Showing 6001 words to 9000 words out of 111233 words

Chapter 3 - Bakar-Tukunya-Compelete

ke gashi har karkarwa jikin nasa ya ke yi ya sanya Annen ta yi nasarar fincikosa ta dawo da shi baya.

Cikin b’acin rai ta ce “

Sannu solob’iyo! To wallahi ba ka isa ba dan ni jarumi na haifa…maza sake ta a yanzu a ta ke! Dan ba ta da wani amfani a cikin gidan nan! Ka saketa Allah zai kawo maka wata…

Ba ta isa ta rafka rashin kunya kuma ta ci gaba da zama da aurenka rangad’ad’au a

ka ba wallahi, k’aryanta….”

ta yi maganar ta na kallon Sajida ta na huci, wadda itama Sajidar ita ta ke bi da wani matsiyacin kallo

Ita Anne lokacin da ta ke nacin auren a tunaninta ma za a bawa Sajidar gida ne ta yadda za ta tare ita da y’ay’anta sai

gashi ashe uban Yarinyar ya fi su wayo…

‘Gara ta tafi kawai duk wata kissa da asiri an yi amma ta ki moruwa…’

Annen ta aiyyana hakan a cikin ranta, Allah Allah kawai ta ke yi a sallami Sajidar ta san na yi da Ya Amir dan shekaru tafiya su ke yi ba ta da

lokaci…

Cikin sanyin murya Baba wanda ya gaji da b’acin ran Anne kwarai ya kalleta sannan ya ce “amma dae kin san ba ki da hurumin sakawa a yi sakin nan ko? Infact auren ma kansa ba ki da hurumin shiga amma ki ka shiga ki ka yi kane-kane ki ka tilasata

komai sannan yanzu kuma ki zo da wannan zancen? To bari ki ji ba ki isa ba…!”

Ya k’arashe da d’an zafi…

Tab’e Baki ta yi sannan ta ce “Ina son in ji kana cewa ban Isa ba d’innan saboda ni kuma a lokacin ne nake nuna maka tabbas na isa!”

Cikin juya aka

lar maganar tata ga Ya Amir ta ce “auren dole na yi maka?”

Kamar ruwa ya cinyesa a wajen haka ya yi, dan a sanda aka yi auren ba ya son Sajida amma yanzu kam sonta ya ke yi kamar hauka…

“Ina fa! Ae ke da shi kun san me ku ka yi har na yarda na auresa…”

Sajida ta fad’a cikin karb’e zancen sannan ta kalli Ya Amir yau kam ko arzik’in yayan bai samu ba ta ce masa “Amir ba ni takardata nima na gaji….”

Ta yi maganar cikin mik’o masa hannu…

A hankali murya ta na karkarwa ya ce “Sajida ki jira za mu yi magana

a ciki, ko?”

Ya k’arashe maganar a hankali…

Yana mai satar kallon Anne wadda tunda Sajida ta yi

mata shagub’e yanzun ta kid’ima sannan ranta ya k’arasa b’aci…

Sam! Har yau har gobe Ya Amir d’in shi kam ya kasa gane mentality d’in Anne na son kud’i, ta

lauchi fa ba abun kyama bane ba..da wani mai kud’in ma gara talaka fa, ya fi shi kwanciyar hankali…

Har ga Allah he love his life a yadda ta ke, amma k’iri-k’iri Anne ta rabasa da matar da ya ke so ta manna masa Sajida k’arfi da yaji saboda lame dalilinta

na kwad’ayi da buri wanda shi kam ya gagara sakashi a mizanin dalilai masu ma’ana…

Ya na wannan lissafin ya ji Sajidar ta haiyyayyak’o za ta yi magana Anne ta rigata ta hanyar cewa “wai dan uwar ubanka ba za ka sake ta ba? Y’ar gwal ce?

Sake ta a take

a yanzu ko in tsine maka albarka wallahi…ka ji dae na rantse…”

Shiruu Baba ya yi ya runtse idanuwansa

kafin kawai su wuce ciki shi da Adda d’auke da Yadikko…

Suna jiyo ta tanata ife-ife ta na zagin karankatakaf danginsu ta na ik’irarin tsinuwa a Ya A

mir d’in itama Sajida ba ta yi shiru ba sun saka shi a tsakiya….

Adda ta so fita amma Baba ya hanata saboda a halin yanzu ana tab’a Anne za ta huce haushinta a kansu ko ta fad’i abunda hankalima ba zai iya d’auka ba, shiyasa ya hanata fita yana mai jin za

fin abunda ake yiwa d’an nasa fiye da shi Ya Amir d’in..

Tun lokacin da aka kinkimi Yadikko ta farfad’o, saboda dama ba suma ta yi ba mayen abubuwan da ta narkawa kanta ne basu gama sakinta ba shiyasanya ta yi likimo ta gagara motsawa

Dan haka suna kw

antar da ita ta samu ta bud’e idanunta bakinta d’auke da salati…

Da yake d’akin akwai d’an duhu ya sanya ba su lura da Kaka Nura a farkon shigowarsu ba sai da suka zo kwantar da ita a kan gado tukunna suka lura da shi wanda hakan ya d’an basu tsoro dan

daga shi sai boxer sannan yanata lullub’awa side drawer wani uban jibgegen bargo…..kana ganinsa ka san ba a dai dai yake ba sannan yana cikin tashin hankali.

K’uraa masa ido su ka yi sosai bayan sun tabbata Yadikko ta farka sai dai ba su yi wani motsin ba

da zai sanya ta fahimci wani abun duk su ukun dan kowa akwai abunda ya ke rayawa a kansa, kawai sun kura masa idone shi da bargon da yake ta faman kaffa-kaffa da shi….

A take gaban Adda ya yanke ya fad’i sai kuma ta nufesu! Tana zuwa ta yaye bargon gaba

d’aya!

Da sauri ta ja baya ta saka hannu ta toshe bakinta ta fashe da wani kalar kuka tana mai runtse idanuwanta da masifar k’arfi sakamokon Talatu mai k’osai da ta baiyyana a idanunsu bayan ta yaye bargon zigidir da ita!

Ko ta Ina ya iya shigowa da ita

sai Allah!

Kaico Allah wadaran naka ya lalace…

Adda ta aiyyana hakan a cikin ranta wani masifaffen Abu mai d’aci da zafi yana tokare mata k’irji.

BULAMA





0806 402 1951

0903 441 3252

[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TU

KUNYA…*



HUMAIRAH BULAMA

Yota

*03*

Cikin wata zazzafar zuciya Baba wanda bai tab’a sanin yana da kalarta ba ya yi wata super ya damk’i wuyan Kaka Nura tun k’arfinsa…so ya ke kawai ya kashe tsohon saboda dama yana

ta tunanin yadda zai Mutu ya barsa da Mahaifiyarsa da wannan halin nasa! Adda mace ce ita ma rauni ne da ita ba zai bar mata

case d’in Kaka Nura a hannunta ba ya san ba iyawa za ta yi ba.

A rikice Adda ta k’arasa wajen ta fara k’ok’arin b’amb’are han

nun Baba yayinda Talatu ta ke ta k’ok’arin ganin ta mayar da suturarta jikinta…

Babu damar yin ihu dan duk wanda su ka yi ihu ko magana da k’arfi ya ji to sai ya shigo

Ita kuwa Adda ko hauka ta ke ba ta bari a shigo a ga wannan gagarumin abun kunyar b

a shiyasa k’asa-k’asa ta ke cewa Baba “Za fa ka kashe sa, ka taimaka ka cika shi dan Allah.

Cika shi kar ka yi b’arna.”

Ba tare da ta bari hatta Yadikko wadda su ke a d’akin tare da ita ta na ta faman cewa “kuna Ina ne?”

ta jiyo su ba.

Kaka Nura shim

a wanda duk idanunsa su ka firfito waje yau kam babu fad’a da duk wannan bala’i da haukar tasa

Dan tashi d’aya ya fahinci Baban yau ransa ya ke nema bagatatan dan haka da mugun kyar ya ce

“Ka yi mini rai dan Allah”

Wani irin kuka ne ya kufcewa Baba ci

kin kukan ya shiga cewa “in na cika ka direct ka fice

Ka saka jallabiya ka fice

kar in sake ganinka dan wallahi in na ganka idona idonka sai na kasheka!

Ka dai san mutuwa zan yi ko? Dan haka ba na jin tsoro a kamani da laifin kisa ko kad’an, gara in ka

sheka in Mutu hankalina a kwance akan in Mutu Ina tunanin halin da zan tafi in bar Mahaifiyata a ciki dan haka in har ka bari mu ka had’u sai na kasheka”

Ya fad’i hakan cikin d’acin zuciya wanda har k’asan ransa da gaske ya ke, ya tafi kawai in ya ga dama

ya shiga duniya..kuma ko Yadikko ta tambaya Ina Kaka Nuran zai ce mata kawai shima ba su san inda ya ke ba. Sai dai in ya mutu ya dawo gidan wallahi.

Yana wannan lissafin ya na kuka wiwi sai dai a hankali sosai

Takaici goma da ashirin duk sun had’e mas

a…..

Tabbas zai fita yanzu

amma fa domin ya tsira ne kuma sai ya tabbata ya saka Baba kuka da tashin hankali kafin ya bar duniyar da yake ta faman ik’irari, in sha Allahu…

Saboda wannan cin mutunci da rainin da ya yi masa!

Wai yau har shi ake trea

tning ake cewa za a kashe! Tab ashe kuwa an ja ruwa..

Kawai dan ya san Baban zai iya aikata abunda ya ce ne shiyasa ya zab’i ya llallab’ashi ya barsa kafin ya sake waigowa kansa……

Kaka Nura ya aiyyana hakan a cikin ransa.

Sai da Baba ya ji Kaka Nura y

a ce masa “Wallahi zan tafi…ka na cika ni zan tafi”

Tukunna ya cika shi ya na wani irin kuka!

Har ga Allah ya san babu kyau dai amma ya yi farin ciki matuk’a da abunda ya same shi!

Tunda ya auri Anne wallahi wallahi haihuwar da ake yi masa ce kawai ta

ke sanya shi farin ciki amma kullum cikin bak’in ciki da tashin hankali ya ke!

Bai tab’a samun kwanciyar hankali da farin ciki daga gareta ba yanzu gashi ta d’aid’aita musu rayuwa daga shi har y’ayansa. Ji ya ke dama kamar ya gudu wallahi..bak’in cikinsa

d’aya bai san wanne hali y’ay’an nasa za su shiga ba in ba ya nan amma tabbas gara ya tafin dan bak’in

cikin ‘ga shi a raye tare da su amma ya gagara gyara rayuwarsu’ dama ya dad’e ya na nuk’urk’usar zuciya da walwalarsa…

Komai babu dad’i komai ya d’au z

afi ta koina babu sauk’i sannan the worst part is that babu abunda ya Isa ya yi domin ya kawo sauk’i ko ya gyara hakan ko ya dakatar da abubuwa daga k’arasa tab’arb’arewa.

‘He is just so very useless’

Ya aiyyana hakan a ransa yana mai zama a k’asa dab’as

s sannan ya sake sakin wani sabon kukan mai cin rai da k’una marar sauti….

Dan bala’i Ashe Kaka Nura shi da daduronsa ta window su ka shigo, dan haka su ka fice ta windown su ka mayar da burglar d’in wadda ashe ya dad’e da b’intiketa a jogane kawai ta

ke sabida shigowa da mata…’tsabar idanunsa sun rufe shi kam bai ma damu b’arawo ya shigo musu ba…dan windown d’akin ya fita ta wani dogon lungu a unguwar ne wanda ba a ma binsa sosai saboda tsayi da duhunsa in dare ya yi…..

Tsoho da shi amma har yau bai

bar bin mata na masifa ba!

Dukda cewa itama Yadikkon she’s not perfect amma tabbas ba ta chanchanci Miji kalar Kaka Nura ba sam! Halaiyyarsa sak irinta y’arsa

babu wani Abu mai kyau a tattare da su…’

Adda ta na wannan lissafin ta k’arasa kusa da d’an uw

anta ta zauna kawai sannan ta saka hannu ta kamo na Yadikko wadda ta ke ta faman kiran sunayensu tun d’azu….

A chan waje kuwa..

Sai da Anne ta zabgawa Ya Amir kyawawan maruka guda biyu tukunna da kyar muryarsa ta na karkarwa ya furta kalmar saki d’ay

a ga Sajidar…

Sai a sannan tukunna Baba ya mik’e ya fito ko kallonsu bai yi ba ya bi bayan Ya Amir wanda ya fita da sauri, Adda kuwa a D’aki ta zauna ta na mai ci gaba da sauraren Anne ta na cewa Sajida “Alhamdulillah mun rabu da marar wadatacciyar zuciya

, mai matsiyaciyar zuciya! Allah ya yaye mana alak’ak’ai…”

Cikin d’aga murya Sajida ta ce “Ae tsiya a gindinku ta k’are wallahi…matsiyatan banza masu jinin zina..Allah na tuba zani nawa na baki? Kuncen kayan Mahaifiyata nawa aka baki?

Ba ki da shi da da

lilin samu, amma kin bi kin kwallafa rai akan y’ay’an da ki ka Haifa za su zamo silar samunki, kina jira su kula da dukkan buk’atunki na kud’i! Za ki sha mamaki wallahi wannan mutuwar zuciyar taki ita za ta janyo ki wahala ki k’are a cikin talauchi..

Ni

Allah ya sa ma ba ki yi mana asiri a jikin kayayyakin da muka baki ba, Muguwa matsafiya kawai...A haka ne wae har ki ke da bakin cewa ba ni da amfani! Ae kuwa kafin in tafi sai kin fito mini da duk wani abun da na tab’a baki…”

Jikin Anne ya d’an yi sanyi

a wannan gab’ar amma sai ta ce “Tsummokara ae ba wata tsiya bace! Kin bi kin ishi mutane ke y’ar masu kud’i shin Ina arzik’in ya ke? Ina gatan naki yake? Ae tunda ubanki ya bari aka kawoki nan wallahi an gama da ke..

Ba ki da wani gata y’ar nan….”

Tafi

Sajida ta yi tae shewa sannan ta ce “Auhoo da so kika yi wato a bani gida? A yi muku ciki sannan a yi muku goyo…to bari ki ji Mahaifina ba dak’ik’i bane ba kamar ki…dabba mahaukaciya kamar ki ba ta isa ta damfareshi ta yi masa wayo ba wallahi k’aryanki!

Ni kaina ae da ke da Amir d’in kun san hanyar da ku ka bi na saurareshi, har na yarda na so shi na aureshi in ba haka ba wallahi ko a mai gadi ba zan d’aukeki ko shi ba

kuma gata an yi mini shi tunda har mutum kamar Mahaifina ya bi abunda nake so ya yarda

ya kawo ni nan ae kuwa kema kin san Ina da gata wallahi ana son farin cikina…

Kawai dae wayo ne jahila irinki ba ta isa ta yi mana ba….”

Kasa ci gaba da danne zuciyarta Anne ta yi a take ta zabgawa Sajida Mari….

Wanda hakan ya kusan d’auke numfashi Add

a wadda ta fito da niyyar yin rabiya.

Ficewa Matan da su ke d’aukar rahota su ka yi, dan kar ta shafesu yayinda Adda

ta k’araso inda su ke da sauri cikin karkarwar jiki ta na cewa

“Anne kanki k’alau kuwa? Me ki

ka aikata….”

Sai a lokacin Sajida wad

da ta dafe kuncinta ta motsa..

Ta juya ta afka d’akinta jim kad’an ta fito rik’e da wayarta da mayafinta a hannunta da makullin motarta…

Ta na fita ta d’auki mota a gidan makwaftansu inda ta ke fakin ta bar unguwar zuciya na cinta….

Ko gama hawa Titi b

a ta yi ba ta kira Abbanta wanda ya kasance baban mutum sosai a Nigeria, mai fad’a a ji..har khaki garesa sannan ana shakkarsa..ta na kuka ta ce masa ‘Anne da Ya Amir sun yi mata duka har sun kumbura mata fuska’

Dan da gaske fuskanta ya kumbura ta wajen k

umatunta ya yi wani kalar jaa da alamun bruises kacha-kacha da shatin yatsu guda hud’u rass! Sun baiyyana duk a ta sanadiyyar marin da Annen ta yi mata na hauka…sakamokon ita Sajidar tunda ta ke a rayuwarta ko mintsini na gaske ba a tab’a yi mata mai zafi

ba sai dai a wasa ko tsokana.

Tunda ta fita su ka yi shiruu hatta Anne ta gagara motsi kwata-kwata…

Yadikko kuwa tunda Adda ta fita ta ja pillow

ta kwanta ta soma barcinta, dan yadda ta ji Sajida ta yasar da ita d’azun ta tsorata kwarai..shiyasa tun

da ta ji an sake ta ta b’uya a d’aki gudun kar a huce a kanta. Dan in Sajidar ta rarumo wani abun kafin ta nemi hanya ta gudu an sauk’e mata.

Bayan kamar mintuna goma da fitar Sajida, Baba ya shigo ya kallesu ya ce “wani abun ya faru bayan wanda na sa

ni?”

Dan su kansu mazan da su ke waje sun ga yanayin yadda Sajidar ta bar unguwar rai a b’ace ga fuska ta kumbura ta yi jaa, tabbas sun san ba lafiya ba…shiyasa yana dawowa daga kai Ya Amir gidan Abokinsa su ka ce ya shiga gida fa ya duba dan kamar ba k’a

lau ba…

BULAMA





0806 402 1951

0903 441 3252

[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*



HUMAIRAH BULAMA

Yota

*04*

Da kyar Adda ta iya ce masa “Anne ce ta mareta…”

Shiruuu ya

yi kawai ya na kallon Anne kafin chaan ya ce mata “ku zo mu bar unguwar na d’an lokaci, yi wa Yadikko magana ta fito yanzu-yanzu….”

Ya yi maganar jikinsa har ya na karkarwa saboda Abban Sajida ba shi da sauk’i! Ya ji ya shaida hakan, masifar tsoronsa ake

ji gashi fad’ansa ba ya mutuwa.

Kwata-kwata da fitar Sajida da zuwan anti daba har da Sojiji bai kai mintuna goma sha a tsakani ba.

Motocin suna dira,

tun daga wajen zaman makoki suka fara nad’e jama’a, duk

wanda ya yi yunk‘urin guduwa kuwa tak

e sa su ke yi ko su buga masa bindiga a ka…

Dan Sajida ta na kuka ta sanarwa Abbanta Anne da d’anta sun taru sun yi mata duka har sun farfasa mata jiki sannan an yi mata saki d’aya…’

Shiyasa shi kuma ya fusata, a ganinsa saki kam

ba komai bane ba dama

abunda ya ke fata kenan amma duka kam

tabbas wannan sai sun yi dana sanin had’a zuri’a da shi wallahi…

Shiyasa ya yi kiran waya ya ce ‘a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login