Showing 99001 words to 102000 words out of 111233 words

Chapter 34 - Bakar-Tukunya-Compelete

08 Sep 2026

22

juya ta fito tausayin Yarinyar fall ranta, in ta huta ko zuwa anjima ne in sha Allahu sai su yi magana a nutse a kan Isma’il.

Yadik

ko kuwa ta na kai mata nata kunun da zagi ta bita, yayinda Kaka Nura ko

kallonta bai yi ba, ya tsani Matar sosai besides ba ya so Yadikko ta fahimci ya na nan.

Anne kam dama ba ta ko

ce mata ta gama ba, ta dai

bar mata nata a rufe.

….

Anne yau wuni

ta yi a

ɗ

aki, mirsisi kuma ko ha

ɗ

a kayanta ba ta yi ba kamar yadda Yadikko ta ce, tana zaune abunta tana ta faman saƙa da warwara.

Tabbas sai ta saka Isma’il kuka wallahi dan yana daga cikin mutanen da su ka

ɗ

aga mata hankali a yau su ka hanata walwala…

Tana cikin wannan lissafin, kamar

daga sama kawai ta soma jiyo sallamar Mama (Mahaifiyar Isma’il).

Ƴ

an Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminc

i, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*

Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*

Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *0814

3828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida d

a dai sauransu....

location:Kano

Delivery:NationWide.

kar ku bari a baku labari, sai kun zo

🙏

SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA





0806 402 1951

0903 441 3252

[10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

*page 33*

“To ka dai ji abunda Uwarka ta ce!

Dan haka ba yawo na tafi ba, idan kuma ka nace akan cewa yawon ne to ka ga da ni da ita ne mu ke da shirin zuwa, Allah bai yi itan ta samu zuwa ba a sabili da nannauyan baccin da ya kwasheta ba gaira ba dalili.”

Cewar

Anne, ta ƙarashe maganar tata ta na wata dariyar rainin hankali ƙasa-ƙasa.

“Tabbas”

Yadikko ta ce cikin ƙoƙarin ganin ta yi supporting Anne duk rintsi.

Tunda Anne ta soma magana Baba ya runtse idanusa.

Ya lura so take ta wulaƙantashi ga Yadikko

ta ƙi komawa

ɗ

aki, dan haka ya shirya kawo ƙarshen komai in ya so ayi uwar watsi! Tabbas gara hakan.

A hankali ya bu

ɗ

e rinannu kuma gajiyayyun idanunsa ya ce “Nuratu halinki ya isheni, ba na jin zan iya ci gaba da haƙuri…”

Duk rashin tsoro, tsaurin ido d

a taurin zuciya irin na Anne, ba ta san lokacin da ta

ɗ

ago manyan idanunta ta zuba masa ba cike da shock, dan sam ba ta yi tunanin zai iya furta mata hakan ba.

“Matsowa kusa da shi Ya Amir ya yi sosai sannan a hankali ya ce “Baba ka yi haƙuri, Anne da a

uren ma ya aka ƙare ballanta babu, dan girman Allah ka yi haƙuri Baba ka rufa mana asiri”

“Hmm”

Kawai Ya Abba ya ce shi kuma ba tare da ya ce uffan ba.

Wani kalar kallo ta

ɗ

ago ta watsawa Ya Abban dama ga takaici da shock

ɗ

in da Baba ya jefata a cik

i, ba ta gama dawowa dai-dai ba Baba ya ce “dan haka ki je har sai na neme ki.”

“A’uzubillahi”

Yadikko ta ce, sannan ta matso inda ta ke jin saitin muryarsa ta

ɗ

aga sandarta ta kai duka, sai dai ba ta sami kowa ba, dan bata saita dai-dai ba, this time

around.

“Ki tattara ki bar mini gidana, kafin in dawo, kar in tarar da ko

ɗ

ankwalinki ne.”

Ya fa

ɗ

i hakan yana mai jin wani sanyi ya na sauƙar masa kamar an zare masa ƙaya.

“Ka na da hankali kuwa Habu? Tun wuri ka janye wannan batu naka kafin in tsin

e maka albarka wallahi.

Babu inda za ta je!

Kuma kar ka fita ko ina ka tsaya har sai an gama magana wallahi.”

Cewar Yadikko wadda duk ta bi ta gigice, yo in aka kori Anne ae tata ta ƙare sai dai ta bita…

ita kanta ta san ta riga ta gama zama addicted

a abubuwan da ta ke sha, dan haka take da tabbacin muddin ta daina to sai dai a kwashi buzunta.

“Gara da Allah ya bu

ɗ

e

maka idanunka! Tabbas wannan Mata taka musiba ce! Yadda ka yunƙuro haka Allah ya baka ikon rabuwa da ita gaba

ɗ

aya, Congratulations d

an wannan abun a tayaka murna ne.”

Cewar wani mutumi maƙofcinsa, wanda ya fa

ɗ

i hakan a iyaka gaskiyarsa, yana gama fa

ɗ

in haka ya juya ya fita gudun kar Anne ta yi masa ashar

ɗ

in da shi kuma zai halakata a wajen.

Ya Abba dai da Ya Amir ba su ce komai ba

.

Haka itama Adda da Afra, kowa ya sunkuyar da kanshi ƙasa.

Yadikko ke ta hayagaga ta na iƙirarin za ta tsinewa Baba in bai fasa korar Anne daga gidan ba, gaba

ɗ

aya ta gigice.

Wata tsohuwa ce ta matso kusa da Yadikko sannan ta ce mata “yanzu ke ƴar

Uwa aka ce miki hakan ba abun alkhairi bane ba? Murna ya kamata fa ki yi Allah zai rabaku da

ɓ

aragurbi. Kamata ya yi ki yi fatan ya sauwwaƙe mata gaba

ɗ

aya in ta tafi kar ta dawo, Inace ke da kanki ba kya son auren nasu a da, shin mai ya faru ya sauyaki y

anzun ne…”

Cikin tarar numfashinta Baba ya ce “ga ta nan! Ya yi maganar cikin nuna Anne sannan ya ce “duk ita ce ta tarwatsa min rayuwata da ta ƴaƴana amma yanzu komai ya

ɗ

auko hanyar gyaruwa in sha Allahu.”

Sai kuma ya nuna ta sannan ya ce “na ce miki

ki fita ki bar mini gidana ko?”

“Allah Sarki rayuwa”

Anne ta fa

ɗ

a muryarta ta na karkarwa! Tsabar bala’in da ya ke cinta. Sannan ta ce “Ɗan adam butulu.

A lokacin da ka

ɗ

irka mini ciki aka ce a rufawa juna asiri a yi auren ae shiru ka yi akayi auren,

sai yanzu da kake fakewa da ayoyin Ubangiji wae kai nan Malami kuma Limami kowa ya yarda da kai, ka ke ci da addini shine za ka tozarta ni ka tona mini asiri ka wulaƙanta ni ko? To bari ka ji! Wallahi wallahi babu inda zan je!, ae Yadikko ma tana da gado

a cikin gidan nan kuma Ubana ta ke aure dan haka zan zauna a ƙarƙashinsu ko saki na ka yi ba zan bar gidan nan ba, ba zan wulaƙanta ba wallahi.”

Ta fa

ɗ

i hakan ta na jin zuciyarta na sacewa, ranta fess!! Dan tabbas ko haka ta barshi ta san an yi 1-1, shi

kanshi ya Amir

ɗ

in ae ba ƙaunarta ya ke yi ba, munafuki! A bayan Ubansa ya ke, dan haka ba ta damu ba in an fara yi masa kallon shege daga yau! Ta san in sha Allahu ko hauka su ke yi daga yau har gaban abada ba za su sake yi mata wani shirmen da tujara ba

, za su dinga shakkarta gudun kar ta sake yi musu kalar wannan tujarar sannan gara kowa ya san cewa suma fa akwai kashi a gindinsu…kalli fa yadda ake yiwa Baba murnar somi-somin rabuwa da ita kamar wata guba!.

Wallahi ba inda za ta je kuma ko da ace saki

nta ya yi ba za ta yarda ba sai ta koma

ɗ

akinta! Kamar da ƙasa! Yo

Hauka ake…..ba za ta yi accepting defeat ba, ba a isa a koreta a bata hutu ko a sake ta ba, in ma rabuwar ce gara ita ta barshi ba dai shi ya barta ba, sannan inama za ta je in ya kore ta,

kuma ko da ace ba ta bar gidan ba ta san in har ta yarda da wannan yajin to fa duk tsiya sai powerta ta ragu a cikin gidan, kar ma ya auro wata! Inaa ba zai yiu ba.

A hankali Ya Amir ya zame ya bar wajen ya nufi

ɗ

akinsa, yana ganin Adda ta biyoshi ya

rufo ƙofar kawai ya saka sakata da sauri, ba dan ta so ba ta haƙura ta koma inda su ke ranta a masifar

ɓ

ace.

A chan soron kuwa gaba

ɗ

aya ƙafofin Baba sagewa su ka yi a take kamar zai zube haka ya ji, ga jiri da ya ke kwasarshi kamar hauka!!! Tabbas Anne

Annoba ce, ba ya ko tantama sarai ta san Amir ba shege bane ba kawai dan ta firgita kowa ta rama abunda su ka yi mata shine ta gwammaci ta yi haka a gaban jama’a….

Ƙ

us-ƙus aka fara yi a wajen…wanda hakan ya sake tsorata Baba.

Duk yadda Adda ta so ta ha

na kanta kuka sai ta gagara, ta na ƙarasawa soron ba ta san lokacin da hawaye suka shiga zubo mata ba ganin an fara magana ƙasa-ƙasa, ga takaicin abun, cikin kukan ta ce “haba Anne! Da ke da mu duk mun san ƙarya ki ke yi!

Wanne irin abune wannan? Wacce ka

lar zuciya ce da ke ne? Amir fa

ɗ

anki ne”

“Eh ae

ɗ

azu da ake ci mini fuska da

ɗ

i ki ka ji har kwanyarki, yanzu kuma da yake an ta

ɓ

o

naki shine za ki yiwa mutane kukan munafurcin da ki ka soba. Munafuka Annamimiya kawai.”

Da sauri Ya Abba ya ce “Ya isa

haka!”

Muryarsa na baiyyana

ɓ

acin ran da yake a ciki, maƙura.

Tutture mutanen wajen Kaka Nura ya yi tukunna ya samu ya shigo, tun asuba ba ya gidan ya zagaya gidan wata Mata da su ka ha

ɗ

a Ap, akan zai je da sassafe saboda dare unguwar a cike take sos

ai Safiya ce ba za a iya ganin shige da ficensa ba, dan haka ya tafi ko sallar asuba bai yi ba.

“Abba lafiyanka na ji ka na magana a dake kamar da ƴaƴan cikinka? In ce dai ba jikokina ka ke yiwa wannan gadararriyar maganar ba.”

Cewar Kaka Nura, yana ma

ganar ya na kallon kowa one by one…

Cikin takaici Anne ta ce “da ni ya ke!”

Juyawa Kaka Nura ya yi ya sake kallonsa sosai sannan ya kalli Anne irin abun mamakin nan kafin ya sake maida dubansa zuwa ga Abban sannan ya ce “kai! Dan Ubanka ‘Mai Dala’ wa

nda ya tsaneka ya tsani jin ko da sunanka ne wannan ta yi maka kama da sa’ar wasanka?”

Ya yi maganar ya na nuna masa Anne sannan ya sake juyowa ya kallesa bai damu da yadda Yanayin Abban ya sauya a take a lokacin ba! Ya

ɗ

aura da cewa “dan ka samu an yi ma

ka gata? An rufa maka asiri shine za ka zaƙe?.

Ae da mun bar ka da Uban naka ka na binsa ya na korarka! Ka ga sai ka ƙare rayuwarka a kan titi ka na galantoyi.”

Da masifar ƙarfi Ya Abba ya runtse idanunsa trying very hard to control himself dan a yadda y

a ke ji tsaf zai iya damƙo Kaka Nura kuma in ya ruƙosa zai yi wuya in bai masa illa ba…..”

Cikin tsantsar tsana Kaka Nura ya ce “ka kiyayeni wallahi! Ka kama kanka. Butulu kawai wanda bai san an yi masa halacci ba!

Tirr da kai, a haka za ka ƙare kai ba s

hege ba kai ba

ɗ

an halak ba.”

Sai kuma ya waiga zuwa ga Anne sannan ya ce “menene wai ya ke faruwa ne, na ga an cika?”

Kafin ya kalli jama’ar wajen ya ce “bayin Allah lafiya kuwa!? A watse haka dan Allah…..”

Da sauri Ya Abba ya shige cikin

ɗ

akinsa…

C

ikin ta

ɓ

e Baki Anne ta ce “Habu ne wai ya koreni daga gidan nan. Ya ce in fita in tafi koina ma har sai ya nemeni”

Rasss!!! Haka gaban Kaka Nura ya yanke ya fa

ɗ

i amma sai ya dake!

Bai bari yanayinsa ya nuna hakan ba.

Sai da ya

ɗ

an dawo dai-dai daga girg

izar da maganar ta sanyashi ya yi, tukunna ya kalleta sosai kafin ya ce “ae ta kwana gidan sauƙi. Abu guda dai da na sani shine babu uban wanda ya isa ya koreki daga cikin gidanga, dan haka ki shiga

ɗ

akinki ki kwaso kayanki ki koma

ɗ

akin Yadikko ku zauna t

are, babu inda za ki fita ki je ina cikin gidan nan…

Ki bashi lokaci, in bai ce ki koma ba sai mu nemi saki da kanmu. Kar ki wani damu ba kanki farau ba.”

Tunda Kaka Nura ya shigo dama Yadikko ta

ɗ

an sha jinin jikinta shiyasa ta yi tsit. Da kyar ta iya c

ewa “a ganina da an sasanta abun, kar ka ce haka ka bari in har ni na haifi Abbakar to zan saka ya barta a

ɗ

akinta, wanne kalar shirmene haka zai yi kamar a garin ga

ɓ

a-ga

ɓ

a, auren aka ce masa abun wasa ne, in sha Allahu wannan tsari nasa ba zai yi aiki ba.



Juyawa Baba ya yi ya fita bai bi ta kan kowa ba, dan ba zai iyaba…..Tabbas dama ya san abunda za su yi kenan shiyasa kawai ya fasa sakinta dan kamar yadda Ya Amir ya fa

ɗ

a Anne ba za ta fito da kwayar zarrar mutunci a bazawara ba kuma ba gidan za ta ba

ri ba (ga zahiri ya gani) dan haka a fili za ta dinga tafka

ɓ

arna a gaban idanunsu, ko dan ta baƙanta musu rai ma…

Ya na tafe ya na wannan lissafin hawaye su na zubo masa kamar wani ƙaramin Yaro, ba ya son Anne! Tabbas Azaba ce ita ga rayuwarsa!!!

A haka

ya zagaya wani lungu a bayansu ya zauna a kan wani dandamalin sokaway, yana gama zaman kawai ya rushe da kuka sosai.

……..

Banza Kaka Nura ya yi da Yadikko, kamar wata banza ta na magana.

Kafin ya yi

kwafa ya wuce cikin kitchen kawai ya rarumo itace ya

yo kan ragowar jama’ar da su ka yi gardamar tafiya da masifar gudu kuma wallahi da niyyar sauƙewa duk wanda ya sama ya taho…

Aikuwa rututu haka aka hau gudu har da ihu, cikin hukuncin Ubangiji bai samu kowa ba, dan haka ya mayar da ƙofar gidan ya rufe

ya na haki!

Ba ya so a gane halin da yake ciki!

Ƴ

ar sa aka kora? Kut sai da ya gama tsotse mata duk albarkatun jikinta ta haihu ta tsofe tukunna zai ce ya koreta, daga ƙarshe ya san cewa zai yi ya saketa.

Tabbas Habu ya na wasa da wuta.

Cikin shesh

sheƙar kuka Adda ta ce “ita

ɗ

in da kake goyawa baya yanzun nan ta gama sheganta maka jika a gaban idanun kowa…

Bayan duk

ɗ

inmu nan na san mun san ƙarya ne…yanzu na san ta gama dasa zargi a zuƙatan jama’a, shikenan za a je a yi ta magaana.

Shin me za ka c

e game da hakan shi kuma?”

Kallon Anne Kaka Nura ya yi kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya

ɗ

auke kansa bai ce komai ba ya

mayar a Adda sannan ya ce “sannu mahaukaciya! Dukanta ki

ke so in yi yanzu kenan ko me? Ɗan uwanki ya ja na tabbata koma menen

e ta yi, magana kuma uban kowa ma ya

ɗ

auki abunda ya ke so ya yi a kai, shi ya sani ko kin ta

ɓ

a ganin alamun shakka ko gudun magaana a tare da ni?”

Lumshe idanu Adda ta yi a hankali, a take wasu kalar hawaye su ka shiga zubo mata rututuuuu na tsantsar b

aƙin ciki…ta matse bakinta sosai trying very hard ta hana kanta kuka!

“Ki kiyayeni kar ki ƙara kawo min munafurcin Nuratu ba na son shirme….ko meye ta fa

ɗ

a akwai dalili ko kuma ma dai-dai ne.”

Juyawa kawai itama Afra ta yi ta bar wajen jikinta har ya

na karkarwa tsabar damuwa da

ɓ

acin rai.

….

Tunda Ya Abba ya shiga

ɗ

aki ya ke ta faman safa da marwa.

****“Eh tabbas

ɗ

ana ne! Ni ne na haifesa, amma ba ni da abunda na tsana in gani ko in tuna da akwaishi a doron ƙasa kamar shi!

Ba ni buƙatarsa in kuna

so he’s all yours and dan Allah ku yi controlling nashi within yourselves…kar ya bari

In sake ganin fuskarsa har gaban abada!…”

Yana gama fa

ɗ

in haka ya juya su ka ci gaba da hira shi da Abokinsa ya na dariya sosai kamar bai yi komai ba….****

Murya da mo

ment

ɗ

insu da Daddy (Mai Dala) ya shiga dawo masa tarr a kwanya kamar yanzun ne ya ke gaya masa…..

Wani irin karkarwa jikinsa ya ke yi tsanar mutumin ta na sake shigarsa!!! A hankali ya

ɗ

aga fuskarsa ya na kallon kansa a jikin madubin

ɗ

akin nasa, fuskar

sa sak!sak!! Ta Daddy ce babu kwaskwarima, har ma da yanayinsa…dan ko ba a gaya maka ba in ka kalli Abba ko da a duhun Magriba ne sai ka san cewa Daddy ne Ubansa….

wani irin bugawa zuciyarsa ta ke yi! Dan the fact that ya na kama da mutumin sosai sake tar

watsa masa lissafinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login