Showing 54001 words to 57000 words out of 191594 words
sannan ya bu
ɗ
e su a hankali.
Ya kalli Ummee cikin nuts
uwa, kafin ya ce da muryar da ba ta nuna fushi ba amma cike take da ƙarfi,
"Ummee... idan abin da ke cikin saƙon nan gaskiya ne..."
Ya yi
ɗ
an tsayawa.
"...to Jalaluddeen ya riga ya yi aure na halal."
Ya sake kallon Yasmeen cikin tausayawa.
"Kuma a add
ininmu, ba wanda yake da ikon raba miji da matarsa saboda son zuciya ko wata alkawari ta baya."
Kalaman Dad suka sa Yasmeen ta sake fashewa da kuka, yayin da Ummee ta matse haƙoranta cikin tsananin fushi.
A karon farko a rayuwarta, ta ji kamar an ƙalubal
anci matsayinta a cikin wannan iyali
*Maman Ihsan ce*✍
️
.
09065327995
[7/13, 9:00 AM] Antysalima Grp: *MAKAHO NE*
_BOOK 2_
*NA*
Maman Ihsan ce✍
️
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
"LITTAFINA NA KUƊI NE KADA KI KARANTA MANI LITTAFI BA TARE DA KI
N BIYA NI HAKKINA BA. NAIRA DUBU ƊAYA NE KACAL . A TURA NAIRA DUBU ƊAYA CIKIN WANAN ACCOUNT 2242538358 Zainab Abdullahi UBA bank. Sai a tura shaidar biya ta wanan lambar waya. 09065327995.
Page1
️
⃣
1
️
⃣
1
️
⃣
Kalaman Dad suka sa Yasmeen ta sake fashewa da
kuka, yayin da Ummee ta katse haƙorants cikin tsananin fushi.
A karon farko a rayuwarta ta ji kamar an kalubalanci matsayinta a wanan Iyali.
Mom ce ta janyo hannun Yasmeen ta fadi jikinta. Rungume ta ta yi tana kuka sosai.
Rarrrashinta Mom ke yi tana
sauke ajiyar zuciya.
Abbi ya kalli Ummee ya ce,
"Ki koma gida. Ba da iznina kika fito daga gida ba."
"Ai munafurtata ka yi, ne ya sa ba ka fada Mani cewar ga abin da kuke shirin ƙullawa ba, sai da aka kturs Mani saƙo ta waya ake sanar da ni halin da
kuke ciki ba ai da ban sani ba."
Juyawa ta yi ta kalli Jalaluddeen ta ce.
"Son."
"Na'am Ummeena."
Ka tuna ranar da muka fara magana da kai akan auren Yasmeen. Kai fa bakinka ka amsa Mani ka amince za ka aure ta, kuma za ka riƙe ta amana da yardar Allah
, ka yi Mani alkawarin rayuwa tare da ita, amma daga baya shi ne ka aure wata mace?"
"Ummeena wallahi ba yadda kika dauka na ne, aure na da Ma'eesha ya zo a yadda ban yi zato ba, kuma a yadda bani da wani za
ɓ
i da ya wuce na amince da ita, daga ni har suka
ita ba wai auren soyayya muka yi da ita ba. Lokaci daya mahaifinta ya ce ko nawa nake da shi sadaki na kawo ya bani aurenta. A lokacin da nake aikin sirri a matsayin makaho faƙiri wanda ba shi da abincin yau bare na gobe. Ke kafin gyaran takalmin nake yi,
Amma a haka ta yi biyayya ta yarda da ni lokcin da nake aiki bakan canza rayuwar da na taso ciki ne na koma rayuwar da na saka kaina a lokacin. Aka ce na kawo kudin sadaki na auren ta. Kin san nawa nake da shi a lokacin?"
Sai da ya yi murmushi sannan ya
ce.
"Nairs dubu uku nake da ita , ita ba bayar ba kayan lefe ba komai haka aka bani ita, wacce na san ko kaza ce ba zan same ta a dubu uku ba ballantana bil adama. Haka na je gidan aka ce na
ɗ
auki matata mu tafi.
Bayan mun fito gidan ko Naira biyar bani
da ita, ita ce ta biya mai nape kudi muka je unguwar da nake. Ita ce ta siyar da wayarta ta kama mana kudin haya da kudin, ta siya mana kayan amfani daidai gwargwado. Sannan ta siya ma na abincin da za mu ci na tsawon watanni. Ita ta
ɗ
auki nauyina a loka
cin ita take bani ci da sha da sutura ta siya mun waya take kula dani , ba ta duba nakasar da nake da shi ko takaicin da nake ciki ba. Kullun burin ta ta kyautata mani. Ba ya taba zato ni ba makaho ba ne, kuma ba ga taba tunanin cewa ita tafi ƙarfin ta z
auna da talaka musaki ba, ba yadda ƙawarta ba ta zuga ta akan cewa ta saka na sake ta ba amma ba ta amince ba. Ummeena idan ban saka wa Ma'eesha ba me ya kamata na yi ma ta irin sadaukarwar da ta yi saboda ni? Kina ganin a zamanin yanzu ana samun mace iri
nta kuwa ?"
Abbi ya karbi zancen da cewa.
"Da wuya gaskiya samun mace kamar ta. Kuma na tabbatar wallahi Yasmeen ba za ta iya yin haka ba."
Nisawa ya yi sannan ya ce.
"Kuma gaskiya ba ta cancanci zama da kishiya ba, don haka zan ba wa ƙaninsa Sadik aur
en Yasmeen."
Wata uwar ashar Ummee ta yi tana cewa .
"Akan me za ka yi haka, ba zai yiwu ba, Jalaluddeen na ba auren Yasmeen ba Sadik ba. "
"Au yaushe mace ta fara bada aure ban sani ba? Na gama magana, don haka ba na bukatar sake jin kin tayar da magan
ar nan."
Ya yi magana yana kallon Dad, kafin ya ce .
"Ka ja wa ƙanwarka kunne."
Yana fadar haka ya yi ma su sallama.ya fice daga cikin falon.
Har lokacin Yasmeen kuka take yi wanda take yin shi har ƙasar ranta.
Sosai take yin kuka wanda sai da Jalalu
ddeen ya tausaya ma ta sakamakon ya san yadda take ƙaunarsa.
Sai dai a ƙasar zuciyarsa yana farin ciki sakamakon wannan al'amari da ya kasance, ya san dole yanzu za'a ba shi matarsa su tafi da ita.
Fuuu Ummee ta fice daga gidan tana cika da batsewa ita k
adai.
Ko ta kan Yasmeen ba ta bi ba ta fice daga ciki gidan.
_Abba_
Ƙ
arar motar Abba ce ta cika harabar gidan da misalin ƙarfe bakwai na yamma.
Tun kafin motar ta tsaya cak, masu aikin gidan suka yi saurin fitowa suna gaishe shi. Fuskar Abba babu w
alwala, babu murmushi. Kallon farko da mutum zai masa zai fahimci yau akwai abin da yake
ɗ
auke da shi a zuciya.
Ya miƙa wa direbansa jakar takardu ba tare da ya ce komai ba, sannan ya nufi cikin gidan da takunsa masu cike da izza.
A falo kuwa, Sidra tana
zaune tana kallon talabijin, amma hankalinta ba ya kan abin da ake nunawa. Tun daga ranar da Abba ya ba ta wa'adin wata
ɗ
aya ta samo miji, zuciyarta ta kasa samun natsuwa.
Da ta ji ƙarar takun Abba, ta mike tsaye da sauri.
"Abba... sannu da zuwa."
Sai
ya
ɗ
an kalle ta na daƙiƙa biyu.
"Yauwa."
Kalma
ɗ
aya kacal ya fa
ɗ
a, ya wuce ciki.
Sidra ta sauke numfashi a hankali.
"Da alama yau ba lafiya..." ta fa
ɗ
a a zuciyarta.
Can ciki kuwa...
Abba yana shiga falonsa ya cire hularsa ya ajiye a kan tebur. Bai za
una ba ma.
Ya juya ya kalli matarsa.
"Umma."
"Na'am."
"Ki kira Sidra."
Gabanta ya fa
ɗ
i.
"Yanzu?"
"Eh. Yanzu."
Sai ta ƙara kallon fuskarsa.
"To."
Ta juya tana tafiya da sauri.
A hanya zuciyarta cike take da tambayoyi.
"Allah Ya sa ba abin da nak
e tunani ba ne..."
Ta fito falon.
"Sidra."
"Na'am Umma."
"Abba yana kiranki."
Kalmar ta bugi zuciyar Sidra kamar guduma.
"Wai... yanzu?"
"Eh."
Sidra ta ha
ɗ
iye yawu.
Ta gyara mayafinta.
"To."
Tana tafiya kamar wacce aka yanke wa hukuncin dauri.
Da suka isa babban falon cikin gida, sai suka tarar da wata tsohuwa mai cike da kima zaune kan kujerar da aka fi girmamawa.
Ammi.
Mahaifiyar Abba.
Idan tana gidan nan, ko Abba kansa yana rage murya saboda girmamawa.
Sidra ta durƙusa.
"Ammi... ina wuni
."
"Lafiya lau."
Ta juya.
"Abba."
Ya
ɗ
aga kai ka
ɗ
an.
"Zauna."
Sidra ta zauna a ƙasan kafet.
Umma ma ta zauna gefe.
Shiru...
Shiru mai nauyi.
Ana jin ƙarar agogon bango kawai.
Sidra kuwa zuciyarta kamar za ta fito.
"Me zai ce? Allah Ka sauƙaƙa..
."
Abba ya ha
ɗ
e hannuwansa.
Ya fara magana cikin nutsuwa.
"Sidra."
"Na'am Abba."
"Kin tuna abin da na gaya miki kwanaki goma sha hu
ɗ
u da suka wuce?"
Sidra ta sunkuyar da kai.
"Na tuna."
"Ki maimaita."
Sai ta lumshe ido.
"Ka ce ka ba ni wata
ɗ
aya.
.. in fito da mutumin da zan aura."
"Daidai."
Ya
ɗ
an yi shiru.
"Sati biyu sun shige."
Sidra ta ji gabanta ya ƙara fa
ɗ
uwa.
"Kin rage da sati biyu."
Babu wanda ya ce komai.
Abba ya ci gaba.
"Na yi miki wannan alfarma ne saboda ke 'yata ce. Da ba ke b
a ce, wallahi ban ma ba ta wannan damar ba."
Sidra ta ha
ɗ
iye hawaye.
"Na'am Abba."
"Saboda haka ki ji ni da kyau."
Muryarsa ta ƙara tsauri.
"Idan wa
ɗ
annan sauran satittika biyu suka cika..."
Ya dakata.
Ya kalli kowannensu.
"...ba ki fito da mijin d
a za ki aura ba..."
Ya nuna ƙasa da yatsarsa.
"Da kaina zan kai ki ƙauye."
Sidra ta
ɗ
ago kai a firgice.
"Abba..."
Bai bari ta ƙarasa ba.
"A can."
Ya ci gaba.
"Zan ha
ɗ
a aurenki da duk mutumin da na ga ya dace."
Shiru ya sake mamaye falon.
Idan all
ura ta fa
ɗ
i za a ji.
Sidra ta ji tamkar jinin jikinta ya tsaya.
"Abba..."
Muryarta na rawa.
"Don Allah..."
Ya
ɗ
aga hannu.
"Ban gama ba."
Nan take ta yi shiru.
Abba ya ci gaba.
"Ba zan zauna ina kallon yarinya ta girma tana za
ɓ
en rayuwar da ba ta d
a makoma ba."
"Abba ni ba..."
"Kin ce ba me?"
Ta yi shiru.
"Na ba ki dama. Ban ta
ɓ
a hana ki za
ɓ
ar mijinki ba. Na ce ki nemo wanda kike so."
Ya
ɗ
an matsa gaba.
"Amma kin mayar da abin wasa."
Umma ta kasa haƙuri.
"Alhaji..."
Ya juya.
"Na'am."
"Ka
yi haƙuri. Ai har yanzu saura sati biyu."
"Na sani."
"To me zai hana mu jira su cika?"
Abba ya girgiza kai.
"Ina sanar da ita ne. Kada ranar ta zo ta ce ban fa
ɗ
a mata ba."
Ammi ta gyara zamanta.
Ta kalli Sidra.
"Ke Sidra."
Sidra ta amsa cikin girma
mawa.
"Na'am Ammi."
"Gaskiya mahaifinki bai cuce ki ba."
Sidra ta yi saurin kallonta.
"Ammi..."
"Ki saurare ni."
Muryarta cike take da hikima.
"Yarinya idan ta kai shekarun aure, iyayenta suna da haƙƙin su tabbatar ta samu gida."
Sidra ta runtse id
o.
Hawaye suka cika mata ido.
Ammi ta ci gaba.
"Kin san dalilin da ya sa mahaifinki yake matsa miki?"
Sidra ta girgiza kai.
"A'a."
"Saboda yana son ya ga kina cikin mutuncin aure kafin ya tsufa sosai."
Kalmar ta soki zuciyar Sidra.
Ta kalli Abba.
Sai ta ga ko ka
ɗ
an ba ya wasa.
Abin da ya fa
ɗ
a zai aikata.
Ta ha
ɗ
iye kukan da yake son ƙwace mata.
"Abba..."
"Na'am."
"Idan..."
Ta kasa ƙarasa.
"Yi magana."
"Idan ban samu ba fa?"
Abba ya amsa ba tare da wani tunani ba.
"To zan kai ki ƙauye."
"A
bba..."
"Na fa
ɗ
a."
"Amma..."
"Ba zan sake maimaitawa ba."
Sidra ta fashe da kuka.
"Don Allah Abba..."
"Ki daina kuka."
Ya fa
ɗ
a cikin ƙarfi.
"Kuka ba zai canja hukuncina ba."
Ta rufe fuskarta da tafukan hannunta.
Umma ta share mata hawaye.
"Yi ha
ƙ
uri, 'yata."
Sidra ta girgiza kai.
"Umma... ban san me zan yi ba."
Abba ya miƙe tsaye.
Alamar taron ya ƙare.
Yana tafiya ya tsaya ba tare da ya waiwayo ba.
"Sauran kwanaki goma sha hu
ɗ
u."
Ya
ɗ
an dakata.
"Bayan haka... ni zan yanke hukunci."
Ya fi
ce daga falon cikin izza.
Ƙ
ofar ta rufe.
Sidra ta durƙushe a kan kafet tana kuka mai ciwo, yayin da Umma ke rungume da ita. Ammi kuwa ta zuba mata ido cike da tausayawa, amma ta san halin Abba sarai—idan ya yanke hukunci, sai dai Allah Ya sauya shi.
_
Jabeer_
Daren ya sauka cikin natsuwa.
Hasken fitilun gidan ya mamaye harabar katafaren gidan, amma a
ɗ
aki na sama, inda Jabber yake, akwai duhun da ya fi na dare—duhun da ya mamaye zuciyarsa.
Tun da ya dawo daga aiki bai sauya kaya ba.
Har yanzu rigar
jikinsa ce, tayinsa a sake, ma
ɓ
allan wuyan riga biyu a bu
ɗ
e. Ya zauna a gefen gadonsa, hannayensa sun ha
ɗ
u, idanunsa kuwa sun kafu kan ƙasa.
Ba talabijin a kunne.
Ba waya a hannu.
Ba ki
ɗ
a.
Shiru ne ka
ɗ
ai.
Sai kuma zuciyarsa da take ta maimaita masa a
bin da yake son mantawa.
Ya lumshe idanunsa da ƙarfi.
"Me ya sa na aikata haka?"
Tambayar ta sake dawowa.
Kowace rana tana dawo masa.
Kowace dare tana hana shi barci.
Ya dafe goshinsa.
A da bai ta
ɓ
a ganin kansa a matsayin mutumin da zai iya cutar da
mace ba. Amma tun bayan wannan ranar, duk lokacin da ya tuna yadda Sidra ta firgita, yadda ta yi kuka, yadda ta roƙe shi ya dakata...
Sai cikinsa ya mur
ɗ
e.
"Ya isa..."
Ya fa
ɗ
a a hankali kamar yana yi wa kansa magana.
"Ka daina tunawa..."
Amma ƙwaƙwal
wa ba ta bin umarni.
Ya miƙe tsaye ya fara yawo cikin
ɗ
akin.
Mataki biyu.
Ya dawo.
Mataki uku.
Ya sake juyawa.
Numfashinsa yana fita da ƙarfi.
"Ni ne na lalata komai..."
Ya furta da muryar da babu kowa ya ji sai shi.
"Kila har yanzu tana tsoro sab
oda ni..."
Ya buga bango da tafin hannunsa.
A fusace.
Amma ko wannan bai rage masa zafin zuciyar da yake ji ba.
Ya sake komawa ya zauna.
Ya
ɗ
auki wayarsa.
Ya bu
ɗ
e.
Ya sake rufewa.
"Yi haƙuri?"
Shin kalmomi biyu za su iya goge irin ciwon da ya jaw
o mata?
A'a.
Ya jefar da wayar kan gadon.
Ya dafe fuskarsa.
"...Allah..."
Kalmar ta fito daga bakinsa a hankali.
"Ban san me zan yi ba."
---
A ƙasa kuwa...
Mimi ta fito daga
ɗ
akin girki tana duban agogo.
"Har yanzu Jabber bai fito ba?"
Mai aikin
gidan ta girgiza kai.
"A'a Hajiya."
"Ko ya ci wani abu?"
"A'a."
Ta
ɗ
an yi mamaki.
"Wannan yaron fa tun da ya dawo bai fito ba."
Ta
ɗ
auki farantin abinci da kanta.
"A bar ni, zan kai masa."
Ta haura bene.
Ta isa bakin ƙofar
ɗ
akinsa.
Ta buga a han
kali.
"Jabber."
Shiru.
Ta sake bugawa.
"Jabber, bu
ɗ
e mana."
Sai aka ji muryarsa daga ciki.
"Shigo Mimi."
Ta tura ƙofar.
Da ta shiga, gabanta ya fa
ɗ
i.
Ɗ
akin a duhu yake.
Sai hasken fitilar gefen gado.
Jabber kuwa yana zaune kamar mutumin da aka k
wace wa wani abu mai muhimmanci.
Mimi ta kalle shi da kyau.
"Wai lafiya?"
Ya yi ƙoƙarin murmushi.
"Lafiya lau."
"Idan lafiya ce, me ya sa ba ka sauya kaya ba?"
Shiru.
"Me ya sa ba ka sauko ka ci abinci ba?"
Ya kau da kai.
"Ba na jin yunwa."
Mimi
ta ƙarasa kusa da shi.
Ta ajiye farantin.
Ta
ɗ
ora hannunta kan goshinsa.
"Ba ka da zazzabi."
Ta sake kallonsa.
"Jabber."
"Na'am."
"Ka kalle ni."
A hankali ya
ɗ
ago kai.
Ta yi mamakin yadda idanunsa suka yi jajir.
"Kana kuka ne?"
Ya yi saurin girg
iza kai.
"A'a."
"To me ya faru?"
"Ba komai."
Ta zauna kusa da shi.
"Ni ce fa Mimi."
Ta shafa kafa
ɗ
arsa.
"Na haife ka."
"Na san lokacin da wani abu yake damunka tun kana ƙarami."
Ya yi shiru.
"Ka gaya min."
Jabber ya ha
ɗ
iye yawu.
Yana son ya fa
ɗ
a.
Yana son ya sauke nauyin da ke kansa.
Amma ta yaya zai iya kallon mahaifiyarsa ya ce mata...
"Na cutar da wata yarinya."
Bai iya ba.
Idan ya fa
ɗ
a...
Ta yaya za ta sake kallonsa?
Duk da tana masa kallon mara jin magana,.amma ba ya san zai iya aika
ta haka ba
Ya girgiza kai a hankali.
"Mimi..."
"Na'am."
"Kaina ne kawai yake ciwo."
Ta
ɗ
an ƙanƙance idanu.
"Kai ka
ɗ
ai?"
"Eh."
"Kana da wata matsala a aiki?"
"A'a."
"Ko wani ya
ɓ
ata maka rai?"
"A'a."
"Ko kana cikin wata damuwa?"
Ya yi shiru na
ɗ
an lokaci.
Sai ya tilasta murmushi.
"Kawai ciwon kai ne."
Mimi ta ci gaba da kallonsa.
Ta san
ɗ
anta.
Ta san wannan murmushin ba na gaskiya ba ne.
Amma ta fahimci ba zai yi magana ba.
Sai ta shafa gashinsa.
"To ko da ciwon kai ne, ba za ka zauna da
yunwa ba."
Ta matsa masa farantin.
"Ka ci ko ka
ɗ
an."
Ya girgiza kai.
"Ba zan iya ba."
"Jabber."
"Na'am."
"Ba na son ganin ka haka."
Ya sauke idanunsa.
"Yi haƙuri Mimi."
Ta numfasa.
"Allah Ya yaye maka duk wata damuwa da kake
ɓ
oyewa."
Kalmar ta
bugi zuciyarsa.
Ya ji kamar kuka zai ƙwace masa.
"Da ace kin san irin damuwar da nake
ɓ
oyewa..."
Ya fa
ɗ
a a ransa.
"Da ace kin san irin laifin da na aikata..."
Amma bakinsa ya kasa furta ko harafi
ɗ
aya.
Mimi ta miƙe.
"Zan bar abincin nan. Idan ka ji
da
ɗ
i ka ci."
Ya
ɗ
aga kai ka
ɗ
an.
"To."
Ta taka zuwa ƙofa, amma kafin ta fita sai ta waiwayo.
"Jabber."
"Na'am?"
"Ko me yake damunka... ka tuna cewa babu laifin da ya fi ƙarfin mutum ya fuskance shi. Gudu daga gaskiya ba ya kawar da ita."
Ta fice ba
tare da ta san cewa kalamanta sun soki zuciyar
ɗ
anta ba.
Ƙ
ofar ta rufe.
Jabber ya zauna yana kallon farantin abincin da bai