abotar d
a ta bayyana a tsakanin su.
Yayin da ake ci gaba da shagulgula, Khalid ya dubi Jalaluddeen cikin murmushi ya ce a hankali,
"Wallahi, zuwanka shi ne ya cika mini farin cikin wannan rana."
Jalaluddeen ya amsa da murmushi mai natsuwa.
"Allah ya ƙara maka s
hekaru cikin lafiya, albarka da nasara. Wannan shi ne abin da ya fi kowace kyauta daraja."
Taron ya ci gaba da gudana cikin annashuwa, raha da kyakkyawar mu'amala har zuwa dare, yayin da baƙi suka riƙa tafiya da kyawawan abubuwan tunawa daga bikin.
_Ma
'eesha_
Tun bayan rabuwarta da mutumin da ta ta
ɓ
a
ɗ
auka ba komai ba ne, rayuwar Ma'eesha ta sauya gaba
ɗ
aya. Murmushinta ya zama baƙo a fuskarta. Duk ranar da ta wayi gari, sai ta tuna shi. Duk da ita ce ta gudu daga gidansa, zuciyarta ba ta daina komawa
gare shi ba.
Ta yi ƙoƙarin shawo kan kanta da cewa ta yanke shawara mai kyau. Amma duk dare idan ta kwanta, tambayoyi suke dawo mata.
"Shin da gaske zai aure wata ne?"
"Ko da gaske ban ta
ɓ
a zama komai a wajensa ba?"
"Me ya sa bai biyo ni ba?"
Ba ta san ce
wa ya neme ta har ya gaji ba. Ita kuwa tana ganin ko ka
ɗ
an bai damu da tafiyarta ba.
.
A wannan yammacin, tana zaune ita ka
ɗ
ai a
ɗ
akin Saddiƙa, don kowa na falo suna hira, hatta Mom ta shigo ta ce ta fito ayi hira da ita cikin mutane ko za ta sake amma sa
m taƙi.
Wayarta na hannunta, amma ba ta da niyyar shiga kafafen sada zumunta.
Wayarta ta janyo
Ba tare da sanin me za ga yi ba ta shiga kafafen sada zumunta.
Duk da ba ta yi niyyar bude bidiyon ba amma ganin video ne kuma ba'a da
ɗ
e da
ɗ
aura shi ba amm
a ya samu tarin views da comments ya sa ta danna video.
Da farko ta ga katafaren falo ne.
Fitilu.
Baƙi.
Waƙa.
Sai kyamara ta juya...
Numfashinta ya tsaya.
Wayar ta kusa zamewa daga hannunta.
Idanunta suka ƙanƙance.
"...Shi?"
Ta sake matsowa kusa da allo
.
A karo na biyu.
A karo na uku.
Babu kuskure.
Shi ne.
Mutumin da ta aura.
Mutumin da ta raina tsawon watanni.
Mutumin da ta bari saboda ta yi zaton zai auri wata.
Sai dai yau...
Ba irin mutumin da ta sani ba ne.
Sanye yake cikin kaya masu tsadar gaske, y
ana tafiya cikin kwarjini. Kowa yana girmama shi. Manyan mutane suna yi masa maraba kamar wanda suka da
ɗ
e suna jira.
Lokacin da ya miƙa kyautarsa ga Khalid, falon gaba
ɗ
aya ya cika da tafi.
Ma'eesha ta zaro ido.
"Wane ne... wannan?"
Ta ra
ɗ
a a hankali.
Ta
sake kallon bidiyon.
An nuna lokacin da Khalid ya rungume shi.
An nuna yadda suka yanka cake tare.
An nuna yadda kowa ke ƙoƙarin
ɗ
aukar hoto da shi.
An nuna yadda mutane suke girmama shi.
A ƙasan bidiyon kuma sharhi ya cika.
"Mr. J. is different."
"Humi
lity at its peak."
"One of the youngest successful businessmen."
"Allah ya ƙara masa
ɗ
aukaka."
"Mutumin kirki ba ya surutu."
"I like the Mr J."
Kowa da comments da yake yi akan video na Jalaluddeen.
Hannun Ma'eesha ya fara rawa.
"Mr... J?"
Ta bu
ɗ
e w
ani bidiyon.
Sai wani.
Sai wani.
Duk inda ta shiga...
Shi.
Hotunansa.
Bidiyoyinsa.
Ana yabonsa.
Ana girmama shi.
Ana kiransa da sunaye masu
ɗ
auke da martaba.
Idanunta suka cika da hawaye.
"Ya Allah..."
Ta dafe kirjinta.
Ashe...
Ashe wannan mutumin ne yake
zaune da ita a ƙaramin gida ba tare da ya ta
ɓ
a nuna mata komai ba?
Ashe kullum idan ya fita yana dawowa da sandar jagorasa da kayan gyaran takalmi , ba talauci ba ne...
Ya kasance yana
ɓ
oye asalinsa ne.
Ta tuna irin kalaman da yake yawa fada ma ta .
"Ki
yi hakuri wata rana sai labari"
Kalaman suka dawo suna dukan kunnuwanta kamar ana maimaita su.
Ta rufe bakinta da tafin hannunta.
Kukanta ya ƙaru.
"Innalillahi..."
Ta sulale daga kan gadon zuwa ƙasa.
Ta rungume gwiwowinta.
Hawayen da ta yi ƙoƙarin hanaw
a tsawon kwanaki suka
ɓ
alle lokaci guda.
Ba wai saboda ta ga yana da ku
ɗ
i ba.
Sai saboda ta fahimci irin mutumin kirki da ta rasa
Mutumin da ya
ɗ
auki rainin hankalin mutane da haƙuri.
Mutumin da bai ta
ɓ
a bayyana mata ko waye shi ba saboda wani sirri da
yake karewa.
Sai ta tuna ranar da ta same shi yana waya.
"Eh... Ranar juma'a za'a
ɗ
aura aure na da Yasmeen....
Kalmar ta sake dawo mata.
Ta fashe da kuka.
"Da ace na tsaya na tambaye ka..."
Muryarta ta
ɓ
ace cikin kuka.
Wayar ta sake
ɗ
aukar ƙara.
Wata s
anarwa ta bayyana.
"Video of Mr. J at Khalid's Birthday reaches over one million views."
Ta kalli sanarwar cikin idanu masu cike da hawaye.
Gyambon da ya
ɗ
an soma warkewa a zuciyarta ya sake bu
ɗ
ewa.
A wannan karon, ba ƙaramin ciwo ba ne.
Ciwo ne mai
ɗ
auke
da nadama.
Nadamar rashin yarda.
Nadamar gaggawar yanke hukunci.
Nadamar rasa mutumin da zuciyarta ta fara gane darajarsa ne bayan ya
ɓ
ace daga gabanta.
Ta
ɗ
aga idanunta sama, cikin muryar da kuka ya dusashe ta ce,
"...Ina kake?"
"Ko sau
ɗ
aya ne..."
"In
a so in gan ka..."
"Ko don na yi ma ka wata tambaya..."
Amma amsar da ta samu ita ce shiru.
Sai sautin zuciyarta da ke bugawa da sunansa, alhali ba ta ma san cikakken sunan mutumin da ta aura ba.
*Maman Ihsan ce*✍
09065327995
[7/5, 8:40 AM] Antysal
ima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Na
Maman Ihsan ce✍
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFINA NA KUƊI NE KADA KI KARANTA MANI LITTAFI BA TARE DA KIN BIYA NI KUƊINA BA. ZAKI TURA KUDIN KU NAIRA DUBU ƊAYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2242538358 ZAINAB ABD
ULLAHI UBA BANK. SANNAN A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR.09065327995
Page 9
️
⃣
5
️
⃣
Sai saitin zuciyarta da take bugawa da sunansa.alhali ma ba ta ba ta ma san cikakken sunan mutumin da ta aura ba.
.
Ƙ
arar bude kofa da ta ji ne ya saka ga yi saurin g
oge hawaye tana kokarin daidaita kanta .
"Daughter ya dai?"
,"Ba komai Mama."
"Okay tashi ki yi sallah lokaci ya gabato kada barci ya dauke ki."
Ba ta yarda ta ha
ɗ
a idanu da Mom ba sai dai mike ya shiga bathroom.
Daga nan Mom ta fita ya bar ma ta da
kin.
Mai'eesha ta fito ta yi sallar magrib, tana nan har aka yi sallar ishai.
Bayan ta isar ne ta nufi dakin Mom dan ta san su kadai ne a gidan sauran sun fito wai za su je super market.
Ma'eeha ta nufi
ɗ
akin Mom, ta same ta tana shirin barin
ɗ
aki .
"Shiga ina zuwa."
Jin haka ya sa Ma'eesha ta shiga ta zauna saman sofa ya
Babbar baƙar ƙofa ta gidan ta bu
ɗ
e a hankali bayan mai gadi ya tabbatar da motar da ta iso. Motar ƙirar alfarma ta Jalaluddeen ta shigo cikin harabar gidan mai fa
ɗ
i, inda lambu
na masu kyau da rijiyar ruwa mai fesawa suka ƙara wa wajen armashi.
Da zarar motar ta tsaya,
Wallahi wani direba ya yi saurin bu
ɗ
e masa ƙofa, yayin
"Assalamu alaikum.
" Yallabai."
"Wa alaikumus salam.."
Mama tana gida?"
.
"Tana babban falo tare d
a baƙuwarta."
Ba tare da ya tambayi wace baƙuwar ba, ya nufi cikin gidan.
A wannan lokacin kuma
A saman bene,
Ma'eesha tana cikin
ɗ
akin Mom ita kadai
Tana kallon a tv
Ɗ
aya daga cikin ma su aiki. Gidan ne ta gigta
Mom na zaune ne ta lalubi waya ba t
a kusa da ita ashe tana daki.
"To."
Mai aikin ta shiga fakin ta cewa Ma',eesha Mom ta ce ta kawo ma ta wayarta.
A ƙasa kuwa...
Jalaluddeen ya shiga babban falo. Ya rungumi mamansa cikin girmamawa.
"Sai yanzu ka tuna da ni?"
Ya yi murmushi.
"Aiki ya
yi yawa ne, Mama."
Suna hira, ana kawo masa lemo da kayan ciye-ciye.
Can sama...
Ma'eesha ta dauko o wayar Mom , ta fito daga
ɗ
aki tana shirin saukowa..
Har ta kai rabin matakala...
Sai ta tuna ba ta sake hijabi ba.
Ma'eesha ta tsaya.
Ta juya ta koma
sama.
A ƙasa kuwa...
Jalaluddeen ya kalli agogo.
"Mama, zan wuce. Ina da wani taro."
"Ka jira ka ci abinci mana."
"A'a, idan na dawo zan ci."
Ya miƙe ya fita.
Da ya isa bakin ƙofa...
Ma'eesha ta sauko da sabon mayafin.
Har ta doshi falo...
Sai wata b
aiwar gida ta fito da sauri.
"Hajiya, Yallabai ya tafi."
"Ya tafi?"
"Eh."
Goggo ta yi dariya.
"Da kin fito da wuri da kin ha
ɗ
u da
ɗ
ana."
"Wa?"
"Jalaluddeen."
Kalmar ta bugi kunnuwanta kamar tsawa.
Waywr da ke hannunta ya zame ya fa
ɗ
i ƙasa.
Ta juya d
a gudu zuwa babbar tagar falon.
Ta hango baƙar motarsa tana fita ta ƙofar gida.
Ta dafe ƙirji.
"Haka nan...?"
A waje kuwa...
Jalaluddeen yana shiga mota, amma sai ya ji zuciyarsa ta cika da wani irin rashin natsuwa.
Ya waiwayi gidan.
"Ban san me ya sa b
a... amma kamar akwai wanda nake nema a cikin gidan nan."
Direban ya ce, "Ranka ya da
ɗ
e?"
Jalaluddeen ya girgiza kai.
"Ba komai. Mu tafi."
Motar ta fice.
Shi bai san matarsa tana cikin gidan ba.
Ita kuma ta tsaya tana kallon motar har ta
ɓ
ace.
_,Faha
d,_
Da zarar motarsu ta tsaya a harabar gidan, Fahad ya fito ya zagaya ya bu
ɗ
e wa Nadra ƙofa.
Ta sauko cikin fara'a, tana gyara hijabinta yayin da murmushi ya bayyana a fuskarta.
"Mu shiga,Mama i ta da
ɗ
e tana jiranmu tun da na ce za mu zo sallamar t
a ,"
in ji Fahad cikin taushin murya.
Nadra ta amsa da murmushi, suka shiga gidan tare.
Murna ta cika gidan da shigowarsu
. Mama da Inna suka rungume ta ita ma ta rungume Nadra da ƙauna, Baba kuwa ya tarbi Fahad da fara'a. Gaisuwa ta gudana cikin anna
shuwa, har sai da wata murya ta fito daga cikin gida.
" Yaya Fahad..."
Duk suka juya.
Farida ce.
'fuskarta mai cike da kwalliya da annuri. A zahiri, fuskarta cike take da murmushi, amma a
ɓ
oye zuciyarta cike take da wani irin kishi da ba wanda ya sani.
Da sauri ta ƙaraso gaban Fahad.
"Ashe ka zo? Ban ma san yau za ku iso ba."
Fahad ya yi murmushi.
"Eh, mun zo ne mu yi sallama.d Mamai."
Farida ta jinjina kai kafin ta juya ga Nadra. Dai da ta
ɗ
an tafe
"Sannu da zuwa."
Nadra ta yi mata murmushi ciki
n ladabi ta ce.
"Nagode."
Duk wanda yake kallonsu zai rantse babu wata matsala a tsakaninsu. Amma Farida ce ka
ɗ
ai ta san abin da take
ɓ
oyewa a zuciyarta.
...
Bayan
ɗ
an lokaci, miama ta ce wa Nadra ta shiga kitchen domin ta taimaka wajen shirya abin sha.
"Karki damu Ummi, zan raka ta,"
Farida ta fa
ɗ
a da sauri.
Da suka shiga kitchen, Nadra ta fara neman kofuna. Sai dai kafin ta ankara, ta ji ƙofar an rufe a hankali.
Ta juya.
Farida ce tsaye, fuskarta ta sauya gaba
ɗ
aya.
Murmushin da take yi a falo ya
ɓ
a
ce tamkar bai ta
ɓ
a wanzuwa ba.
Ta matso kusa da Nadra tana kallonta kai tsaye.
"Ki saurare ni da kyau."
Nadra ta
ɗ
an daure fuska.
"Ina ji."
"Kar ki kuskura ki
ɗ
auka cewa saboda kin auri Fahad kina nufin kin zama ta musamman."
Nadra ta yi mamaki.
"Ban fah
imce ki ba."
Farida ta yi wani
ɗ
an murmushi mai cike da raini.
"Ba sai kin fahimta ba. Abin da nake so ki sani shi ne, bana son ganinki tare da shi."
Nadra ta yi shiru na
ɗ
an lokaci kafin ta ce cikin sanyin murya,
"Idan na ta
ɓ
a yi miki wani abu, ki gay
a mini."
Farida ta yi dariya a hankali.
"Laifinki guda
ɗ
aya ne."
"Mene ne?"
"Kasancewarki matar Fahad."
Nadra ta ji gabanta ya fa
ɗ
i.
Ta fahimci cewa wannan ba ƙiyayya ce ta yau ba, wata tsohuwar wuta ce da take ci a zuciyar Farida.
A dai-dai lokacin aka
ji muryar Mama
daga falo.
"Farida! Nadra! Kun gama ne?"
Nan take Farida ta sauya fuskarta zuwa fara'a kamar ba ita ba ce ta yi wa
ɗ
annan maganganun.
"Gani nan Umma
.
Ta
ɗ
auki tray
ɗ
in shayi, sannan kafin ta fita ta ra
ɗ
a wa Nadra a kunne,
"Ki ci gaba da
murmushi a gabansu... amma ki sani, daga yau ba zan bari ki huta ba."
Nadra ta tsaya cak, zuciyarta na bugawa da sauri, tana kallon bayan Farida har ta
ɓ
ace.
Ta fara fahimtar cewa zaman da za su yi a gidan iyayen Fahad ba zai kasance cikin sauƙi ba.
Nadr
a ta lumshe ido na
ɗ
an lokaci tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta. Ta
ɗ
auki tray
ɗ
in da ke gabanta, ta bi bayan Farida zuwa falo kamar ba wani abu ya faru ba.
Da suka fito, Mama ta yi murmushi..
"Har kun gama? To madalla."
Farida ta ajiye tray
ɗ
in a kan ce
nter table cikin natsuwa, tana yi wa kowa hidima kamar babu abin da ya faru tsakaninta da Nadra.
Fahad ya
ɗ
aga kai ya kalli Nadra.
"Lafiya kuwa? Kamar kin
ɗ
an canza."
Nadra ta yi saurin murmushi.
"Ba komai, zafin kitchen ne kawai."
Fahad bai ƙara magana
ba, amma zuciyarsa ta kasa yarda da amsar da ta ba shi.
Bayan sun gama shan abin sha, Baba ya ce,
"Fahad, zo mu shiga
ɗ
aki ina son mu tattauna wani abu."
"To Baba."
Da suka shiga
ɗ
aki, Nadra ta rage ita ida M Farida a falon.
Ummi ta tashi ta ce,
"Zan
duba girki, ku ci gaba da hira."
Da zarar Ummi ta fita, shiru ya mamaye falon.
Farida ce ta fara magana.
"Kin iya
ɓ
oye damuwarki sosai."
Nadra ta kalleta ba tare da ta ce komai ba.
Farida ta
ɗ
an matso kusa.
"Amma ki tuna abin da na gaya miki. Wannan gid
an ba zai ta
ɓ
a zama wurin da za ki sami kwanciyar hankali ba."
Kafin Nadra ta ba ta amsa, aka ji karar takun Fahad yana dawowa.
Nan take Farida ta sake canza fuska, ta yi dariya.
"Nadra, kina da kirki sosai. Allah ya ƙara muku zaman lafiya."
Fahad ya is
o yana murmushi.
"Me kuke tattaunawa ne haka?"
Farida ta amsa cikin sauri.
"Ina yaba mata ne. Gaskiya ka yi dace da mace ta gari."
Fahad ya kalli Nadra, ya ga murmushinta amma idanunta sun nuna wata damuwa da take ƙoƙarin
ɓ
oyewa.
A zuciyarsa ya ce,
"Akwa
i wani abu da ya faru... amma meye?"
Sai dare suka komai gida.
A wannan daren, bayan kowa ya kwanta, Nadra ta zauna kusa da taga tana kallon hasken wata. Tana tunanin ko ya kamata ta gaya wa Fahad abin da Farida ta fa
ɗ
a mata
.
Sai dai ta ji tsoron kada
hakan ya jawo rikici tsakanin 'yan uwa.
A gefe guda kuma, Farida tana cikin
ɗ
akinta tana kallon wata tsohuwar hoto da ke hannunta—hotonta ne tare da Fahad tun suna yara. Ta shafa hoton a hankali, sannan ta ce cikin murya mai cike da ƙuduri,
"Na rasa shi
sau
ɗ
aya... amma ba zan bari Nadra ta more shi cikin kwanciyar hankali ba."
Ta
ɗ
auki wayarta ta kira wani lamba.
Da aka
ɗ
aga, ta ce cikin ƙasa da murya,
"Lokaci ya yi. Ki fara abin da muka tsara."
Daga
ɗ
aya
ɓ
angaren aka amsa da kalma
ɗ
aya kawai:
"An gama.
".
Farida ta kashe wayar tana murmushi, alamar cewa wata sabuwar fitina ce ke shirin kunno kai.
*Maman Ihsan ce*✍
[7/5, 8:18 PM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Na
Maman Ihsan ce✍
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFINA NA KUƊI NE KADA
KI KARANTA MANI LITTAFI BA TARE DA KIN BIYA NI KUƊINA BA. ZAKI TURA KUDIN KU NAIRA DUBU ƊAYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2242538358 ZAINAB ABDULLAHI UBA BANK. SANNAN A TURA SHAIDAR