Showing 1 words to 3000 words out of 121625 words

Chapter 1 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

11

FREE BOOK.

KUNCIN ZUCI

📖📚

Written By Bintu Musa





.

Author's Note.

Bismillahir'rahmanur Rahim..

wannan littafi qirqirarren labari ne ba don wani ko wata ba, kuma ba nayi bane da wata manufa, in yazo daidai da naku rayuwan,ayi hakuri kuskure

ne.

Sadaukarwa....

Ga duk macen da take fuskantar qalubalen ta cikin shiru, wadda hawayenta suke zuba acikin duhu saboda ba wanda zai fahimci zafin da takeji.

Wannan littafi sadaukarwa ce a gareki domin:

Kin cancanci soyayya ta gaskiya.

__________

____________________

Kin cancanci samun nutsuwa.

______________________________

Ke farin cikin rayuwan wasu ce.

To whomever come across this book, please say a prayer for my beloved mother who now rest in peace, May Allah forgive her shortcomings

, Amin.

Trigger warning:

This story may contain contents related to Assault, Abuse and Trauma...

_____________________________

A Blurb for you:

Daga ranar da ya fara ganinta, idanunta suka zamo abun begensa..

Daga ranar da ta fara ganinsa,

zuciyarta ta fara bugawa da sunansa..

------------

Shin kalubalen da tayi nufin binnewa a baya zasu bari ta karbi wannan sauyin yanayin da zuciyarta tazo mata dashi kuwa?

Shin har wane mataki ze kai na ganin ya share duk wani kalubalen da zai masa

katanga da ita?

Ku kasance tareda ni Bintu Musa

Zan baku labarin da zai taba muku zuqata...





📖📚

Chapter 01

Oxford, England

Zaune take kan sofa cikin madaidaicin apartment din nasu,gabanta laptop ce da textbooks guda biyu wanda ta a

jiye kan karamin tebur dake cikin falon nasu tana typing, agefenta kuma cookies ne acikin plate da coffee a ajiye, jifa jifa take kai hannu tana dauka tanaci.

Dukkan hankalinta tamaida kan abunda take typing a laptop din wanda hakan yasa bata juya ta ka

lli wadda ta fito daga daya daga dakin dake cikin falon ba.

A sannu Nafisa ta qaraso gurinta ta zube akan kujerar, batareda ta juyo ba ko kuma ta bar abunda takeyi ba tace "Good morning" cikin sanyin muryarta wanda yasa Nafisa juyowa tana duban abunda t

ake typing tace

"Morning, what are you working on?"

Matashiyar tace "just some essay"

Nafee tace "shine yayi keeping dinki almost all night?,nafarka around 1 naga lights are still on"

Matashiyar ta sake amsawa da "Eh" Nafee ta tsaya kallont

a kawai,can tace "Na'ima" tsayawa matashiyar tayi da rubutun da takeyin ta juyo tana kallon nafisan da manyan idanunta, cikin sanyin muryarta tace "I have deadline for this" Nafee tace "I know, but girl..give yourself a break mana" bata jira amsan Na'ima b

a ta miqe ta wuce zuwa kitchen domin hado nata morning coffee din, na'ima batace komai ba ta maida hankalinta kan rubutun da takeyi while sipping her coffee, sanye takeh cikin kayan bacci peach color wanda ya haska farar fatarta, gashinta rufe yake cikin h

ulan bacci, sai ta ajiye coffee din akan table din tareda dan komawa baya ta manna bayanta da kujerar tana cigaba da cin cookies dinta idonta nakan rubutun nata tana nazarin each line.

Nafee ta fito daga cikin kitchen din hannunta riqe da mug itama ta z

auna wajen da ta tashi dazun, a gefen na'ima ta ajiye coffee din saman table tace "kaii, i slept like a baby today" murmushi na'ima tayi tace " you always sleep like a baby ai" 'yar dariya nafee tayi tace "yau na daban neh" na'ima ta sake cewa " i hear you

" nafee tace "whatever...zanje shopping anjima naga fast foods dinmu sunyi qasa sannan inason cin tuwo miyan ganye yau dinnan dan nagaji da noodles gaskiya" na'ima tace "dazu nima nayi tunanin nan but my plan was tomorrow don yau nakeson kammala essay dinn

an" nafee tace "yaushe neh deadline?" ta amsa da "jibi" nafee tace "toh ai akwai gobe, in Allah ya kaimu sai ki qarasa, muje tare ajiman" sai na'ima ta juyo ta kalleta tace "nafee bansan me goben zatazo dashi ba,tunda I'm halfway through gwara in qarasa on

ce and for all. Beside, saura kadan fa" nafee ta juya idonta dramatically tace "yeah,right" sannan ta dauki satchet na cookies din tana duba calories din jiki tace "wait....these much calories in one cookie?, have to keep my body in check,I have a reputati

on to protect" na'ima batasan lokacin

da ta fara yar dariya ba tace "sannu miss world contestant" nafee ma tana dariya ta dauki throw pillow ta jefa mata suna dariyan tare.

Saida suka lafa da dariyan nafee tace "nayi waya da Mami dazu, ta kiraki kuwa?"

na'ima tace "Eh nayi waya da ita jiya da dare, meya faru?" Nafee tace "bawani abu bane,munyi magana akan bikin anty salma ne zan koma next month shine takeson mu taho tare,so i thought ta kiraki" Duk wani annurin dake fuskan na'ima a takeh ya bace tana kal

lon nafisa. itama nafisan kallonta take tana nazarinta da kuma jiran me zata ce,can ta juya tana jawo laptop dinta tace "A'a bata kirani ba maybe tayi tunanin ban tashi ba amma zan kirata, Allah ya kaimu lokacin zanje..why not?" Nafee dai kallonta take sti

ll,ta riqo hannunta daya tace "you don't have to go indai ranki bayaso, nima baifi nayi one week bama in dawo,ni na cewa Mami zan fara tuntubanki da zancen tafiyan tukunna don nasan inta fada miki straight zakice Toh, but kinsan Mami,ban zata ma zata jira

nayi miki maganan ba i thought harta kiraki" ta qarasa maganan tana dan dariya, na'ima ta juyo tana murmushi tace "zanje nafee i missed Mami" nafee tace "aikuwa dai ta qagu bikin nan yazo dan kije taganki, always asking ko kinacin abinci ko kuma kinyi qiba

ko rama" dan dariya na'ima tayi idonta nadan cikowa da hawaye tace "Mami dai" squeezing hannunta nafee tayi tana reassuring dinta tace "She Cares, and i do too,I'm here always" jijjiga kanta na'ima tayi tana hana hawayen idonta zubowa, nafee ta rungumota

kadan tana dan buga bayanta batareda tace komai ba sukayi shiru na wani dan lokaci sannan ta sake ta tace "coffee na yayi sanyi" na'ima tace "nawa yayi qanqara nima" miqewa nafee tayi "bari kiga na dafa mana ko noodles ne" na'ima ta amsa "da kuwa kin taima

keni,yunwa nakeji" wucewa tayi zuwa kitchen din tana cewa "A'a ki dai tsaya nan yin assignment yunwa ta illataki baruwana" murmushi na'ima tayi tana maida hankalinta kan laptop dinta,fara typing dinta keda wuya tunanin maganarsu akan komawarta Abuja ya fad

o mata rai, shiru tayi ta fada tunani abubuwa dayawa suna dawo mata kanta, The last time she left Abuja in za'a tambayeta biggest wish dinta na rayuwa shine "karta sake komawa Nigeria" Amma yazatayi...shi gida,gida neh ko bata koma domin Mami ta fada ba,ta

san dole watarana saita waiwayi rayuwar da ta baro acan Nigeria, dole ne watarana saita koma gida, she's here to find solace amma babu ranar da bata tuna abunda ya sa ta baro gida Nigeria..Ganin tunanin babu inda zai kaita yasa ta rufe laptop din ta wuce n

ata dakin dake gefen na nafisa don tayi wanka.

Zuwa 11 na safe bayan sun kammala breakfast sun tsaftace gidan nafisa ta tusata a gaba ta chanja kaya suje shopping din tare,a cewarta tunda ta ajiye schoolwork din nata to bazata zauna ita kadai a gida ba.

.tana murmushi ta tambayi nafisan "ni ke ina naki school work din?" Dariya nafee tayi tana mata wani kallo tace "ni nawa bana hana bacci bane,ke nifah ko exam bazata hanani bacci da hutu ba,Ina dalili" na'ima tace "Eh nima shaida ce" tana tuna lokacin da s

uke Bayero University Kano nafee dai baza'a taba ganin ta maida hankali akan lectures bama balle sauran school activities, Kuma batacin grade mara kyau domin Allah ya bata ilimin daidai gwargwado,kawai ita haka Allah yayita irin mutanen nan ne marasa sawa

aki damuwa bakowanne abu ne yake daga mata hankali har ta sashi arai ba balle lamarin makaranta, sai abun nata ya hadu da gata kuma kasancewarta ita kadai mace wajen iyayenta babu abunda ta rasa daga wajensu da kuma siblings nata maza.

Haka na'ima ta sh

irya cikin maroon abaya tayi rolling gyalen ta saka flat shoe ta fito zasu tafi tana kallon kayan jikin nafeesa wadda sanye take da white silk jersey short dress ta hada da blue jean trouser tayi rolling white gyale hannunta riqe da car key, farkon zuwan n

a'ima England nafisa ta sha convincing dinta ta fara dressing kaman nata but she always stand by NO

Abune wanda bata taso taga anayi ba a inda tayi rayuwa. Rayuwarta da ta nafisa kamar banbancin fari da baqi neh wanda tun daga nesa zaka iya hango banba

ncin su batareda ka matso kusa ba,Amma haka Allah ya hada jininsu suka zamo kawaye tun level 100 a BUK har ila yau da suke Msc tare a Oxford University England.

Haka suka tafi wajen siyayyan a motan da Abban nafisan ya siya musu domin uzurin makaranta d

a kuma na yau da kullum.

Sun siyo duk kayan buqatunsu harda personal essentials dinsu suka koma gida cikin walwala

Bayan sun huta sunyi sallah nafee ta tafi kitchen zata jera kayan ta bar na'ima nan falo zaune kan sallaya saiga kiran Anty Amnah, qanw

ar baban nafisa ceh da take aure a London da yaranta biyu twins maza, daukan kiran tayi suka gaisa anty Amnah tace "na'ima munata jiran zuwanku tun jiya i thought zakuzo weekend, Boys suna ta murnan zakuzo har sun gaji,hope kuna lfy" na'ima tana murmushi t

ace " lafiya anty ,we are sorry, muna research akan wasu essays ne shiyasa bamu samu zuwa ba" anty Amnah tace "No bakomai na'ima dama saida nayi tunanin school activities ne suka riqeku this week, nakira nafee ma no answer hope she's okay" ta amsa cikin sa

nyinta "Eh lafiyanta kalau anty tana kitchen ne...In Sha Allah next week zamuzo abawa boys hakuri" tace "it's Okay kuhuta gajiya" sukayi sallama ta kashe wayan batakai ga ajiyewa ba kiran Mami yashigo ta daga da sallama tana gaisheta ta daya can bangaren M

ami ta amsa da "lafiya kalau Habibti yakuke, ya karatu?" Na'ima tace "Lafiya Mami,yasu yah faruk?"

"Lafiya na'ima,fatan babu matsala ko"

tace "Alhamdulillah Mami"

Mami tace "nafisa tace zakuje siyayya yau" "Eh har mun dawo"

"Ma Sha Allah, Ha

bibti ki kwantar da hankalinki kiyi karatu kinji, sannan ki rinqa addu'a"

Muryar na'ima na dan rawa ta amsa da "in Sha Allah Mami"

Mami tace "it's alright Habibti, everything is going to be fine..in kinji bakyason zuwa bikin Salman ma kiyi zamanki in

su amnah zasu dawo zan biyosu inzo na dubaki kinji" Na'ima tace "A'a Mami zanzo, zamu taho tare da nafisan"

Mami tace "Toh na'ima,Allah ya bada sa'an karatu kinji"

Hawaye na taruwa a idonta tace "Amin Mami nagode"

Da haka sukayi sallama tagama

goge idonta nafisa tafito daga kitchen hannunta riqe da chocolates guda biyu ta qaraso ta miqa mata daya itama tana bare daya ta zauna kan kujera

tace "Anty Amnah ta kiraki?"

Na'ima ta amsa da "Eh bamu jima da yin waya ba, takiraki baki dauka ba"

Nafee tana gyara zamanta a kujera tace "Nakirata ai, wai tsaya... don't tell me anty amnah tana expecting mu rinqa driving for 2 hours to go to London every two weeks to spend weekend there" murmushi na'ima tayi ta miqe tana cire hijabin jikinta tana girg

iza kai draman nafee nabata dariya.

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa





Chapter 02

Lagos, Nigeria

Mutane akalla sha biyar ne zaune cikin conference room din Oil & Gas company dake victoria island cikin garin Lagos, suna gudanar da meeting me m

uhimmanci tsakaninsu da turawan dake other side of the conference table.

Cikin nutsuwa suke tattaunawa da Ahmad dakeyin nashi bayanin  cikin harshen turancinsa mai dadin sauraro, kasancewarsa mutumin da yayi rayuwan qasan turawa na tsawon lokaci, he sure

has his way of interacting with them.

Can dai yayi shiru kawai yana sauraronsu batare da yawan basu dogon amsa ba, Dan'uwanshi Adam dake gefenshi neh yayi saurin amshe conversation din knowing Ahmad bazai sake doguwar magana ba kuma tunda al'amarin yafara

bashi haushi.

Haka Adam suka gama sauran tattaunawan , suka miqe gaba dayansu akayi musabaha har dashi Ahmad din telling them zasuji nasu final answer dinsu zuwa jibi.

Fitowa sukayi daga conference room din Ahmad yatafi wajen elevator zai koma nashi off

ice din while Adam ya tsaya magana da wani employee dinsu.

Shigarshi office din nashi keda wuya Adam ya biyo bayanshi, ya qarasa kan executive chair dinshi ya zauna at the same time yana duba wasu folders da yasa secretaryn shi yakawo masa dazu, wucewa gu

rin fridge Adam yayi ya bude zai dauki ruwan sha , cikin husky voice dinsa  Ahmad yace "pass me one please" Adam ya dauko bottle water guda biyu ya qarasa ya ajiye masa saman table dinsa,

Ahmad ya jawo ruwan yana muttering "thanks". shiru sukayi da fari s

ai can Adam yace "so what do you think?" batareda Ahmad ya kallesa ba yace "I'm Out" cike da mamaki Adam ya ajiye nashi ruwan shima kan table din yace "what?..Dude are you serious?"

sai Ahmad ya dago kanshi yana kallon Adam with seriousness, cikin idonsh

i Adam din yake kallo yace "You can't be serious"

Ahmad ya juya yana duban foldern gabanshi yace "Well..too bad i am" Adam ya sake cewa "You can't cut out on this, ta ina aka samu matsala kuma?"

Ahmad ya amsa da "The percentage...I don't like it" sai A

dam ya juya tareda nufan gurin small lounge dake cikin office din a gefe yayi settling akan kujera ya juyo yana kallonshi yace "You know this deal is a fair one right?"

Ahmad na kallonsa yace "we need to include some high risk, high return options" Adam

yace "but we can't gamble with anything high risk"

sai Ahmad ya sauqe numfashi yayi dan daga kafadarsa like he don't care, yace " No good thing comes without a little risk" Adam yace " then what are you going to do now?"

Baya Ahmad yayi akan kujeran ya

yi relaxing bayansa yana kallon Adam yace "I'll sort everything out" sanin waye Ahmad yasa Adam din cewa "Okay..it's settled then" don yasan wasting din energy dinsa kawai zeyi wajen convincing din Ahmad saboda ya riga yayi making mind dinsa, sai yakuma ce

wa "I'll be flying back today, in few hours ma" Ahmad yace "Okay, take care" miqewa Adam yayi yana cewa "Dude, ka kwana biyu baka leqo ba fah"  sai Ahmad ya shafa kanshi kadan yace "akwai bikin yarinyar can wai ko, I'll be there next month in Sha Allah"  d

a haka Adam ya qaraso garesa ya miqa masa hannu sukayi shaking yace "see you then" Ahmad ya amsa da "thanks man,safe flight".

Bayan tafiyar abokin nashi kuma dan'uwa, Ahmad ya maida hankalinsa kan desktop din dake gabansa can kira yashigo wayanshi, Sunan

ne Laila ya fito akan fuskan wayan ya juya yana kallo har ta tsinke bai dauka ba yakoma kan ayyukanshi.

Daren ranar na'ima ta fito daga wanka tana zaune gaban madubi  tana shafe shafenta da ya zame mata daily night routine yanzu,

Kuma duk nafisa ce ta

koya mata this kind of routine, ita ta siyo mata all skin care sets da suka dace da kalan farin fatarta sannan ta rinqa koya mata a sannu sannu har ya zamto bata iyayin bacci yanzu batareda tayi shafe shafennan ba, dago hannunta tayi tana ganin yanda yaza

ma smooth and glowy, tasan kayan ba masu sauqin kudi bane domin fenty skin care sets nafisa ta siyo mata, And she's very grateful for all of it, when she says all of it tana hadawa da kyautatawan da nafee tayi mata a baya da kuma wanda take kan yi mata har

zuwa yanzu.

Nafee ba qawarta bace kawai, ta zame mata yar'uwa or even more so, dan bazata taba mantawa da ita ba a duk inda taje a rayuwan nan.

Tana cikin wannan tunanin nafisa ta shigo dakin hannunta riqe da laptop a bude alamun tana kallon movie, qara

sawa tayi kan gadon Na'iman tareda kwanciya tasa laptop din agaba itama kayan bacci neh jikinta, tace "BoBo, my crush is killing it in this new series" Na'ima ta juyo tana dan dariya tace "Au wai haryanzu dai Witcher din kike kallo?" Nafee tace "kinsan All

ah..sabon nan yafi dadi ma, ki gama kizo ki gani"

Na'ima ta juya ta cigaba da daure tumilin gashinta guri daya tace "A'a bazan gani ba" 

Nafee tace "dalla can ya hadu kizo mugani, Ina zuwa ma" sai ta miqe ta fice daga dakin bayan minute sai gata tadawo

dakin riqe da packs na cheese balls ta wulla na na'ima kan gado sannan ta kwanta a gurbin da ta tashi ta cigaba da kallonta tanacin cheese din.

Bayan Na'ima ta gama itama ta hau gadon ta matso tareda daukan nata cheese din tana budewa tace "Gaskiya ni ki

n taquramin da series dinnan" Nafee tace "kiyi shiru ni mugani"

Haka suka kai almost sha biyu suna kallon, na'ima da tace an taqurata sai ga ta itama ta zage tana kallon with full interest har Nafisa tayi bacci ta barta, saida ta gaji sannan ta tashi t

aje bandaki tayo uzurinta ta fito bayan tayi alwala tayi sallah sannan ta kwanta a gadon tana jawo duvet dinsu da Nafee ta kwashe a jikinta ta lulluba, bata qara wasu mintuna masu tsawo ba itama baccin ya dauketa.

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa





Chapter 02

Schoolwork dinda Na'ima batayi ba washegari kenan suka shiririce wajen kallo, da suka gama na'ima ta tafi kitchen zata dafa musu tuwo miyan ganye

Nafisa na tayata tana bata labarin samarinta, da wa'inda ta baro a gida Nigeria da kuma wa'ind

a take kulawa sama sama anan oxford din,

Na'ima sai dariyan draman nafisa da saurayinta umar take, saurayinta da tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login