Showing 168001 words to 171000 words out of 191594 words
zaune a ƙasa kan wani lallausan carpet mai launin ruwan madara , cikin cikakkiyar shigar amarya. An lullu
ɓ
e fuskarta da mayafi mai siririn yadi wanda ke ƙara mata kwarjini. Hannayenta masu
ɗ
auke da lalle sun ha
ɗ
u wuri guda
a gabanta, kanta kuma a sunkuye yake cike da kunya da tunanin sabon rayuwar da za ta shiga. Ga shi ta saka ran Nadra za ta rako ta amma ba ta ganta cikin masu rakiyarta ba, dama Nadra ce sai ƙawarta Humaira da kuma ƙawar Sidra ta baya wato Khadijah. Abun
da ya sa Nadra ba ta biyo tawagar kawo amarya ba kuwa ganin yadda take kuma ita ma Nadra na kuka ya da Umma ta hana ta zuwa . Dan ta san wajen dawowar ta sai an yi da gaske idan suka rike juna.
Da ƙawayen suka ga Mimi ta shigo, gaba
ɗ
aya suka miƙe tsaye
cikin girmamawa.
Ba tare da
ɓ
ata lokaci ba, Mimi ta taka har inda Sidra take. Ta durƙusa gabanta, sannan ta kama hannunta cikin tausayi irin na uwa.
"Sidra..."
A hankali Sidra ta
ɗ
ago kanta, idanunta cike da kunya da
ɗ
an fargabar sabuwar rayuwa.
Mimi
ta yi murmushi.
"Tashi, 'yata."
Sidra ta miƙe cikin nutsuwa, har yanzu kanta a ƙasa yake.
Mimi ba ta saki hannunta ba. Ta riƙe shi da ƙarfi irin na uwa mai son
ɗ
anta ta fara tafiya da ita. Jama'a suka matsa gefe suna kallonsu cikin farin ciki, wasu ma m
urmushi suke yi saboda ganin yadda Mimi ke nuna ƙauna da kulawa.
Suka fito daga
ɗ
akin suka nufi hanyar da ta kai zuwa part
ɗ
in Jabeer.
Gidan ya yi tsit idan aka kwatanta da wajen taron biki. An yi wa hanyar ado da furanni da fitilu masu haske. A hankali
suke tafiya, Mimi na gaba, Sidra na biye da ita cikin sanyin jiki.
Da suka isa ƙofar part
ɗ
in Jabeer, Mimi ta tsaya na
ɗ
an lokaci ta kalli ƙofar da aka yi wa ado cikin tsari mai kayatarwa. Ta tura ƙofar a hankali.
Da suka shiga ciki, sai ƙamshin turare m
ai da
ɗ
i ya bugi hancinsu. An gyara falon cikin tsari na musamman. Furanni kala-kala sun kawata wurin, yayin da fitilu masu laushi ke ba
ɗ
akin wani irin annuri.
Mimi ta ci gaba da tafiya da Sidra har zuwa babban
ɗ
akin kwana.
Da suka shiga, Sidra ta
ɗ
an sa
ki ajiyar zuciya saboda kyawun
ɗ
akin. An shimfi
ɗ
a farin Royal bed da sabbin zanen gado masu tsada, an yi masa jere da furanni masu kyau ta ko'ina. Komai na
ɗ
akin ya nuna cewa an shirya shi ne domin maraba da sabuwar amarya.
Mimi ta kai Sidra bakin gadon.
" zauna, 'yata."
Sidra ta zauna a gefen gadon cikin ladabi, tana gyara mayafinta.
Mimi ta zauna kusa da ita. Ta kamo hannayenta biyu cikin nata.
"Sidra... yau kin shiga wata sabuwar rayuwa ce. Aure ibada ne kafin ya zama zama tare. Ki yi haƙuri a duk l
okacin da haƙuri ya zama dole. Ki girmama mijinki, ki mutunta shi, ki riƙe amana. Kada ki bari fushi ya fi muku magana. Duk gidan da aka gina da soyayya da yafiya, Allah Yakan albarkace shi."
Hawaye suka cika idanun Sidra.
Mimi ta share mata hawaye da ta
fin hannunta.
"A'a, kar ki yi kuka. Ina son ganin murmushinki. Allah Ya ha
ɗ
a zukatanku cikin alheri. Ya sanya zaman aurenku ya zama mai albarka, Ya ba ku zuri'a ta gari, Ya cika muku burinku na alheri."
"Amin..." Sidra ta fa
ɗ
a da ƙyar saboda muryarta ta
cika da kuka.
Mimi ta shafa kanta cikin ƙauna.
"Ke ma kin san Jabeer. Yaro ne mai zuciya mai kyau. Duk da cewa yana da rashin jin magana wasu lokuta , amma sanadiyar abun da ya faru tsakanin ki da shi, ya zama sanadin shiryuwar sa, Ina da yaƙinin zai kul
a da ke. Ku riƙi junanku da mutunci da fahimta. Ni mahaifiyarsa ce idan har ya yi maki wani abun da ba daidai ba ki sanar da ni, zan
ɗ
auki matakin da ya dace."
Sai Mimi ta zaro wayarta daga jakarta.
Ta danna lambar Jabeer.
Bayan ƙira ta shiga, bai jima
ba ya
ɗ
aga.
"Assalamu alaikum Mamy."
"Wa alaikumus salam."
"Barka da dare Mimi, kina lafiya kalau?"
"Lafiya lau. Ina kake ne?"
"Ina wajen abokaina ne. Ina sallama zan dawo."
Mimi ta
ɗ
an yi murmushi.
"To ka hanzarta dawowa. Kada ka bar yarinyar muta
ne tana jiranka. Na kawo maka amanarka, tana nan cikin
ɗ
akinku."
Daga can
ɓ
angaren kuwa Jabeer ya yi murmushi mai cike da farin ciki.
"In sha Allah Mimi Ga ni nan zuwa yanzu."
"Allah Ya tsare hanya."
"Amin."
Ta kashe wayar sannan ta mayar da ita cikin
jaka.
Ta sake kallon Sidra.
"Kin ji ko? Yana hanya."
Sidra ta yi murmushi a karo na farko tun da suka shiga
ɗ
akin.
Mimi ta miƙe tsaye.
Ta gyara mayafin Sidra cikin kulawa, ta daidaita mata zaman gyalenta sannan ta
ɗ
an shafa kumatunta cikin ƙauna.
"A
llah Ya yi muku albarka, ya sanya farin ciki da zaman lafiya su zama baƙi na dindindin a gidanku."
"Amin, Mami."
Mimi ta juya zuwa ƙofar
ɗ
akin. Kafin ta fita sai ta sake waiwayowa ta kalli Sidra, wadda ke zaune cikin kunya da nutsuwa a bakin gadon.
Ta y
i mata murmushi mai cike da ƙauna irin ta uwa.
"Allah Ya kiyaye ki, 'yata."
"Amin."
Mimi ta yi sallama a hankali, ta rufe ƙofar ba tare da hayaniya ba, ta bar Sidra ita ka
ɗ
ai cikin
ɗ
akin, zuciyarta cike da fargaba, fata da kuma addu'ar Allah Ya sanya al
heri a sabon babin rayuwarta.
_Jabeer_
Yana gama sallama da abokansa ya nufi motatsa. Don ya ce ba wani abokin da zai raka shi
ɗ
akin amaryarsa. Shi kadai zai je, dan haka abokan ma suka hakura suka yi masa fatan alkhairi.
A hanya ya sauka ya siye kaz
a da fresh milk sanan ya sa a gefensa wajen me zaman banza, ya nufi hanyar komawa gida, zuciyarsa cike da farin ciki yau ya zama angon Sidra.
*Maman Ihsan ce.*✍
️
09065327995
[8/8, 8:10 AM] Antysalima Grp: 1
️
⃣
6
️
⃣
2
️
⃣
A hanya ya sauka ya siye kaza d
a fresh milk, sanan ya ajiye a gefen wajan me zamam banza, ya nufi hanyar komawa gida, zuciyarsa cike da farin ciki yau ya zama angon Sidra.
Ƙ
arar bu
ɗ
ewar ƙofar falon part
ɗ
in ce ta katse tunanin Sidra.
Zuciyarta ta buga da sauri.Ta
ɗ
an gyara zamanta a
bakin gadon, ta sake jan mayafinta ya rufe fuskarta yadda ya kamata. Hannayenta kuwa suka ha
ɗ
u wuri guda cikin tashin hankali da kunyar da ta mamaye zuciyarta.
A hankali ya bu
ɗ
e ƙofar
ɗ
akin .
Jabeer ne.
Sanye yake cikin wata farar shaddar
ɗ
injint babba
r riga mai tsananin kyau, hularsa a hannunsa. Da ya taka cikin
ɗ
akin, ƙamshin turarensa ya gauraya da ƙamshin.
Da idanunsa suka sauka kan Sidra, sai ya tsaya cak.Na wasu daƙiƙu ya kasa motsi.Kamar dai yanzu ne ya fara ganinta.
A cikin shigar ta irin ta a
marya, fuskarta na
ɓ
oye da siririn mayafi, hannayenta na
ɗ
auke da jan lalle, ta yi kyau fiye da yadda ya ta
ɓ
a hasashe.
Ya saki murmushi mai cike da farin ciki da godiya.
"Subhanallah..."
Ya furta cikin ƙaramar murya.
"Alhamdulillah..."
A hankali ya ta
ko zuwa gare ta.
Sidra kuwa zuciyarta sai faman bugawa take. Ba ta iya
ɗ
aga kai ta kalle shi ba.
Da ya ƙaraso gabanta, ya tsaya na
ɗ
an lokaci yana kallonta.
Sai ya zauna kusa da ita, amma ya bar tazara mai nuna girmamawa.
"Assalamu alaiki, matata."
Mur
yarsa cike take da taushi.Sidra ta amsa cikin kunya.
"Wa alaikumus salam."
Shiru ya ratsa tsakaninsu.Ba wanda ya yi magana na
ɗ
an lokaci.Jabeer ya yi murmushi.
"Ashe kunya haka take..."
Sidra ta
ɗ
an murmusa ba tare da ta
ɗ
aga kai ba.
"Idan kika ci gab
a da kallon ƙasa haka, ni fa zan fara kishin tiles
ɗ
in nan."
Maganar tasa ta sa Sidra ta yi dariya ƙasa-ƙasa.
Da wannan dariyar ne ta fara
ɗ
aga idanunta ta kalle shi.Idanunsu suka ha
ɗ
u.
Na
ɗ
an lokaci kamar duniya ta tsaya.Jabeer ya ce cikin natsuwa,
"N
a da
ɗ
e ina jiran wannan ranar."
Ya
ɗ
an yi shiru kafin ya ci gaba da cewa.
"Amma duk da farin cikin da nake ciki... akwai wani abu da ke yi min nauyi a zuciya."Murmushin Sidra ya lafa.
Ta saurare shi cikin nutsuwa.Jabeer ya sauke numfashi.
"Sidra... ba
n san ko zan ta
ɓ
a iya yafe wa kaina ba."
Kai tsaye ya kalle ta.
"Na san kalmar 'yi haƙuri' ka
ɗ
ai ba za ta goge abin da ya faru ba. Na san na jawo miki ciwo mai girma. Akwai kwanakin da nakan rasa barci ina tuna irin abun da na yi miki."
Muryarsa ta som
a rawa.
"Wallahi, bana neman ki manta abin da ya faru saboda yana da sauƙi. Ina neman gafararki ne saboda zuciyata ta yi nadama da gaske. Kowace rana ina roƙon Allah Ya gafarta mini, kuma ina fatan wata rana ke ma za ki sami salama daga wannan ciwon."
"I
dan akwai abin da zan yi tsawon rayuwata domin in rama kuskuren nan da alheri, zan yi. Ina son ki sani cewa daga yau, ba zan ta
ɓ
a zama sanadin hawaye a idanunki ba. Burina shi ne in zama dalilin murmushinki."
Sidra ta yi shiru.Ta kalli fuskar Jabeer.Ta ga
nadama ta gaskiya a cikinta.
A hankali ta miƙa hannunta.Ta
ɗ
ora shi kan nasa.
Jabeer ya kalli hannun nata, sannan ya
ɗ
ago idanunsa ya kalle ta.
Sadra ta yi murmushi mai laushi.
"Jabeer..."
Ya amsa da sauri.
"Na'am."
"Abin da ya faru ya faru, ba wan
da ya isa ya haka hakan faruwa, ka mata da baya. Ina son wannan maganar ka nan ka dunƙule shi ya saka a bakinka, ka ha
ɗ
iye shi, sannan ka kora da ruwa ka ha
ɗ
iye ."
Ya yi shiru yana sauraronta.
"Na yi kuka saboda shi. Na sha wahala saboda shi. Amma yau..
. bana son wannan daren ya fara da hawaye."
Ta
ɗ
an matse hannunsa da ya rike ta da cikin taushi.
"Na yafe maka."
Jabeer ya lumshe idanunsa, hawaye guda ya zubo masa.
"Gaskiya?"
Ta gyada kai.
"Eh."
"Ba wai saboda abin da ka yi ba ne ya yi daidai. A'
a. Amma saboda bana son rayuwarmu ta ci gaba da zama a cikin tsohon ciwo. Ina so mu fara sabon shafi da yardar Allah."
Jabeer ya sunkuyar da kansa cikin godiya.
"Nagode... Wallahi nagode."
Ya
ɗ
aga hannunta cikin girmamawa, ya riƙe shi a hankali tsakanin
tafukan hannayensa.
"Zan kula da ke. Zan mutunta ki. Zan yi iya ƙoƙarina kullum in zama mijin da zai sa ki yi alfahari."
Sidra ta yi murmushi.
"Ni kuma zan yi iya ƙoƙarina in zama mata ta gari."
Sai suka yi shiru na
ɗ
an lokaci, kowannensu yana kallon
ɗ
ayan cikin nutsuwa.
Jabeer ya yi dariya a hankali.
"To... yanzu dai zan iya ganin cikakkiyar fuskar matata ko kuwa har yanzu sai na ci gaba da jiran izini?"
Sidra ta yi murmushi cikin kunya.
"Ka fi son izini ko?"
"Eh. Saboda daga yau ina son komai ts
akaninmu ya kasance cikin mutuntawa da fahimtar juna."
"Amma fa sai ka biya kudin siyen baki, da na ganin fuska."
Ya fito da dukan ku
ɗ
a
ɗ
en da suke cikin aljihun sa, za su kai kimanin Naira dubu
ɗ
ari biyu ya ajiye mata. Murmushi ta yi sanan ta
ɗ
an
ɗ
aga m
ayafin fuskarta da kanta.
Jabeer ya kalleta na wasu daƙiƙu, murmushi ya bayyana a fuskarsa.
"Alhamdulillah..."
Shi ka
ɗ
ai ya iya furtawa.
A cikin zuciyarsa kuwa ya yi addu'a cikin sirri:
"Ya Allah, Ka ba ni ikon gyara abin da na lalata. Ka sa in zamo m
afaka ga wannan baiwarKa, ba sanadin ciwonta ba."
Sidra ta amsa addu'ar da "Amin" a hankali, sannan murmushi mai cike da fata ya bayyana a fuskokinsu, alamar fara sabon babi na rayuwarsu cikin fahimta, mutuntawa da bege..
Shiru ya sake mamaye
ɗ
akin.
B
ayan kalaman da suka yi wa juna, wani irin natsuwa ya sauka a tsakanin Sidra da Jabeer. Ba irin shiru na rashin abin fa
ɗ
a ba ne, a’a, shiru ne wanda ke
ɗ
auke da abubuwa da yawa—nadama, gafara, fata da kuma addu’ar samun sabuwar rayuwa.
Jabeer ya kalli Sid
ra na
ɗ
an lokaci, sannan ya sauke idanunsa.
“Sidra…”
“Na’am.”
“Tun da muka fara wannan sabon shafin da sunan Allah, ina ganin abu mafi kyau da za mu fara da shi shi ne mu gode wa Allah.”
Sidra ta
ɗ
ago kai ta kalle shi.
“Yaya?”
“Mu yi alwala, mu yi ra
ka’a biyu na nafila. Mu roƙi Allah Ya sa wannan aure ya zama alheri a gare mu. Ya ba mu zaman lafiya, fahimtar juna da haƙuri. Kuma Ya taimake mu mu manta da duk abin da ya gabata, mu gina abin da yake gabanmu.”
Fuskar Sidra ta yi haske da murmushi.
“All
ah Ya saka maka da alheri.”
Jabeer ya gyada kai.
“Amin.”
Ya miƙe daga bakin gadon, sannan ya tsaya yana kallonta ya ce.
“Ki je ki
ɗ
auro alwala. Ni ma zan shiga
ɗ
akina in
ɗ
auro tawa.”
Sidra ta gyara mayafinta.
“To.”
Ta miƙe a hankali daga bakin gadon
, tana gyara doguwar shigar amaryarta kafin ta nufi hanyar fita. Kafin ta kai ƙofar, sai Jabeer ya kira ta.
“Sidra.”
Ta juyo tare da cewa.
“Na’am?”
“Ki kula da kanki. Kar ki yi sauri.”
Ta yi murmushi ta ce.
“Insha Allah.”
Sai ta nufi kofar da take t
unanin bathroom ne
Jabeer ya tsaya yana kallon ƙofar da ta rufe a bayanta.
Ya sauke numfashi mai zurfi.
A karo na farko tun bayan abubuwan da suka faru a rayuwarsu, zuciyarsa ta ji wani irin sauƙi.Ya
ɗ
aga hannuwansa zuwa sama.
“Ya Allah… Ka taimake ni.
”
Ya furta a hankali.
“Ka sa ni zama mutumin da ya dace da wannan amanar da Ka
ɗ
ora min.”
Bayan haka ya nufi
ɗ
akinsa domin ya
ɗ
auro alwala.
Bayan
ɗ
an lokaci, Sidra ta dawo.
Ta zauna a bakin gadon tana jiran Jabeer, tana kallon yadda hasken fitilun
ɗ
a
kin ya sauka a kan furannin da aka kawata shi da su.
A zuciyarta kuwa addu'a take yi.
Ya Allah, Ka sa wannan sabon shafin ya zama mafi alheri fiye da abin da ya gabata.
Ba da jimawa ba sai ƙofar
ɗ
akin ta sake bu
ɗ
ewa.
Jabeer ya shigo.
A hannunsa akwai
Sallaya da ya
ɗ
auko domin su yi salla.Ya kalli Sidra.
“Kin shirya?”
Ta gyada kai.
“Na shirya.”
Ta bude wardrobe ta dauko sabon hijabinta. Jabeer ya shimfi
ɗ
a tabarmar cikin nutsuwa. Sidra ta tsaya kusa da shi.
Ba tare da wani dogon bayani ba, suka fara
sallar nafila.
Raka'a ta farko ta kasance cikin cikakkiyar nutsuwa.
Kowannensu yana tsaye gaban Ubangijinsa da zuciya mai cike da buƙatu.
A lokacin sujada, Sidra ta ji hawaye sun cika idanunta.
Ta yi addu'a a cikin zuciyarta.
Ya Allah, Ka bani ƙarfin
mantawa da abin da ya cutar da ni. Ka sa zuciyata ta samu salama. Ka sa wannan aure ya zama mafita gare ni, ba wata sabuwar fitina ba.
Jabeer kuwa shi ma yana cikin irin wannan yanayi.
Ya roƙi Allah Ya gafarta masa, Ya gyara halayensa, Ya ba shi haƙurin
zama miji nagari, Ya sa ya iya kare mutuncin matarsa da hakkokinta.
Bayan sun kammala raka'a ta biyu, suka zauna.
Jabeer ya
ɗ
aga hannayensa.
“Ya Allah…”
Muryarsa ta kasance ƙasa, amma cike da tawali'u.
“Ka sanya wannan aure namu ya zama aure na raham
a da albarka. Ka sanya soyayya ta gaskiya, amana da fahimta su zauna a tsakaninmu.”
Sidra ta
ɗ
aga hannayenta ma.
“Amin.”
Jabeer ya ci gaba.
“Ya Allah, Ka wanke zukatanmu daga duk wata ƙiyayya, fushi da tsoron abin da ya gabata. Ka ba mu ikon fara sabuw
ar rayuwa cikin tsoronKa.”
“Amin.”
“Ka kare gidanmu daga fitina. Ka sa duk wanda zai shigo cikinsa ya zo da alheri. Ka sa mu zama sanyin idon juna.”
“Amin.”
Sidra ta ƙara da kanta cikin hawaye.
“Ya Allah, Ka ba mu zaman lafiya. Ka sa mu fahimci juna.
Ka ba mu haƙuri da juriya. Ka albarkaci rayuwarmu.”
“Amin, Ya Rabbal Alamin.”
Suka shafe fuskokinsu.
Na
ɗ
an lokaci babu wanda ya yi magana.
Kamar kowannensu yana sauraron nutsuwar da ta sauka a zuciyarsa.
Daga baya Jabeer ya kalli Sidra.
“Muna gode w
a Allah.”
Ta yi murmushi tare da cewa
“Alhamdulillah.”
Bayan
ɗ
an lokaci, Jabeer ya miƙe.
“Ki zauna. Zan dawo.”
Ta kalle shi ta ce.
“Za ka je ina?”
Ya yi murmushi.
“Wani abu zan kawo.”
Sidra ta kalle shi cikin mamaki.
“Me?”
“Za ki gani.”
Ya fit
a daga
ɗ
akin.Sidra ta gyara zamanta a bakin gadon, tana kallon ƙofar.
Bayan wasu mintuna, sai Jabeer ya dawo.A hannunsa akwai faranti mai
ɗ
auke da naman kaza gasasshiya, tare da ƙaramin kofi da kwalbar fresh milk. A
ɗ
ayan hannunsa kuma akwai cokali da wuƙ
a.
Sidra ta kalle shi.
“Jabeer…”
Ya yi murmushi.
“Me?”
“Duka wannan fa?”
“Kin yi salla. Kin