Showing 33001 words to 36000 words out of 111233 words

Chapter 12 - Bakar-Tukunya-Compelete

08 Sep 2026

26

har ya rasu da laifin yake ganin yayan Uwani dan gani yake yi kamar shi ne ya aikata. Uwani da yayanta da Mahaifiyar Uwani sai shi Kaka Nuran ne kawai suka san asalin gaskiya…….

Fusatar da Mallan ya yi ne

ya sanyashi ya cewa yayan Uwani ya fito da mata ya yi masa aure aka cire sa daga makaranta babu kalar kuka da roƙon da bawan Allahn nan bai yi ba amma haka yana ji ya na gani aka ciresa daga makaranta aka aura masa wata Yarinya ƴar makwabton su a lokacin s

hekarun sa goma sha shidda a duniya, to dai ya samu bayan auren ya ci gaba da karatunsa dan har aiki ya yi kafin Allah ya kar

ɓ

i ransa...amma fa har Alhaji Ali(yayan uwani) ya bar duniya kwata-kwata baya son kuma ba sa shiri da Kaka Nura kamar Annabi da kaf

iri haka su ke…..

Nura ya na kammala secondary school shima akace ya fito da mata a yi masa aure, dan zuwa wannan lokacin Mahaifiyar Uwani cewa ta yi 'Wallahi sai dai Mallan ya za

ɓ

a ita ko Muhammadu Nura.'

Wallahi abun kamar tsafi dan tashi

ɗ

aya Mal

lan ya ce ‘ya ba shi Uwani’ wanda hakan ya girgiza Mahaifiyar Uwani sanadiyyar samun hawan jininta kenan har ta rasu ta na fama da shi...saboda ana sanar da ita zancen ta yanke jiki ta fa

ɗ

i sai a asibiti ta farfa

ɗ

o.

Ta san halin Mallan ba ya magana biyu a

mma haka nan ta dage ta dinga gwada sa’arta har ƙaninsa sai da ta sako a cikin zancen amma furr!! Mallan ya ce ya gama magana ƙarshe ma da ta

ɗ

aga masa hankali matso da ranar auren ya yi ya zaftare wajen watanni biyu a ciki wanda hakan ya sanya ta ja baki

nta ta yi shiru ta zubawa sarautar Allah idanu..

Har da tsoron kar a bawa Nura ƴartata ne dama ya sanya ta azalzala ta

ɗ

agawa Mallan hankali a kan ya yiwa Nuran aure saboda tun lokacin da ta lura da irin kallon da ya ke yiwa ƴartata hankalinta ya yi mas

ifar tashi kuma ta lura har Abu ya ke siyowa ya bata abunda ba

ɗ

abi’arsa bace ba shiyasa tun kafin ya furta ta so ta yiwa tufkar hanci sai dai abunda ba ta sani ba Nura ya fi ta sammako dan Allah ka

ɗ

ai ya san kalar shige da fice da makirce-makircen da ya y

iyyi aka basa Uwani, dan indai makirci ne da juya kwakwalwar

ɗ

an Adam to tabbas ya ci a bawa Kaka Nura tutar yabo.

Mallan bai kai ga

ɗ

aura musu auren da ya ci buri ba Allah ya kar

ɓ

i ransa, gajeruwar jinya ta kwana biyu kacal ya yi yace ga garinku, tsaba

r bala’i irin na Kaka Nura ana kai Mallan makwancinsa ya nemi limamai da dattawan layi da su

ɗ

aura masa aure da Uwani a cewarsa kar Mahaifiyar Uwanin ta dawo dai-dai ta raba abunda Mallan ya so ƙullawa, sun gasgata zancen

nasa dan ƙiyayyar Mahaifiyar Uw

ani ga Kaka Nura a fili take ga kowa! Makwabta da ƴan uwa, yayinda shi kuma manya-manyan mugayen halaiyyarsa su ke a

ɓ

oye, sun shaida kuma sun san Mallan ya bawa Nura Uwani shiyasa suka goya masa baya a ranar sadakar farkon rasuwar Mallan aka

ɗ

aura auren N

ura da Uwani a cewarsu sun cikawa Mallan burinsa.

Ga zafin baƙin ciki ga zafin rasuwa, su suka taru suka sanya Mahaifiyar Uwani ta kasa ta

ɓ

uka komai ta kwanta ciwo ya yi mata ruff ko iya gane waye a kanta ba ta yi dama tunda aka yi rasuwar ta ke kwance,

amma a hakan Nura ya

ɗ

agawa kowa hankali ranar sadakar uku Uwani ta tare a gidansa wanda ke a Unguwa Uku mai

ɗ

akuna biyu a jere da ban

ɗ

aki da kitchen wanda ya tara ku

ɗ

i ya siya da ku

ɗ

in Allah ya Isa da ku

ɗ

in haram da na sata….….

Rigima sosai aka yi da

shi aka yi baram-baram tsakanin sa da ƴan uwan Uwani kowa ya fita a harkarsa sai dai kuma tausayin ƙanwarsu bai sa sun janye ba hakanan Yusufa da Ali su ke

ɗ

an leƙata from time to time dan idan akwai wanda ba ta so a kaff fa

ɗ

in duniyar nan a wannan lokacin

har da yanzu ma to Nura ne…..

Bayan aurensa da Uwani ya nuna mata soyayya kwarai dan har ya kai ga sanyawa ta

ɗ

an fara shaƙuwa da shi abunka da zuciyar mace yau da gobe sai Allah miji da mata sai dai kallo wanda kwanciyar hankalin da Mahaifiyar Uwanin

ta gani a tattare da ƴartata ne ya sanya ta

ɗ

an kwantar da hankalinta dukda har gobe tun ranar da Kaka Nura ya tattara kayanshi ya tare a Unguwa Uku da Uwani bai ta

ɓ

a zuwa ya gaishe ta ba amma ta zuba musu ido kuma sam ba ta ƙorafi kullum addu’ar ta Allah

ya bawa ƴarta farin ciki da ribar rayuwa, ko a waya bayan waya ta fito har matar ta rasu ba ya kiranta baya kulata kwata-kwata a cewarsa ita

ɗ

in maƙiyiyarsa ce, ita ma kuma ba ta zuwa gidansa sai dai in ta je gidan Baba Yusufa Uwani ta je har chan tukunna

su ha

ɗ

u su ga juna, dan ba ya hana Uwani zuwa chan

ɗ

in ta gaisheta amma shi kam ba ya zuwa, ko gidanta ko gidan Baba Yusufa.

Ƴ

ar soyayyar da ya nuna mata ta iyaka watanni uku ce kacal bayan aurensu da kuma shaƙuwar da suka yi ne ya sanya ta fi shan wah

ala a lokacin da ya juya mata baya, dan tun da ta rufe watanni ukun nan a gidansa shikenan uƙubarsa da cin mutunci kala-kala su ka ce salama alaikom..

Shekara

ɗ

aya kacal aka

ɗ

auka da yin auren su ya fara mitar shi fa ya ji shiru ko dai juya ce…a cikin

shekara

ɗ

ayan nan wanda sai da aka ƙara shekar

ɗ

aya da wata takwas tukunna ta

ɗ

auki cikin Anne sai da Kaka Nura ya auri mata har guda biyu kuma matan ta farkon babbar ƙawarta ce ta unguwar,

ɗ

ayar kuma ƴar makwabta mai tayata kwana idan ba ya nan..kaff ciki

nsu ko alamun ciki babu a tare da su har ya sakesu amma a ko da yaushe cewa ya ke yi rashin haihuwar a jikin Uwani ne dan gashi kaff cikin danginta da suka yiyyi aure sau

ɗ

aya tak aka haifi twins (Mustapha da Abbakar) ƴaƴan babban yayanta (Baba Yusufa) sai

yanzu da matar ta sake

ɗ

aukar ciki.

Cewa ma yake ita ce ta shafawa ragowar matan da yake aurowa rashin haihuwa sannan tsabar baƙin kishinta ne ya sa suka kasa haihuwa da shi.

Kasancewarsa mutum mai matsanancin son ƴaƴa ya sanya ya rufe ido ya dinga kaft

a mata ruwan takaici ba dare ba rana.

Ko da aka haifi Zainab Baba Yusuf ya so ya bawa Uwani ita tun da

ɗ

anye cibinta sabida zaman ka

ɗ

aici da baƙin cikin da take yi, amman furr Kaka Nura ya ƙi yarda dukda masifar son ya ga Yaro a gidansa amma sai cewa

yayi 'shi ya fi son tsattson sa'.. hakanan Uwani ta haƙura ta ci gaba da kar

ɓ

ar uƙuba kala-kala daga garesa gashi a lokacin Mahaifiyarta itama ta rasu dan haka hakanan take na

ɗ

ar baƙin ciki ita ka

ɗ

ai…

Gaba

ɗ

aya sai da ya ja mata raina da ƙananun maganga

nu a wajen makwabta dan hakanan yake bin Yaran layi masu tasowa zawarawa da manyan mata...babu abunda ya shafesa zai kashewa wadda yake tare da ita ku

ɗ

i amma ita Uwani dai-dai da kukar ka

ɗ

a miya daga gidan Baba Yusufa ake aika mata kuma idan ta dafa ya zau

na ya na

ɗ

a hankali kwance ya kuma je waje ya zubar da abunda ya tara a ƙadangarun bariki..

Baba Yusufa ya so ya raba auren amma sai Uwani ta ce ya barshi kawai ta ƙarasa a haka ba don komai ba ita kanta ta san ba ta da wani gata yanzun kam,

ɗ

ayan yayan na

ta soja ne a portharcourt ya ke shi kansa ba zama ya ke yi a gidansa ba, zamanta a gidan Baba Garba kuwa ba zai ta

ɓ

a yiwuwa ba saboda yadda ya tsani mijita itama haka ya ke jin haushinta da kyar ya ke iya amsawa in ta gaishesa tunda ta auri Nura ta yarda t

a zauna a gidansa shikenan ƙiyayyar da ya ke yiwa Nuran ta shafeta...gidan Baba Yusufa kuwa yau da gobe sai Allah dan ba wani shiri take da matarsa ba (Yadikko) kasancewarta mace mai son abun mijinta, shiyasa kawai ta za

ɓ

i ta zauna ta ƙarasa a haka duk tsi

ya ita

ɗ

aya dai ranta a gidan mijinta ta san wuya ba za ta kasheta ba...

Da

ɗ

in da

ɗ

awa kuma Kaka Nuran ya kafeta ne a gidan saboda ko ba komai ya san ya na morarta duba da yadda Baba Garba da Baba Ali (Yayanta na portharcourt) su ke ciyar da shi da ita, ya

san ba duk mace zai samu a yi masa hakan ba.

BULAMA





0806 402 1951

0903 441 3252

[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*



HUMAIRAH BULAMA

Yota

*14*

Shekarar Zainab

ɗ

aya a duniya

lokacin Kaka Nura ya na tsaka da yiwa Uwani gorin haihuwa kwatsam sai ga cikin Anne ta samu da ikon Allah, dan kowa sai da ya yi mamaki saboda a yadda Kaka Nura ya ke shelar ita

ɗ

in juya ce a Unguwa duk an

ɗ

auka ya je asibiti ne an bashi shedar ba za ta h

aihu ba.

Kaka Nura har kukan murna sai da ya yi, ya kwana ya na sallar godiya ga Ubangiji ya yi azumi ashirin na godiya sannan ya

ɗ

auki soyayyar duniya ya

ɗ

aurawa cikin. Tun cikin ya na jinjiri dama yake addu'ar Allah ya sa mace za a haifa masa saboda

shi a cewarsa idan ya haifi Namiji jidali ne dan kafin ya gama rainon sa ya yi karatu ya fara aiki za a

ɗ

auki lokaci kuma aure zai yi dan haka ba lalle ya ci moriyarsa sosai ba amma idan Allah ya bashi ƴa mace ya san jari ce musamman ma idan Yarinyar ta y

o kyawun shi

da tsantsar farin jinin shi ya san tabbas kakarsa ta yanke saƙa, shiyasa ya duƙufa addua Allah ya bashi ƴa mace.

Tabbas Kaka Nura ya na son haihuwa kuma ya na son ƴa mace amma bayan an haifi Anne da ya

ɗ

auketa ya san ita

ɗ

in fa tashi ce a

nan soyayyarta ta nunku a cikin zuciyarsa fiye da tunanin mai karatu, ba yadda ba a yi da shi akan ya bari a saka mata wani sunan ba amma ya ce sunanta ‘Nuratu’, Nuratu Muhammad Nura..dan ko a suna ba ya ƙaunar abunda zai banbamta su.

Dama tun asali K

aka Nura ya kasance mutum mai tsananin son abunsa nan take gaba

ɗ

aya tunda aka haifi Anne komai nashi ya sake fitowa fili kwata-kwata ba shi da kara a duk abunda ya shafe ta, ba kalar cin mutunci da zagin da Uwani ba ta fuskanta a duk lokacin da ya shigo

ya tarar Anne ta na kuka…

Kai tsaye sannan tashi

ɗ

aya za a saka Kaka Nura a cikin jerin talakawa amma tunda aka Haifa masa Anne aka fara cin abinci na gani na fa

ɗ

a a gidansa saboda ruwan Nono, kalar kayan jikin Yarinyar kuwa abun kallo ne, ko kyalle bai

siya ya bawa Uwani ba amma Anne kam sai da ya yi mata akwati uku duk wani abu da aka san Jariri zai buƙata babu wanda Kaka Nura bai siya ya ajjiye ba. Cs aka yiwa Uwani saboda ba zata iya haihuwa ba amma sam Kaka Nura bai damu da magani ko lafiyar ta ba s

hi dai kawai komai ƴarsa.

Gobara ce ta rabo su daga Unguwa Uku, ta inda gidan ya ƙone ƙurmus to the ground su kansu da kyar su ka fita, daga nan su ka bar Unguwa Uku su ka koma Mariri da zama lokacin tun bata kafu ba gidan Baba Yusufa, inda ya ware musu



ɗ

akuna biyu ya zagaye a cikin gidansa suka zauna.

Baba Yusufa shima ba wani mai ku

ɗ

i bane ba, ya na da dai rufin asiri kuma ƴaƴansa biyu ne a gabansa dan Abbakar tun ya na ƙarami ya ke makarantar sojoji (a wajen ƙanin mahaifin nasa) wanda hakan ya kasanc

e burinsa ne, dan haka Zainab da Mustapha ne kawai a gabansa sai matarsa guda

ɗ

aya Yadikko shiyasa ba shi da wani nauyi sosai.....

Gidan nasa irin gida ne mai babban fili dan tun ana yankar fili da daraja a Unguwar ya yanka, su ne farko-farkon Unguwar. Ha

kan ya sa bayan gidansu Anne ya ƙone ƙurmus ya yi ƙoƙari ya gina ciki da parlour da toilet da kitchen a wawware ya zagaye musu, ita Uwani ma ta

ɗ

auka a cikin ku

ɗ

in rabon gadonta wanda ke hannunsa ya yi mata ginin sai da ta tare ya bata ku

ɗ

inta a hannunta

ya ce ta ja jari tukunna ta san tsantsar zumunci da so da tausayinta ne ya sanyashi yin hakan.

Dukda cewa a wannan lokacin ko ku

ɗ

in hayan gidan wanka Kaka Nura bashi da ikon biya amma sai da aka kai ruwa rana da shi ya kakkafa sharu

ɗ

ansa tukunna ya yard

a ya biyota aka tare a gidan da shi ya na ta kumbure-kumbure haka itama matar Baba Yusufa (Yadikko) ba ka

ɗ

an ba ta

ɗ

aga masa hankali ta yi ta bori kafin daga baya komai ya

ɗ

an lafa dan daga ita har Kaka Nura babu wanda ya tanka su….

Tun a kan Zainab da

Anne Kaka Nura ya fara bawa al’umma mamaki da tsoro saboda ƙiri-ƙiri irin abun nan na Yara idan Zainab ta daketa muddin idanunsa suka gani to fa haka nan zai zage ya

ɗ

a

ɗɗ

aka mata duka a cewarsa ai ta girmi Annen saboda ita Anne a lokacin shekararta

ɗ

aya it

a kuma

Zainab ta doshi uku…Abun Yaro sai da ta kai ta kawo Zainab ta daina shigowa shashensu Anne ko Mustapha ya shigo da ita a hannu to fa ta dinga tsala ihu har sai an fitar da ita dan sosai Kaka Nura ya ke makarta ko bige Anne ne idan ta yi ba tare da s

anin ta ba sai ta kar

ɓ

i hukunci gashi kullum ya na gida dan zuwa lokacin ko ƴar kasuwar da ya ke zuwa ya daina a cewarsa shekaru sun ja mutumin da ko talatin bai rufe ba, tunda aka bawa Uwani jarinta idanunsa su ka gani ta fara sayarda gumama shikenan ya

koma ya zauna ya na

ɗ

e hannuwansa ta ke yi musu komai, ƙarƙari idan aljihunsa ya yi ƙasa ya

ɗ

auki asusunta ya fasa ya siyamusu kayan maƙulashe shi da ƴarsa kuma Uwanin ba ta Isa ta yi magana ba idan kuma buƙatar auren sa ta motsa hakanan zai

ɗ

agawa kowa han

kali da roƙo da bashi da ku

ɗ

in Allah ya Isa zai

ha

ɗ

a ya yi…dan zuwa wannan lokacin Alhamdulillah tunda aka Haifa masa Anne ya daina neman mata ammafa aure-aure kamar an ce masa bismillah!

Hakanan zai tara ƴan ku

ɗ

a

ɗ

e da kyar ya kama haya ya yi sabon aure

su tare, tare da shi da Amarya da Anne.

To dai tun bayan haihuwar Anne gaskiya kusan duk itace ta ke kashewa Kaka Nura aure, wanda a da halinsa ne amma fa tunda aka haifeta duk aurarrakinsa ita ce silar mutuwarsu…shi dama Kaka Nura ba ya aikin fari balle

na baƙi kuma tunda Anne ta kai shekaru uku tun a zance ma tare ya ke zuwa da ita dan kullum tana hannunsa maƙal-maƙal.

Da zarar ya yi aure a tare ya ke tarewa a gidan da ita ranar da amaryar ta tare sai an lalla

ɓ

ata ta ci kaza ta ƙoshi ta yi barci an kait

a

ɗ

aki tukunna ake samun lokacin amarya, mai kirsa itace ta ke iya tolerating Anne a gidan na sati

ɗ

aya mara kirsa mara haƙuri kuwa tun a ranar farko ake fara gani a kan fuskarta…..

Ba wai saboda tarairaya ko fifikon da Kaka Nura ya ke nunawa Anne ne si

lar janyo matansa jin haushinta ba, sam abun ba haka ya ke ba…

Ita dai Anne tun ta na Yarinya kwata-kwata ba ta san wani abu wai shi tsoro ba, dan tun ta na jaririya ko irin ƙarar nan ko tsawa kwata-kwata basa firgitata duk wani abu dai da za a ce ya na b

awa jariri ko Yaro tsoro to sam ba sa bawa Anne tsoro, da ta taso kuma ta fara takawa tana da

ɗ

a wayo ko horo film ake kallo a talabijin manya da Yara su na rurrufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login