Showing 51001 words to 54000 words out of 191594 words

Chapter 18 - MAKAHO NE COMPLETE

daga bene.

Ta tsaya cak.

Abin farko da idanunta suka gani shi ne Fahad

yana rungume da Nadra ta baya hannayensa na yawo a saman cikinta.

Wani irin k

ishi ya cika zuciyarta.

Sai dai ta

ɓ

oye komai.

Ta yi murmushi.

"Ashe na katse ku?"

Fahad ya saki Nadra.

"A'a. Zo mu karya."

Suka zauna.

Farida ta zauna a gefen Fahad.

Duk da cewa akwai sauran kujeru.

Nadra ta lura.

Ta ci gaba da zuba tea ba tare

da ta ce komai ba.

Ana cikin cin abincin sai wayar Fahad ta yi ƙara.

Ya duba.

"Minister."

Ya miƙe.

"Ku ci gaba, zan dawo."

Da zarar ya fita...

Shiru ya ratsa tsakanin matan biyu.

Farida ce ta fara magana.

"Kin san me yasa na zauna kusa da shi?"

Nadra ta

ɗ

aga kai.

"A'a."

"Saboda na saba."

Nadra ta yi mamaki.

"Na saba zama kusa da shi tun muna yara."

Ta

ɗ

an yi dariya.

"Kuma zan iya sake sabawa."

Nadra ta ajiye cokalin hannunta a hankali.

Ta ce cikin sanyin murya,

"Farida."

"Na'am?"

"Kin

zo nan ne domin karatu. Ina fata wannan shi ne abin da zai fi

ɗ

aukar hankalinki."

Farida ta yi murmushi.

"Kina bani shawara ne?"

"Ina tuna miki manufar zuwanki."

Farida ta jingina da kujera.

"Ke kina tsoro na."

Nadra ta girgiza kai.

"Ba na tsoron ko

wa."

"Sai dai kina tsoron rasa mijinki."

Nadra ta yi shiru na daƙiƙa ka

ɗ

an.

Sannan ta ce cikin natsuwa,

"Namijin da Allah Ya rubuta zai kasance tare da matarsa, ba saboda wata mace ta yi ƙoƙari ba."

Farida ta yi murmushin raini.

"Za mu gani."

A dai-

dai lokacin Fahad ya dawo.

Ya tarar da su duka suna murmushi.

Sai ya ce,

"Da alama kun fara sabawa da juna."

Nadra ta amsa cikin ladabi.

"In sha Allah."

Farida kuwa ta ce a zuciyarta,

"Eh... na fara. Amma ba sabawa ba ne..."

"Yaƙi ne kawai bai fara

bayyana ba."

A can saman bene kuwa, tsohon mai gadin gidan, Malam Bashir, ya hango duk yadda Farida ke kallon Fahad tun daga zuwanta.

Ya girgiza kai a hankali.

Ya furta cikin ƙasa-ƙasa,

"Ya Allah... Ka tsare wannan gida. Domin idan zuciya ta ƙi yarda

da ƙaddara, fitina kan fara ne cikin murmushi."

_Abbi_

Ya kalli kowa dake cikin falon sanan ya yi gyaran murya.

Ya kalli Jalaluddeen da Ma'eesha sanan ya kalli Dada.

"Wanan ne zama da nake so ayi domin warware matsalar da ta tunkaro mana. Wanda a da

lilin haka ne ya sa na dakatar da auren Jalal da Yasmeen har sai mun gano gaskiyar lamarin .

Dada ta gyara zamanta a kan kujera. Tun da suka shigo idanunta ba su bar kallonsu ba.

Ta fara daga ƙafafunsu har zuwa fuskokinsu.

Ta sake kallonsu karo na biyu.

Sai ta mur

ɗ

e baki.

"Ku ƙaraso nan."

Muryarta ta fito da ƙarfi, har ta sa Ma'eesha ta yi firgigit.

Jalaluddeen ya ƙarasa gabanta.

"Na'am Dada."

Ta

ɗ

aga hannu ta hana shi magana.

"Shiru!"

Sai ta nuna shi da yatsa.

"Kai tsaya nan."

Ta kuma nuna Ma'eesha.

"Ke

ma tsaya kusa da shi."

Duk falon ya yi tsit.

Dada ta ci gaba da kallonsu cikin nazari.

Can sai ta ce,

"Ni ko idanuwana sun fara tsufa ne?"

Mom ta

ɗ

an yi murmushi.

"A'a Dada."

"To me nake gani haka?"

Ba wanda ya amsa.

Ta nuna rigar Jalaluddeen.

"Wannan kay

an ba su ne ka fita da su ba."

Sai ta juya ga Ma'eesha.

"Ke kuma... wannan rigar fa?"

Ma'eesha ta kasa

ɗ

ago kai.

Dada ta

ɗ

aga murya.

"Na tambaye ki!"

Cikin sanyin murya Ma'eesha ta ce,

"Eh... ba ita ba ce."

"Aha!"

Dada ta buga cinyarta.

"Na sani!"

Ta juya

tana kallon Mom da Dad.

"Kun ji ko? Ban yi ƙarya ba."

Mom ta dafe goshinta tana murmushi.

Dad kuwa ya

ɗ

an sosa gemunsa yana

ɓ

oye dariya.

Dada ta sake juyowa gare su.

"To ku gaya min. Daga asibiti ina kuka bi har kuka samu damar yin wanka, kuka sauya kaya,

kuka fito kamar masu shirin zuwa walima?"

Shiru.

Jalaluddeen ya

ɗ

an motsa baki.

"Dada..."

"Kar ka ce min Dada! Ni ba yarinya ba ce."

Ta sake kallon Ma'eesha.

"Ke kuwa ba ki da wayo sam."

Ma'eesha ta lumshe ido saboda kunya.

"Wai ya ce miki mu tafi, kika bi

shi kawai? Ko tambayarsa ba ki yi ba?"

Ma'eesha ta ce a hankali,

"Na yi..."

"Ya ce miki me?"

Ta yi shiru.

Dada ta

ɗ

aga hannu.

"Kin gani? Ya yi miki wayo."

Mom ta kasa riƙe dariyarta, sai ta juya gefe.

Dad ma murmushi kawai yake yi.

Dada ta ci gaba,

"Mutan

e suna nan suna ta fama da tashin hankali. Ni har na fara tunanin ko wani ya sace ku. Ashe ranku yana can kuna hutu."

Ta sake nuna kayan jikinsu.

"Shaidar laifi tana jikinku. Kun yi wanka, kun canza kaya. Ai ba sai kun fa

ɗ

a min ba, idanuwana suna gani."

Ma

'eesha ta ji kamar ƙasa ta bu

ɗ

e ta shige saboda tsananin kunya.

Jalaluddeen ya yi murmushi ka

ɗ

an.

"Dada, ki saurare ni..."

"Ba zan saurare ka ba! Kai ne shugaban wannan shiriritar."

Sai ta juya ga Mom.

"Ke Fatima, ki kula da

ɗ

anki. Yana ta yaudarar yarinya

kamar ba ta da iyaye."

Mom ta girgiza kai tana dariya. Duk da ba su san yaushe ya aure ta ba amma suna da cikakken yaƙini akan Ɗan su ba zai aikata fasiƙanci ba. Ita da Dad sun yarda da Ɗansu.

"Wallahi Dada, ni ma ban san inda suka shiga ba."

Dada ta sake

hararar Jalaluddeen.

"Yanzu dai Allah Ya kawo ku lafiya. Amma idan ka sake

ɗ

aukar yarinya ka

ɓ

oye ba tare da an san inda kuka je ba, sai na sa a kama ka."

*Maman Ihsan ce*✍



[7/13, 9:00 AM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*

_BOOK 2_

*NA*

Maman Ihsan ce✍



*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*

"LITTAFINA NA KUƊI NE KADA KI KARANTA MANI LITTAFI BA TARE DA KIN BIYA NI HAKKINA BA. NAIRA DUBU ƊAYA NE KACAL . A TURA NAIRA DUBU ƊAYA CIKIN WANAN ACCOUNT 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank. Sai a tura shaidar bi

ya ta wanan lambar waya. 09065327995.

Page1





1





0





Dada ta sake hararar Jalaluddeen.

"Yanzu dai Allah ya kawo ku lafiya. Amma idan ka sake

ɗ

aukar yarinya ka

ɓ

oye ba tare da an san inda kuka je ba sai na sa an kama ka."

Kallonnta kawai Jalaluddeen y

a yi tare da girgiza kai, da ba domin iyayensa dake wajan ba to da zai ba ta amsa daidai da kalamanta.

"Jalaluddeen."

Abbi ya kira sunan sa."

"Na'am Abbina."

"Ina son ka bani amsar tambayar da zan yi ma ka. Wace ce wanan yarinyar a wajen ka?"

"Abbi

wallahi tallahi matata ce ta sunnah."

Tsit falon ya yi ana sauraren abun da Jalaluddeen yake fa

ɗ

a

"Ko za ka iya fada mana yadda ka aure ya ba tare da sanin mu ba"

Nan

Nan ya ba su labarin abun da ya faruwa tun daga ranar da ya faru tun ha

ɗ

uwarsa da

Mummy, ranar da ya taimake ta har ta kawo shi gidanta ta ce dnga zuwa kar

ɓ

ar abinci ta rasu. Da yadda aka aka aura ma sa Ma'eesha da zaman wahalar da ta yi da shi ba tare da sanin ko waye ba. Har zuwa ranar da ta ja yana waya akan zai auri Yasmeen, ta kw

anta asibiti wamda daga na bai sake sake ganinta ba sai wajen dinner party na aure na da Yasmeen. Amma wallahi matata ce ita."

Shiru ya ratsa falon ba wasu mintuna. Abbi ya kalli Ma'eesha ya ce .

"Ke ma ina sauraren bayanin ki."

Nan ta bayar da labarin

kamar yadda Jalaluddeen ya fada. Sai dai ta bayar har da haduwar ta dangin Mahaifiyarta . Wanda sai a lokacin Jalaluddeen ya san cewa Mahaifiyarsa ita ce yar mahaifiyar Ma'eesha. Domin ya dauka sun hadu ba ta da kowa ne suka taimaka mata

Jalaluddeen y

a yi farin ciki da da jin wannan labarin. Har murnar sa ta ki

ɓ

oyiwa.

_Yasmeen_

Yasmeen na zaune a kan doguwar kujera, kanta a jingine da matashin kujera. Idanunta sun kumbura saboda yawan kuka. Tun da aka

ɗ

aga

ɗ

aurin aurenta da Jalaluddeen, rayuwarta

ta sauya gaba

ɗ

aya. Ta daina walwala, ta daina cin abinci yadda ya kamata, har ma ta daina kula da kanta.

Ummee ta fito daga

ɗ

akin girki da kofin madara mai

ɗ

umi a hannunta. Ta ƙarasa kusa da Yasmeen ta zauna, sannan ta shafa bayanta a hankali.

"Kar

ɓ

i ki

sha, 'yata."

Yasmeen ta girgiza kai.

"Ba na jin yunwa, Ummee."

Ummee ta yi murmushi mai cike da tausayawa.

"Ba wai saboda yunwa ba. Ki sha don jikinki ya samu ƙarfi. Kukan nan ba zai canja ƙaddara ba."

Yasmeen ta runtse idanunta, hawaye masu zafi suka sake

zubo.

"Ummee... me ya sa Allah ya bar abin nan ya faru da ni? Me na yi?"

Ummee ta ja ta jikinta, ta rungume ta tamkar ƙaramar yarinya.

"Ki daina fa

ɗ

in haka. Allah ba ya zaluntar bayinsa. Wataƙila akwai alherin da ba mu gani ba."

"To ina alherin?" Yasmeen

ta fashe da kuka. " kowa ya san ni matar Jalaluddeen ce. Ke kika raina shi, kika raini ni. Ni ma zuciyata ta ginu a kansa... sai kwatsam komai ya rushe."

Ummee ta sauke numfashi mai nauyi.

Ta san gaskiya.

Tun lokacin da ta

ɗ

auko Jalaluddeen ta raina shi t

a kasance tana kallonsa tamkar

ɗ

anta. A zuciyarta kuwa ta da

ɗ

e da burin ha

ɗ

a shi da Yasmeen domin su ci gaba da zama iyali guda.

Sai dai ƙaddara ta zo dabam.

"Yasmeen..." Ummee ta kira sunanta cikin lallashi. "Ki saurare ni da kyau."

Yasmeen ta

ɗ

ago tana g

oge hawayenta.

"Jalaluddeen ba mugun yaro ba ne. Idan ya ce a dakata, akwai dalilinsa. Ban yarda ya watsar da ke haka kawai ba."

"Amma ya yi."

"Bai yi ba."

"Ya yi, Ummee!"

Ta sake fashewa da kuka.

"Da yana sona da bai bari a

ɗ

aga

ɗ

aurin aurenmu ba."

Ummee

ta kama hannunta.

"Ki daina yanke hukunci cikin fushi. Na san Jalaluddeen fiye da yadda kowa ya san shi. Na raina shi da hannuna. Idan ya yi shiru, ba yana nufin ya daina ƙauna ba ne."

Yasmeen ta girgiza kai.

"Ban san abin da zan yi ba."

Ummee ta shafa kan

ta.

"Ki yi haƙuri. Ki rage wannan damuwar. Wallahi zan tabbatar kin auri Jalaluddeen."

Yasmeen ta

ɗ

ago da sauri.

"Da gaske?"

"In sha Allah."

"Amma ya ƙi fa."

Ummee ta

ɗ

an yi murmushi.

"Ni ce Ummeensa. Ko da ba na haifarsa ba, ya san babu abin da zan ce mas

a face alheri. Zan yi magana da shi. Zan nemo abin da ya sa ya canja ra'ayi. Idan akwai matsala za a warware ta."

Wani

ɗ

an haske ya bayyana a fuskar Yasmeen.

"Kin tabbata?"

"Na tabbata."

Ta share mata hawaye da gefen mayafinta.

"Saboda haka daga yau ba na

son ganin kina kuka. Ki ci abinci, ki kula da kanki. Idan Allah Ya ƙaddara ke ce matarsa, babu wanda zai iya hanawa."

Yasmeen ta gyada kai a hankali, duk da zuciyarta ba ta gama yarda ba.

A dai-dai lokacin...

Tirr...!

Ƙ

arar saƙon waya ta katse shiru.

Ummee

ta

ɗ

an waigo inda wayarta take kan ƙaramin tebur.

Ba kasafai take samun saƙo cikin dare ba.

Ta miƙa hannu ta

ɗ

auki wayar cikin sanyin jiki.

Da ta danna allon wayar...

Sunan wanda ya aiko ya bayyana.

Numfashinta ya tsaya cak.

Idanunta suka bu

ɗ

e sosai.

"Wan

e ne wannan?" Yasmeen ta tambaya tana kallonta.

Amma Ummee ba ta amsa ba.

Ta bu

ɗ

e saƙon.

Da zarar idanunta suka sauka kan rubutun farko...

Jikinta ya yi sanyi.

Wayar ta kusan zamewa daga hannunta.

Ta tashi tsaye a zabure, zuciyarta na bugawa da ƙarfi har a

na iya ganin motsin kirjinta.

"Innalillahi..."

Ta furta cikin murya mai rauni.

Yasmeen ta miƙe da sauri.

"Ummee! Me ya faru?"

Ummee ta ci gaba da kallon wayar cikin firgici, kamar ba ta yarda da abin da idanunta suke gani ba.

Ta sake karanta saƙon.

Sau

ɗ

ay

a...

Sau biyu...

Sau uku...

Ko ka

ɗ

an kalmomin ba su sauya ba.

Hannunta ya fara rawa.

Fuskarta ta sauya launi.

A hankali ta

ɗ

aga idanunta ta kalli Yasmeen, amma ta kasa furta ko kalma

ɗ

aya.

Saƙon da ke kan wayar ya isa ya girgiza rayuwarta gaba

ɗ

aya...

Ya

smeen ta ci gaba da kallon fuskar Ummee cikin tsoro.

"Ummee... don Allah ki fa

ɗ

a min me ya faru."

Ummee ta yi ƙoƙarin ha

ɗ

iye miyau, amma maƙogwaronta ya bushe. Hannunta har yanzu yana rawa yayin da ta miƙa mata wayar.

"Karanta..."

Yasmeen ta kar

ɓ

i waya

r da sauri.

Da zarar idanunta suka sauka kan saƙon, sai ta ji kamar ƙasa ta tsage ta fa

ɗ

a cikinta.

«"An bar Ma'eesha a gidan Jalaluddeen. Ita ce matarsa ta halal. Aurensu tun da

ɗ

ewa aka

ɗ

aura a

ɓ

oye."»

Wayar ta ku

ɓ

uce daga hannunta ta fa

ɗ

i kan kujera.

"A'a..."

Ta girgiza kai da ƙarfi.

"A'a... wannan ƙarya ce... ba zai yiwu ba... ba Jalaluddeen ba ne..."

Hawaye suka cika idanunta.

"Ummee, ki ce ƙarya ce!"

Amma Ummee ta riga ta fusata.

Fuskarta ta sauya gaba

ɗ

aya.

Idanunta suka yi jajur tamkar garw

ashi.

"Na rantse da Allah idan wannan gaskiya ne..."

Ta

ɗ

auki mayafinta da sauri tana

ɗ

aurawa.

"...yau sai an ji ni!"

Ta juya tana kallon Yasmeen.

"Ki tashi!"

Yasmeen ta kalle ta cikin ru

ɗ

ani.

"Ina za mu je?"

"Gidan Yaya! Wato har tamabya kike yi g

a shi can ana ƙulla munafurci za'a raba ki da Jalaluddeen.

Ta

ɓ

e baki ta yi.

" Ashe suna

ɗ

aukar ta wawiya ce? Ashe ni ba komai ba ce a gidan nan?"

Ta bu

ɗ

e ƙofa da ƙarfi.

"Ki zo mu tafi!"

Yasmeen ta share hawayenta da sauri ta bi bayanta.

---

Bayan m

intuna ka

ɗ

an...

Motar Ummee ta tsaya da wani irin ƙarar birki a harabar gidan Dad.

Masu gadi suka yi saurin bu

ɗ

e ƙofa saboda sun san motarta.

Tun kafin motar ta tsaya cak, Ummee ta bu

ɗ

e ƙofar ta fito.

Fuskarta cike take da fushi.

Tafiyarta ma ta nuna

cewa yau ba zaman lafiya ya kawo ta ba.

Yasmeen na biye da ita a baya, idanunta jajaye saboda kuka.

Da suka shiga falon gidan...

Dad, Mom, Dada, Abbi, Alhaji Sulaiman, Hajiya

Da suka ga yanayin fuskar Ummee, gaba

ɗ

ayansu suka

ɗ

aga kai.

"Ummee, lafiya

kuwa?"

Ba ta zauna ba.

Ba ta gaisa ba.

Tsaye ta yi a tsakiyar falon.

"Tambayar lafiya za ka yi min?"

Dad ya

ɗ

an daure fuska.

"Me ya faru?"

"Dama kun yanke shawarar Jalaluddeen zai zauna da yarinyar nan a matsayin matarsa?

Um

Shiru ya yi.

Wannan

shiru ne ya ƙara fusata Ummee.

"Ka yi shiru kenan?"

Ta

ɗ

aga murya.

"Ka san abin nan?"

Mom ta shiga tsakanin maganar.

"Ummee, ki kwantar da hankalinki..."

"Ba zan kwantar ba!"

Ta katse ta da ƙarfi.

"Wallahi ba zan kwantar ba!"

Ta juya ta kalli Dad.

"Ni na raini Jalaluddeen!"

Ta danna ƙirjinta da hannu.

"Ni na raine shi tun yana shekara

ɗ

aya kacal a duniya! Ni na ba shi abinci! Ni na yi masa wanka! Ni na kwantar da shi! Ni na tashi da shi dare da rana!"

Muryarta ta fara rawa saboda baƙin ciki.

"

Na

ɗ

auke shi tamkar

ɗ

ana!"

Ta share hawayen da suka cika idanunta.

"Amma yau..."

Ta yi dariyar takaici.

"...yau har za a zauna a yanke irin wannan babbar shawara ba tare da an sanar da ni ba?"

Ta sake kallon Dad.

"Wato ni ba ni da wani matsayi kenan?

"

Dad ya bu

ɗ

e baki zai yi magana.

Sai ta

ɗ

aga hannu ta hana shi.

"A'a! Ka bari na gama!"

Falon ya yi tsit.

Ko masu aiki da ke gefen

ɗ

aki sun kasa motsi.

Ummee ta ci gaba.

"Na shekara da shekaru ina rainon Jalaluddeen, ina kallonsa a matsayin

ɗ

ana. T

un yana ƙarami an san cewa Yasmeen za ta aure shi."

Ta kamo hannun Yasmeen ta jawo ta gaba.

"Ga yarinyar nan."

Yasmeen ta sunkuyar da kai, hawaye na zuba ba ƙaƙƙautawa.

"Kun bar ta ta rayu da wannan buri."

Ta sake

ɗ

aga murya.

"Yanzu saboda me za ku z

o ku ce wai ya yi aure a

ɓ

oye?"

Ta girgiza kai.

"Wallahi ban yarda ba!"

Ta nuna Dad da yatsa.

"Ko wanene ya shirya wannan aure, ya yi kuskure."

Dad ya ce cikin sanyin murya,

"Ummee, ki zauna mu yi magana cikin natsuwa."

"Natsuwa?"

Ta maimaita.

"Wa

ce natsuwa?"

"An cuce ni! An cuce 'yata! An ci amanar amanar da na yi shekaru ina riƙewa!"

Numfashinta ya fara

ɗ

aukar nauyi.

Sai ta furta cikin murya mai cike da ƙuduri.

"Na fa

ɗ

a kuma zan sake fa

ɗ

a."

Ta kalli kowa

ɗ

aya bayan

ɗ

aya.

"Ba zan ta

ɓ

a yarda

Yasmeen ta rasa Jalaluddeen ba."

Ta

ɗ

ora da ƙarfi.

"Dole Jalaluddeen ya auri Yasmeen."

Kalaman nata suka sauka a falon tamkar tsawar aradu.

Kowa ya yi shiru.

Dad ya runtse idanunsa na

ɗ

an lokaci,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login