Showing 1 words to 3000 words out of 190498 words

Chapter 1 - Buzu Book 1 Complete

??ࡱ?>?? &?????????????? ?
?
? ?
?
??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????V

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument?????$0Table????????? Data
???????????????????? P?t?KSKS??$?????????pp]]]]-A?? a
?]?? ? ? ? ? ? ? ? ? $E??*p]]? ? ]]]]? ! ?A! ? A? ! A? ? ]A ?>`??>Normal$a$KHOJPJaJ???-?@4["u?????*???n:?V?t
?????.?????D]6v?? ?*?r????8`[?wn???N?Z :$?5"M?c?xf?\????????:F8?I e?F?T????R?T?9PDp???:?|?x????6?P?gL?B?????? ?<?`????:?,???8 ` B4 ?F b ?x ? N? BUZU

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA/002)

Bright pens 3rd batch.
(2025)

Bismillahirahmanirrahim.

*Labarin BUZU ?ir?irarren labari ne, duk wani sashi na labarin na iya faruwa a gaske, idan ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne.*

?&? Labarin mallakina ne, ban yarda wani ko wata, su yi amfani da shi ta kowace irin siga ba, sai da izina.

AISHA ADAM
(Ayshercool)
08081012143
Arewabooks; Ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724

Page 1


Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka.

Dan?areriyar mota ce, ?irar highlander ba?a, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta.
Gefe da gefen hanyat baki Waya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huWu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado.
Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi.

"Kilom?tre nawa ce ta rage mana ne?"

Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilom?tre ba"

"Dans? quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)".

"Bai fi awa Waya ya rage ba"

"Dole fa mu ?arasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka"

Ya yi maganar yana haska fuskar wani matashin mutum, da yake kwance a jikinsa ya haWa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai? yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ?irjinsa da yake Wagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ?yar.

Ya kai hannunsa, ya Wora a kan ?irjin matashin, idan zuciyar sa ta buga sau Waya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ?arfi take bugawa tamkar za ta tsaga ?irjinsa ta fito dummm!.

Cikin damuwa ya ce "Lowalli, sai ka ?ara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi"

Lauwalli ya jinjina kai yana ?ara gudun motar.

*****

Misalin ?arfe shida da mintuna goma sha biyar na safiyar ranar asabar, Waki ne madaidaici, wanda ya samu kyakkyawan ginin ?asa ma ?warin gaske, duk da kasancewar sa na ?asa, amma adon da aka yi masa ya bayyanar da darajarsa.

Can daga kusurwar Wakin wata matashiyar mace ce, kwance a kan matsakaiciyar katifa ta yi WaiWai ta na bacci, zaninta ne kawai ya kare bayyanar tsiraicinta, amma idan ta yi kyakyawan yin?urin za ta yi tsirara.

Iya ?arfinta take ?o?arin tashi daga baccin, amma abu ya gagara a sakamakon sleep paralysis, wanda a hausance da kuma fahimta ta mutane suke kira da dannau, a cewar mutane wani aljani ne mai suna dannau, yake danne mutum ya kasa motsi, alhali idanunsa biyu, kamar a zahiri haka ta din ga ganin abubuwan da suke faruwa da ita, amma ta kasa motsawa.

Tamkar an cire mata wani abu mai nauyi, haka tayi firgigit ta tashi zaune, ta na mayar da numfashi, a sakamakon fafutukar da ta sha, kafin ta samu ta iya farkawa daga nannauyan baccin da take yi mai kama da na mutuwa.

Ware ido tayi, ganin yadda gari ya yi haske, ba tare da ta gabatar da sallar asuba ba.

Ta yin?ura za ta sauka daga kan katifar, ta ji duk gaSoSinta na yi mata ciwo, jikinta kamar wadda aka yi wa dukan tsiya, zanin jikinta ya yaye.

Shiru ta yi ta na ?o?arin tuna abin da ya faru a daren jiya, a iya saninta ninkin kaya take yi, ba ta kai ga kwanciya ba, daga nan ba ta san abin da ya faru ba.
Ita dai ta san sanye take cikin suturarta, amma yanayin da take ganinta a ciki, yana sanya mata wasi-wasi.

A hankali ta tashi ta gyara zaman zanin ta nufi banWakin da yake cikin Wakin, domin ta kintsa jikinta ta gabatar da sallar asuba.

*****
Sannu a hankali yake buWe idanunsa, da suke yi masa wani irin zugi saboda hasken da ya cika masa su, sai ya ji tamkar hasken wani ba?on abu ne a cikin idanun nasa. Yanayin ya yi masa kama da farkawa cikin wata duniya ta daban.

A hankali ya daina jin zugin da idanun suke yi masa, ya buWe su tanagrau, ya ?urawa wurin da yake ido, yana ?o?arin gano a ina yake.

Wani dogon mutum ne ba?i, fuskarsa Wauke da jan rawani hannunsa rike da Wan ?aramin kofi, ya shigo cikin tantin.

Jifa yayi da kofin hannunsa, ya nufi mutumin da yake kwance da matu?ar hanzari.

Taimaka masa yayi ya tashi zaune, fari ne amma ba tas ba, irin mai sirkin yellown nan, ya na da Wan siririn hanci, dai-dai da siririyar fuskarsa, sai gashin baki kaWan da ya haWe da Wan madaidaicin gemunsa, sai kuma manyan idanuwa da yake da su, da su ka kaWa su ka yi jawur tamkar jini zai kwararo daga cikinsu.

Zaman da ya yi, ya bawa gashin kansa damar kwanciya a kafaWarsa zuwa bayansa, tamakar mace.

A hankali Wayan ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Sannu ya jikin naka?" Maimakon ya bashi amsa, sai ya yi shiru ya na bin sa da kallo.

"Akwai abin da yake yi maka ciwo ne?"

A hankali ya motsa bakinsa ya ce "Ina ne nan?"

Ba?in ya kalli gurin sannan ya mayar da idonsa kan shi ya ce "Mun shigo Nigeria ne yanzu haka"

"Nigeria?" Ya maimaita.

"Eh Nigeria" ya amsa masa.

Ya yi shiru ya na ?o?arin tuna a ina ma ya taSa jin sunan.

"Ya na ga ka yi shiru ne? Ka gane ni ma kuwa?" Ya Wago ya kalle shi a hankali ya girgiza masa kai alamar a'a.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, ba ka sanni ba ka ke nufi?" Ya jinjina masa kai.

"To ka san sunanka?"

Yayi shiru yana ?o?arin yin tunani, amma ya gaza tuna komai, sai ma wani irin rugugi da ya ji a cikin kansa tamkar an yi aradu, hakan ya tilasta masa dafe kansa yana rintse idanunsa.

"Shi kenan ya isa, ba sai ka tuna ba, amma ka san alwala da salla?"

Ya Waga masa kai alamar eh, ba tare da ya yi magana ba.

"Sallar asuba raka'a nawa ce?" Ya Waga masa yatsunsa guda biyu.

"Azahar fa?" Ya nuna masa huWu.

"Ka san salla, amma ba za ka iya tuna komai ba bayan haka?"

"Eh" ya amsa a ta?aice.

"Shikenan, ka zo ka yi alwala sai ka rama sallolin da suke kanka, ka yi ?asaru, tun da mun yi tafiya mai nisa daga Nijar".

Shiru ya yi ya na son tuna a ina kuma ya taSa jin sunan Nijar, sai kawai ya bar shi a sunan da ya ji ya faWa Wazu ne Nigeria.

Cif ya jera sallolin kamar yadda wanda suke tare da shi, ya gaya masa waWanda su ka tsere masa.

Ya Waukko abinci ya bashi, ya saka hannu ya karSa ya fara ci.

Bayan ya kammala cin abincin, ya tsiyaya masa shayin da ya dafa a cikin Wan ?aramin kofi ya mi?a masa.
Ya karSi shayin ya fara sha, hakan ya sanya shi fara ?o?arin tuna wani abu, amma abu ya ci tura. Bayan ya gama shan bunun, Wayan ya fito da wani ?yalle ya tattare masa dogon gashinsa, ya naWe masa shi, sannan ya naWa masa rawani ya kamo hannunsa su ka fito daga cikin tantin.

Tsayawa yayi, ya yi wa wurin ?uri da ido, jeji ne babu kowa a wurin, sai bishiyu sai kuma wani ra?umi da yake gefe a Waure ya na ta taune-taune.

Ya tafi ya kwanto ra?umin, ya janyo akalarsa zuwa gabansa, ya kalle shi ya ce "Ka san menene wannan?"

Ya jinjina kai.

"Mene ne shi?"

"*Le chameau*" (Camel/ ra?umi ne)

Yayi sassanyar ajiyar zuciya ya ce "Hau mu tafi" ya taimaka masa, ya hau kan ra?umin, shi kuma ya ja akalar ra?umin su ka tafi.

*****

Tafe take sannu a hankali, ta na ratsa matsakaitan gidajen da su ka haWu suka samar da rukunin gidajen da suka samar da wani Sangare na unguwar.
Mamakon ruwan saman da aka tafka kamar da bakin ?warya awanni kaWan da suka shuWe, ya wanko datti da ?azanta daga mabanbanta wurare, sai dai rashin kyakyawar hanya da magudanan ruwa, ya sanya ruwan shiga gidajen mutane, wani kuma ya kwanta a cikin layuka, ta yadda ba a iya banbance kwata da hanya, duk sun haWu sun shafe.

Gabanta ne yayi mummunar faWuwa, abin da take tsoro da fargaba ta tarar, tun da hadarin nan ya taso aka fara ruwa, hankalinta ya kasa kwanciya.

Daga in da take ta na hango tsakiyar tsakar gidansu, a sakamakon fiye da rabin katangarsu ta zube.

Ta lallaSa ta ?arasa, duk mutanen gidan su na tsaye sun yi cirko-cirko su na jajanta abin da ya faru.

Sai dai abin da ta tarar ya fi wanda ta hanga daga nesa, domin ?arasawarta gidan ke da wuya, ta tarar rijiyar gidan ta burma, ta haWe da masai kasancewar daf da juna suke, daga in da aka yi rijiyar babu tazara.

Wani babban mutum ne ya fito daga cikin banWakin, ya dubi matashiyar ya ce "Nana kin dawo?"

Jiki a sanyaye ta amsa ta ce "Eh Baba"

"Kin ga abin da ya faru ko"

Nana ta ce "Eh baba, tun ina makaranta da aka fara ruwan nan, hankalina yake tashe nake a tsorace"

"Ai mu na cikin jarrabawa, yanzu lalubawa zaki yi, Wan abin da aka samu a hannunki, ki kawo a samu ko katangar a fara tayarwa".

Saroro Nana ta yi baki buWe tana bin Baba da kallo, duk da ba abin mamaki bane ba, jin hakan daga bakinsa, cikin ?arfin hali ta ce "Baba dubu bakwai ne fa albashin nawa, kuma yau goma sha Waya ga wata, ko sisi ba ni da ita ka manta dubu biyar ka karSa ka bani dubu biyu"

"Kai Nana, ina ki ke kai kuWi ne? kullum da an taSa ki babu, ai shikenan sai ku zauna haka, duk wanda ya ji turotso sai ku bi ma?wabta ko ku tafi jeji ku yi, ni ba ni da yadda zan yi"

Wata mata da tun da su ka fara maganar ba ta yi magana ba, sai yanzu, ta kada baki ta ce "Ai kuwa sai ka san yadda za ka yi, haka zamu dauwwama mu na gantalin yawon kashi a ma?wabta kai ko kunya ma ba ka ji, Nana ka tsare ka na ta baka kuWin da zaka Waga katangar gidanka, kai fa take mi?awa albashin nata, dubu bakwan nawa take, ka bi ka kashe zuciyarka, wallahi dole ka nemi yadda za ka yi"

Nana dai ba ta sake cewa komai ba, ta nufi hanyar wurin kwananta, ta na jiyo Waya daga cikin yaran gidan ya na cewa "Abu mai sau?i, a samu ?aton bokiti kawai, kowa ya din ga juyewa a ciki, a tara a sayar zazzafan taki ne fa, tsaf za a samu kuWin Waga katangar gidan nan, gwargwadon ?wazonmu wurin tarawa da yawa gwargwadon.....

"Za ka rufe mini baki, ko sai na daka ka a wurin nan, shashasha mara tunani kawai"

Baba kuwa waje ya yi, saboda tijarar da mama ta fara yi masa, ma?wabta duk sun fito waje, ana jajanta Sarnar da ruwan yayi a layin, tare da jajantawa su Baba abin da ya faru da su.

Jiki a sanyaye ta shiga wani Wan madaidaicin Waki, bakinta Wauke da sallama.

'yan mata biyu ne a kwance su na danna waya, da ?yar Waya ta amsa, Wayar kuwa ko Wagowa ba ta yi ba.

Nana ta ajiye jakar hannunta tare da faWin "Jamila, ashe ruwa ne yayi mana gyara haka?"

Jamila ta ce "Aikam, Sarna ma ba ?arama ba, kin ganni nan lissafi nake yi yadda zan tsallake na bar gidan nan, wannan abin kunya da mai yayi kama, ace in da zaka tsuguna ka juye najasarka babu, sai dai ka bi ma?wabta, wannan gidan Allah kaWai ya san lokacin da za a gyara shi".

Nana ta nemi wuri ta zauna ta ce "Idan kin bar gidan nan, ina za ki je?"

Cike da takaici Jamila ta ce "Ko ma ina ne, tun kan jarabar talauci ta kashe mutum, kullum gida babu cigaba ba a Wauki Wawainiyarka ba, amma ana nema a wurinka"

Nana ta girgiza kai ta ce "To, Allah ya sa mu dace, ya bamu mafita".

"Amin, kalli wurin kwanciyar ki ma duk ya ji?e, nan wurin ma zuba yake yi".

Nana ta kalli wurin tare da yin ajiyar zuciya, ba tare da ta ce komai ba.

Haka gidan su Nana suka kwana, rabin katanga a zube, kowa ya zo wucewa ya na kallon cikin gidan.

Washegari da asuba da 'yan kame-kame su ka kama ruwa, wasu su ka zagaya ma?wabta wasu kuma suka yi a wani wurin, su ka yi alwala su ka gabatar da sallar asuba.

Tun daren da abin ya faru ma?wabta suke shigowa yi musu jajen abin da ya faru.

Jamila sai masifa take yi tana mita, "Wallahi na san ikon Allah ne kawai zai sanya a gyara katangar nan, haka zamu ci gaba da zama da zubabbiyar katanga, ni matsalar banWakin nan ba ta dame ni ba sama da katangar nan, duk asirinmu a tone, kodayake wane asiri ne ma da mu, banda damin talauci da tsiya"

Nana ta na jin ta ba ta ce uffan ba, ta Waukki Alqur'aninta tana dubawa.

*****

Tsura masa ido yayi, yana nazarinsa, sannu a hankali yake cin abincin gabansa, ya gama ya wanke hannunsa, ya gyara zaman rawaninsa ya rufe fuskarsa.

Habu ya dube shi ya ce "Ka ?oshi?" Ya jinjina masa kai alamar eh.

"Yanzu za ka iya tuna sunanka?" Ya girgiza kai alamar a'a.

Habu yayi ajiyar zuciya yana sake jinjina lamarin, ya sake kallonsa ya ce "Babu abin da yake iya zuwa kanka ka tuna?"

"Eh" ya faWa a ta?aice.

"Shikenan, kar ka matsawa kanka sai ka tuna wani abu, amma a duk lokacin da ka tuna wani abu ka sanar mini, dole in fara tunanin nema maka magani kafin yin komai, amma sai mun samu wurin masu amana" shi dai yayi shiru bai ce masa komai ba.

Ya saka hannu a aljihun babbar rigarsa, ya Waukko waya, ya duba wata lamba, ya kara wayar a kunnensa.

Mintuna kaWan ya amsa sallamar sannan ya Wora da cewa "Mun iso Nigeria tun jiya, yanzu mene ne abu na gaba?" Ya Wan yi shiru tsawon wasu mintuna sannan ya ce? "Ka tabbatar babu matsala? Ba na son azo a samu matsala, dole ayi taka tsantsan da lamarin nan, kafin mu san ma in da za mu nufa neman maganin" ya sake yin shiru sannan ya ce "Shikenan, ina sauraronka" har ya kammala wayar bin sa yake yi da ido, kamar zai yi magana amma bai ce komai ba.

*****
Kwanaki uku suka shuWe ana tsilla-tsillar makewayi a gidan Malam Isa, wato gidansu Nana, ?arshe katanga sai buhu aka saka aka rufe ta.

Cikin ikon Allah, ma?wabta su ka yi ta kawo masa gudunmuwa, sai dai idan kuWi ne sai ya karSa ya saye abin sa, tun da matarsa rabi ta fuskanci haka, ta sanya shi a gaba da tijara, da masifar ya fito da kuWi a san abin yi.

Nana ta na Waki tana shafa mai, amma hankalinta yana kan su Baba sa suke ta faWa.

"Amma rabi da kuWaWen gudunmuwar nan, nake ta baku kuWin cefane, kuWin nan fa ba isa za su yi ba ayi aikin katangar nan"

Ta hayya?o masa cikin Waga murya ta ce "Wane cefanen, ba wata tsiyar ka bamu ba, makewayi ya gagari mutum, kamar mun fi kowa talauci a tsukin nan"

Nannauyar ajiyar zuciya Nana ta yi, ta tashi ta ?arasa shirinta, ko sallama ba ta yi wa su Baba ba ta fice, dan wannan rashin girmamawar da suke yi wa juna ba ?aramin ?ona mata rai yake yi ba.

Kamar yadda ta saba, tana ?ule a gefe guda, tana dudduba cikin Alqur'ani, yayin sa sauran 'yan ajin suke ta tilawarsu daban.

A hankali ta fara jin jikinta yana wani irin sanyi, ta fara jin tamkar daga wata duniyar take jiyo karatun 'yan ajin nasu.

"Nana" ta ji muryar Amira ?awarta.

Tayi jarumta ta Waga kai ta kalleta, Amira ta zauna a kusa da ita ta ce "Na biya miki makaranta, ashe abin da ya faru kenan, Allah ya mayar da alkhairi ya tsare gaba, na tarar da baba yana ta faWa, wai kowa ya nemi in da zai tafi kafin Allah ya hore masa abin da zai gyara gidan"

Sai Nana tayi da gaske take fahimtar me Amira take faWa, ganin yadda Nana ta ?ura mata idanu ko ?iftawa ba ta yi, ya sanya ta Wan matsa baya kaWan ta ce "Nana lafiya kuwa? Ko baki da lafiya ne?"

Ta girgiza mata kai, ba tare da ta ce komai ba. Amira ta koma gefe ta Waukko Alqur'aninta, ta koma nesa da Nana.
kamar wadda ake zarewa laka, take ji, wani irin sanyi jikinta yayi zuciyarta ta din ga bugawa cikin matsanancin tsoro da fargaba, numfashinta ya dinga sama-sama kamar zai bar gangar jikinta, ji tayi kamar ta kurma ihu, sai dai jikinta babu wannan ?warin, ji take kamar ajalinta ne ya risketa.
Alqur'anin gabanta take kallo, zuciyarta ta din ga raya mata, ta yi jifa da shi.
Ganin yadda yanayinta ya sauya, ya sanya 'yan ajijsu darewa suka koma gefe daga kusa da ita.

Malam Auwallu ne ya shigo, 'yan ajin duk suka yi shiru, hankalinsa ne ya sauka a kan Nana, da take ta fizgar numfashi idanunta sun yi jawur.

Girgiza kai ya yi ya ce "Nana Asma'u" kamar wadda aka jonawa shocking, haka ta ja da baya a razane, tare da sunkuyar da kanta.

Ya janyo kujerarsa zuwa gabanta, ya ce "Yau haddar ki zan fara ji, matso ki karanto mini, kin san ina son ?ira'arki" ba ta yi magana ba ta ci gaba da sunkuyar da kai tana haki.

Ya kalli ta kusa da ita ya ce "Amira dawo nan gefe ki fara ke"

Cikin damuwa Amira ta tashi, tana kallon Nana cike da tausayawa, hatta 'yan ajin kallon Nana suke yi cike da tsoro, su na jiran kyat su falla da gudu su na iface-iface.

Amira na zama a gaban malam Auwal ta fara karatu, a haka ya ci gaba da sauran karatun Waliban Waya bayan Waya. Nana tana gefe a zaune tana ta gurshe?en kukan da ita kanta ba ta san dalilin sa ba, adadin yadda suke karatun ya ingiza bugun zuciyarta, tare da jin jikinta na ci gaba da yin sanyi.

Malam Auwal na fita amsa waya, Nana Asma'u ta tashi ta fice ta bar ajin, ba tare da wani ya yi yin?urin tare ta ba, har ta yi nasarar barin cikin makarantar.

Ayshercool
08081012143
BUZU

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login