Showing 159001 words to 162000 words out of 191594 words
ha
ɗ
u ba, har zukata da suka da
ɗ
e cik
in ciwo suka fara samun hanyar warkewa.
Nan Mom ta ce ta shiga ta yi wanka ta fito. Ba musu ta koma sama ta je ta yi wanka ta shirya. Shi ma Jalaluddeen
ɗ
akinsa ya je ya ya wanka ya shirya.
Kusan a tare suka sauko aka yi Liyafar tarbon su sa aka shirya.
An ce an sha an yi photo da Video.
Bayan an gama ne kowane ya fara kokarin barin gidan. Abbi ya wuce tare da Ummee, Dad ya wuce tare da Mom. Ma'eesha ta roki su Daddynta da kada su tafi dan Allah su tsaya su kwana a nan.
Jalaluddeen ya sa aka gyara ma
su bangaren baƙi dan su kwana a can. Sosai Ma'eeha ta ji dadin hakan a zuciyarta. Ta tambaye su su Mamy, nan Dady ke sanar da ita cewa ya saki Mamy bai san halin da suke ciki ba. Budar bakinta ta ce .
"Allah Sarki Yaya Jamil, shi nake tausayawa. Domin sh
i yana da kyakkyawar zuciya. Ba irin Mamy da Laila yake ba. Shi ya fita daban a cikin su. Ranar da aka daura aure na muka hadu da shi a harabar gidan hankalin sa ya tashi sosai.ya ce wanan na zai yiwu ba. Har ya biyo mu waje yana ta kiran mu ban saurare sh
i ba. Duk da haka bayan wani lokaci ya je ya sami ƙawata Nasreen ya ce ta kawo shi gidana. Har gudana ya zo da muke zaune ya bani kudi masu yawa. Ban karba ba na shige daki na bar sa. Bayan haka yazo sama da sau uku ina ƙin sauraren sa domin laifin mahaifi
yarsa nake kallonsa da shi. Allah Sarki Yaya Jamil."
Su dafe suna fitar sai sallar La'asar ne kowa ya watse.
Haka daddare ma bayan Ma'eesha ta saka masu aiki sun yi girki a can bangaren baƙi suka zauna gabadaya har da Jalaluddeen da Ma'eesha tare suka ci
abinci a bangaren baƙi tare da su Dady.
Daga nan aka dinga hira cikin farin ciki. Sai karfe goma sha biyun dare ya yi, Alhaji Babba ya ce su koma part dinsu su kamata su huta.
Sanan suka yi wa su Daddy sallama suka tafi .
_Sadiƙ_
Bayan an gama liy
afar tarbar su Jalaluddeen suka fito a tare da Yasmeen za su koma gida.
Da ido Ummee ta bi motar Sadik ganin yadda suke hira da ƴarta Yasmeen cikin so da kauna. Ta fara hakura saboda ta lura sun fada soyayyan juna. Don Yasmeen ta fadawa Ummee Kai tsaye ce
wa ba za ta rabu da mijinta ba. Dady ma ya shata mata layi akan lamarin auren na Yasmeen. Dole ta zuba masu ido.
Har motar Sadik ta bar harabar gidan Ummee na kallonsu yadda suke ta hira cikin nishadi.
Sadik ya juya ya kalli Yasmeen dake kallonsa tana mu
rmushi.
"Madam wanan kallon na maye haka kamar za ki cinye ni?"
"To idan ban kalle ka ba wa kake so na kalla? Ko wani namijin zan dinga kallo."
Da sauri ya ce.
"Subhanallah meye na fadar haka?"
"To Na ji kana korafi ne."
"Ban yi korafi ba sweet heart
. Ni naki ne ki yi ta kallona muna jin dadi."
"To yaushe kake so mu je namu Honeymoon namu ne?"
Dariya ya yi tare da cewa.
"Ke nake jira ki yi magana, dan ban sani ba ko za ki amince, don har yanzu Ban tabbatar kina so na ba."
Hararar wasa ta yi masa.
"Wani irin baka tabbatar da cewa ina son ka ba, bayan zaman da muka yi nake kukla ka ba naka lokacina na yi maka komai da mace ya kamata ta yi mijinta ba abun da na rage ka da shi, amma duk da haka kana tantanmar son da nake yi maka ne?"
"To ban taba jin
kin furta ba."
"Ai ko ban furta ba na yi shi a aikace."
"Ban yarda ba sai ki fada."
A hankali ta Matsar da kanta saitin kunnesa ta rada maka kalma" I LOVE YOU."
Saannan ta sumbace shi a kumatu wanda hakan ya sa sitiyarin motar ta kusa ƙwace masa.
"K
ina neman ki saka mu mutu ne?"
"Idan mun mutu a tare ai ba komai, ba za ka tafi ka bar ni ba, kuma ba zan tafi na bar ka ba. Sai dai mu tafi a tare ."
Daga nan suka cigaba da fura cikin so da kauna har suka karasa gida.
Bayan ya yi parking ne ya fito
daga cikin motar ya bude mata murfin motar Yasmeen ta fito, sanan ya rufe hannunsu a cikin na juna suka nufi ciki.
*Maman Ihsan ce*✍
️
[8/5, 10:15 PM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_Book 2_
Maman Ihsan ce✍
️
JAJIRTSTTU WRITERS ASSOCIATION
*LIT
TAFINA NA KUƊI NE KI BIYA NI HAKKINA KAFIN KI KARANTA MANI LITTAFI.NAIRA DUBU ƊAYA NE KACAL. ZA KI TURO MANI KUƊINNTA WANAM ACCOUNT NUMBER 2242538358 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAMBAR. 09065327995.*
Page1
️
⃣
5
️
⃣
8
️
⃣
Bayan ya yi parking ne ya fito
daga motar ya bude mata murfin motar Yasmeen ta fito. Sanan ya rufe hannunsu a cikin na juna nufi ciki.
*Bayan sati
ɗ
aya.*
Yau Alhamis ake ta shagalin bikin Sidra da Fahad. Kamar yadda Mama ga yi masi alkawarin ba za ta fada wa kowa ba kuwa haka aka yi
ba wnada ta fadawa wa daga kan Abba har yau.
Gidan ya cika da jama'a ana shirin zuwa taron reception.
Safiyar ranar da aka
ɗ
aura domin bikin auren Jabeer da Sidra ta waye cikin cike da hayaniya. Gidan Abba ya cika da ƴan uwa, maƙwabta da baƙi. Kowa na
kai da kawo; wasu na shimfi
ɗ
a kujeru, wasu na shirya kayan tarba, wasu kuma na ta
ɗ
aukar hotuna tun kafin a fara komai. Ƙamshin turaren wuta da na abinci ya gauraye da ƙamshin sabbin kaya, yayin da dariya da surutun mata suka cika harabar gidan.
A cikin
ɗ
akin Sidra kuwa, yanayin ya bambanta da na waje.
Tana zaune a bakin gado, kanta a sunkuye. Hannayenta a ha
ɗ
e cikin juna, idanunta sun yi ja saboda yawan tunani. Duk da cewa kwanakin baya ta amince da wannan auren saboda girmama iyayenta da kuma neman sab
on farawa a rayuwa, zuciyarta har yanzu ba ta gama samun nutsuwa ba.
Wata mata ta shigo
ɗ
akin tare da wasu ƙawayen amarya.
"To ku tashi mana. Yau ranar farin cikin ku ce."
Sidra ta
ɗ
aga kai da ƙyar, ta yi murmushin dole, sannan ta miƙe tsaye.
An zaunar
da ita a gaban madubi. Aka fara yi mata kwalliya cikin tsanaki. An shafe mata fuska da kayan kwalliya masu laushi, aka zana mata gira cikin kyau, aka saka mata jan baki mai laushi. Aka
ɗ
aura mata mayafi mai sheƙi da ya yi matuƙar dacewa da kayan da take s
anye da su.
Duk wanda ya kalli Sidra zai ce ita ce amarya mafi kyau a ranar.Sai dai idan aka kalli cikin idanunta...
Za a fahimci cewa akwai wani abu da ke damunta.
Mata suna ta yaba.
"Masha Allah!"
"Wallahi Sidra ta yi kyau sosai."
"Kai, Jabeer ya y
i dace."
Amma ita...Sai murmushi take yi na dole.
Ba wanda ya san irin yaƙin da zuciyarta ke yi da kanta.
A gefe guda kuma...
Jabeer yana cikin wani irin farin ciki.
Yana zaune tare da abokansa, suna ta zolayarsa.
"Wai angonmu yau ba ya zama wuri
ɗ
aya
."
"Ka dai nutsu mana."
Jabeer ya yi dariya.
"Ku kyale ni mana. Na da
ɗ
e ina jiran wannan rana."
Abokansa suka fashe da dariya.
Daya ya ce,
"Da alama idan aka gama yau ba za ka ma tuna da mu ba."
Jabeer ya girgiza kai yana murmushi.
Duk da yake yana
dariya, zuciyarsa cike take da godiya ga Allah.
Ya tuna wahalhalun da suka faru tsakaninsu, hawaye, nadama da gwagwarmayar da suka sha kafin wannan rana ta zo.Yau kuwa...
Allah Ya kawo su ga wannan rana.
_Sidra_
Bayan an kammala shirye-shiryen amary
a, aka fito da Sidra daga
ɗ
aki.Da ta bayyana...
Sai gaba
ɗ
aya wajen ya
ɗ
auki shiru na
ɗ
an lokaci.
Kowa ya zuba mata ido.
Mata suka fara shewa.
"Masha Allah!"
"Allah Ya sanya alkhairi."
Masu
ɗ
aukar hoto suka fara
ɗ
aukar hotuna ba tare da tsayawa ba.Si
dra tana tafiya cikin natsuwa, kanta a
ɗ
an sunkuye.
Ba ta yawan kallon mutane.
Sai dai lokaci-lokaci idan ta
ɗ
ago idanunta...
Sai ta ga dubban idanu suna kallonta.
Wannan ya sa zuciyarta ta ƙara bugawa.Ta sake sunkuyar da kanta.
A lokacin da Jabeer ya
hango ta...
Numfashinsa ya
ɗ
an tsaya.
Ya kasa
ɗ
auke idanunsa daga kanta.
A ransa ya ce,
"Subhanallah... wannan ita ce Sidrata?"
Murmushi ya cika fuskarsa.
Idanunsa suka cika da farin ciki.
Abokansa suka lura.Daya ya ta
ɓ
a kafa
ɗ
arsa.
"Ango, ka rufe
baki mana."
Duk suka fashe da dariya.
Jabeer ya yi murmushi kawai.
An fara gudanar da shagulgulan bikin cikin tsari.
Masu gabatar da shiri suna ta sanar da abubuwan da za a yi.
Ana ta
ɗ
aukar hotuna.Ana ta taya amarya da ango murna.
Manyan baƙi suna z
uwa suna gaisawa da iyalai.
Yara suna gudu suna wasa.Mata suna ta shewa. Maza kuma suna ta hirarsu.
Jabeer kuwa...
Sai farin ciki yake yi.
Duk wanda ya zo wajensa sai ya tashi ya rungume shi ko ya gaisa da shi cikin annashuwa.Yana ta murmushi babu ƙaƙƙ
autawa.
Amma idan ya juya ya kalli Sidra...
Sai ya lura tana zaune cikin nutsuwa.
Ba ta magana sai idan an yi mata magana.
Ba ta dariya sosai.Sai dai tana kallon jama'ar da ke shigowa da fita.Kowace fuska da ta gani...
Sai ta
ɗ
an tsaya tana kallonta.
Kamar tana neman wani abu.
Ko kuma tana tunanin yadda rayuwarta ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci.Jabeer ya matso kusa da ita a hankali.
Ya yi ƙasa da murya.
"Sidra..."
Ta
ɗ
an juya ta kalle shi ta ce.
"Lafiya?"
Ya girgiza kai.
"Lafiya."
"Kin tabbata
?"
Ta sake gyara murmushinta.
"Eh."
Jabeer ya san wannan murmushin ba na gaske ba ne.
Sai dai bai so ya matsa mata ba.Ya san lokaci ne kawai zai warkar da wasu raunukan zuciya.
Saboda haka sai ya ce cikin taushin murya,
"In sha Allah... komai zai yi
kyau."
Sidra ba ta ce komai ba.Sai ta
ɗ
an gyada kai kawai.
An ci gaba da gudanar da taron.An gabatar da addu'o'i.
An yi nasihohi masu ratsa zuciya game da zaman aure, haƙuri, yafiya da gina gida bisa amana da tsoron Allah.
Iyayen ango da na amarya suka
yi godiya ga baƙi.
Kowa ya yi farin ciki da yadda komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Da yamma ta fara yi...
Baƙi suka fara sallama
ɗ
aya bayan
ɗ
aya.
Masu
ɗ
aukar hoto suka kammala aikinsu.
Ƙ
awayen amarya suka yi ta rungumar Sidra suna yi mata fata
n alheri.
Abokan Jabeer kuwa suka ci gaba da zolayarsa har zuwa lokacin tafiya.
A hankali...
Filin taron ya fara yin shiru.Kujeru aka fara tattarawa.An fara kwashe kayan ado.
Hayaniyar da ta cika wajen tun safe ta fara raguwa.Sidra ta sake kallon waje
n.
Ta ga yadda taron ya watse cikin lokaci ka
ɗ
an.
Ta sauke wani dogon numfashi.
Jabeer ya tsaya kusa da ita.
Ya kalle ta cikin tausayi da bege.
Shi kuwa zuciyarsa cike take da farin cikin fara sabuwar rayuwa da matar da yake fata Allah Ya sanya soyayy
a, kwanciyar hankali da rahama a tsakaninsu.
Sai suka fara shirin barin wajen taron, yayin da iyalai da ƴan uwa suka ci gaba da yi musu addu'o'in fatan alheri, kuma rana ta ƙare cikin lumana da bege na sabon babi a rayuwarsu.
_Jamil_
Tun da sassafe
Jamil ya fita daga gidan da wata ƙaramar fata a zuciyarsa. Ko da kuwa ba zai samu duka ku
ɗ
in da likita ya buƙata ba, ya yi imanin ko kwatan kudin ta samu ya samu, watakila asibitin zai tausaya musu su fara kula da Mamy.
Ya
ɗ
aure tsohuwar jakarsa a kafa
ɗ
a
, ya kalli Laila da ke zaune a gefen Tabarmn da aka kwanmmmr da Mamy. Fuskar Laila ta kumbura saboda kuka, idanunta sun yi jajur.
"Mamy..." Jamil ya furta a hankali yana matsowa kusa da ita.
Mamy tana kwance ba motsi. Numfashinta na fita da shigowa a wah
ale. Miyau ya bushe a gefen bakinta, idanunta a lumshe suke, ba ta san abin da ke faruwa a kanta ba.
Ya durƙusa ya riƙe hannunta.
"Mamy... ki yi haƙuri. Wallahi zan nemo ku
ɗ
in nan ko da me zan yi. "
Ba ta amsa ba.
Laila ta share hawayenta.
"Allah Ya t
aimake ka, Yaya Jamil."
Ya gyada kai kawai ya juya ya fita.Tun daga wannan lokacin ya fara zirga-zirga kamar wanda ya rasa mafaka.
Ya fara zuwa wurin wani tsohon abokinsa.
Da ya yi sallama, aka fito aka ce,
"Ya fita tun da safe."
"Yaushe zai dawo?"
"
Ba mu sani ba."
Jamil ya juya cikin sanyin jiki.
Ya je wurin wani
ɗ
an uwansu.
Da ya bayyana buƙatarsa, mutumin ya sauke numfashi.
"Wallahi Jamil, da ina da shi ba zan hana ka ba. Ni ma ina cikin wata matsala."
Jamil ya yi murmushin dole.
"Na gode."
Ya fita. Ya sake zuwa wurin wani attajiri da ya ta
ɓ
a yi masa aiki.
An bar shi yana jira fiye da awa guda.
Da aka shigo da shi ciki, mutumin bai ma bari ya gama magana ba.
"Kullum sai neman ku
ɗ
i. Ni ba banki ba ne."
Jamil ya yi shiru.
Ya miƙe.
"Allah
Ya saka da alheri."
Ya fita ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Rana na ƙara tsanani.Gumi ya jiƙa rigarsa.
Cikinsa babu komai tun safe.amma bai damu da yunwa ba.
Abin da yake gani kawai shi ne fuskar Mamy kwance a kan gadon rashin lafiya.
Ya shiga wani
unguwaya yi knocking a ƙofa.
Wata mata ta fito.Da ta ga shi, ta ce,
"Lafiya?"
Ya yi mata bayanin halin da suke ciki.
Matar ta girgiza kai.
"Allah Ya ba ta lafiya. Amma ni ma ba ni da komai."
Ya gode ya juya.
Yana tafiya ƙafafunsa suna rawa saboda ga
jiya.
Ya tsaya ƙarƙashin wata bishiya.a jingina bayansa.
Idanunsa suka cika da hawaye.
"Ya Allah..."
Ya furta cikin raunin murya.
"Ban san ta ina zan shiga ba..."
Ya
ɗ
aga kansa sama.
"Ka ceci Mamy... Ka bu
ɗ
e mana wata hanya."
Hawayen da ya da
ɗ
e yan
a dannewa suka gangaro kan fuskarsa.
YSai dai babu lokacin yin kuka.
Ya sake miƙewa ya ci gaba da nema.
Har zuwa yamma...
Ba ko sisi.
Ba wanda ya taimaka masa.
Wasu sun ce ba su da shi.
Wasu sun yi masa alkawarin ƙarya.
Wasu kuwa ko sauraron matsal
arsa ba su yi ba.
A ƙarshe...
Jamil ya gaji.y a tsaya a bakin hanya.a zura hannu cikin aljihunsa.
Ku
ɗ
in da ke ciki ba su isa ko magani
ɗ
aya ba.ya lumshe idanunsa.
A karon farko...
Ya ji kamar rayuwa ta rinjaye shi.
Ya jawo ƙafafunsa da ƙyar ya nufi gi
da.
Tun bai ƙarasa bakin ƙofar gidan haya ba.Sai ya fara jin hayaniya.
Muryoyin mutane suna tashi sama, kuma mutane gidansu ne kasancewar gidan haya ne.
"Wai har yaushe za mu ci gaba da zama da wannan warin?"
"Wannan ai ya wuce kima!"
"Ba za mu iya
cin abinci ba!"
"Wai me ya sa ba sa kai ta asibiti?"
Jamil ya ƙara sauri.
Zuciyarsa ta fara bugawa.
Da ya shiga cikin harabar gidan...
Ya tarar da kusan duk masu gidan haya sun fito.
Wasu sun toshe hanci da mayafi.
Wasu suna girgiza kai cikin ƙyama.
A tsakiyarsu kuwa...
Laila ce tsaye.
Hawayenta na zuba babu ƙaƙƙautawa.
Hannayenta a ha
ɗ
e tana roƙonsu.
"Don Allah ku yi haƙuri."Wallahi ba don muna so ba. Muna ta neman hanyar kai ta asibiti. Ku yi mana afuwa."
Amma babu wanda ya saurare ta.
Wata
mata ta
ɗ
aga murya.
"Haƙuri? Haƙurin me?"
"Wallahi gidan nan ya kasa zama!Warin nan yana shiga
ɗ
akunanmu."
Wani dattijo ya ce cikin fushi,
"Idan ba za ku iya kula da mara lafiyan ba, ku fitar da ita."
Nan take Laila ta fashe da kuka.
"Don Allah..."
"Kada ku ce haka.Ita mahaifiyarmu ce.Wane
ɗ
a ne zai jefar da mahaifiyarsa a waje?"
Sai wata mata ta tabe baki.
"Mu ba ruwanmu."
"Mu ma muna da yara.Warin nan yana kashe mu."
Wani saurayi ya ce da tsawa,
"Kullum sai wari.Ba a iya zama lafiya."
"Wai ku
na jira ta mutu ne?"
Kalmar ta fa
ɗ
i kamar wuka a zuciyar Laila.
Ta dafe kirjinta.
"Kada ka fa
ɗ
i haka..Kada ka fa
ɗ
i haka don Allah..."
Amma sai suka fara yi musu zage-zage.
"Marasa kirki."
"Kun mayar da gidan nan kamar
ɗ
akin gawa."
"Ba ku da tausayi
ga sauran mutane."
Kalaman suna fa
ɗ
owa kan Laila kamar ruwan wuta.
Ta durƙusa a ƙasa tana kuka mai ban tausayi.
"Wallahi ba mu da ku
ɗ
i.Wallahi muna ta ƙoƙari."
"Don Allah ku yi mana haƙuri."
A dai-dai wannan lokacin Jamil ya shigo harabar gidan.
Ya t
saya cak Ya ga ƙanwarsa durƙushe tana kuka.Ya ga maƙwabta suna ta masifa.
Ya kuma ji warin da ke fitowa daga
ɗ
akin Mamy, warin da rashin lafiya ta haddasa bayan kwanaki ana fama ba tare da an samu cikakkiyar kulawa ba.
Jamil ya runtse idanunsa.Hawaye mas
u zafi suka sauko ba tare da izininsa ba.Ya ji zuciyarsa kamar ta tarwatse.
Ba don zagin da ake yi musu ba...Ba don talaucin da ya addabe su ba...Sai don ya kasa