Showing 39001 words to 42000 words out of 111233 words

Chapter 14 - Bakar-Tukunya-Compelete

08 Sep 2026

36

na ha

ɗ

a idanu da shi, ta kurma uban ihu ta kwanta a wajen ta fara birgima….

Cikin tsananin

ɓ

acin rai Baba Ali wanda bai lura da shigowar Kaka

Nura ba dan shi baya ya bashi, ya ce "Bari ki ji abunda baki sani ba nan

ɗ

in ba gidanku bane ba dan Ubanki!

Da ke da Uban naki baku aka yi kyauta babu ko sisin kwabonku ballanta ki yiwa mutane tunƙaho!!!

Shegiyar Yarinya marar..."

Muryar Kaka Nura

ce ta katsesa ta inda ya ke cewa "Na farko dai ƴata ba shegiya baceba! Abu na biyu kuma marin nan da ka yi mata ba soja kake ba ko harsashi ne Kai billahillazi sai na rama mata…."

Ya fa

ɗ

i hakan ya na mai yin kan mutumin….

Tabbas Kaka Nura ya na da tau

rin rai da tsaurin ido kowa ya shaida hakan amma su kansu ba su ta

ɓ

a tunanin zai iya tunkarar soja ba.

Wani Falanke mai uban tsatsa ya

ɗ

auka ya ƙarasa garesa amma wani cilli da Baba Ali ya yi da shi sai a bakin ƙofa aka tsinci Kaka Nura da shi da falanki

n nasa ya na nishi...da kyar ya iya miƙewa cikin zafin nama ya rarumi falankin ya makawa tsohon nan a hannunsa…..

Da sauri tsohon ya shiga tsakanin Kaka Nura da Baba Ali wanda ya yunƙoro da niyyar halaka shi, haka ƴar tasa itama ta miƙe bayan ta sauƙe

kan Anne daga kan cinyarta...amma duk sai tsohon ya dakatar da su har Yadikko sannan ya ce "duk wanda ya ta

ɓ

a shi sai ya tsine masa, in har sun

ɗ

aukesa uba to duk

ɗ

insu su bar abun haka..."

Ba dan komai ba shi tshohon Anne kawai ya ke jiye mawa duba da y

adda take a gefe duk ta sanƙarre su Zainab zagaye da ita amma idanunta a kansu, kyar!! Sannan a ganinsa tunda har su ke zaune gida

ɗ

aya to akwai fahimta kenan shiyasa ba ya so ya zamto silar tada tarzoma babba da shi...

Dan haka ya za

ɓ

i ya sakawa abun ful

lstop tun kafin ya fi haka.

Sosai ya tsawatar wanda hakan kuwa ba ƙaramin baƙanta ran kowa ya yi ba musamman Abbakar dan shi tun daga wannan ranar ya ji kaff a fa

ɗ

in duniya babu wanda ya tsana sama da Nuratu....ya yi mamakin yadda ta ke magana da manya

haka Yarinyar kamar ƴar ido...dan shi bai ma san ana haka ba, gashi dai dukda kasancewarsa mai training

ɗ

in sojoji kuma ba Yaro ba amma haka nan ya danne zuciyarsa ya kame kansa bai tanka ba ko ya tsoma baki saboda babba na magana kuma ya tabbata hakan ne

ya hana Zainab itama hatta da Mustapha yin magana......Baba Yusufa ya na dawowa bayan an wuce da Anne Asibiti tare da Mustapha da Zainab Abbakar ya

ɗ

auki jakarsa ya juyo ko gidan bai yarda ya shiga ba....dan ya san bai isa korarta a cikin gidanba shi kuw

a ba zai iya shaƙar iska

ɗ

aya da Yarinyar ba wallahi...

To dai suma ragowar jama'ar masu ziyarar duk babu wanda ya kai ga shiga cikin gidan, dan Abbakar bai da

ɗ

e da wucewa motarsu ta dawo daga shan mai dan haka suma su ka bi bayansa ba tare da ko ruwa sun

tsaya sun sha ba duk suka kama hanyar komawa ba shiri gaba

ɗ

ayansu...Baba Ali ya na mai jin kamar ya ha

ɗ

iye zuciya ya mutu tsabar takaici! Musamman in ya kalli hannun tsohon da su ka tsaya a hanya aka yi masa dressing da kuma in ya tuna halin da ya bar ƙa

nwarsa a ciki sai ya ji kamar ya mutu kawai ya huta.

Ace a ta

ɓ

a mutumin da ya ke yiwa kallon Mahaifi amma wai ya gagara yin komai ga wani banzan wawa!

Dan har su ka ƙarasa gida mutumin ya na sake jaddada masa cewa 'ko bayan ransa idan ya ta

ɓ

a Kaka Nura t

o Allah ya Isa bai yafe masa ba!'

Saboda shi dai har ga Allah ba ya so ya zamo silar komai, kuma tausayin Uwani ya ke ji sosai, dan haka ba za ta sha wahala a ta sanadiyyarsa ba sam! Ba zai bari ba...dan ya san in har aka yi case to fa komai a kanta zai

ƙ

are.

BULAMA





0806 402 1951

0903 441 3252

[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*



HUMAIRAH BULAMA

Yota

*16*

Tun daga wannan lokacin yayun Uwani da family friends

ɗ

inta su k

a ha

ɗ

e mata Kai!.

Ko ta aika musu da saƙo babu reply kuma ba sa biye mata, gashi tun a ranar da abun ya faru ta ke kwance a gadon asibiti jininta ya hau amma babu wanda ya damu ya ga jikin nata ma ballantana batun zuwa dubiya.

Har shi yayan nata (Baba Yu

sufa) wanda za a iya cewa zugar mace ya

ɗ

auka a wannan lokacin...dan tun a lokacin bayan su Baba Ali sun tafi Yadikko ta hau sababi ta na cewa "ae gashi ita faccalarta da ya ke Mijinta ya san darajarta shi da ba shi ma da ƴaƴa ya yi gaggawar raba mata envi

ronment da Anne da Kaka Nura amma ita ko sau

ɗ

aya Baba Yusufa bai ta

ɓ

a duba tarbiyyar Addanta (Zainab) ya yi yunƙurin raba mata muhalli da Anne ba,

har ce mata ya ke za ta raba zumunci a duk lokacin da ta hana Yarinyar kula Nuratu."

A take tsanarsu (Nura

da Nuratu) ta sake fitowa ƙarara a kan fuskarta, tun daga ranar kuwa ta yi nasarar janye Mijinta ta juyar masa da akala Allah ka

ɗ

ai ya san me-da-me ta gaya masa dan tun daga nan ya juyawa Uwani baya, duk wata alfarma da ya ke yi musu ma janyewa ya yi hatta



ɓ

angaren nasu ma tun daga wannan lokaci ne aka saka musu ku

ɗ

in haya su ke biyan naira dubu goma duk ƙarshen shekara!.

Haka nan Uwani ta ci gaba da jinya a asibiti ita ka

ɗ

ai!

Dan ko da Nuratu ta je ita da Zainab tare da Mustapha, cikin lumana ta lalla

ɓ

a Nuratun ta ce mata “dan girman Allah kar ta sake zuwa, ta yi zamanta a gida, ta gode”

Gashi ita kanta Zainab satar hanya ta yi su ka je ita da Nuratun da Mustapha...wanda daga ita har Mustaphan Yadikko ba ta san sun je ba, shiyasa aka dawo aka barta ita

ka

ɗ

ai dan ba damar Zainab

ɗ

in ta

ɗ

an zauna mata gashi ta ce Nuratu ta tafi.

A hanya babu kalar nasihar da Zainab bata yi mata ba akan ta chanja Hali ta bi Mahaifiyarta.

Zainab kusan za a ce ƙawarta ce kuma ta san ta na sonta tsakani da Allah dan it

a ka

ɗ

ai ta ke iya tolerating

ɗ

inta, shiyasa ta ke cin sa’a wasu lokutan har ta ke iya yi mata nasiha ta barta ba tare da ta yi mata zazzagar kwanyo ba!.

A wannan lokacin Zainab da Mustapha su na fara yi mata nasihar ita kuma ta

ɗ

auki aniyar gyarawa ba w

ai dan ta yi tunanin bata kyautawa mahaifiyartata ba kamar yadda su ke ta nanata mata sai dan ta nunawa dangin mahaifiyartata itama fa ta Haifa kuma banzatar da itan

ɗ

in da su ka yi ba zai rage ta da komai ba!...

Sannan dama tun ba yau ba ta ke da burin

rabata da munafukan dangin nata,kuma ta san ta hakan ne kawai za ta yi nasara, also ta lura da Yadda Yadikko ta tsani ta ga Mustapha ya na kulata wanda a yanzu ta lura ƙoƙari ya ke yi ya nutsar da ita ta san ta hakan ne kawai zai dinga shishshige mata ita

kuwa wallahi sai ta yi amfani da wannan damar ta raba Yadikko da

ɗ

an na ta wanda ta san ta na mutuwar so kamar ranta......

To dai a iyaka ƴan waennan lokutan Uwani ta samu sauƙin Anne...ramuwa, zagi da tsantsar rashin kunya duk ta daina yi mata su,

ammafa mai Hali ba ya chanjawa, ta na yin hakan ne kawai dan ta cimmma wasu burikanta na daban ba wai dan ta daina forever ba.

Hakanan Uwani ta sha jinya a asibiti ita ka

ɗ

ai wanda za a iya cewa rabonta da Kaka Nura tun ranar da aka tafi kaita asibit

i... domin kuwa a mugun ƙule ya ke da ita...dukda kuwa fa

ɗ

an da akayi shine da nasara amma haushinta ya dinga ji saboda a ganinsa ai da danginta aka yi fa

ɗ

an kuma ya san itace sila! Shiyasa tun a ranar ya ƙullaceta bayan kwana biyu kuma aka yanka musu ku

ɗ

i

n haya mai Unguwa da jama'a su ka shaida aka saka dole

sai sun dinga biya shiyasa haushin Uwani ya sake hauhawa a cikin zuciyarsa!

Sosai ya ƙullaceta a ransa ba ka

ɗ

an ba.

Ya Mustapha ne kawai ya ke zuwa ya na dubota a

ɓ

oye sai ko Zainab wadda itama t

a ke binsa a machine

ɗ

insa su je a

ɓ

oye ba tare da kowa ya sani ba su kai mata abincin da su ka siya a hanya. Nuratu ma ta so ta dinga zuwa amma tunda su ka je sau biyu da ita a na ukun Uwani ta dinga kuka ta na roƙonta ta yi nesa da ita shikenan Zainab (A

dda) da Ya Mustapha su ka ce Annen ta haƙura ta bari Idan Uwani ta dawo gida sai ta nemi gafararta!.

Ba ƙaramin da

ɗ

i Ya Mustapha da Zainab su ka ji ba da su ka ga alamun shiriya a tare da Anne, Ya Mustapha har sadaka ya yi saboda babban burinsa kenan a

wannan lokacin (Anne ta shiryu)

Ita kuwa basu san kawai son ta ƙunsawa dangin Uwani sannan ta rabata da su da kuma son tarwatsa farin cikin Yadikko ne su ka taru su ka sanya ta ke yin hakan ba! Dan baya ga haka ko dede da sau

ɗ

aaya Anne bata ta

ɓ

a jin nad

amar abunda ta yi ta shige ta ba! Kuma wani ikon Allah sam Uwani bata ba ta tausayi ba...

Kawai dai ta tsara za ta shiga jikinta ta rabata da su sannan ta nuna musu abunda su ka yi fa ko a jikinsu! Kansu su ka yiwa, bayan ta tabbatar ta raba Yadikko da

ɗ

a

nta Mustapha along the way na tuban muzurun nata.

Abu kamar wasa har aka shafe wata

ɗ

aya ciff! Uwani bata warke ba jinin nata da ya sauƙa sai ya sake hawa Abu ya ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa…

Gashi ku

ɗ

in magani da na gado wanda ta biya lokacin da aka kaita

har sun ƙare ana neman wasu....

Dan haka da Ya Mustapha ya je ganinta ta ce masa “idan ya koma gida ya cewa Nuratu ta duba ƙasan kayanta(Uwanin) ta na da naira dubu

ɗ

ari biyu a ajjiye ta bashi ya kai mata!”

Ya na dawowa ya shiga

ɓ

angaren su Nuratu,

ya same ta a zaune ita ka

ɗ

ai ta na tunani...

Sai da ya zauna a kusa da ita tukunna ya sanar mata da saƙon Uwani! Sannan ya ƙara da cewa “Nuratu tunanin me kike yi ƴar ƙaramar ki da ke?”

Ya fa

ɗ

i hakan ya na mai kallonta sosai.

Shiruu ta yi dan ba ta

so ko ka

ɗ

an ta dinga tallata laifin Kaka Nura amma kuma ta san dole a yanzu Mustapha ya ji komai….

…..Tun sati biyu da su ka wuce Nuratu ta fahimci Kaka Nura ya yi budurwa duba da yadda kullum ya ke sheƙa wanka ya fita ya dawo gab da Magriba.

Da farko,

bai dai gaya mata ba itama kuma bata tambayesa ba saboda ta na kokwanto akan ‘shin aurar matar da ya ke zuwa wajen nata zai yi kenan ko ƙa-ƙa?! Saboda ita dai ta san ba shi da ku

ɗ

in da zai kama haya dan kullum cikin mita da tsinewa duk wani wanda ya hanasa

bashi ya ke yi a cikin ƴan kwanakin, nan inda su ke zaune kuma ta san Uwani ce ta biya ku

ɗ

in da aka saka musu na haya dukda ba ta nan ita....

A cikin sati

ɗ

ayan da ya gabata kuma ta tabbatar dan throughout satin da ita ake zuwa ma zance wanda lokutan zan

cen nasa ya sauya zuwa 8-10 na

dare sannan a gabanta ya

ɗ

aga ƙasan kayan Uwani ya

ɗ

auki ku

ɗ

in da yanzu ta ke so a bayar Mustapha ya kai mata...

Dubu biyar ya bayar a gidan mai

ɗ

an wake wadda ta ke kawo musu kullum idan ta kwashe na siyarwa tun da Uwani ta

kwanta (dan Yadikko hatta abincin sadakar da Baba Yusufa ya ke sawa a yi duk juma'a ta daina zuba musu) dubu uku ya bayar a wajen mai koko da ƙosai na abun kari! Sannan iyaka zirga-zirgar da su ke yi na zuwa zance ita kanta ta san sun kashe sama da dubu b

iyar, da daddare kuma dama ya shigo mata da su biscuits su chocolate ya ce sai su dinga ci a matsayin abincin dare duk ranar da basu dawo da uban abincin da su ke dawowa da shi a ha

ɗ

a

ɗɗ

un kuloli ba, saboda kusan kullum in sun je zance sai an ha

ɗ

osu da abin

cin dare dan ƙiri-ƙiri Kaka Nura ya ke rantsuwa a gaban ƴarsa cewar ba shi da aure itama kuna ƴar da ya ke munafuka ce ta ce musu eh...kasancewar ba ƴan unguwar ba ne ba ya sanya ba su fahimci gaskiya ba.

Haka za su zo da kulolin su ci, da safe ta wanke i

n za su koma zance su mayar da empty a basu mai nauyi su kar

ɓ

a su taho ba kunya ba tsoro Allah alhalin ko biscuit bai ta

ɓ

a kaiwa ba shi, ya ce ae ta san hidimar aure ce a gabansa.....

To dai a halin da ake ciki har an kammala ha

ɗ

a lefe an kai wanda ta ke

da tabbacin da ragowar ku

ɗ

in Uwani da ya

ɗ

auka duk ya yi hidimar komai.....

“Nuratu! Kin yi shiru, akwai matsala ne? Ko zaman shirun ne ya ke gundurar ki? Adda ba ta shigo miki yau ba?”

Tambayoyin da Ya Mustapha ya zaiyyano mata su ka katse mata tunan

i…

A hankali ya na yi mata wani irin kallon ƙurilla ya ce “talk to me mana! Me kike so?

Ko zaki koma Gidanmu da zama kafin Mamanki ta dawo?

Naga yanzu Baba ya na yawn fita kuma ba ki koma makaranta ba.

Ki na jin tsoro ko?”

Saura ka

ɗ

an murmushi

ya su

ɓ

uce mata saboda da

ɗ

in da ta ji....

A hankali ta jinjina masa Kai alamun ‘eh’.

Wanda ba hakan bane ba dan sam! Anne ba ta da tsoro bama ta san menene tsoron ba amma tabbas kam za ta nuna masa tsoron ta ke ji saboda ya

ɗ

auke ta ya kai ta gidansu(

ɓ

an

garensu) dama hanya ta ke nema ta tsani Yadikko kamar mutuwarta ba ta da burin da ya wuce ta ganta cikin masifa! Shiyasa ta na ji Mustapha ya ambaci kalmar 'tsoro' ta yi caraff ta za

ɓ

i fakewa da hakan domin ta samu damar zuwa gidan nasu ta tarwatsa duk wan

i farin cikin Mahaifiyarsa, dama lokaci da dama ta ke jira kawai amma ta da

ɗ

e da yi wa kanta alƙawarin sai Yadikko ta san ta nuna mata tsana ƙiri-ƙiri!”.

Baya ga hakan ita kam ba wani tsoro da ta ke ji, tunanin ma da ya tarar ta na yi na damuwarta

ɗ

aya

ne (haushin auren da Kaka Nura zai yi) dan ko Uwani ba ta wani tausaya mata ba dan an ta

ɓ

a ku

ɗ

inta ko an mata kishiya ko na jinyar da ta ke yi, wannan duk ba damuwarta bace ba....

Jinjina kai Mustapha ya yi kafin ya ce “Okay! To

ɗ

auko ku

ɗ

in sai ki

ɗ

ebo

har da kayanki mu je in kaiki

ɓ

angaren mu daga nan sai in kaiwa Mama ku

ɗ

in da wur wuri ta na jirana za ta biya ku

ɗ

in gado.”

A take wata idear ta sake fa

ɗ

owa Nuratu cikin son sake dasa mishi tausayinta a cikin zuciyarsa ta fashe da wani kuka tashi

ɗ

aya gw

anin ban tausayi ta ce “Babana aure zai yi kuma ina ga da ku

ɗ

i ya yi am…”

Bata kai ga dasa aya ba su ka fara jiyo gu

ɗ

ar Mata kamar za su tsaga gidan!.

A tare su ka miƙe tsaye ita da Mustapha sakamokon turo ƙofar da aka yi aka shigo Mata su na ta faman

ranga

ɗ

a gu

ɗ

a wanda hakan ya ke nuni da tabbas Amarya aka kawo cikin gidan!.

[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: BAƘAR TUKUNYA…*



HUMAIRAH BULAMA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login