Showing 42001 words to 45000 words out of 111233 words
Yota
*17*
Mata ne kusan su ashirin manya da ƙanana sai wata a tsakiyarsu nan
na
ɗ
e da mayafi ta sunkuyar da kanta ƙasa sosai fuskarta a rufe tsoffi guda biyu sun ruƙota..
Da farko kan Mustapha
ɗ
aurewa ya yi
yayinda a ka tsaya kallon-kallo kowa ya gagara cewa komai, haddai ya magantu ya ce "lafiya dai?"
Ƙ
asa-ƙasa wata a cikin m
atan ta ta
ɓ
o tsohuwar sannan ta ce mata "ko dai ba nan ba ne ba?"
Murmushi matar ta yi kafin ta ce "a haba dai, nan ne mana...ga Nuratu chan."
Sai kuma ta maida akalar maganartata zuwa ga Nuratu sannan ta ce "ƴar albarka ina Matan da aka ce su na jira? Y
a na ga daga ke sai yayanki?"
Shiruuu duk su ka yi ganin hakan ya sanya ta yi murmushi sannan ta ce "to ae shikenan.
Bara mu miƙata cikin
ɗ
akinta."
Ta yi maganar ta na nufar inda ta hanga da wata makekiyar katifa dan
ɗ
ayan wajen da su ke kira da pa
rlour in mutun uku su ka shiga na hu
ɗ
u sai dai ya tsaya a kaikaice gashi tulin kayan gumamar Uwani ke a ciki babu masaka tsinke, kasancewar labulayen duk a
ɗ
age su ke ya sanya su ka samu damar ƙarewa
ɗ
akunan kallo wasu a ciki har su na munafurcin rashin ky
autuwar inda za su ajjiye ƴar uwar tasu, a ransu.
Yayinda jikin Amaryar ya yi sanyi sosai itama dan dukda fuskarta a rufe ne hakan bai hanata k’arewa gidan da d’akin kallo ba…ita babbar damuwarta shine ba ta san ta inda uban kayan gadon da su ka siya za s
u shiga ta cikin k’ofar d’akin nan ba…tabbas garama da capinter ya yi disappointing nasu dan sai dai ta siyar da kayan ko an gama wallahi ba za ta yarda a yi asararsu a d’akin nan ba.
A fusace Mustapha ya shiga gabansu ya tsaya sannan ya ce "wanne
ɗ
aki?
Wa za ku saka a
ɗ
akin wa? Lafiya ku ke kuwa?"
Murmushi matar ta yi sannan ta ce "yanzu kai Yaro in banda kai da abunka ae duk wanda ya gammu ya kalleta" ta yi maganar ta na nuna Amaryar sannan ta
ɗ
aura da cewa "tabbas na san ya san Amarya mu ka kawo...
."
"Amarya ku ka kawo za ku saka a
ɗ
akin wata? Ko kuma a wanchan wajen za ku
ɗ
aurata akan kayan ta zauna?"
Ya jero musu tambayoyin takaici kamar ya kar shi.
Kallon-kallo aka hau yi kafin wata a cikinsu ta ce " Yaro mu ce mana aka yi bai da mata, da
hankalinmu ta ina za mu yarda a saka wata a
ɗ
akin wata?" Yadikko kawai ya sanar mana mata a gidan nan wato matar mai gidan, kuma kamar yadda ya kwatanta mun ga
ɓ
angarenta ga shi chan ita da mijinta da ƴaƴanta.
Wani kalar ta
ɓ
e Baki Mustapha ya yi kalar n
a takaicin nan sannan ya
ɗ
aura da cewa "maganinku kenan! Daga an je muku da maganar aure kun yi caraff kun amshe ba tare da kun yi kwakkwaran bincike ba, sannan da
ɗ
in da
ɗ
awa ko zuwa ba a yi an
ɗ
auko ku ba kun taho da ƙafafunku...yanzu ae ga irinta nan.
Wa
nnan
ɗ
akin,
ɗ
akin Mahaifiyar wannan Yarinyar ce kuma yanzu haka ma ta na kwance ne a gadon asibiti ta na jinya, sai ku gaya mini in kun yi wa kanku adalci muddin ku ka yarda ku ka saka wata a cikin
ɗ
akinnta.."
Ɗ
ayar ce ta hau salati idanunta a kan Nurat
u ta ce "ƴar nan ki ka ce mana Mahaifiyarki ta rasu?"
Girgiza kai ta yi kawai ta kawar da kanta dan ba ta so magana ta yi yawa ta yi kwa
ɓ
a a gaban Ya Mustapha.....
To dai Allah ya so Matan an samu masu hankali da fahimta, dan a take su ka yanke sha
warar juyawa da Amaryar bayan itama Amaryar ta tabbatar musu ba za ta shiga
ɗ
akin wata ba....
Haka nan su ka juya da ita zuciyoyinsu fal mamakin sha'anin Nura da ƴarsa wadda ta kashe Uwarta da ranta.
Shi kuma ya fake da ce musu a sirrince ya ke so a y
i auren ashe abubuwa a ƙaasa dunƙule ya ke
ɓ
oyewa.
Su na fita ta fashe da kuka ta ce "ba na so in yarfa Baba ne a gabansu shiyasa na ce musu haka...."
Cikin damuwa Mustapha ya ce "ko ma dai menene bai kamata ki ce Mamanki ta rasu ba, hakan ba kya
u..."
Kamar ba Nuratu ba haka nan ta sunkuyar da kanta ƙasa kawai ta yi kalar tausayi sosai.
Ya jima ya na kallonta a ransa ya na lissafin yadda za ta kaya shi da Kaka Nura a yau idan ya dawo gidan bai tadda Amarya ba, sai kuma kawai ya jaa numfashi
ya sauƙe ya ce mata "je ki
ɗ
auko kayanki in kaiki wajen Adda ina so zan wuce wajen Mama ta na jira na..."
Ya yi maganar tausayin matar ya na sake shigarsa bai ma san ta ina zai fara yi mata bayani ba wallahi.
A tsakar gida su ka tarar da Yadikko, Za
inab da Mai aikinsu su na gyaran kifi.....
Sun ji gu
ɗ
a kuma sun ga shigowar mata, sarai Yadikko ta fahimci Kaka Nura ne ya yi abun shiyasa ta Umarci Zainab da su matsa daga inda za a iya ganinsu, mai aiki kuma aikata ta tsaya a bakin hanya su na dosowa t
a sanar musu Yadikkon ba ta nan ta nuna musu inda za su saka Amarya direct.
Dan duk wata sabga ta Kaka Nura ƙoƙari kawai Yadikko ta ke yi ta ga ta yakice shi daga kanta.
Ɗ
agowa su ka yi kusan a tare su ka kallesu, a take Yadikko ta ha
ɗ
e rai tamau! Ka
mar ba ta ta
ɓ
a dariya ba sannan ta
ɗ
auke dubanta daga kallon Nuratu ta maida a Mustapha ta na jira ta ji dalilansa na shigo mata da Nuratu har inda ta ke bayan ya san ba ta so.
Miƙewa Zainab ta yi ta wuce ciki dan a ƙa'idar Yadikko ko magana ta hana ta
yi da Nuratun sai dai ta yi a
ɓ
oye...
Ƙ
asa-ƙasa yadda Nuratu ta san Yadikko za ta ji ta ce "shegiya Zainab, ji wani gudu kamar mahaukaciya."
Sarai Yadikkon ta fahimci domin ta kunnata ne Yarinyar ta yi hakan, hatta Baba Yusufa ba ya kiran Zainab da sun
anta saboda Yadikkon ba ta so kasancewar Zainab
ɗ
in sunan Addanta ne wadda ta riƙeta kamar Uwa ta aurar da ita, dan ita mahaifiyarta ta na haifarta ta rasu...
Shiyasa sunan ya ke da matuƙar daraja a gidan sannan ba ta so a ta
ɓ
a Zainab ko da wasa.......
Ta na cikin wannan nazarin ta ji muryar Nuratu da
ɗ
an sautin da kowa zai ji ta ce "ina wuni..."
Shiruuu kawai Yadikko ta yi ta gagara magana mamaki gaba
ɗ
aya ya hargitsa mata lissafi wai yau ita wannan ƴar ƙanƙanuwar ƴar ta ke gwadawa kissa da karuwan
ci....'oh, duniya ina za ki da mu??' ta furta hakan a fili ba tare da ita kanta ta san ta furta ba sannan ta
ɗ
ago ta kalli Mustapha ta ce masa "fitar mini da ƴar nan.."
Kwa
ɓ
e fuska ya yi kamar zai yi kuka sannan ya ce " ko gaisuwarta ba ki amsa ba balla
nta ki ji abunda ya kawota"
A harzuƙe sosai Yadiikko ta miƙe Baki da kumfa ta na cewa"wai har yaushe ka soma ƙetare Umarni na ne? In ce dai na hana ka hatta shiga
ɓ
angaren nasu? Ko kaima ta koya maka raina iyayen ne? Na ce ba na sonta ba na son in ganta
kusa da ni da duk wani jinina amma shine za ka shigo mini da ita salon ta hargitsa mini nawa gidan nima ta kwantar da ni a gadon asibiti ko?
Ka san kuwa me ta yi mini daga shigowarta?"
Bata jira jin ta Bakinsa ba ta juya ta kalli Nuratu sannan ta ce"
to ba ki isa ba, tunda na fahimci wayon manya gareki gara in gaya miki dan na san za ki fahimta! Wallahi ba ki isa ba sarai na san mai ya kawoki nan kuma ba za ki taka way forward zuwa cikin gidana ba ballantana har ki samu ki cimma manufarki, ba bu ke bab
u gidana babu duk wani jinina na saka almakashi na datse....."
Cikin tarar numfashinta Mustapha ya ce " haba mana dan Allah....
Yarinyar nan fa shiryuwa ta yi, in muka nuna mata kyama ta koma ruwa mu na da kamosho fa, sannan ba za ki ta
ɓ
a iya raba jini
nki da ita ba saboda mu jinin naki ƴan uwa muke a gareta dole duk abu
ɗ
aya ne ya yo mu....
Kamata ya yi ace kin taimaka wajen gyaruwar Nuratu tunda dai duk tsiya ta mu ce ita ba a chanjawa tuwo suna kuma hannunka ba ya ru
ɓ
ewa ka yanke ka yar ba
"
Ci
kin
ɓ
acin rai sosai kamar za ta mareshi Yadikko ta ce
"ba ni da ha
ɗ
i da ƴar nan, kuma shima uban naka tsaf hannu ya kan ru
ɓ
e a yanke a ƴar in aka ga ya na shirin tarwatsa garkuwar jiki.."
Sannan ta runtse idunta ƙam! Ta nuna Nuratu kamar mai shirin tada
aljanu ta ce "Mustapha ka fitar mini da ƴar nan daga cikin gidana na ce ko?"
Da sauri mai aikin ta shiga tsakani ta ce "Mustapha yaushe ka zama mai taurin kai ne?
Tunda ba ta so ka fitar da ita mana......"
Cikin ƙoƙarin son ganin sun fahimcesa ya ce
"Gwaggo Yarinyar nan shiryuwa ta ke yi, kwa
ɗ
ayin ladan da za mu samu in mu ka taru mu ka bada gudummawa wajen shiryuwar Yarinya kamar Nuratu na ke yi mana gaba
ɗ
ayanmu.
Kuma ni a ganina ko baya ga haka ma in mu ka koreta kamar mun raba zumunci ne, kuma n
a san duk kun san hakan babu kyau.
Sannan ta ce mini tsoro ta ke ji....."
Bu
ɗ
e idanuwanta Yadikko ta yi ta sake nuna Nuratu sannan ta ce "wannan aljannar shegiyar Yarinyar ce, ta ce maka ta na jin tsoro kai kuma ka yarda? Shegiya ƴar iska Uban me ki k
a yiwa
ɗ
a na ne wai!?"
Ta ƙarashe maganar ta na kallon idanun Nuratu wadda itama ta ke kallonta ƙurr!!Farin ciki fall zuciyarta.
A fusace ta
ɗ
aura da cewa " kalli fa kallon da take min ta na min dariya....ba fa za a ta
ɓ
a samun chanji daga gareta ba dan h
aka ka bar kwa
ɗ
ayin samun ladan abunda babu shi kwata kwata a tsarin rayuwarta dan wallahi wannan ta riga ta tafi ita da ubanta har abada ba za su ta
ɓ
a shiryuwa ba wutar jahannama ce kawai za ta shirya su, shegiya tsinanniya, kissa ce ta ke maka babu wani
shiryuwa da ta yi..."
Cikinn
ɗ
aga murya Mustapha wanda ya gama ƙarewa Nuratu kallo dan ya na so ya ga dariyar da Yadikko ta ce ta na mata amma bai gani ba ya ce "ya isa haka dan Allah, ki na ta tsine mata ba gaira ba dalili sannan fisabilillahi Ina wann
an ƴar ƙanƙanuwar Yarinyar ina wata kissa?? Ba na jin ma ta san me ake nufi da hakan..."
Ya lura in aka biyewa Yadikko sai ta raba zumunci sannan ta kai Babansu wuta, dan gashi ƙiri-ƙiri ko sunan Uwani yanzu Baba Yusufa ba ya ƙaunar ya ji an kira, wadd
a a baya ta kasance wadda ya ke tsananin so da tattali, kuma gashi ana so a ha
ɗ
u a taimaka a gyara Nuratu (da ita ce sila) wadda Alhamdulillah a yanzu ta
ɗ
auko hanya amma ta na so ta sake turata ga halaka. Ya san a yadda Nuratu ta ke in aka kyamace ta tsaf
f za ta koma ruwa....
Dan haka cikin son fahimtar da ita da
ɓ
acin rai sosai kwance a kan fuskarsa ya kalleta, dan tunda ya daka mata tsawa ta ƙame ba ta sake iya cewa komai ba hakan ya bashi damar
ɗ
aurawa daga inda ya ke so
"Ballantana har ta gwada mana,
shiryuwa ce ta yi amma gashi ki na so ki sa mu kyamace ta a maida hannun agogo baya.
Kin san cewa in da ace Nuratu ba ta shiryu ta nutsu ba da ba ki isa ki dinga zaginta haka ta kyale ki ba..."
Sai kuma ya yi shiruuu dan shima sai da ya furta sai kuma y
a ji maganar ta yi masa nauyi sosai.
Sai da Yadikko ta sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta kalli mai Aikinta wadda itama jikinta ya yi sanyi matuƙa ta ce "kin gani ko? Kinga somu-somun abunda barin wannan annobar a cikin gidana ka iya janyowa
ko? Wai yau ni Mustapha
ɗ
an da ko musu ba ya iya yi mini ya ke kallon cikin idanuna ya na daka mini tsawa har ya ke ce mini ban isa b...."
Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanya ta gagara sake cewa komai dan haka ta toshe Bakinta sannan ta juya da sauri ta
yi hanyar da za ta kaita parlourn gidan.....
Shiruuu Mustapha ya yi dan a take a lokacin jikinsa ya sake yin sanyi sosai, shiyasa ko da mai aikin nasu ta bashi shawarar ya maida Nuratu ya mayar da ita ba wai dan ya yarda an fishi gaskiya ba sai dan ya
ga ran Yadikkon ya
ɓ
aci sosai.
Da ya je bai koma da wuri ba dan wajen Uwani ma ya tafi, sai da ya tabbatar Yadikko ta
ɗ
an sauƙo tukunna ya je ya bata Haƙuri.....
Bayan sallar isha Mai Unguwa ya biyo limami su ka shigo cikin gidan su ka samu Baba Yusu
fa da Yadikko su ka yi musu nasiha akan yadda su ka banzatar da Uwani wadsa ta ke jinya, dan sun zuba ido sun ga ba su je ba Mustapha ne kawai ta ce ya ke zuwa dan haka su ka basu shawara kasancewar a ganinsu an zama
ɗ
aya.
Su na zaune a yadda su ke ko g
ama tashi daga wajen ba su yi ba su ka fara jiyo ashar
ɗ
in Kaka Nura kafin ya baiyyana a gabansu hannunsa riƙe da bulalar darbejiya da ya tsinko daga jikin bishiya ya na cewa "yau sai na illata Yaron nan wallahi." Bayan idanunsa sun sauƙa a kan Mustapha.
A ƙalla Mustapha ya kai shekaru goma sha takwas a wannan lokacin amma haka Kaka Nura ya shiga zuba masa darbejiya
duk wae a kan ya yi masa raashin kunya ta inda ya fatattaki Amaryarsa da ƴan kawota.....
Mustapha bai ko motsa ba sai wanda su ka zo s
hi da liman da mai ungwa ne da takaicin abin ya ishesa ya zo ya hanka
ɗ
e Kaka Nura ya tafi ya fa
ɗ
a akan Nuratu (wadda au ka shigo tare) ita kuma ta fa
ɗ
i akan glass cup
ɗ
in da aka kawowa baƙi ruwa ta fashe hanunta sosai ta ji ciwo.
To dai kusan za a ce
an kwasheta babu da
ɗ
i dan sai da Kaka Nura ya fasa duk wani abu mai kama da kwalba ko glass a parlourn TV, show glass da kayan turaren wutar ciki, da centre table da duk wani abu dai da za a iya fasawa saboda an ta
ɓ
a hannun ƴarsa ta yanke by mistake, gash
i da shegen ƙarfi duk yawansu su ka kasa riƙesa in aka takura shi kuma ya fara yunƙurin yankar mutum da glass
ɗ
in...
Ko da su mai Unguwa su ka yi magana zagesu ya yi tas dan dama haushinsu ya ke ji tunda aka yanke musu ku
ɗ
in haya ya ce duk munafukai ne sa
boda
Baba Yusufa ya na
ɗ
an yi musu ihsani shiyasa duk in aka yi fa
ɗ
a su ke bin bayansa shi kuma ake bashi rashin gaskiya.
Rikici sosai aka yi dan har sai da wasu daga cikin makwafta su ka shigo ana ta so a raba fa
ɗ
an amma abu ya-ƙi-ci-ya-ƙi- cinyewa d
an Baba Yusufa shima kafewa ya yi akan sai Kaka Nura ya bar masa gida abun nasa ya ishesa haka yayinda Kaka Nura ya ce bai isa ba ae Uwani ta riga ta biya ku
ɗ
i dan haka bai isa ya tashesu ba.
Da mugun kyar mutanen wajen su ka shawo kan Baba Yusufa ganin
ana shirin tado wani ballin saboda su so suke yi su gyara zumucin Uwani da Yusufa da ya ke shirin tarwatsewa dan haka su ka lalla
ɓ
ashi akan ya yi haƙuri ya jira zuwa ƙarshen shekarar sai su tashi
ɗ
in, yanzu ya bari komai ya daidaitu kuma duk wata
ɓ
arna ma
da aka yi musu za su ha
ɗ
a ƙarfi da ƙarfe a gyara, a bar Kaka Nura da halinsa kawai.
Da to Baba Yusufa ya bisu saboda ya na ganin darajar mutanen matuƙa, batun Amarya ne dai ya ce gaskiya ba zai yiu Uwani ta biya ku
ɗ
in
ɗ
aki kuma a saka wata Mace a
ɗ
akinba
.
Still hakan bai sanya zuciyar Kaka Nura ta yi sanyi ba ya ƙara
ɗ
aukar glass