Showing 81001 words to 84000 words out of 111233 words
yanke ni da
ɗ
an u
wansa ya ji ya gani to kuma da ya dawo yau ya na jin kwanakin ya nemi ganinmu…”
Shiruu ya yi kafin ya lumshe idanunsa ya bu
ɗ
e sannan ya ce “duk
ɗ
inmu mun san yawanci jama’a ba sa ƙaunar auren nan, sabili da ana gani kamar an cuci Isma’il ne duba da yadda
tarihin Afra ya ke a Unguwar nan da kuma yadda Mahaifiyarta ta ke!
Kasancewarta Yarinya mai cikar kamala ba shi zai sanya a chanjawa tuwo suna ba duk
ɗ
inmu mun san da haka, gutsiri tsoma da munafunce-munafunce su kan yi tasiri a kan kowa kuma ba a cika so
n yawan magana a kan abu ba!
A duniyar nan bayan ku inaga ba ni da waenda zan ce su ka fiye mini Isma’il da iyayensa dan sun so ni kuma su na kan so na a yadda na ke a lokacin da ya kamata a ce sun guje mini dan shi da kansa mahaifin na sa ya ce saboda g
udun ce-ce-ku-ce ya na so kawai a
ɗ
aura auren wani satin idan Allah ya kaimu(rana ita yau kenan!).”
Da wani kalar azababben sauri Anne ta
ɗ
ago ta kalleshi sai kuma ta mayar da kanta ƙasa kawai ta shiga tsinewa Malaman da ta wuni wajensu yau! Saboda babu k
alar duba da buga ƙasar da ba su yi ba yau
ɗ
innan amma duk cikinsu aka rasa wanda ya hango mata batun matso da aure kwana kusa ballantana ta soma shiri tun
ɗ
azun sai yanzu ne ta ke ji daga bakin Baba.
Muryarsa jin ya ci gaba da Magana ne ya katse mata t
unaninta…
“Dan haka mun tsara a kan nan da sati
ɗ
aya za a yi auren in sha Allahu, Afra za ta wuce Kaduna gidan Amaryar Mahaifinsa wadda ya aura ta rasu, ya ce akwai komai a ciki ba sai mun kaita da ko cokali ba, komai sabbi ne dan wasu ma ba a ta
ɓ
a amfani
da su ba sannan ya ce za ta zauna a chan tunda dama shima Isma’il
ɗ
in a chan Kadunar ne ya samu aikin nasa, har batun gurbin karatu da za a nema mata a chan duk mun yi da su kuma za ta soma da zarar an
ɗ
aura sun tare in sha Allahu….”
Cikin sauƙe ajiyar z
uciya Baba ya ce “dan Allah duk wanda ya yi sallah ina neman alfarmar da ya dinga saka mini mutanen nan a cikin addu’a yana neman musu yardar Ubangiji, tunda aka haifoku cikin wannan zuri’a tawa a kullum tsorona waye zai aureku!
Amma da ya ke Ubangiji ne
me komai gashi zan fara ganin auren Afra waenda mutanen nan su ka zamto silar komai na auren bayan doguwar
ɗ
awainiya da mu da du ka dinga yi, kuma in sha Allahu yadda aka aminta da ita har ake kwa
ɗ
ayi da son aurenta haka Aliya da Zainab(Amal) suma duk za s
u samu mazaje masu nagarta waenda za su kar
ɓ
esu hannu bibbiyu ba tare da sun dubi halin mahaifiyarsu ba”
“Babana”
ya yi maganar referring to Ya Amir sannan ya ce “kai ma in sha Allahu za ka samu mata mai nagarta da kamala bi’izinillahi ta’ala…”
Murmushi
Ya Amir ya yi sannan a hankali ya sunkuyar da kanshi ƙasa a ransa ya amsa da “Ameen”
A hankali Afra itama ta sake yin ƙasa da kanta, ta san ta na son Ya Isma’il kuma aurensa shine burinta amma haka nan a take sai ta ji fargaba da tsoro duk sun mamayeta s
annan wae ba ma a Kano za ta zauna ba a Kaduna ne, tabbas ita kanta ta san za ta yi kewar danginta….
“Sallu Alan Nabiyyil Karim”
Baba ya sake cewa, a tare duk su ka ce “sallallahu Alaihiwasallam….”
Wani kalar tashin hankali da masifa Anne ta ke ciki
, ga baƙin cikin batun aure ga shi ba a nemi yardarta ko
ɗ
aya ba sannan ga bala’in takaici da mamakin yadda yau Baba ya gaggasa mata magana a gaban idanunta ba shayi….
Ganin ya na shirin miƙewa ya sanya rai a
ɓ
ace ta ce “Dakata Habu!”
Shiruuuu kowa ya
yi, yayinda Baba ya runtse idanunsa kamar ba zai kulata ba sai kuma ya koma ya zauna da kyau ya na mai sauƙe ajiyar zuciya sannan ya ce “ki na da magana ne Anne?”
Da sauri Ya Amir ya miƙe zai fita dan ya san in ba a yi sa’a ba Anne sai ta saka shi kuka
a maganganun da ya ke da tabbacin za ta gaggayawa Baba……
Cikin daka masa tsawa Anne ta ce
“Koma ka zauna!!!Munafuki! Ɗan iska kawai ai har da kai aka ha
ɗ
a komai saboda kun maida ni banza ko?”
Sai kuma ta maida dubanta ga Baba sannan ta ce “yanzu kai
ba ka ji kunyar yadda ka saka ranar ƴar da na haifa a cikina ba sannan ka
ɓ
oye mini kuma har ka ke da tsaurin idon wani ce mini ka san wasu a cikinku sun sani wasu kuma basu sani ba, sannan kai har ka isa ka saka ranar ƴata cikin sati
ɗ
aya tak!! Sannan ka
gaya mini yanzu ba tare da neman shawarata ba, ƴar tawa ƴar tsana ce???”
Kamar Ya Amir ba zai ce komai ba sai kuma ya kalleta idanunsa jazir ya ce “Anne saboda munafurce-munafurce da Bakin mutane kar ya yiwa maganar auren illa shiyasa aka ce a
ɗ
aura da
wuri kawai tun kafin batun auren ya zagaya koina…”
“Akan me ake munafurce-munafurcen??”
Anne ta tambayeshi ta na huci!
“Wai shin ni kam na ta
ɓ
a yin zina a bakin ƙofa ne ko kuwa na ta
ɓ
a cin mutum sannan tsirara aka ga ina yawo! Da har shi Usman(Mahai
fin Isma’il)
ɗ
in dan *******uwarsa zai dinga magana ya na nunawa kamar alfarmar zai yiwa Afra shin bai ga ƴar tawa bane ba?!
Ai sai dai mu mu yi masa alfarma wallahi, ke tashi su ganki da kyau ki kwa
ɓ
e hijabin su ganki su san mu ne za mu yi musu alfarma…”
Ta fa
ɗ
i hakan ta na kallon Afra sannan ta
ɗ
aura da cewa “ku kuma da yake ga
ɓ
ayene, wawaye shine ku ka biye masa aka tafi a haka…”
Cikin daka mata tsawa Baba ya ce “Nuratu!”
Kafin ya rufe Bakinsa itama ta ce “Na’am Abbakar!!”
Da gudu Amal ta tashi ta
fice ta na kuka sosai ta fa
ɗ
a
ɗ
akinsu dan ba za ta iya zama ta juri kallon fa
ɗ
an iyayen nata har haka ba.
Tsaki kawai Anne ta yi bayan ta gama hararar inda Amal
ɗ
in ta bi ta fice sannan ta waigo zuwa ga Baba ta ce “abu uku na ke so ka saka a ranka, na
farko yadda ku ka tsara nima dole a bi nawa tsarin kuma ba zan aurar da ƴata kamar wata ƴar tsana ba wallahi, dole in yi taro dole in yi biki dole in yiwa ƴata kayan
ɗ
aki in ya so along the way duk wanda zai saka Baki ko ya yi munafurci shi ya sani in ka g
a Isma’il bai auri Afra ba tabbas ba Matarsa bace ba dama tun farko, abu na biyu kuma ko dan yadda ku ke kallona Allah sai an ja bikin nan saboda in nuna muku cewa baƙin fentin da ku ka yi mini bai hau ba, sannan abu na uku kar ka ƙara zama a gaban idanuna
da ƴaƴana ka na ci mini fuska kamar ka samu mayya har ka na cewa wani wai saboda ni za a fasa aure Uban baban duk wanda ya bari aka yi dan Allah….”
Ta ƙarashe maganar ta na huci sosai, ranta na susa, wato Kaduna ma za a
ɗ
auki ƴar tata a kai ta yadda kafi
n ta bata wani abun alkhairin ma sai an jima, yo ko da ace isma’il
ɗ
in ya zamto choice
ɗ
inta ace ku
ɗ
insa ya yi ku
ɗ
in da za ta iya bashi Afra sam bai isa ya
ɗ
auketa ya yi nesa da ita ba, ba ta haifi ƴaƴanta domin haka ba…
Shiruu Baba ya yi tun fitar Am
al dan sai ya ji bai kyauta ba ya gama yiwa kanshi alƙawarin ba zai dinga biye mata ba, musamman ma in a gaban ƴaƴansu ne….
Da kyar da mugun kyar ya samu ya iya cewa “Afra ke da Amal ku gayawa Adda yadda mu ka yi da ku a nan.
In akwai wasu shirye-shiry
en da za ku yi sai ku yi mini magaana…..”
Daga haka ya miƙe ya fice da sauri Ya Amir shima ya bi bayansa…
“Tashin balagar tsintsaye ma kena!!!!
Idan ita Addar ko Uwarta wani cikinsu ya haifa mini ƴar sai in ga hannunsu a cikin auren da ban aminta da dat
e
ɗ
insa ba dan Uban Mutum”
Anne ta fa
ɗ
i hakan ta na mai ji kamar ta zunduma Uban ihu dan baƙin takaici, shi dai Baba bai biyeta ba haka shima Ya Amir su ka saka kai su ka fice daga cikin gidan ma gaba
ɗ
aya dan sai ta yi barci tukunna za su iya shigowa yau
kam, ko a inda su ka san za ta gansu ba su tashi zama ba dan ka
ɗ
an daga aikin Anne ta bisu har majalisar ko shagon da Baban ya ke a yi ta ka-ce-na-ce da ita.
Ife-ife ta ke yi sosai kamar za ta ha
ɗ
iye harshenta.
Ganin sun fita sun barta su na shirin s
aka mata hawan jini ya sanya ta miƙe tsaye za ta bi su kamar yadda su ka zata.
Da sauri Afra ma ta miƙe dama a bakin ƙofa ta ke dan haka sai ya zamana kamar ta tare mata hanya ne.
Sai da hasken kendir
ɗ
in ya haske fuskar Yarinyar tukunna Anne ta fahim
ci kuka ne ta ke yi sosai dan idanunta har sun sauya, cikin kukan Afra ta shiga cewa “Anne ya kamar ki na baƙin ciki da farin ciki na ne, Anne da gaske tarwatsa aurena da Ya Isma’il ki ke son yi?…”
Shiruu Anne ta yi kafin ta runtse idanunta da masifar ƙar
fi a ranta ta na tsinewa Baba tun daga kan kakannin kakanninsa har shi!
Domin kuwa shi ne ya tunzurata ya sa ta yi behaving hakan a gaban Afra, bata so Yarinyar ta tsaneta fiye da yadda ta san ta tsaneta dan in hakan ta faru ba lalle ta ji ƙanta ta kula d
a ita ba wanda jin ƙan nata shine main goal
ɗ
in komai da ta ke yi yanzun, duk wani plan nata akan Yaran su auri mai ku
ɗ
i da fa
ɗ
i tashin da ta ke yi duk sabili da su ji ƙanta ne….
Dai-dai nan Kaka Nura ya
ɗ
aga labulen ya shigo!
Jin Afra na kuka ya sa y
a ƙarasa shigowa ciki da sauri kamar ba
ɗ
akin surikinsa ba ya
ɗ
an waigo da ita ya na kallonta sosai kafin ya kalli Anne ya ce “Mai ki ka yi mata? Shigowata kenan tun daga waje na ke jin hayaniya sannan na ga su Habu sun fita da wuri”
Sai kuma ya yi shiruu
ya na kallon fuskar Annen itama sosai kafin ya ce “me su ka yi muku dan ubansu?”
Share hawayen takaicin da su ka zubo mata babu shiri! Anne ta yi, sannan ta shiga zaiyyano masa komai, tun daga saka ranar Afra da aka yi a
ɓ
oye(wanda already ta gaya masa
bayan ta sani shima a
ɓ
oye) har kawo yanzu da Baba ya dage sai an yi auren ta na kaiwa nan ta fashe da kuka sannan ta durƙushe a wajen kawai duk dan Afra ta tausaya mata….ta na cewa “saboda ban isa ba saboda ban kai ba in haifi Yarinyar amma a nuna mini i
sa da mallaka….”
Numfashi Kaka Nura ya jaa ya sauƙe sannan ya kamo kafa
ɗ
un Afra ya juyo da ita saitin shi tukunna ya soma magana
“Kinga in har ki na da hankali tou kalmar ba a chanjawa tuwo suna da suka yi amfani da ita su da su ke manya ya kamata ace ke
ma ƙarama kin
ɗ
auka kin yi amfani da ita, kin ga wannan..”
Ya yi maganar ya na nuna mata Anne sannan ya
ɗ
aura da cewa “ba ki ta tamkarta ko da a bola ta ke yawo ita
ɗ
in ce dai ta haifeki ba za ki ta
ɓ
a sauya ta ba, in har ki ka yarda ki ka bari su ka raina
miki ita to wallahi kin shiga ukunki, dan ba ki isa ki chanjawa tuwo suna ba haka maganar ta ke, sannan kalli ki ga tun yanzu sun fara yi miki gori tou na tabbata in ki ka bari aka kai ki gidansa babu kayan
ɗ
aki a yadda su ka iya gorin nan su na gani kama
r sun yi miki alfarma tabbas nan ma wahala za ki sha a hannunsu, kuma above all ma ta ya za ku yi amfani da kayan matar da ba ta raye, ke ba ki da tsoro ne? Ki bari in shi Habu ya ce ba zai yi miki ba, da ni da Annenki mun yi miki alƙawarin za mu yi miki k
inji ko?
Ki tashi ki tsayawa kanki tun yanzu ki san darajarki ki nuna musu ki na da daraja, kar ki yarda wani wai dan a na tausaya miki a yi rushing aurenki in ki ka bari aka tafi a haka har abada gani za su yi kamar alfarma su ka yi miki, ki kwantar da h
ankalinki in kinga ba ki auri Isma’il ba to ba Mijinki bane ba, ina guje miki shiga gidan miji babu daraja Afra sam kar ki yarda da hakan kin ji ko? Kar ki yarda a ci miki fuska!
Ba wai auren ne ba ma so ba a’a rainin wayon da su ka zo da shi ne ba ma so
sam-sam dan Allah kema kar ki yarda da shi, a bi komai a hankali a kwatar miki hakƙinki da darajarki in Mijinki ne za ki aureshi amma in ba Mijinki bane ba yadda su ka soma wulaƙancin nan za su iya ƙasƙantar da ke kuma still su hana auren tunda har su na g
ani kamar alfarma za su yi miki, sannan Annenki mace ce fa kawai da ta ke frank haka Allah ya yi ta ba wai muguwar banzar shaidar da su ke shirin ƙaƙaba mata ku ku ke son kar
ɓ
a hannu bibbiyu ba, akwai Matan da su ka fi ta fitina ma kuma an auri ƴaƴansu was
u ma karuwai ne amma surukansu su na darajasu da girmamasu dan haka kar ki yarda a
ɓ
ata miki sunan Mahaifiya a
ɓ
ata miki tarihinki sannan a raina miki ita, shawara ce kyauta na baki ki yi tunani a kai….ki taimaka ki takawa isma’il burki tun yanzu dan in an
tafi a haka ba za ki ji da
ɗ
i ba gashi da
ɗ
in da
ɗ
awa shine komai naki tun ki na Yarinya dan haka in ya fara goranta miki za ki sha wahala, shi aure daga
ɗ
okin amarci ya fita halin kowa ya ke fitowa…
Kayan
ɗ
aki na yi alƙawari zan yi, ni da Annenki kin san d
ai in na ce zan yi abu to zan yi ko? Dan haka ki nutsu kuma ki yi tunani na san ki na da hankali da zurfin tunani, sai ki yi abunda ya dace…..”
Ga mamakin Anne sai ta ga Afra ta hau
ɗ
agawa Kaka Nura kai a hankali kafin ta ce “tam”
Murmushi ya yi ya shafa
kanta tukunna ya ce shikenan ki je abinki sai da safe ko? Allah ya yi miki albarka….
Jikinta a matuƙar sanyaye dan ba ma ta san ta ina za ta yi tunani ba sun soma birkitata, haka nan ta juya ta fita kamar wadda kwai ya fashemawa a ciki….
Sai da Anne t
a tabbata Afra ta shige ciki tukunna ta ce “ka na ganin maganganun nan sun yi aiki?”
Murmushi Kaka Nura ya saki kafin ya ce “ae shi Yaro duk wayonsa in ka
ɗ
auresa ta koina dole za su bi ta inda ka ke so ne, ki jira ki ga ikon Allah ko duk ba su shiga kant
a ba dole wani ya shiga.
Ki kwantar da hankalinki na san wacece Afra ba ta so a ta
ɓ
a mata darajarta da na ahalinta, ae Habu da shi kanshi Usman
ɗ
in sun yi laifi dan kamar sun bada ƙofa ne…
Yanzun nan fa da Samuel mu ka rabu, jari ya ke shirin bata mil
iyoyin ku
ɗ
a
ɗ
e! A haka su ke so su aurar da ita a Isma’il dan hauka da rashin sanin ciwon kai, hmm Ana nuna musu Annabi su na runtse ido, Allah wadaran naka ya lalace…”
Cikin sauƙe wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Anne ta ce “Ameen”
Sannan ta ce “amma ka na g
a ko ita Afra ta birkice za su yarda a
ɗ
aga bikin nan kuwa anya..”
Dariya Kaka Nura ya yi sannan ya ce “Bari ta birkicema Isma’il
ɗ
in ki ga ikon Allah, ae su kansu akwai shakku a kansu dama trigger kawai yakamata mu nema kuma gashi mun samu damar dasa ta
cikin sauƙi, ke kuma daga nan sai ki san abun yi kafin wani ikon Allahn ya sa a daidaita tsakani.”