Showing 12001 words to 15000 words out of 111233 words
48 hours!”
Sannan ya d’auke dubansa daga kanta ya fara kallonsu one by one yana nuna su tukunna ya d’aura da cewa
“Duk wanda na sake jin
bakinsa kuma wallahi sai an kai shi wajen horo, ya yi 48hours d’in a chan.
Babu waya ko taimako a cikin punishiment d’inku dan haka kar ku b’ata mini rai…”
Daga haka ya juya ya wuce ya bar wajen.
Matar d’azu da ta ke ta jin tausayin Aliyar ce yanzu m
a su ka zo tare da mutumin, dan haka kafin ta wuce a hankali ta d’an durk’usa kamar za ta gyara takalminta cikin dabara ta garo mata wayarta cikin gurin…
Sai da su ka bari sun yi nisa tukunna su ka taso kamar mayunwatan zakuna sun ga nama..haka su ka ra
rumi wayar!
Anne har da y’ar dariyarta…
Sai da su ka danna kiransa wajen sau biyar tukunna Saminu ya d’auka a na k’arshen ta na gab da tsinkewa…
Kasancewar wayar matar ba a ji sai a speaker ya sanya tunda su ka fahimci hakan su ka barta a speaker.
“Assalam alaikom”
Muryar Saminu (Yaron Mai Nasara) ta katse musu addu’o’in da su ke ta jerowa akan Allah ya bashi ikon d’auka a samu ya kawo musu d’ouki…
Aliya kuwa addu’a ta ke yi Allah ya sa ya d’auka d’in in sha Allahu ita kuma ko an zo fita ba za ta
tab’a bari a fita da Amal ba ce masa za ta yi ya barta a cell d’in ita kad’ai duk a watse a barta…Allah ma ya sa abun cikin ramin chan ya kasance mai matuk’ar muni apart from kunamomin da ta ke da tabbacin akwaisu duhu kawai su ke jira su fito… ta yadda za
i fito ya kasheta har lahira kowa ma ya huta…
A hankali ta cewa Saminu “Saminu ni ce, Alhaji ya na kusa?”
Cikin d’an fad’a-fad’a Saminun ya ce “ke ce wa?”
Da sauri ta ce “Aliya, na haihu ne..to jaririn ya koma..”
Jin ya yi shiruu ya sanya ta ce “Al
iya mana Saminu…matar Mai Nasara..Ina so in yi magana da shi, ta gaggawa”
“Aliya Aliya Aliyaaa”
Saminun ya ambata kamar mai son tuno wani abun…
A hankali
ta ce “Aliya ta Mariri”
Cikin fahimta ya ce “Owkay mai cikin nan ko?“
Cikin sauk’e Ajiyar zuc
iya Aliya ta ce “eh, ni” da sauri, sai kuma ta d’aura da cewa “Ina so zan yi magana da shi dan Allah…”
Ashe ma su na tare dan k’asa-k’asa sosai ta ji ya ce “ranka ya dad’e Aliya za ta yi magana da kai, tshohuwar matarka…”
Kamar yadda Saminun ya yi da
farko haka shima Mai Nasara ya yi sai dai shi d’in da ikon Allah ya gagara tunowa da ita sam, sabida cikin ikon Allah matan da ya aura masu suna Aliya su na da yawa gashi dai sunan unique ne amma shi Allah ya had’ashi da su sau dayawa.
Ganin Saminun ya
na shirin saka masa ciwon kai ne ya sanya duk su na ji kawai ya rufesa da fad’a!
Ko bari Saminun ya yi masa cikakken bayanin da zai gane ta bai yi ba hakanan ya rufesa ruff da fad’a kamar mai shirin dukansa, dan shi a k’a’idarsa in ya bar mace to ya bart
a kenan har gaban abada, kuma Saminun ya sani amma ji bi dan iya shege ya na yi masa maganar wata wai ita Aliya.
Cikin tsantsar ladabi bayan Mai Nasara ya dire aya yana haki su ka ji Saminu ya ce “ranka ya dad’e ji na yi ta ce ta haihu ne kuma ta na buk
’atar taimakon ka cikin gaggawa…”
A hankali Aliya wadda jikinta ya yi mugun sanyi ta tari nunfashin Saminun ta hanyar cewa “Yaron ya koma kuma an k’i bari mu binne shi Ina cell yanzu haka har ya fara kumbura…
Sakamokon wajen akwai masifar zafi mu kanmu
da kyar mu ke iya zuk’ar iska, ga numfashi ya yi yawa a d’an k’aramin d’akin da su ka gwamutsa mu…”
“Subahanallah” Saminu ya ce sannan ya shiga sanarwa Mai Nasara abunda Aliyar ta gama zaiyyane masa yanzun…..
Amma ga mamakinsu sai su ka ji a fusace Ma
i Nasara ya ce “ka ci kutumar ubanka Saminu!”
Sai kuma ya warce wayar daga hannunsa sannan ya ce “Ke! Naira miliyan nawa aka baki bayan na sake ki? Meye naki na bibiyar rayuwata ko wani sabon raini ne ya b’ullo muku?
Kin kashe kud’ad’en shine za ki sake
dawo min sabida ga ATM machine nan kin samu ko?”
Cikin sharar hawaye zuciyarta ta na wani kalar k’una ta ce “na haihu d’anka ya rasu, muna cell da gawar har ta fara kumbura, ka zo in ni ba za ka fitar da ni ba shi ka karb’esa a yi masa sutura a binne s
a dan Allah kar ya rub’e…”
Ta k’arashe maganar ta na fashewa da kuka”
Cikin tsantsar rashin imani ya ce “dan uban ki a kan gawa ki ka kirani?”
Zabura ta yi jikinta ya hau karkarwa dan duk rashin imaninsa ba ta tab’a tunanin zai yi hakan ba, haka sum
a mutanen wajen dan haka kowa sai ya yi tsit! Ya sha jinin jikinsa suna masu ci gaba da sauraronsa ya na cewa “Allah ya ji k’ansa ya sa mai ceto ne, duk sanda Allah ya sa ki ka fito ki binne abinki, ba zai yiu ki je ki tafka laifi ki saka ni yawon cell a
banza da mutuncina ba…..wallahi wallahi in ki
ka k’ara kirana sai na tarwatsa ahalinki!
Da ace ma Yaron ya na raye ne to da sai ki kira ki fad’a in so ki ke a karb’a in karb’i abina amma kar ki sake d’agamin hankali a kan abunda ya riga ya shud’e na san
kin san ba na son waiwaye…”
Daga haka ya kashe wayar ko sake sauraronta ta na cewa “yanzu ya rub’e kenan?”
Bai yi ba.
Shiruuu haka kowa ya kasance, tausayin ta ya cike zuciyar kowa a wajen sannan a take duk d’insu su ka fidda ran samun taimako daga
garesa.
Anne kuwa gazawar Aliyar ta gani da Mijinta bai iya cetonsu ba gashi d’ansa ya na shirin fara azabtar da su da wari…ba bu wanda ya iya cewa komai kamar an yi ruwa an d’auke haka cell d’in ya kasance sai sheshshek’ar kukan Aliya da ya ke tashi….d
uk kalar zazzafan rashin adalci da muguwar muguntar da ta tafkawa Amal d’in da kuma mugun aikin da su ka tafka wanda zai zama silar yankewar duk wani sauran farin cikin su…
A take sai ta ji tausayinta ya lullub’eta, abunka da zuciya mai kyau.
Da sauri ku
ma sai ta kawar da kanta ta shiga k’ok’arin korar tausayin Aliyar da ya ke shirin dirar mata….
Cikin inda-inda da kyar Anne wadda itama duk jikinta ya yi sanyi ta ce “duk laifin shegiyar nan Sajida ne…za ta ci ubanta kuwa za ta san ta yi da ni! Wallahi
sai ta yi yawon bara, hmmm, ba ta san wacece Anne ba!
Duk ita ce ta janyo miki halin nan da ki ke ciki har ma da mu kanmu…”
Cikin tarar numfashinta Aliya ta d’ago jajayen idanuwanta ta kalli
Annen sosai sannan ta ce
“Itace ta tilasta mini auren Mai
Nasara shima?”
Inda-inda Anne ta fara, ba ta samu amsar da za ta bawa Aliyar ba ta d’aura da cewa “Anne kin cuceni, sarai da ni da ke duk mun san waye mutumin nan amma haka nan ki
ka bad’awa idanunki toka ki
ka jefani cikin bala’i….”
Mugun kukan d
a ya ci k’arfinta ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana yayinda takardar scholarship d’inta da ta samu a uk ta shiga yi mata gizo, da tuni yanzu haka ta na chan….da tuni ba ta tarwatsa rayuwarta ba…
Cikin b’acin ran da har ya kai ga baiyyana a kan fuska
rta
Annen ta ce “na cuceki ko dae Mai Nasara ya cuceki?
A mugun fusace Aliya ta ce “ae da ban auresa ba da ba zai iya cutar da ni ba!
Kin lalata mini dream d’ina Anne kin tarwatsa mini rayuwata gaba d’aya duk wani Abu na jin dad’i Anne kin janyo mini
na yi hannun riga da shi….
Ki daina cewa Sajida ko Mai Nasara, dan wallahi duk wani halin da mu ke ciki a da da yanzu da har abada wallahi ko wanne duk ke ce sila.
Mai ya sa ki ke da son kanki ne?
Mai ya sa ki ke so ki lank’ayawa mutum sannan ki tabbat
ar da mugun halin a idanun kowa muddin ki ka ji ba kya son shi ko bai yi miki yadda ki ke so ba?
In kud’i ne ae Afra ya kamata ki fara tunkara ba Sajida ba,
Mai ya sa ki ke da son kai ne kuma ba kya son gaskiya? Mai ya sa duk b’arnar da ki
ka tafka in
ta dawo miki sai ki ce wani ne sila? Shin sai yaushe za ki gane gaskiya ne Anne? Halinda nake ciki bai isheki ishara ba?
Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin mutum irinki ba!
Duk son zuciyar ko wacce kalar uwa muddin ta ga abu zai tab’a sannan ya gurb’
ata rayuwar y’ay’anta ta kan sarara amma banda ke Anne!
Ba ki damu mu yi kuka ke ki yi dariya ba! Duk wani kalar Hali marar kyau akwai shi gareki Anne babu wanda ba ki kware a kansa ba!”
Cikin tarar numfashinta Yadikko wadda tunda Anne ta bi ta kanta d
uk wani gigin Maye da zafin cizon kunama suka barta, ta ce “Aliya….”
Cikin kuka ta ce “barni in fad’a mata na ga kamar har yanzun ba ta san wacece ita ba wata k’ila in na fad’a mata ta sani ta shiryu….
Kalli yadda ki ka lalata komai ki ka tarwatsa kowa
duk cikinmu babu wanda ya ke farin ciki..
Hatta ita kanta Afran ae kin san ba wanda ya ke sonta ta aura ba dan haka dole akwai k’alubale a gabanta na sani..”
Cikin tsawa Aanne ta ce “in ji uban waye ne ba ya sonta?”
Ta yi maganar ta na mai satar kall
on Amal, wadda ita kam ta zazzab’in da ya tusota a gaba ma ta ke..
Ya Amir shima ko
kallonsu bai yi ba dan ba ya son jin muryar Aliya, yayinda Baba Adda da Ya Abba kowa ya yi
d’iff dan su kam ba su da ta cewa…..
BULAMA
✍
️
080
6 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*06*
Masu buƙata daga farko su shiga channel
ɗ
inmu.
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T
Wani
mutum ne a cikin mazan wajen ya ce “dan Allah dan Annabi ku barmu mu ji da abunda ya ke damun mu!
Haba mana dan Allah.
Wallahi-wallahi duk wadda ta k’ara yi mana hayaniya a cikinku sai ta daku!
Ku nutsu ku daina ife-ife ko ma samu su ji k’anmu su bud’e
mu kar ku yi abunda za a barmu a nan da wannan Gawar wari ya kashemu…”
Ya k’arashe maganar ya na huci, yana mai jin haushin Anne sosai da tsanarta, gaskiya y’arta ta fad’a dan ko y’an Unguwa dama tuntuni Anne ta addabesu, kwata-kwata matar ba ta da Hali
mai kyau ko guda d’aya.
Ta yunk’uro kenan za ta yi magana kowa ya yi d’iff sakamokon engine mai shayi da su ka ji an kashe wanda ya yi dai-dai da d’aukewar hasken wajen, d’iff!! Haka nan ko Ina ya kasance babu alamun Haske ko k’ak’a.
“Innalillahi wa
inna ilaihirrajiun”Anne ta furta a hankali jikinta ya na wani kalar karkarwa dan ta san wahala kam da azabtuwa sai ta sha ta a wannan k’arnin that’s if an zo an fiddasu basu kai ga mutuwa ba kenan!.
Sai yanzu da Aliya ta ambato Afra tukunna ta tuna
Afran fa za ta iya kawo musu d’ouki tabbas..to amma kuma ta san dole Afran ta sako Asad wanda ta samu ta kad’a su shi da Afran da kyar su ka yi nisa…
Ba ta son ya had’u da Amal ko kad’an dan haka ta kawar da lissafin sako Afra a cikin jerin waenda za su t
aimaketa ta fad’a duniyar neman taimakon wasu…
Ta na cikin nazarin ta ji Ya Amir ya ce “ba ni wayar in gwada kiran Afra”
“Ungo” d’in da Aliya ta ce ta na mai mik’a masa wayar da kunna hasken fuskar wayar ne ya sanya Anne ta zabura..har an mik’a masa ya m
ik’o hannu ta saka nata hannun ta buge nasa sannan ta warce wayar daga hannun Aliya ta na mai zabga masa wata uwar harara, wadda hasken wayar da aka kunna ya taimaka masa wajen ganinta…
Da sauri kusan mutum uku su ka ce “fara bar mana haske tukunna.”
dan
haka ta kunna flash d’in wayar har yanzun idanunta su na a kan Amir wanda ya d’auke kai daga dubanta.
‘In ta ga ba sarki sai Allah za ta kirata kam dan duk yadda ta kai ga son Afran ta yi farin ciki bai kai nata farin cikin da ranta ba, but for now ba za
ta yi garajen bawa Amal abunda ta san ta fi buk’ata ba wallahi…’
Anne ta aiyyana hakan a cikin ranta ta na mai sake yiwa Ya Amir sign d’in ‘kar ka kuskura’
da ido.
Wannan mutumin dae da ya ke ta jin haushinta ne ya ce mata “ki bashi ya kirata mana!”
Sai kuma ta ga duk sun tsura mata idanu.
Dan haka cikin kame-kame ta ce “bara in gwada kiran da kai na..”
Daga haka ta hau daddanna wasu nambobi da ta san ba za su yi ba, sannan ta danna call.
Jin ta yi wani irin sound ya sanya ta yi sauri ta sauk’e ta
kashe ta ce “a kashe ne duk yadda a ka yi, ba zai je ba…”daga haka ta ajjiye wayar su ka ci gaba da zama…..
Har sun d’an samu sauk’in hasken da su ka samu kawai sai ga matar ta dawo ta ce su bata in sun gama…ba ta iya tsayawa ta ji feedback d’in yadda su
ka yi da mutanen da su ka kikkira ba ta yi gaba dan a tsorace ma su ka ganta kamar an kama ta ne.
Tsayuwa gajiya da kuma wahala ne su ka sanya wasu maza a cikinsu su biyu su ka shiga shek’a uban amai mai masifar k’arni ga yawa wanda hakan ya sake tada
hankalin Anne da kowa ma na wajen kwarai da gaske dan babu yadda su ka iya haka nan su ka ci gaba da zama da tsayuwa a cikin aman
nan wanda tun a yi na farko ya cika d’akin ya wanzu a koina saboda ba wani girma ne da d’akin ba…sai kuma chaan su ka ji ya d
’an fara raguwa ya na tsotsewa alamun ya na gangarawa ne cikin wannan rami inda kunamaa ta fito d’azu….
A take tashin hankalinsu ya sake hauhauwa dan basu san me ke tafe ba, gashi sun dad’e da daina ganin hatta tafukan hannayensu, d’id’iff su ke gani kawa
i tsabar uban duhun wajen…
Kayayyakin jikinsu mazan su ka yanke shawarar kwakkwab’ewa…dan haka su ka cire rigunansu su ka danna a ramin aka samu ya rufu tsaf!
Tsoro ya na sake game su sakamokon wani kalar sound da su ke ji ya na fitowa ta ramin kamar mot
sin kwari
kamar kuma hissing na maciji.
Kowa ba energy, barcin ma ya k’aura..Yadikko
sai wannan tsohuwa da Amal wadda ta ke yin nata kamar suma ne kawai su ke d’an gwadawa..dan haka wajen ya kasance shiruuu kowa ya na nasa lissafin…ta inda matan su
ka kasance a zaune yayinda mazan su ke a tsaye.
A hakan su ka yanke shawarar kowa ya yi taimama a jikin bango ko inda sumintin ya farfashe k’asa
mai yawa ta baiyyana a samu a yiyyi sallah…
Hakan kuwa aka yi, har Amal wadda jikinta ya tsananta karkarwa…
su ka yi su na masu jero istighfari da addu’ar su samu su fita su rama sallolin dan su kansu basu gama yarda da sallar ba…Yadikko ta shek’a fitsari a nan inda ta ke ya fi sau biyar dan tun d’azu in ta yi barcinta ta gama fitsarin ne ya ke tada ita
Sanin
babu halin fita ya sanya ta ke fakar ido ta sake shi a wajen kawai…Wanda abunda ba ta sani ba shine rabin mutanen wajen sun fahimceta musamman ma Anne wadda itama ta yi guda d’aya a zaune lokacin da duhu ya wanzu, ga uban zarnin da ya had’e musu da wari….
Kasancewar yanzu duk wani abun maye ya saki Yadikko ya sanya ta na gama wartsakewa garau ta ji wata mahaukaciyar yunwa ta na kwak’ular kayan hanjinta dan haka ta saka kuka marar sauti domin kuwa ta san tabbas wannan yunwar, dafin kunama da warin amai ha
d’e da zarnin fitsari da duhu sai sun yi ajalinta kafin abunda duk a ke tattaunawa ana jin tsoron fitowarsa daga cikin ramin da ya fi komai d’agawa duk wani na cikin d’akin hankali ya fito, dan dukda sun toshe hakan bai hanasu jin wani motsi-motsi a hankal
i ba wanda sautinsa ya na fitowa daga cikin ramin ne…
Wani kalar wahalallen barci ne ya fara fisgar wasu daga cikinsu dan zuwa wannan lokacin dare ya tsala sosai, masu yi a tsaye su na yi a matuk’ar wahale haka suma na zaune yayinda wasu da ga cikinsu bab
u alamun ma barci a idanunsu sam saboda tsabar bak’in ciki