Showing 105001 words to 108000 words out of 111233 words

Chapter 36 - Bakar-Tukunya-Compelete

08 Sep 2026

25

alkhairi ne ya kawota gidan ba.

Still har yanzun goge hawayenta Anne ta ke yi, kafin cikin sheshsheƙar kuka da dasashshiyar murya ta ce “ikon Allah kinga wani kwaro ne ya fa

ɗ

a mini cikin idona na gagara fidda shi sai ruwa idon ya ke min…”

Duk dauriyar Afra kasa ci gaba da riƙe kukan da ya taho mata ya ci ƙarfinta ta yi, ba ta san lokacin da ta rushe da kuka ba dan duk abunda zai saka Anne kuka tabbas ba

ɗ

an ƙarami bane ba.

Gashi dama da kunnenta ta ji ana bada haƙuri, shikenan ita kam ta san tata ta ƙare Allah ya sa ba wani sharrin aka ƙulla mata ba…

Ta aiyyana hakan a ranta a lokacin da ta ke rushewa da kukan, sannan ta ce “Anne ki gaya mini ko ma

menene, zan iya handlin

g dan Allah kukan nan da ki ke yi ya na sake gigita ni ne.”

Miƙewa tsaye Anne ta yi, sannan ta wani juyawa Afra baya cikin sauƙe ajiyar zuciya ta ce “ki tashi ki fita, saboda ni ba kuka na ke yi ba, abu ne ya shiga cikin idanuna.”

A hankali Afra ta

zagaya ta tsaya a gabanta ta na hawaye ta ce “Anne dan Allah ki gaya mini ko ma menene” ta ha

ɗ

e hannuwanta guda biyu waje guda alamun roƙo.

Shiruuuu, Anne ta yi ta na kallonta kafin kuma chaan ta koma bakin katifar ta zauna, ta dunkule tafukan hannayen

ta biyu a waje guda ta saka a ha

ɓ

arta sannan ta zuƙo iska ta busar cikin kafe waje guda da idanu ta sauƙe wata ƙaƙƙarfar Ajiyar zuciya kafin ta soma magaana idanunta har yanzu su na kallon waje guda”….

………….

Mama ta na shiga direct

ɓ

angaren Ya Isma’il ta

nufa abunda ba ta saba yi ba dan sam ba ta cika shiga

ɗ

akinsa ba.

Ba ta tarar da kowa ba amma ta tarar da wayarsa a kan gado, ban

ɗ

aki ma ƙofar a bu

ɗ

e ta ke wanda hakan ya shaida mata ba ya

ɓ

angaren nasa ne kwata-kwata kenan amma da wuya in ba ya cikin

gidan tunda ga wayarsa nan.

Dan haka ta juya ta fita direct ta wuce cikin parlourn.

Ta na shiga ta tarar da shi ya na zaune ya na kallo ya na cin indomie, kallo

ɗ

aya tak za ka yi masa ka fahimci gaba

ɗ

aya hankalinsa ba ya a kan indomien har da ma kal

lon da ya ke yi kawai ya na kalla ne ya na zira indomie…..

Ko da ta kalleshi sosai sai ta ga kamar har ya

ɗ

an rame sannan fuskarsa saman hanci da idanunsa sun yi jaa sosai abunka da farar fata.

A take tausayinsa ya lullu

ɓ

eta, ganin ya na shirin cin galab

a a kanta yanzun ma ya sanya ta yi

saurin korar lissafin ta nufe shi gadan-gadan shi bai ma san ta shigo ba.

Da sauri ƙanwarsa wadda fitowarta daga

ɗ

akinta yanzun kenan ta ƙaraso ta kamo hannunta ƙasa-ƙasa ta ce “Mama, ki zo dan Allah.”

Shiruuu ta y

i kamar ba za ta kulata ba idanunta a kan Isma’il

wanda da ikon Allah har yanzu bai ma san ta shigo ba, sai kuma ta ce “tam, mu je”

Daga haka ta juya suka bar wajen.

Su na shiga cikin

ɗ

akin matashiyar budurwar ta mayar da ƙofar ta rufeta sannan ƙasa-ƙ

asa ta ce “ammm Mama dama…”

Sai kuma ta yi shiru ta hau kame-kame.

“Dama me?”

Mama ta fa

ɗ

a a

ɗ

an zafafe, dan duk haƙurin Matar yadda kowa ya burkita mata lissafinta a yau

ɗ

innan ya sanya ta shaƙa sosai ta ke a fusace.

A hankali Matashiyar budurwar

ta ce “na san, its not important kuma duk

ɗ

inmu ba zargin Ya Afra mu ke yi ba, amma ƙishin-ƙishin mu ke ji a bakin wata a Islamiyyarmu wae Samuel ya na da ciwon HIV….”

Sai kuma ta yi shiruuu, kafin ta ce “a asibitin da ƴar ajin namu ta ke aiki aka fara ma

sa test aka tabbatar, a nan ta gani, har rantsuwa ta yi min

ɗ

azu da muka ha

ɗ

u da ita a islamiyya da safe……”

Yadda gaban Mama ya yanke ya fa

ɗ

i ya sanya sai da ta

ɗ

an durƙusa sannan ta dafe ƙirjinta, da sauri Yarinyar ta saki salati sannan ta

ɗ

an ruƙota t

a na mai sakin salati tukunna ta ce “sannu Mama, menene?”

Yanayinta ya na nuna damuwa sosai.

“La ilaha illa anta subhanaka inni kunta minaz zalimin, lahaula wala quwwata illa billah…”

Mama ta ambato, kafin ta

ɗ

ago a hankali ta zubawa ƴar tata idanu ka

mar mai son gane wani abun a kan fuskarta kafin kuma kawai ta juya ta fita bayan ta ce “ba komai, ina zuwa”

Ga shegantaka da ake zargin akwai a gidan, ga shaye-shaye, ga zina ga ga ga….. Anya kuwa in bar Isma’il ya auri Afra ba ta cuci Yaron nan ba kuwa!.

Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsa ba.

Still har yanzun ya na zaune ya na cin indomienshi wadda ya ke jin

ɗ

acinta akan harshensa kamar panadol, kwata-kwata cokali hu

ɗ

u ya yi amma ji ya ke kamar ya yi amanta. Tun safe bai c

i komai ba da kyar yanzun ya samu zazza

ɓ

in da ya yi masa rubdugu tun

ɗ

aga lokacin da ya dawo daga wajen Afra ya

ɗ

an sake shi shine ya shigo ya cewa ƙanwarsa ta dafa masa indomie wadda itanma shigowarta daga makarantar Islamiyya kenan.

“Isma’il!!”

Mama

ta fa

ɗ

a da

ɗ

an ƙarfi dan karo na biyar kenan da ta ambaci sunanshi bai ma san ta na wajen ba.

Numfashi ya shaƙa da

ɗ

an sauri sannan ya

ɗ

ago idanunsa da su ka yi wani kalar jaaa ya zuba mata….

Da mugun maamaki ya ke kallonta dan ƙanwarsa ta ce masa ba t

a gidan, sam bai san yaushe har ta shigo ta tsaya a gabansa ba.

A hankali ya ce “Mama ina wuni…”

Muryarsa ta na karkarwa sosai very low…

Tausayi ya bata sosai dan haka ta koma gefensa ta zauna ba tare da ta yarda sun ha

ɗ

a idanu ba saboda ta gama tsara

wa kanta ba za ta bari tausayinsa da ta ke yi ya cutar da rayuwarsa ba…

Cikin nutsuwa sosai kanta tsaye ba tare da kwana-kwana ba ta ce “ka

ɗ

auki Afra gobe ku je a yi mata gwajin ƙanjamau.”

Bai san lokacin da cokalin hannunsa ya fa

ɗ

i a kan tiles

ɗ

in d

a ke shimfi

ɗ

e a parlourn ba…

A hankali ya ce “Mama wanchan satin mu ka je mu ka yo fa, mai ya faru ki ke so mu sake komawa?

Yanzu ina yi mata maganar nan wallahi gani za ta yi kamar zarginta ne na ke yi….”

Ya ƙarashe maganar kamar mai shirin fashewa d

a kuka

Ƴ

an Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KI

DDIES CLOTHING*

Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*

Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*

ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....

location:Kano

Delivery:NationWide.

kar ku bari a baku labari, sai kun zo

🙏

SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA





0806 402 1951

0903 441 3252

[10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

*36*

A fusace Mama ta ce “ta gani Mana! Sai me?

Ɓ

acin ranta ya fi safety

ɗ

inka ne.”

Salati Isma’il ya

yi kafin ya ce “Mama safety kuma kamar yaaya? Zargin nata ki ke yi kenan?”

Ya yi mata maganar a

ɗ

an

tsorace.

Itama Mama a

ɗ

an tsorace sannan rai a

ɓ

ace ta ce “Isma’il ja’inja ka ke yi da ni? Gardama za ka yi mini

ko me!?

Ka na so mu rabu lafiya da

kai kuwa?…

Gaba

ɗ

aya tashi

ɗ

aya ka sauya, halayenka sun chanja duk a kan soyayya, ko sirrin cikinka ba ka iya riƙewa, komai sai ka gaya mata…”

Girgiza kai ya shiga yi, ya yi

kalar tausayi sosai, Mama ba ta barshi ya yi magana ba ta ce “eh mana, maganar

zamanta a Kaduna da komai da aka yi ae duk kwashewa ka yi ka je ka sanar mata tun kafin Mahaifinka ya ce komai.

Anya kuwa Isma’il!? Tsoronta ka ke ji ne ko yaya?”

A hankali ya lumshe idanunsa hankalinsa chaaa! A tashe, kafin da mugun kyar ya iya bu

ɗ

esu y

a sauƙesu a kanta, tukunna ya ce “ki yi haƙuri, Allah ya huci zuciyarki, zan je in sameta a sake yin sabo sai mu kawo miki in sha Allah..

Batun Kaduna kuma ban ce komai ba Mama, ki yarda da ni”

“A mafarki aka sanar musu hala?”

Wani abu ne ya tokare

masa maƙoshi ganin yadda yau ƙiri-ƙiri Mama ba ta yarda da shi bane, sannan tashi

ɗ

aya ya fahimci daga wajen Anne ta ke kenan fitar da ta yi kuma tabbas Anne ce ta zugota ta ha

ɗ

a komai shiyasanya ya ganta a haka, dan haka takaicin Matar(Anne) a take ya ƙar

asa hassala shi ya na mai ji kamar ya saka mata bomb kowa ma ya huta.

Da kyar ya iya bu

ɗ

e bakinsa ya ce “ki yi haƙuri Mama dan Allah”

Dan ba ya son magana da ja’injar da ta ce ya na yi da ita, shiyasa kawai ya katse batun.

Daga haka ya miƙe sannan ya

ɗ

a

ura da cewa “bara in watsa ruwa daga nan sai in tadda ita, na barki lafiya, ki yi haƙuri dan Allah.”

Kauda kai Mama ta yi, da mugun kyar ta iya ce masa “tam”

Dan a yadda ta ji abubuwa daga Anne dukda Isma’il

ɗ

in ya ce ya amince za a sake yin wani test

ɗ

in sabo kawai sai ta ke ji ko da ace Afra ta fito negative ta na ji kamar still ta dakatar da auren….ba ta so a samu

ɓ

aragurbi a cikin zuriarta sam! Dan ta lura ta fahimci abun nasu jini ya ke bi.

Hankalinsa a masifar tashe ya ƙarasa

ɓ

angarensa ya ne

mi waje ya zauna ya na tunanin ta ina zai fara cewa Afra ta zo su koma a sake yi mata wani gwajin bayan wanda su ka yi aka tabbatar ƙalau duk su biyun su ke, har an ha

ɗ

a ana shirin kaiwa masallaci! After what he did to her da safe da questions

ɗ

insa gareta

ya san ba lalle ta yarda ba sannan ko da ace ta yardan ma dole za ta gane zarginta ne ake yi kuma hakan ba da

ɗ

i….

Sam-sam ba haka Mama ta ke ba!

Anne ce ta zugota ta hautsina komai ko shakka babu, amma in sha Allahu zai yi tackling komai bi’izinillahi

ta’ala babu she

ɗ

an, mutum ko aljan da ya isa ya raba aurensa da Afra…..

Ya aiyyana hakan a cikin ransa zuciyarsa ta na wani kalar tafarfasa…dan sai yanzu ya sake tabbatarwa tabbas akwai gulmace-gulmace a lamarin, tun farkon komai.

………….

“Afra haƙiƙa na

cuceku na zalinceku! Ko da ace ku kun yafe mini ni ba zan ta

ɓ

a yafewa kaina ba, ƙiri-ƙiri ba ki ji ba sannan ba ki gani ba amma gashi yanzu aurenki ya na shirin tarwatsewa duk domin kurakuraina.”

Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanyata yin shiru..

Cikin

share hawaye Afra ta ce “Anne sai yau Allah ya yi za ki gane hakan kenan?! Sai da ki ka gama yiwa rayuwarmu gi

ɓ

i?”

Sai kuma ta yi shiruuu, kafin ta

ɗ

aura da cewa “Amma hakan ma abun farin cikine tabbas dukda dai kin gama goga mana baƙin fentin da ba na ji

n zai ta

ɓ

a goguwa a rayuwarmu har gaban abada”

Sannan cikin sanyin murya ta jeho mata tambayar “me ya kawo Mama yau?”.

Wani sabon kukan Anne ta sake saki sannan ta ce “zuwan nata na yau ya sanya na sake shan jinin jikina…ki yi haƙuri ki yafe mini Afra d

uk ni na jawo miki…”

Cikin rawar murya Afra wadda ta ke ji kamar ta zaƙulo maganar daga cikin bakin Anne ta ce “Anne me ta ce? Mai ya faru?”

Share hawayenta ta yi ta

ɗ

an yi shiruuu sannan ta soma magana cikin jan hanci da muryar kuka… “Shekaran jiya Ma

ma ta kirani, akan wae ta na so ni da ita mu taru mu sanya ‘a dakata da auren…’

Na so in yi mata jainja amma sai ta ce ‘in yi ƙoƙarin ganin na yi controlling Babanku ta yadda ko su Usman

ɗ

in sun kirashi zai ce musu ba yanzu ba, dan ta ji ƙishin-ƙishin ga

me da abunda su ke shiryawa.

In ta samu lokaci za ta zo mu yi magana da ita.’

To dai nima na ga ƙanƙantar lokacin bayan an sanar mini kuma ina so in yi miki kayan

ɗ

aki sannan ga rashin kirkin da su ka soma yi shiyasa na je wajen Malam Ƙasimu akan ya

ɗ

au

re bakunansu ya zamana sai yadda muka yi da su, sannan kar ta hana auren kuma ko bayan auren ina so ya kasance sai yadda ki ka yi da su saboda bana so a ci miki tuwo a ka ko a wulaƙantaki tunda kinga bana kusa Kaduna za su kai ki kuma kinji dai kalar magan

ganu da cin kashin da su ka soma yi a kanmu.

To sai gashi ban kai ga yin abunba ku ka taru aka tozartani aka jefar shi gaba

ɗ

aya…..amma wallahi wallahi Afra iyaka akan abunda ya sa na kar

ɓ

o tsuntsuwarnan kenan aikin ke zan yiwa saboda nima abun ya fara da

muna kar rayuwata ta shiga rayuwarku ta tarwatsa farincikinku, tunda ni dai an gama goga mini baƙin fenti da abunda na yi da wanda ban yi ba da ƙarya da sharri duk an ha

ɗ

a a cikin tarihina ba zan ta

ɓ

a iya gogewa ba…”

Cikin sauƙe numfashi still ta na jan h

anci ta na sharar hawaye, ta ci gaba da cewa “to kuma a yau dai Mama da ta zo ba ta sanar mini taƙameme dalilin da ya sanya ta ke so a dakata

ɗ

in ba kamar yadda ta alƙawaranta cewa za ta gaya mini in mun ha

ɗ

u, kawai dai ta ce kin yi laiifi, wae bayan ganin

ki da aka yi a hotel akwai wani laifin da ki ka sake yi, sannan Isma’il ya zo kin masa rashin kunya

ɗ

azu da safe kenan inaga ta ke nufi, ta nuna tafiya ba za ta yiu a hakan ba, sannan da na ce mata na kuma dage akan ba ki yi komai ba alamu sun nuna ta fusa

ta, dan ƙarshe dai shi ya sanya ta tafi ko cikakkiyar sallama ba mu yi ba, amma ni dai na san akan laifukana ne kawai har yanzu ba ta son auren fakewa ne ta yi take so ta

ɓ

illo da basaja tunda tun farko sun nuna ba komai shiyasa ba ta so su yi fuska biyu,

dan haka abunda na ke so da ke yanzu shine ki je ki amsa laifin da take ta cewa kin yi, kawai ki na zuwa ki ce mata eh kin yi amma kuskure ne kar ki bari ku jaa maganar sannan ki yi mata alƙawarin ba za ki sake ba kinga in kin yi hakan ae kin rufe mata bak

i kenan ko? Saboda ni na riga na san ba wani laifi da ki ka yi, kame-kame ne kawai take yi auren ne ba ta so a yi saboda sharrin da ake yi mini da kuma wasu daga cikin halayena, Mallan ya tabbatar mini ba ta so ba ta ƙaunar auren ne sam-sam! Akwai ma wadda

ta ke so ta bawa shi Isma’il

ɗ

in (ƴar uwarta)”

Cikin tarar numfashinta Afra wadda ta ke ji kamar zuciyarta za ta hantsilo ta fito waje ta ce “Anne har yanzu ba za ki rabu ki daina yarda da boka da Mallan ba kenan! Ba za ki daina

ɗ

abbaka abunda su ke ce

miki ba! Astaghfirullah Mallan Allah ne? Ya isa ya ga ko ya ji abunda ya ke a ba

ɗ

ini ko wanda zai faru a gaba! Yarda da ki ke yi ki ke saka abun a ranki shiyasa kawai Ubangiji ya ke barinki da halinki.

Kuma ae dama na da

ɗ

e ina gaya miki, ko dan mu Anne

ya kamata ace kin rage wasu abubuwan amma kalli a satin aurena aka kama ki da laifin aikata da yunƙurin yin tsafi sannan Anne kalli abunda ki ka aikata a Ya Amir dole a dinga gudunmu.

Sannan na roƙeƙi da girman Allah kar ki sake yin tsafi ko wani asirin s

aboda ni ko ƴan uwana akan a so mu ko wani abun makamancin haka ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login