Showing 180001 words to 183000 words out of 191594 words

Chapter 61 - MAKAHO NE COMPLETE

farko.

“Wa

ɗ

annan ku

ɗ

a

ɗ

en ne.”

Jalaluddeen ya kalli ku

ɗ

a

ɗ

en na

ɗ

an lokaci.

Sai Taj ya bu

ɗ

e wani.

“Wa

ɗ

annan takardun kadarori ne. Wasu daga cikin takardun gidaje, filaye da wasu kadarorin kasuwanci da na kam

faninsa..”

Jalaluddeen ya

ɗ

auki takardun ya duba su a hankali.

“An tabbatar da su yadda ya kamata kuwa ?”

“Eh. An bincika su.”

“Madalla.”

Sai Taj ya

ɗ

auko wata ƙaramar jaka yana nuna masa

“Wannan kuma an same ta cikin abubuwan da aka tattara.”

Jala

luddeen ya bu

ɗ

e jakar.

A ciki akwai gwala-gwalai masu daraja.

Ma’eesha wadda ta sauka daga motar a hankali ta tsaya a bakin ƙofar tana kallon abin da ke faruwa.

Taj ya ce,

“Duk abin da aka samu an tattara shi nan.”

Jalaluddeen ya

ɗ

an yi shiru.

Sai ya

ce kafin kuma ya ce

“Ajmal ya ce komai yana nan?”

“Eh.”

“Madalla.”

Ya rufe ƙaramar jakar.

Ya fara

ɗ

aukar abubuwan

ɗ

aya bayan

ɗ

aya.

Ku

ɗ

a

ɗ

en.

Takardun.

Jakar gwala-gwalai.

Sai sauran abubuwan da aka tattara.

Ya kai su mota.

Taj da Jalaludden suk

a taimaka masa.

Jalaluddeen ya bu

ɗ

e bayan motar, ya tsara kayan cikin tsari sannan ya rufe murfin.

Ya tsaya na

ɗ

an lokaci yana kallon motar.

Wannan dukiyar ba ta kasance masa ba.

Ba ta Ma’eesha ba ce.

Amma yana jin nauyin amanar da ke kansa.

Ya koma

wajen Ma’eesha.

“Komai yana nan.”

Ta kalle shi.

“Za mu je gidan Daddy kenan?”

“Eh.”

“Allah Ya sa ya kar

ɓ

a.”

Jalaluddeen ya yi murmushi ka

ɗ

an.

“Wannan shi ne abin da nake so, kuma dole ya karbi dukiyarsa ai

Suka shiga mota.

Motar ta kama hanyar gi

dan Daddy.

A cikin motar, Ma’eesha ta yi shiru na

ɗ

an lokaci.

Sai ta ce,

“Yaya Jalaluddeen.”

“Hmm?”

“Ka ta

ɓ

a tunanin Daddy zai yarda da duk abin da ka yi?”

Ya

ɗ

an yi shiru.

“Ba na buƙatar ya yarda da ni.”

Ta kalle shi.

“Me kake nufi?”

“Ina buƙata

r ya san gaskiya. Kuma ya san cewa duk abin da na yi, domin kare shi ne.”

Ma’eesha ta yi murmushi.

“Zai fahimta.”

Jalaluddeen ya kalleta. Tare da cewa

“Allah Ya sa.”

*GIDAN DADDY*

Bayan wani lokaci, motar ta shiga harabar gidan Daddy.

Ma’aikatan

gidan suka fara kallon motar yayin da ta shigo.

Ma’eesha ta kalli gidan.

Zuciyarta ta buga da ƙarfi.

A yau ba za su dawo wannan gidan da hannu wofi ba. Bayan parking motar ne

Jalaluddeen ya yi parking.

Ya sauka sannan ya bu

ɗ

e wa Ma’eesha ƙofar.

“Ki

sauka a hankali.”

Ta sauka.

Jalaluddeen ya kalli bayan motar.

“Ki zo.”

Suka nufi cikin gidan.

Da suka shiga falon, Daddy yana zaune.

Da ya ga Ma’eesha sai fuskarsa ta haskaka.

“Ma’eesha!”

Ta matsa kusa da shi.

“Daddy.”

Ya miƙe da sauri kamar wand

a ya da

ɗ

e yana jiran ganinta.

Ya rungume ta.

“Yaya jikinki?”

“Lafiya kalau.”

Ya kalli cikinta.

Sai murmushi ya bayyana a fuskarsa.

“Yaron nan yana lafiya?”

Ma’eesha ta yi murmushi.

“Lafiya.”

Daddy ya yi dariya cikin farin ciki.

“Alhamdulillah.”

Sai ya kalli Jalaluddeen.

“Ku zo ku zauna.”

Jalaluddeen ya zauna.

Ma’eesha ma ta zauna kusa da Daddy.

Amma Jalaluddeen bai yi dogon zama ba.

Ya ce,

“Daddy, akwai wani abu da nake son gaya maka.”

Fuskar Daddy ta sauya.

“Me ya faru?”

“Babu abin da y

a faru. Amma akwai wani abu da na yi a

ɓ

oye.”

Daddy ya kalle shi cikin mamaki.

“Ka yi me?”

Jalaluddeen ya

ɗ

an yi shiru.

“Na fara bincike kan dukiyar gidan.”

Daddy ya sunkuyar da kai.

Wannan kalmar ta ta

ɓ

a wani tsohon ciwo a zuciyarsa.

“Dukiyata…”

Y

a yi ajiyar zuciya.

“Na yi tunanin ta tafi.”

Jalaluddeen ya kalle shi.

“Ba ta tafi ba.”

Daddy ya

ɗ

aga kai da sauri ya ce.

“Me?”

“Na ce ba ta tafi ba.”

Daddy ya kasa magana.

Jalaluddeen ya ci gaba.

“Na gano yadda abubuwa suke tafiya. Na kuma gano c

ewa akwai wa

ɗ

anda suke ƙoƙarin kwashe abin da ya kamata ya kasance naka.”

Daddy ya fara girgiza kai.

“Jalaluddeen…”

“Ka saurare ni, Daddy.”

Ya ci gaba da bayanin duk abin da ya faru.

Ya gaya masa yadda ya tura mutumin nasa.

Yadda mutumin ya shiga gid

an.

Yadda ya samu kusanci da Laila.

Yadda aka tattara wasu daga cikin dukiyar.

Yadda Taj ya kar

ɓ

a.

Yadda aka tattara ku

ɗ

a

ɗ

e da takardu da sauran abubuwan da suka shafi kadarorin.

Daddy yana sauraron sa.

A hankali idanunsa suka fara cika da hawaye.

J

alaluddeen ya gama bayanin.

Sai ya ce,

“Na kawo maka abin da aka samu.”

Daddy ya kalle shi.

“Ina?”

Jalaluddeen ya miƙe.

“Yana mota.”

Daddy ya kasa tashi nan take.

“Ka… ka dawo min da shi?”

“Eh..

Hawaye suka fara zuba daga idanun Daddy.

“Bayan du

k abin da na rasa…”

Ya kasa ƙarasa maganar.

Jalaluddeen ya matso kusa da shi.

“Daddy.”

Daddy ya riƙe hannunsa.

“Ka dawo min da dukiyata?”

“Eh.”

Daddy ya miƙe.

Sai ya rungume Jalaluddeen da ƙarfi.

Rungumar ba ta kasance irin ta yau da kullum ba.

R

ungumar mutum ce da ya ga abin da yake tunanin ya rasa har abada ya dawo masa.

Hawaye suka cika fuskar Daddy.

“Allah Ya saka maka da alheri,

ɗ

ana.”

Jalaluddeen ya rufe idanunsa.

“Daddy…”

“Na yi tunanin komai ya ƙare.”

Daddy ya ƙara matsa shi a jikins

a.

“Na yi tunanin ban da komai. Na yi tunanin duk abin da na tara a rayuwata ya tafi.”

Jalaluddeen ya ce a hankali,

“Ba zai tafi ba.”

Daddy ya rabu da shi, ya kama fuskarsa da hannayensa.

“Me ya sa ka yi min haka?”

Jalaluddeen ya yi murmushi cikin la

dabi.

“Saboda kai mahaifin matata ne.”

Daddy ya kalli Ma’eesha.

Ta kasa riƙe hawaye.

“Daddy…”

Ya juya ya kalleta.

Sai ya bu

ɗ

e hannayensa.Ma’eesha ta matso.Daddy ya rungume ’yarsa.

“Ke ma Allah Ya miki albarka.”

Ta fashe da kuka a kafadarsa.

“Daddy

…”

“Kin ga mijinki?”

Ta gyada kai tana kuka.

“Eh.”

“Ki riƙe shi da kyau.”

Sai Daddy ya kalli Jalaluddeen.

“Ba wai saboda dukiyar ba.”

Jalaluddeen ya kalle shi.

“Saboda me?”

“Saboda ka nuna min cewa har yanzu akwai wanda yake tunanin abin da zai fa

ru da ni.”

Ya share hawayensa.

“Na gode.”

Jalaluddeen ya ce,

“Babu komai, Daddy.”

“Ba ka san irin abin da ka yi min ba.”

Daddy ya zauna a hankali.

“Na dade ina kallon dukiyata tana fita daga hannuna. Amma ban iya hana komai ba.”

Ya sauke kansa.

“Y

anzu ka dawo min da abin da na yi shekaru ina tarawa.”

Jalaluddeen ya ce,

“Ba zan tsaya nan ba.”

Daddy ya

ɗ

aga kai.

“Me kuma?”

“Za mu tabbatar an kare abin da ya rage. Ba za a sake barin kowa ya samu damar kwashe dukiyarka ba.”

Daddy ya kalli Jalalud

deen na dogon lokaci.

Sai ya ce,

“Allah Ya ƙara maka basira.”

“Amin.”

A wannan lokacin wani ma’aikaci ya shigo.

“Sir.”

Jalaluddeen ya juya.

“Je ka bu

ɗ

e bayan motar.”

“Okay, sir.”

Bayan

ɗ

an lokaci aka kawo akwatunan cikin falon.

Daddy ya kalli abi

n da aka shigo da shi.

Jalaluddeen ya nuna masa.

“Ga ku

ɗ

a

ɗ

en.”

Sai aka kawo takardun.

“Ga takardun kadarorin.”

Daga ƙarshe aka kawo ƙaramar jakar.

Jalaluddeen ya bu

ɗ

e ta.

Gwal-gwalai suka bayyana.

Daddy ya rufe idanunsa.

Hawaye suka sake zubo masa

.

“Subhanallah…”

Ya

ɗ

aga hannu zuwa fuskarsa.

“Na yi tunanin ban sake ganin wa

ɗ

annan ba.”

Ma’eesha ta matso kusa da shi.

“Daddy…”

Ya

ɗ

aga hannu ya dakatar da ita.

“Ki bar ni.”

Ya kalli dukiyar.

“Wannan ba ku

ɗ

i ba ne kawai.”

Sai ya kalli Jalaludde

en.

“Wannan tarihin rayuwata ne.”

Jalaluddeen ya gyada kai.

“Na sani.”

Daddy ya sake kallonsa ya ce

“Allah Ya biya ka da mafificin alheri.”

Jalaluddeen ya ce,

“Amin.”

Daddy ya

ɗ

aga hannuwansa sama.

“Ya Allah, ka kare Jalaluddeen. Ka kare Ma’eesha

. Ka kare

ɗ

an da yake cikinta. Ka ba su zaman lafiya, ka nisanta su daga makiya, kuma ka sa abin da suka yi ya zama sanadin alheri a gare su.”

“Amin,” Ma’eesha ta amsa cikin kuka.

“Amin,” Jalaluddeen ma ya ce.

Daddy ya kalli Ma’eesha, sannan ya kalli Ja

laluddeen.

A wannan ranar, ba wai dukiyar Daddy ce kawai ta dawo ba.

Akwai wani abu mafi girma da ya dawo.

Amincewar uba ga mijin ’yarsa.

Kuma Jalaluddeen ya san cewa daga wannan rana, abin da ya fi muhimmanci shi ne tabbatar da cewa dukiyar ba za ta s

ake shiga hannun wanda ba shi da ikon ta ba.

*Maman Ihsan ce*✍



[8/10, 8:12 PM] Antysalima Grp: 1





6





7





Kuma Jalaludden ya san cewa daga wannan rana abin da ya fi muhimmanci shi ne tabbatar da cewa dukiyar ba za ta sake shiga hannun wanda ba shi da

ikon ta ba.

Daga nan Ma'eesha ta sanar da Daddy za ta je gidan kakanninta.

A tare da Jalaludden suka bar gidan. Tana zaune a mazaunin direba yayin da take zaune a gefensa.

Motar Jalaluddeen ta bar harabar gidan Daddy a hankali.

Bayan sun bar layin gid

an Daddy KoJalaluddeen na driving a hankali Ma'eesha ta gyara hijabinta sannan ta jingina da kujerar, tana kallon titin da ke gabansu.

Sun nufi gidan Alhaji Babba.

A hankali motar ke tafiya, iska tana shigowa ta

ɗ

an bu

ɗ

a

ɗɗ

en gilashin mota. Jalaluddeen ya

na mai da hankali sosai kan tuƙi, lokaci-lokaci yana kallon Ma’eesha daga gefen ido.

Ma’eesha kuwa tana cikin wani irin natsuwa.Duk da farin cikin da ta ji a gidan Daddy, akwai wani abu a zuciyarta da bai gama kwanciya ba.

Ta

ɗ

ora hannunta a kan cikinta.

Jalaluddeen ya kalleta ya ce

“Kin gaji?”

Ta girgiza kai tana murmushi ta ce .

“A’a.”

“Ko akwai wani abun da kike buƙata?"

Ta yi murmushi.

“A’a, kawai ina tunani ne.”

“Me kike tunani?”

“Ban sani ba.”

Jalaluddeen ya yi murmushi sanan ya ce

“Kin

fara zama mai yawan tunani.”

Ta kalle shi.

“Ni fa?”

“Eh.”

Ta yi

ɗ

an dariya sanan ta kalle shi ta kau da kai daga kallonsa

“Ka daina.”

“Shikenan na daina."

Motar ta ci gaba da tafiya. Bayan

ɗ

an lokaci, Ma’eesha ta

ɗ

ago kai tana kallon gefen hanya.

Sai kwatsam idonta ya tsaya kan wasu mutane biyu da suke tafiya a gefen titi.

Wani saurayi ne da wata budurwa.

Saurayin yana tafiya a hankali, jikinsa ya rame sosai. Tufafinsa sun yi masa girma saboda yadda jikinsa ya yi ƙanƙanta. Fuskar sa ta yi duhu,

idanunsa sun yi zurfi kamar wanda ya kwashe kwanaki ba tare da samun cikakken barci ko abinci ba.

Budurwar da ke tare da shi ma ba ta fi shi ba.

Tufafinta sun yi mata ƙanƙanta, fuskarta ta rame, idanunta sun yi ja. Tana tafiya cikin rashin kuzari, kamar

wadda ta rasa wani abu mai girma a rayuwarta.

Ma’eesha ta kalle su na wasu dakiku.

Sai wani abu ya doki zuciyarta.

Ta sake kallon saurayin.

Sai ta bu

ɗ

e idanunta da mamaki.

“bYaua Jalaluddeen!”

“Hmm?”

“Ka dakata!”

Jalaluddeen ya kalleta cikin mamaki

.

“Me ya faru?”

“Ka dakata!”

Sautin muryarta ya nuna cewa akwai wani abu da ya faru.Jalaluddeen bai ƙara tambaya ba.

Ya kunna signal, ya rage gudun motar sannan ya faka a gefen hanya.

Da motar ta tsaya, Ma’eesha ta bu

ɗ

e ƙofa da sauri.

“Ma’eesha.”

Ba

ta saurare shi ba.Ta sauka daga motar.

Jalaluddeen ya kalleta ta madubi, sannan ya juya kansa yana kallonta.

Ma’eesha ta tsaya a gefen hanya.

Ta sake kallon saurayin. A wannan karon ta tabbatar.

Zuciyarta ta buga da ƙarfi.

Ta

ɗ

aga murya.

“Yaya Jamil

!”

Saurayin bai juyo nan take ba.

Sai da ya ji muryar ta sake maimaitawa.

“Yaya Jamil!”

Ya tsaya.A hankali ya juya.Da idanunsa suka sauka kan Ma’eesha, sai jikinsa ya tsaya cak.

Da madaukakin mamaki yake kallon ta.

Ya kalle ta kamar wanda yake ganin

wani mutum daga duniyar da ya yi imanin ba zai sake ha

ɗ

uwa da ita ba.

“Ma’eesha…”

Muryarsa ta fito a hankali. Ma’eesha ta matso kusa da shi.

“Yaya Jamil…”

Ta kasa ci gaba. Yadda ta gan shi ya karya mata zuciya.

Jamil wanda ta san shi a baya ba haka ya

ke ba.

A lokacin da ta san shi, yana da kuzari, yana da annashuwa, yana iya yin dariya har ya sa mutane su manta da damuwarsu.

Amma yanzu.Ya yi ƙanƙanta. Ya rame Ya yi baƙi.Fuskarsa ta rame.Kumatunsa sun shiga ciki.Idanunsa sun yi wani irin nauyi na damu

wa.

Ma’eesha ta

ɗ

aga hannu zuwa bakinta.

“Ya Allah…”

Jamil ya sunkuyar da kai.

Sai budurwar da ke tare da shi ta

ɗ

ago kanta.Ma’eesha ta kalleta.Ta gane ta.

“Laila…”

Laila ta kasa magana.

Sai hawaye suka fara zubo mata.Ta kalli Ma’eesha, sannan ta sun

kuyar da kanta.

“Ma’eesha…”

Jamil da Laila suka ha

ɗ

a baki.

“Ma’eesha.”

Muryoyinsu sun fito cike da rauni.Ma’eesha ta matso kusa da Laila.Ta kama hannunta.

“Laila.”

Laila ta fashe da kuka.Ma’eesha ta jawo ta jikinta.

“Ki daina kuka.”

Amma Laila ta ƙ

ara kuka.

“Ki daina, Laila.”

Ta shafa mata baya a hankali.

“Komai ya wuce.”

Laila ta girgiza kai tana kuka.

“Bai wuce ba, Ma’eesha.”

Ma’eesha ta kalleta.

“Me ya faru?”

Laila ta kasa amsawa.

Jamil ya tsaya yana kallonsu, idanunsa cike da hawaye.Ma’

eesha ta juya gare shi.

“Yaya Jamil, me ya same ku?”

Jamil ya sauke numfashi.

“Rayuwa ce”

“Wace irin rayuwa?”

Ya yi shiru.

Ma’eesha ta sake kallon Laila.

“Me ya faru da ke? Kin yi rama sosai.”

Laila ta share hawayenta da gefen hijabinta.

“Babu kom

ai.”

Ta ba ta amsa tana sunkuar da kai kasa. Ma'eeha ta sake tambayar ta.

“Laila, ki fa

ɗ

a min gaskiya.”

Laila ta kalli Jamil.Jamil ya sunkuyar da kai.Ma’eesha ta lura da yadda suka kalli juna.

Sai ta tambaya cikin damuwa.

“Ina Mamy?”

Suna jin ta amb

aci sunan Mamy, Laila ta rufe fuskarta da hannayenta.Jamil ya

ɗ

aga kai.Shiru ya mamaye wurin.

Ma’eesha ta sake tambaya.

“Ina Mamy?”

Jamil ya kasa magana.Laila ta fara kuka sosai.Ma’eesha ta matso kusa da ita.

“Laila, me ya faru da Mamy?”

Sai Jamil ya

furta cikin muryar da ta yi rauni.

“Ma’eesha... Mamy ta rasu.”

Kamar an buge ta da wani abu, Ma’eesha ta tsaya cak.

“Me?”

Jamil ya maimaita cikin hawaye.

“Mamy ta rasu.”

Ma’eesha ta

ɗ

aga hannu zuwa bakinta.

“Inna lillahi wa'inna alaihi raji'un."

Ha

wayenta suka fara zubo mata.

“Laa ilaha illallah…”

Ta girgiza kai.

“A’a…”

Jamil ya share hawayensa ya ce .

“Mun yi duk abin da za mu iya.”

Ma’eesha ta kalli Laila idanunta cike da ƙwalla ta ce.

“Yaushe?”

Laila ta kasa amsawa.

Jamil ne ya yi karfin

halin amsa wa ya ce .

“Ta rasu bayan rashin lafiyar ta ta tsananta.”

Ma’eesha ta rufe idanunta.Ta tuna Mamy.Tuna yadda take magana.Tuna yadda take yawan zama a cikin gidan. Tuna duk abubuwan da suka faru a baya.

Hawayenta suka ƙara zuba.

“Allah Ya jik

anta.”

“Amin,” Jamil ya amsa.

“Allah Ya gafarta mata.”

“Amin.”

“Allah Ya sa Aljanna ce makomarta.”

“Amin.”

Laila ta sake fashewa da kuka.Ma’eesha ta kama hannunta. Tana rarrashinta ta ce .

“Ki yi haƙuri.”

Cikin kuka da bakin ciki Laila ta ce.

“Ta

bar mu mu ka

ɗ

ai.”

“Allah ba Ya bar bayinsa.”

Laila ta kalleta cikin hawaye.

“Ba mu san inda za mu dosa ba.”

Ma’eesha ta ƙara kallon Jamil.

“Yanzu ina kuke?”

Jamil ya yi shiru.

Ma’eesha ta sake tambaya.

“Ina kuke zama?”

Ya yi ƙasa da murya yana ba

ta amsa cikin sanyin murya .

“Gidan haya.”

“Gidan haya?”

Ya gyada kai.

“Eh.”

“Ku biyu?”

“Eh.”

“Bayan Mamy ta rasu?”

“Eh amma tun kafin ta rasu muke tare da ita a gidan, nuna da yawa amma daki daya muka kama muke maneji .

Ma’eesha ta kasa magana na



ɗ

an lokaci.

Ta kalli Laila daga sama zuwa ƙasa.Sai ta kalli Jamil.

“Me ya sa ba ku zo gidan Daddy ba?”

Jamil ya yi murmushi mai cike da ciwo.

“Ba mu san ko za a kar

ɓ

e mu ba.”

Ma’eesha ta kalleshi cikin mamaki.

“Yaya Jamil, Daddy ba zai bar ku haka b

a. Matukar ya ji halin da kuke ciki zai tausaya maku."

Jamil ya sunkuyar da kai.

“Muna ji tsoro ne.”

“Tsoro?”

“Eh.”

Ma’eesha ta share hawayenta.

“Ku jira ni nan.”

Ta juya.

Jalaluddeen yana zaune a cikin motar yana kallonsu.

Tun lokacin da Ma’eesha

ta fito, bai katse mata ba. Ya ga yadda suka yi magana.Ya ga kuka.

Ya kuma fahimci cewa abin da ta gani ya shafi wani abu mai girma.

Ma’eesha ta bu

ɗ

e ƙofar motar ta shiga.

Jalaluddeen ya kalleta

“Me ya faru?”

Ta zauna, sannan ta share hawayenta.

“Ya

ya Jalaluddeen…”

“Hmm?”

“Ka san wanda na gani?”

“Jamil da Laila?”

Ta

ɗ

aga kai.

“Eh.”

Jalaluddeen ya kalle ta.

“Me ya same su?”

Ma’eesha ta

ɗ

an yi shiru.

“Mamy ta rasu.”

Jalaluddeen ya yi shiru.

“Allah Ya jikanta.”

“Amin.”

Ma’eesha ta ci gaba d

a magana cikin muryar da ta cika da tausayawa.

“Ka ga yadda suke?”

“Na gani.”

Ta cigaba da magana cikin tausaya wa.

“Sun rame sosai.”

“Na gani.”

“Sun fita hayyacinsu.”

Jalaluddeen ya

ɗ

an sauke numfashi.

“Yanzu ina suke?”

“Gidan haya suke.”

Jalalu

ddeen ya kalleta.

“Gidan haya?”

“Eh.”

Ma’eesha ta kama hannunsa.

“Yaya Jalaluddeen.”

“Na ji.”

“Ina son mu

ɗ

auke su.”

Ya kalleta.

“Mu

ɗ

auke su?”

“Eh.”

“Ina za mu kai su?”

“Gidan Daddy.”

Jalaluddeen ya yi shiru.

Ma’eesha ta ci gaba da roƙo.

“Do

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login