Showing 30001 words to 33000 words out of 111233 words
tafi turai a gyara miki ki kwanta
r da hankalinki kar ki sakawa kanki ciwon zuciya…."
Ya ƙarashe maganar ya na huci...
Dukda su Aliya sun tabbatar masa ba Baba bane ba amma shi ya ke zargi, batun garkuwa wannan ma ya san in ba kyar ba duk Baban ne ya yi mata chune ya cewa sojojin Sajida
su bincika har cikin ƙasa ko kuma dae wani abun makamancin haka duba da yadda surukin nasa ya tsani ƴar tasa kamar mutuwarsa.
Shigowar Likita wanda ya yi alƙawarin dawowa yanzun ne ya katsewa Kaka Nura aikin rarrashi da tunanin da ya ke yi.
Da sauri
ya miƙe sannan ya juyo ya mayar da hankalinsa kachokam ga Likitan ya na jira ya ji bayani……
Kallonta Likitan ya yi ya
ɗ
an kalli Kaka Nura kafin ya ce "Baba a
ɗ
an bamu guri…Ina so zan yi mata magana in private…"
Cikin fushi Kaka Nura ya ce”zancen banz
a kenan!!! A wannan halin da ta ke buƙatata a ko da yaushe ka ke tsammanin in fita?? Ba ka ganin hatta sojiji sun sarara mini saboda sun san darajar Uba?
Dan haka Mallan fa
ɗ
i duk abunda ka zo da shi ba ni da tamkar ta itama ba ta da ya ni!!"
Kallont
a sosai Likitan ya yi kafin ya ce "in fa
ɗ
i komai a gabansa?"
Cikin fushi Kaka Nura ya bu
ɗ
e Baki zai yi magana sai kuma ya juya ya kalli Anne wadda a hankali ya ji motsi ya ga ta
ɗ
an girgizawa Likitan Kai alamun A’a…shiruu Kaka Nura ya
ɗ
an yi kafin ya ƙa
rasa ya shafa kanta ya ce "idan kun gama sai ki sakashi ya shigo da ni ko?Allah ya yi miki albarka ki kwantar da hankalinki" daga haka ya wuce da sauri ya fita gudun kar ya
ɓ
ata musu lokaci……
Sun riga sun saba da Likitan ya santa ta sanshi farin sani sh
iyasa ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita nan gefen gadon kafin ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya ya furzar da iska ya zare gilashin idanunsa ya
ɗ
an mitsitstsika idanunsa kafin ya mayar da gilashin ya sake sauƙe ajiyar zuciya tukunna ya fara magana ba tar
e da ya kalleta ba saboda har ga Allah tausayinta ya ke ji matuƙa.
“Nuratu da farko dai inaso duk abunda zan fa
ɗ
a miki a yanzu ya zamana kin runguma kin kar
ɓ
i jarabawarki hannu bibbiyu, hakan ake so musulmi ya kasance a ko da yaushe idan musiba ko ƙaddara
ta same shi mummuna ko kyakkyawa….."
Numfashi ya sauƙe wanda ita kuma Anne tuni tashin hankali da masifar da take ciki ya sake hauhawa....tsoro da firgici ba sa daga cikin
ɗ
abi’arta amma a yau kam tsoron da ta tsinci kanta a ciki ba zai misaltu ba, ga wa
ni Irin firgici da ban
ɗ
okin zullumin jin abunda zai fito daga bakin Likita…tuni rigarta ta jiƙe sharkaf da gumi tsabar masifa har ma da gashin kanta ga azabar da fuskarta da ƙirjinta su ke yi mata ba na wasa ba ne! Tabbas ta san koma menene zai fito daga b
akin Likita ba abun alkhairi bane ba tunda ya fara furta mata irin waennan kalaman a gabannin bayanin nasa....ga shi ta rasa fuskarta da ƙirjinta wanda surar jikinta kyan fuskarta su ne abun taƙamarta, ta san ko da ace za a gyara mata ba zata koma kamar da
ba shiyasa kawai ta shiga addu’ar Ubangiji ya
ɗ
auki ranta a take saboda bayaga musibar da take a ciki ba ta jin za ta sake karbar wata sabuwar jarabawar…..
Cike da alhini muryar Likita ta dira a dodon kunnuwanta ta inda ya ci gaba da cewe "Ɗazu dama na
gaya miki kuma kema kin ga yadda acid
ɗ
innan ya tauye Mamanki na hannun dama(right breast) kasancewar ya shafi na hannun hagun shima ya sanya jejin da ke
ɓ
oye a jikinki ya ruru matuƙa! dan haka a gaskiya dole sai dai mu ha
ɗ
a duka biyu a yanke saboda na yi
testing acid
ɗ
in mai mugun ƙarfi ne dan haka gara a yi maganin sa da jejin gaba
ɗ
aya tun kafin jejin ya ya
ɗ
u a jikinki sannan
ɓ
arnar acid
ɗ
in ta fi haka.
Karkarwa jikinta ya
ɗ
auka a take, zuciyarta tana wani irin ƙuna…Bata gama nemawa bal’in masauƙi a
cikin zuciyarta ba ƙirjinta ya yi wani kalar mahaukacin bugawa zuciyarta ta hantsila kamar za ta faso ƙirjinta ta fito sakamokon sautin muryarsa da ta ji yana da
ɗ
a cewa "Sannan nan da kwana biyu sun ce za su wuce da ke prison a ta sakamokon laifin garkuwa
da Yara har biyu da ki ka yi ki kai tsafi da su, dan haka za mu kammala komai da wuri in yi miki duk abubuwan da ki ke buƙata sai ku wuce, ki ci gaba da jinya a cikin asibitin da yake prison
ɗ
in in mun saka ranar da za a miki aikin za mu je mu
ɗ
aukoki a yi
miku in ya so a sake mayar da ke chan
ɗ
in ki ci gaba da jinyar kafin a yanke miki hukunci."
Cikin sauƙe numfashi ya
ɗ
aura da cewa “mun yi miki gwajin jini saboda musan ta yadda za mu fi baki kulawa da kuma jinin da za'a samu a ƙara miki in an shiga dake
aikin da za a yi miki a ƙirjin ki unfortunately Nuratu ki na
ɗ
auke da cutarnan mai karya garkuwar jiki na san baki sani ba saboda ko last time da kuka zo da ke da Alhaji Nasiru aka
duba sam babu ita a jikinki, sannan hantarki ta ta
ɓ
u amma ita ba mu yi sca
nning mun tabbatar da matsalar wacca iri bace ba.."
Cikin sauƙe numfashi ya ce "na gwada neman alfarmar a barki a nan dan sai kin fi samun kulawa duba da tarin ciwukan da su ke damunki gashi akwai wani aikin a gaba wanda dole sai an yi amma kuma kasancewa
r ba a da
ɗ
e da miki aiki a ƙafa ba ya sanya dole sai an jira..
But sun ƙi yarda, sannan duk yadda na so in samu wata ƙofa da za ta bani damar da za a yi miki aikin lokaci guda hakan ba zai ta
ɓ
a yiwuwa ba, dan haka nan za mu haƙura mu yi addu'ar Allah ya
sa kar abun ya fi haka mu jira har nan da tsawom mako biyu tukunna sai ki dawo a yi miki aikin ƙirjin...."
Shiruu ya
ɗ
an yi sai kuma ya fesar da numfashi kafin ya ce
"Anyways...
Za mu
ɗ
auraki a kan magunguna yanzu kafin a dawo yi miki aikin, sai ki wuc
e da su chan ki ci gaba da sha
Allah ya rufa asiri ya baki lafiya ….."
Tabbas duk wanda ya ce bala’i ya ishe shi ya ke ganin kamar babu yadda za a yi ya sake shiga cikin wata masifar to Allah ne kawai bai so ba….Allah ne kawai ya barshi amma duk ta
inda ka kai ga shiga tashin hankali ka ke ganin ka kai peak in dai Allah ya ƙaddara to akwai gaba da shi… da aka watsa mata acid gani ta ke yi kamar kawai ƙarshen masifar da za ta iya samunta kenan…da ta kalli ƙirjinta ta ga yadda ya koma sannan babu ƙafaf
u sai ta ga Ashe akwai level two, kwarin guiwar da Mahaifinta ya bata ne ya sanya ta
ɗ
an yarda akan wataƙila za ta iya samu rayuwarta ta
ɗ
an daidaita ta samu ta zama mutum ta ci gaba da rayuwarta dukda babu ƙafafu da ƙirji ta san za ta lalla
ɓ
a da babu gara
ba da
ɗ
i sai dai abunda ba ta sani ba ashe ba ta ga komai ba kuma ba ta ji komai ba..a haka ma ba a zo kan maganar hukuncin da za a yanke mata ba na laifin da take da tabbacin ita ta aikata ita da tshohon saurayinta
ɗ
an fashi ta inda ya sace Yaran su ka da
ɗ
e a wajensa ya na ta amshe ku
ɗ
a
ɗ
e a wajen iyayen Yaran, wanchan satin da ya gabata bokanta ya ce ta kawo Yara maza biyu a yi mata aiki da ta gaya masa(saurayin nata) ya ce akwai su ka kai Yaran ta yanka su da hannunta bayan ta yi zina da ko wanne a cikin
su tukunna aka yiwa yaran filla filla kamar yadda ake daddatsa kaza aka tsafe su tass aka ha
ɗ
a da kayan tsafi aka saka mata a cikin tukunyar ƙasa da wani ruwan da boka ya rantse mata akan ba zai bari su
ɓ
aci ko su yi wari ba ita kuma ta kar
ɓ
a
ta binne a ƙa
san drawer kayanta har da kayan jikinsu ta binne a gefe da zobunansu na azurfa dan gudun kar ta je jefarwa ko ta yar a kamata...kuma sai da bokan ya tabbatar mata kar ta bari a gani in ba haka ba aikin ya lalace amma in ta
ɓ
oye da kyau to har abada asiri y
a na nan kuma ba zai lalace ba kamar yadda tsoka da halittun gangar jikin yaran za ta kasance fresh saboda ruwan da ya zuba aljanun za su dinga kula da shi ba zai lalace ba…
Wanda abunda ba ta sani ba ma warin ne ya janyo hankalin sojojin zuwa inda ajiyar
tata ta ke....
Kuka Anne ta saki wanda ba a ji ba a gani ta na sake jaddadawa kanta tabbas tata fa ta ƙare...Dan a yadda Allah ya yi fushi da ita
ɗ
innan ta fara ganin jarabawa kamar ruwan sama ta koina tabbas ta san wataƙila azabar da za ta gwammaci m
utuwa za a yi ta gana mata a prison
ɗ
innan dan ita kanta ta san ƴaƴan waye ne amma da ya ke idanunta sun rufe a lokacin ta ce a yi mata aikin da su………ita da farko da ta ji Kaka Nura ya na batun police da hukunci sannan da ta ga soja a
ɗ
akin ta
ɗ
auka duk Sa
jida ce ba ta barsu ba ashe wannan
ɗ
anyen aikin nata aka binciko....
A hankali ta samu da kyar ta rufe idonta tana kar
ɓ
ar azaba ta ko wanne fanni zuci, kwanya da gangar jikinta zuwa yanzu ta daina jin abunda Likita yake fa
ɗ
i da bayanan sa dan iyakacin abu
nda ta sani shine tata ta ƙare!! Gashi komai ya lalace mata ya ta
ɓ
ar
ɓ
are mata! Tabbas wannan shine asalin mutuwar tsaye haƙiƙa babu yadda Ubangiji baya iya juya al’amari kuma
ɗ
an Adam ba a bakin komai yake ba duniya da abunda ke cikinta zancen banza! wai y
au ita Nuratu ita ce ake yiwa zancen babu Nonuwa babu ido babu fuskar data tsolewa dubu ido fuskar da take taƙama da ita sannan gata dumu dumu a hannun hukuma, dan haka babu isa sannan babu gadara..wani irin kukan zuci ta ke yi saboda ta riga ta san ba ta
da wata sauran mamora gashi dai da sauran shan miyarta dan bata kai arba’in da biyar ba ma a duniya amma ta san ko tshohuwar mahaukaciya sai ta fita daraja da mutunci a idanun maza da duniya ma gaba
ɗ
aya dan ko da ace ta tsallake case
ɗ
in da yake jiranta t
a fito ba a kashe ta ba, kuma ciwukan jikinta suma ba su tarwatsata ba tabbas a yadda halittunta suka koma ita kam ta san an gama yi mata mutuwar tsaye.……………
SHEKARUN BAYA DA SU KA SHUƊE
(Waiwaye)
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*13*
SHEKARUN BAYA DA SU KA SHUƊE..
(Waiwaye)
KANO
Ƙ
OFAR MATA
Asalin sunan Anne Nuratu Muhammad Nura, Mahaifiyarta cikakkiyar ƴar Kano ce anguwar zage ƙofar mata yayinda Mahaifinta ya kasance
bafulatanin chad
ɗ
an sarkin rugarsu a wanchan lokacin….fa
ɗ
a ne ya korosa shi da Mahaifinsa daga chad tun lokacin da aka ci Mahaifin nasa da yaƙi wanda hakan ya sanya aka kwace matarsa da ragowar magoya bayansa waenda basu fi mutum biyar ba, sarkin da ya k
ar
ɓ
i mulki shi ya auri matarsa shi kuma kakanta aka koresa kora ta har abada daga ƙasar gaba
ɗ
aya da shi da mahaifinta (Kaka Nura) wanda a lokacin ya ke Yaro ƙarami.
A Nigeria suka yada zango garin Kano unguwar ƙofar mata a lokacin Mahaifin Mahaifiyart
a shine Mai Unguwa..shi ya kar
ɓ
esu hannu bibbiyu ya musuluntar da shi da
ɗ
an nasa (Kaka Nura) su ka za
ɓ
i sunayen musulunci ya koya musu karatu har ta kai ga sun zama kwararru suma dan har koyarwa Mahaifin Mahaifinta ya ke yi a tsangayar kakanta (na
ɓ
angar
en uwa), Mahaifin Mahaifinta bai kai ga yin wani auren ba, kwata-kwata shekaru bakwai Ubangiji ya bashi ikon ƙarawa a duniya ya kar
ɓ
i ransa….ya rage saura Mahaifinta (Nura) ka
ɗ
ai wanda da shi da maraya ba su da maraba dan ko da wasa a yadda Mahaifinsa ya f
aiyyace tsarin rugar tasu ba a isa a mayar da shi garin ba tsaff za su yi masa yankan rago tunda korar su aka yi….
Mahain Mahaifiyarta (Mallan) ya yi iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya inganta rayuwar Nura, bayan karatun allo har a makarantar da ƴaƴansa
su ke zuwa ya saka shi dan Mahaifinta (Nura) yanada shiga rai farin bafulatani ne kwarai kyakkyawan gaske sai dai kuma tun Nuratu ta na ƙarama ta ke ji a wajen Mahaifiyarta da ƴan uwan Mahaifiyarta kuma itama ta ji ta gani cewa ‘Mahaifinta sam ba mutumin
kirki bane ba’
Dan tun ya na Yaro yana da taurin kai, riƙeƙƙen ra’ayi, cin amana, sata, ƙarya, son abun duniya da shegen son abunsa ga kwa
ɗ
ayi da son abun wani…ƴan uwan Mahaifiyarta (Uwani) maza su uku ne Yusufa, Ali da Garba! Ita ka
ɗ
ai ce mace a gidansu
, ƴar auta..hakanan a ka ja shi a jiki a ka mayar da shi
ɗ
an gida duk wani abu idan suka samu tare su ke rabawa da shi haka iyayen suma tare su ke yi musu komai da shi amma shi ko ruwa pure water idan ya siya ya na sha ka ce ya rage maka ba zai bayar ba sa
i dai ya ce 'shima ba zai ishe shi ba', ku
ɗ
i kuwa ta jikin Kakanta(Mallan) ya ke samu amma naira biyar
ɗ
insa ba ka isa ka ci ba gashi da shegen tsaurin ido Hakanan zai siyo Abu a gaban idanun kowa ya zauna ya ci ya yi ƙatt! Ya yi gyatsa ko magen gidan haka
nan za ta ƙaraci kukan ta ta gama zagayeshi amma ba zai bata ba…
Wannan
ɗ
abiar ta Mahaifin Nuratu (kaka Nura) ita ta janyo masa baƙin jini a wajen Mahaifiyar Mahaifiyarta saboda dama ita tanada
ɗ
an zafi kuma ba ta son raini…Mahaifin Mahaifiyarta(Mall
an) kuwa shi kam bai cika son gutsiri tsoma ba shiyasa bai ta
ɓ
a biye mata ba ƙarshema ce mata ya yi ‘kar ta sake kawo masa ƙararsa, ai kowa da halinsa ake zaune da shi kuma har yanzu Nura (Kaka Nura ) Yaro ne dan haka baya son yawan zance iyakaci shi dai y
a san zai ciyar da shi ya yi masa tufafi ya bashi muhalli har zuwa lokacin da Allah zai ƙaddara ya yi aure ya kama gabanshi.’.
Tsanar Kaka Nura ba ta sake samun wajen zama a cikin zuciyar Mahaifiyar Uwani ba sai lokacin da ya kawo ƙarfi, a lokacin mazan
gidan guda biyu sun yi aure saboda dama duk sun girme masa sosai mutum biyu ya girma Uwani da yayanta, dan haka gidan sai ya rage daga shi sai Uwani da yayanta wadda take da shekaru sha hu
ɗ
u dan yayunta maza biyu sun basu tazara sosai har ana tunanin ma M
allan ya daina haaihuwa ne tukunna aka haifi yayanta (saƙonta)itama aka haifeta.
A wannan lokacin shekarun yayan nata sha shidda sai Kaka Nura shima sha shidda dan watanni uku ne a tsakaninsa da yayan nata.
A lokacin ne Mahaifiyar Uwani ta fahimci shege
n son matan Kaka Nura dan har Mata ta ji ƙus-ƙus
ɗ
in ya na kaiwa shagon su wanda ke a waje saboda duk mazan manya sun yi aure kuma dama a
ɗ
akinsu ya ke sai ya zamana
ɗ
akin ya zama nasa shi ka
ɗ
ai, dan Yayan Uwani wanda ya rage a cikin gida nasa
ɗ
akin yake..
...
Ita ta
ɗ
agawa Mallan hankali akan batun amma sai dai ba a yi mata yadda take so ba ƙarshema abun ca
ɓ
e mata ya yi dan Mallan cewa yayan Uwani na cikin gida ya yi 'ya tartara kayansa ya koma
ɗ
akin Kaka Nura da ke a waje idan har gaskiya Mahaifiyar Uwan
i take fa
ɗ
a to hakan zai takawa Nura burki daga
ɓ
arnar da yake yi'. Sai dai kuma ko sati ba ayi da komarwa yayan Uwani shagon ba Kaka Nura ya yi
ɓ
arnarsa da ƴan mata har biyu kuma ya shiga ya fita aka kama yayan Uwani da laifin dumu-dumu, laifin da har ya
u har gobe kowa yake ganinsa da shi, Mallan shima